GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Allah ya taimaki Gimbiya Hakima takawarki Lafiya yar’sarki jikar sarki gaba dai gaba dai Uwar Marayun kano baki ɗayanta.”

“Lantana maza kije ki kiranta shugaban gidan horo inasan ganinshi yanzun kafin mu tafi ziyarar nan.”

“Angama Uwargijiyata, muna neman sausaucin Uwar Marayu, na barki Lafiya.”

“Bilkisu yi maza ki ɗauko kan wayata wanda nike waya da ita dan naga alamu baku fito da ita ba ko ni kuka bari na ɗauko maku wayar.”?

“Allah ya ja da tsawancin kwana ina neman afuwar Gimbiya Hakima Uwar Marayu wallahi safa’a nayi nasa duka na ɗauko su.”

“Ya isa haka Bilkisu ba abunda zanyi maki tashi kije ki ɗauko karki ɓatamana lokaci da wannna shurutun naki, kudai baki ɗayanku kun cika shurutun masifa wallahi haba.”

Nan Bilkisu ta tashi ta ɗauko waya tana godema Allah da Gimbiya Hakima tace batayi mata komai dan ba ƙaramin tashi hankalinta yayi ba, dan taji ta aika a kira mata shugaban gidan horo baki ɗaya bama sarkin Bulala ba..

“Allah ya taimakeka, Gimbiya Hakima tace tana san ganinka yanzun -yanzun nan inma da hali mu taho tare ƙafata ƙafarka.”

“Lantana Allah yasa ba wani abu kuka yi mata ba.”?

“Ba abunda mukayi kawai dai tana san ganinka , amman ba abunda akayi mata.”

“To shikenan, mu tafi daman bansan naji ance wata baiwa tayi laifi a shashen Gimbiya Hakima dan bansan naga a na hukunta mata dama maza lafiya lau.”

“Aiko dai Allah ya ƙara mana hakurin zama da ita, “Amin ya Allah Lantana.”

Nan suka tare da Lantana su tautaunawa yanda lokaci guda Gimbiya Hakima ta chanza halinta baki ɗaya bayan sun isa Lantana tayi mashi iso wajen Gimbiya Hakima sannan suka shigo tare..

“Allah ya taimakeki Allah ya ƙarama Gimbiya Hakima tsawon rai, gani na ansa kiranki cikin gaugawa ina jiran umirninki.”

“Mudi kana jina.”?

“Eh Uwar Marayu ina sauraranki.”

“Duk wanda yake cikin gidan horo a sallameshi ya koma bakin aikinshi, na yafema kowa koda bani yayi ma laifi ba balle nasan duk wanda yake cikin gidan nace sillar Shigarshi ciki.”

“Godiya suke Uwar Marayu yanzun nan zai zartar da umirninki, na barki Lafiya.”

Nan Mudi ya tafi fiddo bayin dake kulle gidan horo, ita kuma Gimbiya Hakima ta tafi ziyara gidan bayi ba ƙaramin kyauta tayi ma bayi ba daga nan ta wuce gidan waziri ta duba jikinshi sannan ta wuto shashen ta..

Masauratar kano a ranar ba ƙaramin murna sukayi ba dan har sai da bayi suka haɗama Gimbiya Hakima walima gobe za’ayi ta..

“Uwar Marayu gobe insha Allah baki ɗaya bayin gidan nan suna gaiyatarki walima bakin ruwa, zamu nuna maki godiya da jindaɗin abunda kikayi a jiya.”

“Bilkisu Allah ya kaimu goben, yanzun bacci zanyi sannan kuma ku fara shiryawa jibi zamu koma makaranta.”

Washe gari bayan Gimbiya Hakima ta gama shiryawa direct shashen Gimbiya Yakumbo ta wuce kafin dare yayi taje walimar da bayi suka shirya mata..

“Momy kin tashi lafiya.”?

“Lafiya lau Hakima ya koƙari?, “Alhmdulillah Momy, Momy gobe zan koma school fa.”

“Ai ya dace a koma tunda ankusa gamawa insha Allah.”

“Aiko dai Momy sauran Shekara ɗaya insha Allah, “Allah ya kaimu Hakima, “Amin Momy Yaya Annas shima da mukayi yawa yace next year ɗin nan zai dawo ya gama shima baki ɗaya.”

“Eh kinga tare zaku gama keda shi, “Aa Momy shi harda masters yayi fa nikuma degree kinga ai da banbanci sosai.”

“To Allah ya baku Nasara baki ɗayanku, “Amin ya Allah ni barki lafiya Momy zan biya na gaise da Fulani.”

“To Daugter Allah yayi maki al’barka, “Amin Momy.”

Bayan ta wuce shashen Gimbiya Fulani suka gaisa sosai, “Fulani zanyi missing ɗinki gobe ne zan koma school.”

“Nima zanyi missing ɗinki Hakima, dan Allah ki kula da mutuncin kanki kiyi abunda ya kaiki wannan gari.”

“Insha Allah zan kiyaya, “idan mu iyayenki bamu ganinki to Allahn da ya halliceki yana kallonki kuma duniya duk abunda ka suka shi zaka girba dan haka kiji tsoran Allah sannan ki guji abunda zai ɓatama iyayenki rai har ya sasu hawaye.”

“Insha Allah Fulani, bayan Fulani ta gama yi ma Hakima wa’azi sanann ta fito ta wuce shashen ta, shiryawa tayu sannan suka wuce walima.

Ba ƙaramin dadi Gimbiya Hakima tayi dan bayi sunyi koƙari sosai wajen ganin sun faranta ma Gimbiya Hakima rai, kuma Alhmdulillah suma sunji dadi dan a fuskar kawai zasu gane Gimbiya Hakima taji dadin abunda suka yi mata dan sai murmurshi take, bayan anci ansha sanann kowa ya tafi makwancinshi..

Wanka kawai Gimbiya Hakima tayi sannan ta kwanta bacci, washe gari karfe biyun rana suka ɗauki hanyar Zaria..

Oooooooo????wallahi nagaji sosai typing is no essay guy kuyi manage da wanannna pls inayinku ovver and over????????❤️????????

ANJIMA ZANYI MAKU WANI UPDATE INSHA ALLAH

By Jameelah Jameey✍????

Share
COMMENT
Vote
Like
Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

53&54

“Boka Turmurturs na kawo kukana wajenka ina san ka shareman hawayena.”

“Ina san haka, Gimbiya Kilishi ai ke ta daban ce wata matsala ce kuma ta kunno kai kuma.”?

“Turmurturs kwana biyu maimartaba baya kulani ba kamar da ba shine nace anya ba shiga tsakaninmu akayi dashi ba.”?

“Tabbas Gimbiya Kubrah ta shiga tsakanin ki da mai gidanki, dan haka idan muka cigaba da yin wanka lafiya lau kin fi karfin duk wani makirci.”?

“Ni Kubrah zata haɗa da maimartaba shikenan Turmurturs kabarta tayi lokacine nan da shekara biyu sai Kubrah ta zama baiwata.”

“Au to dan aiki yana nan yanda ya kamata dan Turmurturs yace ankusa gamawa da Hakim harda Hamad ɗin da kikace a kashe maki.”

“Yauwa ina godiya Turmurturs.”

Nan Turmurturs yayi mata wanka da abunda suka saba duk sati sanann ta wuce gida hankalinta kwance..

Bayan ta dawo gida wanka kawai tayi ta kwanta cikin farin ciki, dan gani take Humad ya gama Mulkin zaria, dan bata ɗauki shekara biyu wani abu ba tunda har tayi hakurin shekaru tana bin bokaye amman ba biyan bukata sai yanzun ta Zulaha ta haɗata da Turmurturs tasan bukatar ta tabiya, haka dai har bacci ya kwasheta..


Bayan Gimbiya Hakima sun iso gida, gyara gidan akayi sannan ta shirya ta wuce school dan suna da lecture three dan haka hutawa kawai tayi sannan ta wuce school..

“Hakima kinga yanda kika koma kamar wata sarauniya matar Sarki.”

“Kinji ki wallahi Maryam kin cika surutu har wani abu na ƙara kenan? Ke bance kin ƙara wani abu ba sai ke.”?

“Ai ni ba abunda na ƙara, amman ke baki ganki ba masha Allah kamar yar India, anya Hakima bakida dangi a Indiyawa ko kuma larabawa.”?

“Ke dai akeji Maryam, wani lecturer ne zan ɗaukemu 300lvel wai.”?

“Prof Hakim da Dr Moha sai wasu ni ban riƙe sunansu ba dan vistors lecturers ne.”

“Ok Allah ya bamu sa’a, “Amin ya Allah result ya fito naga kece over’roll ma, gaskiya Hakima kinyi koƙari sosai Allah yasa ki gama da First class ɗinki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button