GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Dan haka ku bude kunnuwanku da kyau zan sake maimaita maku ka’idojina, dan na lura ku jaikaine da man jaiki shi ake maimaitama magana..

“Daga yau karku kuskura na sake taraku akan magana daya, kunajina ko?

“Eh muna ji uwargijiyarmu, Allah ya kara tsawaucin kwana..

A’bu ke da Murja daga yau ku zaku ringa yi man sauwar abinci , karfe bakwai na safe na tadda kun gama hada man abinci, karfe biyu na rana kungama na rana, karfe bakwai na dare kungama na dare, kunji ni ko?

“Eh muna ji, insha Allah, bazamu sake mu sake karya umurnin Gimbiya ba..

“Dan haka ku tashi ku bani waje, salan na kama maku da laifi, kusan hukuncin da zan yi maku, “insha Allah zamu kiyaye..

“Ladi da Larai ku kuma daga yau aikin gida ya dawo kanku, dan na gaji da cin jagwalgwalon abincin ku da kullun sai kun cika mashi gishiri sai kace ba yan-mata ba..

“To godiya muke Gimbiya yar’masu gida..

“Ku tabbatar kafin na tashi bacci kun gama gyara ko ina cikin gidan nan banda dakin da nike bacci shi daya ne ban yarjemaku da ku shiganman daki ba, dan ba daukar kazantarku banzaye kazaman banza kazaman wofi, ku tashi ku bani waje..

“Godiya muke Gimbiya Hakima..

“Bilkisu ke kin san aikinku ai ke da Lantana, dan haka sai ku kara hinma, dan na lura yanzun kuma kuna san ku sa lalaci cikin aikinku, idan kuma ku ka bari raina ya baci bansan abunda zan yi maku ba, dan haka wuce ki karaman Sarkin bulala..

“To Gimbiya, nan Ba’ba Bilkisu ta tashi ta tafi kiran sarkin bulala..

“Sarkin bulala, Gimbiya Hakima tana san ganinka..

“Lafiya dai ko? “Eh lafiya lau tana san ganinka dai, “to gani nan zuwa, nan Ba’ba Bilkisu ta taho gaya ma Gimbiya sako..

“Ranki ya dade gashi nan zuwa, “naji tashi ki ban waje kika yi man wani tsugune gabana…

“Gimbiya Hakima, uwar Marayun masarautar kano, gani na ansa kiranki, ina mai jiran umarninki na zartas..

“Sarkin bulala, ina san kayi ma Lantana bulala goma, yanzun in dan ta motsa ko tayi kuka bulalar ta zube a sake wata daga farko, in dan ka gama hukunta ta a sako ta ta dawo bakin aikinta..

“Angama ranki yadade, yanzun zani zartas da umirninki, nan sarkin bulala yaje, ya fiddo Lantana yayi mata hukuncin da Gimbiya Hakima ta bashi umirni sannan yace tace ta wuce ta koma bakin aikinta..

Haka Inna Lantana ta taho, tana mamakin halin Gimbiya Hakima yanzun ace wai bakin aiki zata koma, bayan duk wahalar da tasha, haka ta koma shashen Gimbiya Hakima..

“Godiya nike Gimbiya nagode da sausaucin hukuncin da na samu daga gareki..

“Lantana daga yau ki kiyaye duk abunda zai bata man rai, tashi ki ban waje..

Nan Gimbiya Hakima ta shirya, ta dauki hanyar Shashen Gimbiya Yakumbo daga nan ta wuce Shashen Gimbiya Fulani dan ta gaidasu,da kuyangirta Aisha tana biye da ita a baya..

Bayan Gimbiya Hakima sun isa bakin turakar Gimbiya Yakumbo, nan aka yi masu iso wajen Gimbiya Yakumbo sannan Gimbiya Hakima ta shiga..

“An tashi lafiya Momy? “Lafiya lau Daughter, fatan ki tashi lafiya?

“Lafiya lau Momy, wai Momy yanzun tsakani da Allah Baffah yayi man adalci?

“Daughter ba yanda banyi da Maimartaba ba akan ya kaiki Turkey karatu, amman yace shi a dole nan kasar zakiyi karatu to ya zanyi dole sai dai muyi hakuri, kawai in kinje ki maida hankali kayi karatu da man ban jinki a famnin karatu, dan haka ki fidda komai a ranki Hakima ki maida hankali kiyi karatu..

“Nidai gaskiya ba’ayi man adalci ba, ace ni Hakima zani university a Nigeria, duka karatu a nan kasar nayi shi, shi ko Yaya Annas yana can yana karatun shi Dubai, niko za’a hadani da tallakawa su gogeman zufar tallauci..

“Daughter ki tuna tallaka da mai kudi da mai sarauta duk Ubangiji Allah ya hallicemu, bamu da banbanci a gurin Allah sai wanda yafi bauta mashi, dan haka ina bukatar ki gyara kalamanki..

“Afuwa nike nema Momy, “shikenan akiyaye gaba, kinje kin gaida Fulani?

“Aa daga nan zan wuce wajenta, “to yi maza ki tashi kije ki gaidasu dan Baffanki yana shashenta, “to ni zan wuce a huta lafiya, “Uhmm..

Nan Gimbiya Hakima ta wuto Shashen Gimbiya Fulani dan gaidata itama, suna zuwa aka yi mata iso nan ta shiga ta samu waje ta zauna..

“ina kwana Fulani? “Lafiya..

“Fulani ko na yi maki laifi?

“Ko daya mai kika gani Hakima?

“Naga duk kin chanza mani baki daya, wallahi Fulani baki sona kamar bake kika haifeni ba, Yakumbo tafi sona..

“Hakima tashi ki bani waje tunda mun gaisa, haka kike so na soki baki jin tausayin bayin dake cikin gidan nan balle tallakawan waje?

“Haba Fulani, ni kullun sai kunce man naji tausayin tallakawa da bayin gidan nan, to ya kuke so nayi bayan ina iyakar bakin kokarina..

“Naji Hakima, tashi ki ban waje, karki manta ki fara shiri kafin Maimartaba ya ce ki fito…

“To shikenan Fulani, amman ina Maimartaba na gaidashi Yakumbo tace yana na?

“Eh! Yau bai san yin magana da kowa, yau ko fada baya fita, “to an gaidashi ni na tafi…

Nan Gimbiya Hakima ta koma shashenta, tace ma su Lantana yau bata san ganin kowa, sannan ta shiga bedroom dinta tayi wanka ta kwanciyarta…

By jameelah jameey ????

Share and comment pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY
Jameelah jameey ????

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

05&06

Wacece Gimbiya Hakima!!

Masarautar kano, Babbar masarautace wanda tana daya daga cikin masarautar da take babba a Nigeria..

Sarki Abdulsamad Abdulrazak shine mahaifin Sarki Abdulhadi Abdulsamad, sarki Abdulhadi Abdulsamad shine mahaifin Gimbiya Hakima Abdulhadi Abdulsamad…

Sarki Abdulhadi Abdulsamad adalin sarkine, yana mulki cikin Ilimi da adalci baya san yaga tallakawanshi cikin hukubar yunwa ko wani abu na wahalar rayuwa..

Wannan kyaukywan hali na sarki Abdulhadi Abdulsamad ya gajeshine a wajen mahaifin shi Sarki Abdulsamad Abdulrazak..

Mahaifin Abdulhadi su biyu ya haifa shida da kaninshi Yarima Annas, sun taso cikin kulawa ta sarauta, mahaifinsu ya koya masu yanda ake mulkin adalci ya tusa masu soyayyar tallakawa a cikin zuciyoyinsu..

Sunan Mahaifarsu Hakimatu, gimbiya Hakimatu ta ba yaranta da Allah ya bata guda biyu tarbiya iyakar bakin kokarinta, ta koya masu gwamawarar rayuwa ta bada gudun muwa wajen gani soyayya ta shiga tsakanin su da tallakawa domin ita macece mai tausayin na kasa da ita..

Abdulhadi yayi karatun addini dana boko, shida kanin shi Annas..

Annas yana final year yayi accident ya rasu, haka su Sarki Abdulhadi suka yi kukan rashin da sukayi suka barma Allah lamarinshi..

Mahaifiyarsu diyar sarkin katsina ce Gimbiya Hakimatu tana da faranfaran da mutane, ta zauna da sirikarta lafiya har mai rabawa tazo ta raba su..

Bayan Abdulhadi ya gama karatu ya auro yar’sarkin sukaja Gimbiya Yakumbo, Gimbiya Yakumbo Allah ya albarkace su da d’a daya Yarima Annas daga shi Allah bai sake ba Gimbiya Yakumbo haihuwa ba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button