GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL


Rayuwa na tafiya komai faruwa yake cikin gidan su Hakim dan Gimbiya Kilishi ta zage wajen bin bokaye dan yanzun ba wajen Turmurturs kawai take zuwa ba.

ita kuma Gimbiya Zulaha bata damu da zuwa wajen ko wani boka ba, dan tasa ma ranta shekara biyar nayi zataga gawar Hakim, amman daga baya tana yi ma Kilishi zagon kasa wajen Maimartaba dan so take kafin shekara biyar Maimartaba ya saki Kilishi, saboda bata shirya zama da Kilishi ba.

(Kuma kai su Gimbiya Zulaha ba Amana tsakanin ki da Gimbiya Kilishi ko wananku yi ma dan uwanshi yake daga boye????.)

Ita ko Gimbiya Fulani Kubrah bata damu da abunda suke ba duk da tana sane da dun wani tungu da kulle-kullen da suke cikin gidan amman bata damu ba ta barma Allah lamarinta baki daya..


Rayuwa ma tafiya dan Hakima yanzun an shiga 400lvl yanzun haka second semester take final year, Allah yaso Hakima ba Hakim ke mata project supervisor ba, shiyasa hankalin ya kwanta ta cigaba da hidimar gabanta dan yanzun bata da damuwar komai sai ta karatunta..

yau Hakima suke fara exams shiyasa ta cika zaman gida, ba dan so take ta gama fresh ba tare da spell over ba shiyasa bata tsayawa baye ma kowa duk da Samari sunyi ma Hakima ca, amman basu gabanta.

Exams sai dai ace Alhmdulh yau Hakima ke gama Exam kuma take gama AHAMADU BELLO UNIVERDITY ZARIA bayan sun fito final exmas ba karamin murna suka yi ba nan sukayi exchagings numbers da kawayenta sannan ta wuce gida tana zuwa gida suka dauki hanyar Kano daman already su Azima sun shirya masu kayan su jiran fitowarta suke su kama gabansu dan suma murna suke zasu zauna waje daya, amman da basu kano basu zaria karatun ne kawai basu yi ba amman suma sun sha wuya..

Tafiya suke dan sosai Bala yake ba mota wuta cikin ikon Allah suka iso gida lafiya..

Direct shashen Gimbiya Yakumbo a ka wuto da ita dan yau shima Yarima Annas ya dawo gida shima dan shi da safe ya dawo da shi yayi niyar zuwa ɗauko ƙanwar tashi Maimartaba ya hanashi yace itama zuwa anjima zata iso sai gashi ta shigo itama..

“Momy Momy Momy! Alhmdulillahi Momy yau nayi degree.”

“Oyoyo! Daughter am so happy today, Daughter kinga komi yayi farko yana karshe ko.”?

“Hakane Momy, ina Yaya Annas?, “yana shashen Fulani kin sani.”

“Na tafi naga Yayana, “to nima da man yanzun zan tafi shashen ta Baffanku nacan shima, “to Momy mu tafi.”

Nan suka tafi tare shashen Gimbiya Fulani ko wacansu fuskarta dauke da murmushin farinciki..

Suna shiga Hakima ta ruga da gudu ta fada jikin Annas tana cewa, “Yaya Annas am so happy to see you yau, congrats Yaya angama phd lafiya Allah yasa angama a sa’a.”

“Congrats tooo,, ƙanwa kema ina taya ki murnar gama degree ɗinki, “thank you Yaya.”

Bayan sun gama murnarsu Maimartaba yake shida masu gobe za’a yi masu walima a bakin kogin masarautar haka suka gama sanann kowa ya wuce shashen shi cikin farinciki..

Tana zuwa shashenta bayi suka fara yi mata Allah yasa alkhari, yasa ta gama karatun nan nata a sa’a..

Amin kawai take ce mashi bayan ta shiga wanka ta fito ta shirya hutawa tayi sannan ta kira Maryam waya nan take gaya mata Annas ya dawo gida shima ya gama karatun shi bayan sun gama waya ta kwanta bacci..

Shima Annas bayan ya gama gaisaPlease

bayin shi yayi wanka ya kira Hakim waya yake gaya mashi ya dawo gida shima bayan sun gama waya shima ya kwanta dan yana san ya tashi da wuri gobe insha Allah…

By Jameelah Jameey✍????

JameelarhSadiq

Share

Comment

Like

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

57&58

“Allah ya taimakeki angama haɗa ruwan wankan yana jiran ki.”

“Azima ki fiddo man kaya masu sauki dan kwaliya kawai zamu tafi sai gyaran jiki cikin gari kafin lokacin walimar yayi.”

“Angama uwar marayu a fito lafiya, “Uhmmm.”

Bayan Gimbiya Hakima ta shiga wanka Azima ta fido mata wani material wanda ya ansa sunan shi material, dan Azima ba daga baya ba wajen iya zaɓen kaya shiyasa Gimbiya Hakima take san duk inda zata ta tafi da Azima dan tana da kallar waye wa..

Sai da tayi kusan awa biyu sanann ta fito daga wanka, nan su duka ukku suka haɗu wajen shirya ta, bayan sun gama shirya ta ita da Azima suka ɗauki hanya sai salon dan Gimbiya Hakima ba daga baya ba wajen tsata ba..

Shiri akeyi naga ni na faɗa dan sai mutun yayi tunanin biki ake ko suna amman ba ko ɗaya kawai walimar gama karatun su Hakima Sarki Abdulhadi ya shirya dan ba ƙaramin san yaran nashi biyu yake ba dan su kawai Allah ya bashi kuma gashi Allah yasa yana da rabon ganin kammala karatunsu lafiya dole ya haɗa liyafar da ba’a taɓa yin kamarta ba a masarautar kano.

Niko nace ina da zaiyi masu aure ai abun mai faɗuwa sai dai.. Ba ruwa ????.

Shima Yarima Annas ba’a barshi a baya ba wajen shiri duk da ba wani aboki ga gareshi ba a cikin masarautar hakan bai hanashi yayi abunda ya ga ya dace ba, shida Hakim abokaine a makaranta suka haɗu lokacin shi yarima Hakim yana Phd ɗinshi shi kuma Yarima Annas yazo yin masters degree nansu haɗu sai tasu tazo ɗaya duk da Hakim ya dan girmi Annas amman ba wani girma yayi mashi sosai ba kuma halin su yazo ɗaya shiyasa freindship ɗinsu yazo dai-dai.

Sai da Yarima Annas ya gaiyyaci Hakim yazo walimarsu amman Hakim yace yayi hakuri bai da lokaci comitement sunyi mashi yawa amman insha Allah ya samu time zai zo yayi mashi congrats ya gama karatu lafiya..

Bangaren sarki kuwa ya gaiyaci ko wani sarki da yake Nigeria suzo su taya shi murnar kammala karatunsu Hakima, su ma su Gimbiya Yakumbo ta gaiyyaci ko wace matar sarki da matan yan siyasa dan tayata murnar gama karatun su Hakima.


× ZARIA×

“Hakim cikinku ku ukun nan ɗaya ya shirya insha Allah zamu masarautar kano , domin taya Sarki Abdulhadi murnar kanmalawar karatun yaronshi da ya dawo daga dubai.”

“Ba sai na gaya maku ba waye Sarki Abdulhadi ba a wajena ba, don Sarki Abdulhadi Aminane na hannun dama tare mukayi karatu da shi masarautar su na zauna da nayi karatu B. U. K Kano, dan haka hallatar walimar ta zamai mana dole koda muna da uziri mu ajiyeshi gefe muje.”

“Allah ya taimaki adalin Sarki Abdulmatalak, ai ba wanda ya dace da ya baka zaria inba Hamad ba tunda shine babba.”

“Zulaha wa ya baki izinin magana ?, “Ina neman afuwa, “ni ban damu da babba ba kuma in ta girma zan bi ai da Hakim zan tafi kenan tunda kinsan ya girmi Hamad kowa ma ya sani cikin masarautar nan ban san tashin hankali Zulaha dan haka akiyaye.”

“Cikin ku wa kuka fidda mu tafi tare.”?

‘Allah ya taimakeka, nidai na hakura cikinsu sai ka tafi da ɗaya.”

“Ina ai ba zai yuyuba idan har za’a tafi da Hamad sai dai a tafi da Humad dan shima Humad ɗin ba wani girmanshi a kayi sosai ba da za’a ringa nuna mana banbanci.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button