GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tunda Sarki Abdulmatalak ya ga Gimbiya Hakima ya ji yana san ya haɗata aure da Yarima Hakim, dan ya yaba da tarbiyarta da hankalinta yana yi ma Hakim sha’awar auren ta, dan haka ya gudurinma kanshi zai nema ma Hakim auren Hakima bayan an gama taro.
Bayan sun gama gaida manyan da ke wajen suka koma suka zauna, nan Sarki Abdulhadi ya tashi yayi bayanin ya kuma miƙa godiya ga manya baƙin da su hallaci taron.
Anci ansha an koshi sanann ko wani sarki ya kama gabanshi yana yi masu fatan alkhari, bayan ko ya watsa Sarki Abdulmatalak ya bukaci san yin magana da sarki Abdulhadi.
Bayan sun ƙara gaisawa nan Sarki Abdulmatalak ya fara magana kamar haka, “Abokina gaskiya ina mai ƙara taya ka murnan sosai, Allah yasa karatun da sukayi ya anfani al’ummar musulmai baki ɗaya.”
“Amin ya Allah, nagode sosai Abokina dan kunyi man kara kuma naji dadi sosai, “haba ai yi ma kaine, ai wannan abun na taya murna ne, in tambayeka mana Abokina.”?
“Sosai ma ina saurarenka yi man ko wace tambaya ce Allah yasa inada answer ɗinta.”
“Da man ina san naji ko ka fidda ma Gimbiya Hakima miji, idan baka fidda mata ba muna bisa ga so dan zanso mu haɗa jini da kai, ina nemama ɗ’ana YARIMA HAKIM auren GIMBIYA HAKIMA amman idan ba’a rigamu ba.”
Wani kallar farin cikine ya mamaye Sarki Abdulhadi dan daman yana da niyar yi ma Sarki Abdulmatalak maganar Hakima ya haɗa ta cikin yaranshi, dan zumincin su ya ƙara ƙarko.
“Alhmdulillahi Wannan magana tayi daɗin ji sosai, ai Abokina ba sai ya nemi aure ba ni Abdulhadi Abdulsalam na ba ɗ’ana Hakim auren Hakima kawai yazo suga junansu sanann a ɗaura tunda daman ta gama karatunta.”
“Aiko naji daɗin wannan kyautar da kayi mana ina godiya Abokina.”
Nan suka gama maganarsu sannan suka fito, shi kuma Hamad yana can yana san magana da Gimbiya Hakima amman bai ga fuska ba, yana cikin haka sarki Abdulmatalak yace su wuto su wuce gida, haka suka ɗauki hanyar Zaria ba dan ya so ba.
Wata sabuwa inji an ca_ca Sarki Abdulmatalak ya nema ma Hakim auren Hakima ba tare da sanin Hakim ba????
Sarki Abdulhadi ya Amince da magana har ya bada ba tare da sanin Hakima ba????
Yarima Hamad ya faɗa kogin son Gimbiya Hakima ba tare da shirya ba????
Wai Allah wannna shine ɗaurin goron????, kudai ku cigaba da biyoni
Shin Gimbiya Hakim zata amince da auren Yarima Hakim kuwa?
Yarima Hakim zai Amince da Auren Gimbiya Hakima shima?
Yarima Hamad zaiyi hakuri da soyayyar da yake yi ma Gimbiya Hakima ya barma Yarima Hakim tunda shi ance na bashi?
su Gimbiya Zulaha zasu yarda Hakim yayi aure nan, kuma zasu hakura da shekara biyar ta ida cika suka aikin boka Turmurturs yana yi?
Turkashi wanann ansoshin duk suna nan gaba cikin wannan labari mai albarka na Gimbiya Hakima ku cigaba da biyo kawai
#JameelarhSadiq
Share
Comment
Vote
Like
Please
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
*M. W. A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer
STORY AND WRITING BY
_Jameelah jameey ????_
*(Yar mutan kankia????????)*
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI
Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.
NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????
61&62
Bayan tafiyar Sarki Abdulmatalak, Sarki Abdulhadi ya haɗa Gimbiya Fulani da Gimbiya Yakumbo cikin daren nan yace yana san yayi magana da su.
Bayan sun zauna suna jiran jin maganar da Maigidan nasu zai yi su cikin daren nan, bayan bai taɓa yi masu kallar wannan neman na gaugawa ba.
“Yakumbo! Fulani.”
“Allah ya taimakeka, Allah ya sa lafiya dai? Dan tunda nike dakai baka taɓa taramu cikin dare ba, koda zaka auri Fulani ba cikin dare kayi man maganar auren ta ba.”
“Yakumbo lafiya lau, wanann abun a faɗi ne da zafin-zafinshi ba sai ya huce ba shiyasa na tare ku.”
“To Alhmdulh yanzun hankalina ya kwanta, muna sauraranka Mijinmu.”
“Da man maganar Hakima ce.”
“Hakima kuma Maimartaba sarki Abdulhadi.”?
“Eh Yakumbo Hakima Allah yayi na fidda ma Gimbiya Hakima miji.”?
“Miji? Hakima ka fidda ma Miji.”?
“Eh miji, ya naga kamar hankalinki ya tashi wani abu? Ko tana da wanda take so.”?
“Aa ko ɗaya, kawai ina mamakin Hakima da miji, naga duka duka yaushe ta gama karatun har kuma an fara maganar aure.”
“Karki damu, daman ai nasha tambayarki nace Daughter ɗinki tanada wanda takw so kice babu, to ni Abdulhadi Abdulsalam na baka Yarima Hakim Abdulmatalak auren Gimbiya Hakima ko bayan raina ban yarda a ɗaura ma Hakima ko wa ba inba Hakim ba.”
“Ai ba matsala naji dadi da Hakim ka ba auren Hakima, dan nasan Gimbiya Kubrah zata kula da Hakima sosai.”
“To kunji abunda zan gaya maku, in Allah ya kaimu gobe ina san sake ganinku baki ɗaya harda su yaran, dan inasan gaya ma Hakima wannan albishir ɗin.”
“To Allah ya kaimu goben lafiya.”
Nan Gimbiya Fulani ta fito tana murna dan taji dadin haɗin da mijin nata zaiyi ma ɗiyar tata, nan ta bar Gimbiya Yakumbo dan ita take da kwana a turakar mai Maimartaba.
×ZARIA×
Bayan Sarki Abdulmatalak ya huta yake tara duka iyalanshi taron gaugawa a babban parlournshi.
Sai da kowa ya zauna sannan ya fara magana, “dalilin da yasa na tara ku ba komai bane ila maganar auren Hakim.”
Ba su Gimbiya Zulaha ba, harda shi kanshi Hakim ɗin sai da hantar cikinshi ta motsa dan baiyi tunanin wanann ranar tana gan da zuwa ba, kawai kallon Maimartaba yake shi ba a mutun kuma ba mataitace ba.
”Aure kuma? Auren ma na Hakim ba na Hamad ba.”?
“Haka kikaji nace Zulaha auren Hakim,na nema ma Hakim auren yar’sarkin Kano dan haka kai Hakim Umirni na baka ba shawara ba kaje ku gana da junanku.”
Zubewa Hakim yayi yana kwasher godiya wajen mahaifin nashi, “godiya nike Abba Allah ya ƙara tsawancin kwana bani da zaɓi da ya wuce zaɓin iyayena, nasan kun fini sani abunda ya dace dani.”
“Allah yayi maka albarka, daman abunda yasa na taraku kenan sai Ku tashi Allah ya yi maku albarka baki ɗayanku.”
Haka suka fito ko wane da abunda yake cikin ranshi kallon kallon kawai ake yi ma juna.
Bayan su Yarima Hamad sun shiga shashen Gimbiya Zulaha ya fara magana, “Gimbiya wallahi mudun Abba ya ɗaura ma Hakim Gimbiya Hakima wallahi sai na kashe Hakim dan dani Hakima ta dace ba Hakim, dan akan Hakima ina iya kashe ko waye koda shi Abban ne wallahi.”
“Wacece Hakima kuma?, “Gimbiya Hakima itace yarinyar da mukaje walimar gama karatun su ita da Yayanta Yarima Annas, Gimbiya inason Hakima ina kaunar Hakima akan Son Hakima zan iya kashe waye wallahi.”
“Baka da hankali Hamad? Bani san kana faɗin wannan kalmar ta kashe mutun kai tsaye haba Hamad ka bari nayi tunani mana.”
“Har sai yaushe zakiyi Tunani? bayan kin san Abba yace Hakim ya shirya yaje su ga juna, kuma Abba magana ɗaya yake baya chanzawa.”
“Ba dai kana san Gimbiya Hakima ba.”?
“Eh inasan Hakima, Gimbiya ki taimakeni wallahi Hakima ce rayuwata mudun ban samu hakima ba zan iya kashe kai na ko kuma a waye gari ki tadda gawata ciwon son Hakima yayi ajalina.”
“Yau ɗin nan zani wajen Turmurturs ba sai gobe ba Hamad, dole ka auri Gimbiya Hakima ko ta wani hali ne nayi maka wanan alkwarin.”