GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ehmana Yarima Hakim ne, da man kasanshi? Dan nasan rabonsu da nan masarautar tun haihuwar Hakima dasuzo sunan Hakima.”
“Eh nasanshi sosai muna mutunci sosai da shi muyi zama dashi a dubai.”
Ita dai Gimbiya Hakima batace komai ba, kuma bata kowa komai a ranta ba duk taji sunce Hakim amman bata kowa prof Hakim ba dan ta manta dashi ma.
{gaskiya Hakima bata kaunar Hakim tunda ta iya mantawa dashi, salan naji Team Hakim kunce ba haka bane????}
Bayan sun gama maganarsu dan Gimbiya Yakumbo taba Hakima shawara sosai yanda zata zauna masarautar su Hakim ta gaya mata shirin masarautar sosai har suna mamakin yanda Yakumbo ta san masarautar har haka.
“Momy ni wallahi har na fara tsorata taya zan iya da halin su Gimbiya Zulaha? Bayan ni ban taso naga gidan mu ana haka ba.”?
“Zaki iya Hakima sosai ma, abunda zakiyi shine karki yarda kice wani abu da ya fito daga hannu baiwar gida ko kuma hannun su Zulaha da Kilishi, karki yarda da ko wace baiwa sai wanda zaki tafi dasu daga nan masarautar suma da mutun uku zaki Lantana da Bilkisu sai Azima suma dan na yarda dasu amintaitun bayine nasan basu yarda a haɗa baki dasu a cuceki ba.”
“Sannan karki shiga sabgar kowa, kuma nace maki Gimbiya Kubrah bata da matsala dan matace mai kawaici da mutunta mutane dan haka sai ki yaye Hakima, nasan ki baki ɗaukar rainin bayi to karki yarda wata baiwa daga cikin masarautar ta ringa shigarmaki shashen har zuwa cikin ɗakuna dan haka su azima su zasu gyara ɗaki da girki kinjini ko.”?
“Eh Momy, naji kuma insha Allah zanyi abunda kikace man, dan ba zan yarda ba su Gimbiya Kilishi su raina ni nafi karfinsu da ayar Allah, amman Momy taya kikasan sirin masarautarsu har haka.”?
“Nasan sirinsu wajen Gimbiya Zulaha, da aminatace sosai saboda amintakar da ke tsakanin mijina da mijinta, lokacin daga ni har ita bamu samu haihuwa ba taso taja ra’ayina wajen bin bokaye da malamai nice ban bata fuska ba muna cikin haka sai Sarki Abdulmatalak ya bujuro da auren Gimbiya Fulani Kubrah, hankalin Gimbiya Zulaha ba ƙaramin tashi yayi ba dan ba wajen bokon da bataje ba amman bakinsu ɗaya aure sai anyi ba, bayan anyi aure Allah mai iko yaba Fulani Kubrah ciki daga zuwanta nan ma Gimbiya Zulaha ta fita ta shiga taga cikin zube amman babu nasara har aka haifi Yarima Hakim, bayan haihuwar Yarima Hakim Gimbiya Zulaha itama ashe tana ɗauke da ciki, Hakim yana da wata biyar a duniya Gimbiya Zulaha ta haifi yaronta namiji shine akazo dashi wajen walimarku Sunanshi Hamad, Hamad yana da wata biyu na haifi Annas tunda Gimbiya Zulaha taga Hakim shine magajin sarki Abdulmatalak ta tada hankalinta shine take bin bakoye dan har yanzun tana kan bakarta na Hamad sai yayi mulkin Zaria ba sirihin da bata yi ma Hakim amman Allah ya kareshi daga sharinta, Gimbiya Kilishi kuma su Hakim nada shekara biyu a duniya sarki Abdulmatalak ya aureta da basu yar ga maciji tsakaninta da Zulaha daga baya da suka fahimci halin su ɗaya suka zama Aminan juna dan tare suke komai nasu ita kuma Kilishi ita ta haifi Yarima Humad kinji taƙaitacen labarin gidan surukanki Hakima zaki shiga gidan sarauta mai rikici dan haka sai kin iya takunki karki kuskura ki nemi bokaye dan haka ki riƙe Allah da ibadodi sune gatanki dan ita addu’a takobin mumunice.”
“To Momy insha Allah, amman Momy taya kuka bar Abokantaka keda Gimbiya Zulaha.”?
“Lokacin da Baffahnki zai auri mahaifiyarki, dana gaya mata shine ta nunaman naje wajen boka a hana bikin, ni kuma nace ban ƙaucema Allah saboda ɗ’a Namiji naje nayi saɓon Allah dan haka ban hana Abdulhadi aure koda mata uku zai aure nidai fatana muyi zaman lafiya, shine tace ba ita bani tunda ba halinmu ɗaya ba,daga ranar bata ƙara zuwa wajena ba sanan ku za’azo wannan masarautar bata zuwa ko sunanki ba ita tazo ba Gimbiya Fulani Kubrah tazo sunanki ita da Yarima Hakim kawai sukazo suna kinji abunda ya rabamu.”
“Mutane saboda san duniya da san zuciya sai suyi abunda zasuyi da nasi nan gaba, Allah yasa mu dace, “Amin Hakima.”
Nan dai suka gama maganganunsu sannna kowa ya wuce shashen shi.
×ZARIA×
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
YAR UWA KADA KI WUCE BAKI KARANTA BA DOMIN KUWA AKWAI ƘARUWA A CIKI
*_????️ALBISHIRIN KU????️_*
JAMA’A KO KUSAN MATASHIYAR MARUBUCIYAR NAN WATO JAMEELAH JAMEEY WANDA AKA FI SANI DA YAR’MUTAN KANKIA TAYI SHIRI TSAF DOMIN FITO MAKU DA SABBABIN LITTATAFANTA GUDA BIYU.
SANADIN LINK
HAHAHA YAR UWA DAGA JIN SUNAN WANI BOOK BASAI NA FAƊA BA KINSAN ZA’A SHA SOYAYYA.
IZZA KO MULKI
WAI WANNAN KO BANSAN MAI ZANCE BA KUNSAN DAI YANDA LABARIN GIMBIYA HAKIMA YA KASANCE TO GA WANI NAN KUMA DAN SHI DABAN YAKE DA SAURAN☺️
TAKU CE JAMEEY YAR’MUTAN KANKIA MARUBUCIYAR????
NANA JAWAHEER
GIMBIYA HAKIMA
A HAKA NIKE SONTA
YAN MATAN ZAMANI
SAI KUMA
SANADIN LINK
DA
IZZA KO MULKI
MASOYANA KUDAI KU CIGABA DA BIYONI DOMIN SUNA KAN HANYA, ????KARKI BARI A BARKI A BAYA????
JameelarhSadiq@wattpad
Share
Comment
Vote
Like
Please
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
M. W. A
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
STORY AND WRITING BY
Jameelah jameey ????
(Yar mutan kankia????????)
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI
Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.
NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????
65&66
×ZARIA×
Tunda su Gimbiya Zulaha suka dawo daga wajen Turmurturs, Gimbiya Zulaha ta kasa zaune ta kasa tsaye dan gani take kamar boka yana yi mata yawo da hankali amman da ta tuna Turmurturs ne sai taji hankalinta ya kwanta dan boka Turmurturs ta amince yana share hawaye waya ta ɗauka ta kira Hamad akan komai yake ya ajiyeshi yazo tana san ganinshi.
“Hakim ya na ganka cikin damuwa Allah yasa lafiya.”?
“Aliyu ina fa lafiya Abba zaiyi man aure.”
“Aure kuma Hakim.”?
“Wallahi aure zaiyi man wai yar’sarkin kano, maganar da nike yi maka Fulani tace gobe zani je wajen yarinyar.”
“Innalillahi wa’inna’alaihirajiun, Hakim abunda nayi maka gudu kenan shiyasa naso kanemi yarinyar nan Hakima dan wallahi ba ƙaramin marching kukayi ba, amman girman kai yana hanaka wai kai cewa ma kake ka tsaneta bayan ga sonta nan cikin idanunka ina gani.”
“Allah ya tsareni Aliyu, ai gwara da Abba ya fidda man mata, ni natsi Hakima bansan Hakima ban ƙaunar Hakima kai mai ma irin sunan Hakima bani santa da wall… “Da kata haka Hakim, wallahi karya kake ni Aliyu nace karya kake kana san Hakima kuma nan gaba zakace na gaya maka.”
Aliyu ya ƙarashe maganar cikin fushi dan bala’in haushi yake ji idan Hakim yace baya san Hakima bayan ga sonta yake ta ɗawainiya dashi wannan abun na bashi haushi gashi har za’ayi mashi auren dole.
???? niko nace Aliyu kwanatar da hankalinka burinka ya kusa cika
“Ya isa haka Aliyu enough, taya zaka zo kasani gaba kana gaya man maganganu saboda wata useless girl zaka sani gaba kana yi man tsawa, ka wuce ka ban waje kabarni da abunda ke damuna please.”