GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ali.. yu.. Wayyo.. All. ah na.. Mut.. Uwa. Zan.. Yi,”Hakim ban gane mutuwa zakayi ba, mai ke faruwa ne wai.”?
“Ciki.. Ciki. Na. Aliyu.”.. Yana cema Aliyu cikin shi yagane matsala cikin ɓacin rai Aliyu ya ɗauko magani masu yawa ya taho dasu, cikin daren nan ya taho shashen Hakim dan ma yana da keys shima bai kai da maidama Hakim ba tunda yanzun yana mata, buɗewa yayi ya shigo, tunda ya shigo ciki ya tsaya yana kallon parlourn da ko ba’a gaya maka ba kasan anyi kokoyi cikinshi ko kuma dambe, girgiza kai kawai yayi ya wuce bedroom ɗin Hakim, kwance ya taddashi kasa baya ko motsi dan ya galabaita sosai, da sauri ya ida isa wajenshi ya kamashi ya maidashi bisa gado, sananan ya fita ya koma kitchen ya ɗauko ruwa ya ɓalli magani ya bashi yasha, bai cemashi komai ba dan shi Aliyu abun haushi yake bashi kawai ya bashi magani yace mashi sannu, cikin minti hudu da shan magani wani wahalalan bacci yayi gaba dashi, tashi Aliyu yayi ya ajiye mashi magani cikin dirowa sannan yaje wajen toilet yace ma Hakima, “sai ki fito ki kizo ki kwanta shi har ma yayi bacci, ni na barku lafiya idan kun gadama karku sama ma kanku mafita ni ba ruwana watarana dai idan haka zakuyi sai ko kun kashe juna nan ku.”
Haka Aliyu ya tafi ya bar Hakima da mamaki taya yasan yata cikin toilet, {niko nace tun shigowarshi yaji shesheƙar kukanta da kuma yanda take sauke ajiyar zuciya alamun tayi kuka sosai duk yana jinta har ya gama abunda yake yayi mata magana}, fitowa tayi tana sanɗa kamar ɓarauniya haka ta samu ta fita daga room ɗin Hakim ta wuce room ɗin ta ruwan da bata sha ba kenan wankan tsarki tayi ta sake kaya sanan ta kulle kofa ta kwanta bacci, dakal bacci mai nauyi ya kwashe Hakima ta cigaba da baccinta, amman da ka kalleta zakasan baccin ma cikin tsoro take yin shi.
Tun kafin asuba Hakima ta tashi sake wani sabon wankan tayi sannan tayi alwallah ta fara raka’atul fijir tana gama ta fara lazimi tana cikinyi taji fitowar Hakim, kusan sakin fitsari tayi dan taji kamar room ɗin ta zai shigo daurewa tayi ta cigaba da yin laziminta, turo kofar yayi da mamakinshi sai ya ganta bisa abun sallah baice mata komai ba ya juyawarshi ya wuce mousque daman zuwa yayi ya tada tayi sallah tunda ta tashi ba amfanin magana kenan.
Bayan ta gama sallah komawa tayi ta kwanta, dan Fulani tace zata ringa kawo masu abinci har sai tayi sati sannan ta fara sauwa da kanta, daman ba wani baccin kirki tayi ba nan ta kwanta bisa abun sallahr da tayi sallah a takure ta cigaba da baccinta.
Bayan su Hakim sun fito daga sallah ta howa sukayi shi da Aliyu direct shashen shi suka wuto a parlour suka tsaya suka fara magana.
“Hakim wallahi ka bani kunya sosai jiya, taya zaka bari ka kashe kanka da kanka, bayan kana da mata, amman ka tsaya sokanci ka kasa ansar haƙinka wajen Hakima.”
Mtssss, “ba wani haƙina da zan ansa wajen yarinya ta rainani, jiya ma akashi aka samu ita ta yanyo komai da bata janyo ba ba abunda zaisa na nemaita har ta ga hanyar raina man wayou.”
“Hakim anya kana da hankali kuwa? Yanzun dan kace ta baka haƙinka shine zai zama raini.”?
“Ehmana raini sosai ba, ka haɗa shimfiɗa da ƙaramar yarinya mana, dan haka ni Hakim daga jiya ban sake neman Hakima har sai in ita ta kawo man kanta da kanta sannan.”
“Tabbas ko kana da babban aiki, ni kuma daga yau karka ƙara kirana nazo na taimaka maka, tunda kana da maganin matsalarka yanzun ba kamar da ba, dan haka ina yi maka fatan alkhari zan zuba ido nayi kallo wannan zama naku kuna bukatar gyara, byee.”
‘Ok bye nagode kuma idan na fita zan ƙara sawo maganin da naga ka kawoman insha Allah, “Hakim kenan watarana magani baya maganin komai fa, “acewarka ba, “ok angon Hakima bada kanka a sare kaje gida ka ya faɗi, “so what dan nace ya faɗi kaidai ka wuce ka tafi ni zanyi azkar ka sani, “ok na tafi tunda korata ma akeyi, “ka dai ce komai zakace naji.”
Nan Aliyu ya tafi yana mamakin halin Hakim, yana hangen kallar zaman da masoyan zasuyi, tunda suka fara magana Hakima ta tashi daga bacci kuma taji komai sukace, itama ta sama ranta ko zata mutu bazata nemi Hakim ba sai dai su mutu a haka.. [TO WATA SABUWA KUNJI ITAMA HAKIMA BAZATA NEMI HAKIM BA KODA ZATA MUTU ANYA ZAMAN NAN ZAI YIYU A HAKA???? INA JIRAN ANSAR WAJEN TEAN HAKIMA DA TEAM HAKIM????????]
Da safe wanka Hakima ta shiga ta kusa one hour tana wanka dan sai da ta gasa jikinta sosai da sosai sannan ta fito, key tasa ma door ɗin room ɗnta sannan ta fidda towel ɗin duka ta tsane jikinta sosai ta fara kwaliya, kwaliya tayi mai kyau dan ba ƙaramin kyau tayi ba wata yar’rigace ficiciya tasa iyakarta giwwa sannan ta ɗauko hula ta tasa sanann ta jefa chigum a bakinta, dan tace yanzun ta fara shigar da zata kunna Hakim, kuma ta ɗaura abota da chigum dan haka ita dashi cikin gidan taga masha wuya, haka ta fito tana hangoshi zaune a parlour yana wani aiki dan ƙeta sai ta chanza tafiya dan tafiya take mai ɗauke hankali duk wani lafiyaiyan ɗ’a na namiji koda tazo kusa dashi sai da ta ƙara rage chanza wata tafiyar, sakin baki yayi yana kallon hips ɗinta yanda suke juyawa dan ji yake kamar yaje ya rungumota, Hakima jikinta ya bata kallonta Hakim yake sai ta juya suka haɗa ido saurin ɗauke kanshi yayi, yayi kamar baisan da fitowarta ba murmushi tayi ta wuce taje dining ta fara yin breakfast hankalinta kwance tasan dai ta sa mutun cikin wani mood dan kallo ɗaya tayi mashi taga yanda ya sauya lokaci guda tana mamakin kallar jaraba irin ta Hakim, Hakim da yaga zai afka ruwa sai ya haɗa kayanshi ya wuce room.
BY Jameelah Jameey✍????
Share
Comment
Like
Vote
Please
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
*M. W. A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
STORY AND WRITING BY
_Jameelah jameey ????_
*(Yar mutan kankia????????)*
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI
Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.
NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????
81&82
Koda ya shiga room ɗinshi toilet ya wuce direct, shower ya kunnama kanshi tundaga sama sai da yaji ya dan dawo dai dai sannan ya ɗauro towel ya fito, maganin da Aliyu ya kawo mashi ya ɓalla ya sha, dafe kanshi yayi da hannu biyu yana mamakin yanda da yaga Hakima sai yaji shi’awa ta taso mashi kamar ya mutu, ashe daman haka yake da saurin shi’awa bayan shi dai yasan ba haka yake ba, kwanciya yayi rubda ciki yana yana tunanin yanda zamanshi da Hakima zai kasance cikin wannan yanayin idan ko haka ne gaskiya da matsala babba tunda ya fahimci shi mabukacine sosai, haka ya kama juye juyenshi bisa gado har lokacin sallah yayi ya tashi ya tafi massallaci.
Tunda Hakim ya tashi ya shiga room ɗinshi, Hakima take dariyar ƙeta dan ta lura Hakim bai da wuyar shiga hannu, tana gama breakfast ta shiga su Lantana suka shigo suka cigaba da firar su, da ta gaji da surutun ta tashi ta shiga room dinta ta cigaba da waya da Maryam sai da lokacin sallah yayi Sannan sukayi sallama, Hakima taji dadin wayar da sukayi da Maryam dan ta kara bata shawara sosai kuma ta dauka, wanka ta shiga sannan tayi kwaliya tasa shidda darkblue ɗinkin doguwar riga fiketgown da tasha aikin paintward abun yayi kyau sosai sallah tayi sannan ta wuce kitchen dan sama ma kanta abunda zataci, fitowa tayi tana gyara ɗaurin dan kwalinta bata lura da mutun ba sai kawai taji sunci kwaro da juna, dan kwalin faduwa yayi gashinta baki ɗaya ya baje bisa fuskarta, hannu tasa ta matsar da gashin tana sosa goshinta dan zafi yake mata sosai ji tay yana cewa, “wai ke wata kallar wawiyace? Ko ke makauniyace da zaki wani taho baki kallon gabanki sai kace gidanki.”?