GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
M. W. A
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
STORY AND WRITING BY
Jameelah jameey ????
(Yar mutan kankia????????)
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI
Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????”’
49&50
Tunda Yarima Bishir ya tafi Hakima batayi motsi ba tana mamakin yanda Bishir yake yi mata gadara har haka, “sai mu gani Bishir ni kuma bani sonka, baka isa ka sani dole ba.”
Haka Hakima ta ce sanann ta wuto warta shashen su ta cigaba da hidimarta hankali kwance dan tasa a ranta ko kasheta za’ayi baza ta iya auren Yarima Bishir ba…
Haka suka gama shagalin bikinsu sanann suka dawo gida..
“Lantana anjima ki shirya zani wankin kai da gyaran jiki dan haka a gaya ma masu shirya fita cikin gari.”
“Angama uwar marayu, Allah ya kaimu anjimar lafiya.”
“Amin sanann kice ma su A’bu kar suyi abincin dare dan yau shashen Fulani zanci abincin dare.”
“To Allah ya taimaki Gimbiya Hakima komai kika ce haka za’ayi zan isar da saƙonki yanzun nan na barki lafiya.”
“Ki turoman da Azima tazo yanzun ba sai anjima ba ina san ganinta.”
“Angama uwargijiyata, na barki lafiya.”
Nan Lantana ta tafi kai saƙon Gimbiya Hakima, ita kuma Gimbiya bayan ta fiyar Lantana kwanciya tayi tana waya da Maryam dan Maryam ta gaya mata gobe ake resuming school…
“Haba Maryam! Am tire wallahi ko, wanann karatun ya fara fita raina sai mutun yana cikin hutu yana jindaɗinshi sai a wani koma school.”
“Gaskiya ne Hakima dole kice haka tunda kina gida kina mulki, kuma mai ya rage tunda mun shiga 300 level saura one year fa.”
“Haka mutane ke cewa saura one year, bakusan wata kalar kura ke cikin one year ɗin ba.”
“Kuma kinsan karatun ba dadi sai dai hakuri kawai Hakima, “wallahi Maryam abun ba dadi sai addu’a nima this week zan dawo insha Allah.”
“Allah ya kaimu lafiya, “Amin ya Allah byeee zana shirya zan tafi gyran kai da jiki.”
“Ehyeeh! Gyaran kai da jiki kamar wata amarya, “wannan al’adata ne Maryam na saba gyaran jiki duk mouth koda ina ƙauyenku.”
“Kindai faɗi dan kiji dadi amman kinsan Zaria tafi ƙarfin a kirata da sunan ƙauye.”
“Naji masu kishi, kowa kanshi ya sani byee.”
Bayan ta gama waya da Maryam Azima ta shigo ta haɗa ma Gimbiya ruwan wanka..
“Ranki yadaɗ’e ga ruwan can yana jiran ki.”
“Ok kisamu kaya mararsa nauyi ki fiddo man, dan naji ana zafi ba laifi.”
“Angama uwargijiyata.”
Nan Gimbiya ta shiga wanka Azima ta fiddo mata kaya, bayan ta fito Gimbiya ta shirya tayi kyau sosai sannan suka tafi gyaran jiki…
“Kilishi nifa Ina lissafi saura shekara uku Hakim ya mutu.”
Hahahhahhaha! “Haba Gimbiya ai nafiki lissafi dan har rubutawa nayi a litaffi, dan na gaji da ganin Hakim yana yawo bisa doran kasa.”
“Na tsani Hakim, ban ƙaunar na bude ido naga Hakim yana numfashi baki yanda nike ji ba Kilishi.”
“To ai hankalinki ya kwanta Gimbiya tunda Turmurturs yace shekara biyar nasan aikinshi ba wasa daga ganinshi.”
“Tabbas ni zan cemaki aikin Turmurturs bana wasa bane, kawai musa ido muga ranar wasa-wasa ta kusa zuwa tunda har munyi shekara biyu da zuwa.”
“Aiko kinga bayan ya mutu da kamar sati sai mu sama ubanshi maganin nan yasha kinga sai muce baƙin cikin matuwar Hakim yasa jininshi ya hau ya bishi tunda yana sonshi.”
“Haka mana kinga ba mai sama mana alamar tambaya, hahahhaha! Wallahi Kilishi inacikin farin ciki na kusa zama uwar’sarki.”
☺️☺️☺️☺️☺️ Niko nace GIMBIYA ZULAHA ko sakara tana ta dariya gaban makasarta bata sani ba, amman ita taba GIMBIYA KILISHI Amana, Allah ka tsaremu daga sharin zuciya????????????..
Wani kallar kallo Gimbiya Kilishi tayi ma Gimbiya Zulaha da taji tace ta kusa zama uwar’sarki ji tayi kamar ta sheƙeta ta huta dan ita duniya ba wanda ta tsana kamar Gimbiya Zulaha itada ɗanta Yarima Hamad..
“Aiko dai munkusa zaman uwar’sarki nan da shekara uku masu zuwa.”
“Daman Kilishi ni kaɗai nasan abunda zanyi ma Fulani Kubrah idan Hamad ya hau milki dan sai na wulakanta ta nasa Hamad yayi ma wanann yan-iskan yaran nata faɗe sanann mu koresu subar garin baki ɗaya nasan bata nisa zata mutu saboda bakin ciki.”
“Kin kyauta ko Gimbiya ni zan wuce kinga dare yayi, “to mu kwana lafiya.”
Bayan Gimbiya Kilishi ta fito shashen Gimbiya Zulaha ba inda ta wuce sai wajen Turmurturs..
Sai da suka gama sheƙe ayarsu sanann ta wuto gida, wanka kawai tayi ta kwanta bacci..
Bayan Hakima sun dawo daga salon ta wuce shashen Fulani taci abincin dare sannan ta dawo ta kwanta…
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya dan yau Gimbiya Hakima take komawa school bayan ta gama shiryawa sukayi sallama dasu Gimbiya Yakumbo sannnan suka wuce school…
Bayan sun isa su Lantana suka gyara gida tas sannan suka haɗama Gimbiya ruwanka…
“Allah ya taimakeki ga ruwan wanka can yana jiranki.”
“Bilkisu Ki haɗoman Tea.”
“Angama uwar marayu, amman asa sugar ko kar’asa.”?
Wani kallar kallo Gimbiya Hakima tayi ma Bilkisu sannan ta wucewarta toilet, dan gani take raini ya fara shiga tsakaninta da Bilkisu…
Bilkisu take jikinta ya fara rawa tana mamakin yanda baki ɗaya Gimbiya Hakima ta chanza daga tambayar asa sugar, “oh ni Bilkisu mai hali dai baya chanza halinshi.”
Abunda Bilkisu tace kenan sannan ta tashi taje ta haɗo ma Gimbiya Hakima Tea amman bata sa sugar ba sai dai ta ɗebo sugar ta shigo dashi baki ɗaya…
Bayan Gimbiya Hakima ta fito wanka Azima ta shafa mata mai ta tayata shiryawa sanann ta kalli Bilkisu tace, “idan kin tashi kijuyo buhun sugar kinji ni ko.”?
“Ina neman sausaucin uwar marayu tuba nike bazan sake kallar wannan laifin ba.”
Uhmmmm! Abunda tace kenan sannan ta anshi Tea ɗin tasa aka zuba mata sugar ta fara sha..
Kash! Itadai Gimbiya Hakima badai Mulki ba yanzun common imaging sugar ma baki sawa da hannunki sai anzuba maki????..
Tana shan Tea su Bilkisu nayi mata tausa ita kuma Azima tana karanta mata novel bayan ta gama shan Tea ta kwanta bacci sannan suma suka wuce suka kwanta..
By Jameelah Jameey✍????
Share
Comment
Vote
Like
Please
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
*M. W. A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
STORY AND WRITING BY
_Jameelah jameey ????_
*(Yar mutan kankia????????)*
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI
Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.
NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????
51&52
Washe gari bayan Gimbiya ta tashi daga bacci shiryawa tayi sannan ta fito yin breakfast..
Tafiya take kamar bata san taka kasa dan yau zata kaima bayin masarautar ziyara sannan ta wuce shashen wazari zata gano shi da jiki dan baiji daɗin jikinshi ba kwana biyu..