GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ya isa haka Hakim, baka isa ka gaya man magana ba, bayan bugeni da kayi kuma ka dawo kana gayaman maganganu mararsa dadin ji, idan ni makauniyace to kai mai zance maka? Naji ban gani kai da kake gani waya hanaka kaucewa da ka hangoni.”?
“Ke har kin isa kiyi man wannan questoin ɗin sai kace sa’anki.”?
“Gashi kuwa ai gaskiya na faɗa, ta faɗi tana murguɗe mashi baki, kallon dan ƙaramin bakinta yake dan tayi mashi kyau sosai dake murguɗe bakin sai yaji dama ta dawo tasake yi mashi, cewa yayi, “Ni Hakima kike murguɗe ma baki, kamar abokin ki.”?
“Eh ɗin an murguɗe.”… tace tana ƙara murguɗe wa biyota Hakima yayi da gudu itama ta ruga, haka suka kama zagaye parlourn suna gudu shi dole sai ya kamata, yana sane yaƙi kamata dan abun yayi mashi dadi sosai shiyasa bai kamata ba, da Hakima ta gaji ta faɗa ɗakinta ta kwanta bisa gado tana maida numfashin wahala, tana cewa, “mugu kawai kaidai Hakim wallahi mugune ko dan baka sona shiyasa kake san cin zalin ɗina.”…. Haka ta kamaa surutunta sannan ta tashi ta fito dan ta ɗauki dan kwalinta, zaune yake cikin parlourn yana kallon NTA NEWS, ta gefenshi ta wuce ta shiga kitchen indomie ta dafa sannan ta fito ta zauna ta fara ci tana kallo tashi tayi ta ɗauko remote ta sake tasha ta mai TELEVISTA TV tana kallon music, shima Hakim tashi yayi ya maida NTA NEW haka ta tashi ta chanza inda take haka sukai tayi ba wanda yayi ma wani magana, tashi taga yayi ya nufo ta ta shi da gudu ta shiga, ɗaki dariya ya kamayi yana cewa, “ga jan faɗa dai shigen tsoro.”
“Kilishi kinga Amaryar Hakim, kamar ita tayi kanta dan kyau.”?
“Hmm, ni bansan mai ma zance ba Gimbiya kawai ace shi maimartaba baya san yaranmu sai dai Hakim, inba ba’ason yaranmu ba mai zai hana idan ya tashi neman auren ya nema masu lokaci guda, amman sai ya nema ma Hakim shi ɗaya dan yana ɗan so.”
“Kilishi kin sosa man ida keman ƙaiƙayi, sai yanzun kika gane ba’ason yaranmu sai dai Hakim? Da yake abun harda ke ya shafa tunda Humad ya isa aure shima idan aka bashi mace tsab zaiyi mata ciki ta haihu, amman duk bai gani ba sai girman Hakim kawai yake gani shi da yake da kwain haihuwa , shi ya isa haihuwa banda namu.”
“Yanzun ba wannan ba yaushe zamu wajen Turmurturs akan wannan yarinyar karfa mu tsaya sanya tazo ta samu ciki saduwar farko fa.”
“Hakane fa Kilishi dan ni ban kawo wanann a ran nan ba dan haka tashi mu tafi yanzun dan zama bai ganmu ba, yau kwana uku da biki wallahi ko ta samu cikin sai an zubda shege dan bama ta yuyuwa Hakim ya haihu ai aikinmu zai dawo baya tashi mu tafi mana.”
“Gimbiya ki fara fita mana sai na biyoki, karda mu fita tare mu janyo idonun mutane, “to naji nayi gaba sai kin fito, “to yanzun ko.”
Haka Kilishi ta fito suka nufi wajen Turmurturs, tunda suka je suka gaya ma Turmurturs abunda yake tafe dasu wani baƙin magani ya basu yace su tabbatar da Hakima ta ci shi cikin abinci tana ci bazata ɗauki cikin Hakim ba sai dai na Hamad kuma ya ƙara ce masu suna nan suna aikinsu nan da wata tara Hakim zai mutu, haka suka taso cikin farinciki dan yau sunji dadin zuwa wajen Turmurturs, nan Gimbiya Kilishi tace, “Gimbiya kinga sannu bata hana zuwa {sunan novel ɗin Bikinsu S FAri ya nan yana yawo a social media????karki sake a baki labari}, “aiko dai Kilishi sai dai a daɗe ba’aje ba, amman Kilishi mai yasa kikace haka.”?
“To da muna hangan shekara biyar tayi nisa yanzun gashi saura wata tara, “hakane gaskiya kuma Kilishi ni yau ina cikin farin ciki gobe da safe da kaina zanyi masu abincin safe kinga sai na sa mata maganin da taci shikenan bukata ta biya.”
Haka suka kama magana har suka iso gida ko wace ta wuce shashen ta ta kwanta.
Bayan Hakima ta gama duk abunda take ta tashi ta wuce kitchen ta haɗo coffe tasha sannan ta yi hanyar room dinta, a haka suka hadu da Hakim shima zai shiga kitchen din ya haɗa tea tayi mashi kyau sosai dan kasa boye maitarshi yayi dan fili fuskarshi ta nuna hakan, wucewarta tayi dan tasan halin shi ba kunya ta isheshi ba yana iya rungumota, tana shiga ɗaki ta kulle ta bar key ɗin jikin door ɗin tayi addu’a ta kwanciyar ta.
Koda Hakim ya gama duk abunda yake ɗakin Hakima ya nufi direct amman ya tadda kulle baiyi yunkurin budewa ba ya koma nashi ɗakin ya kwanta, amman da tunanin Hakima bacci ya kwasheshi.
Tun asuba suka tashi Hakim ya wuce massallaci ita kuma tayi sallah, koda ta gama sallah kitchen ta shiga tayi masu dankali da tea sai kosai dan angaya mata Hakim yana son kosai sosai, koda ta gama wanka ta shiga ta shirya cikin wasu riga da wando ba ƙaramin kyau tayi ba ta tunke gashinta ta ajiyeshi a chests ɗinta sannan ta fito direct room ɗinshi tayi, nocking tayi amman baiyi magana ba, shi yasa ta shiga lokacin da ta shiga dai dai time din ya fito daga wanka daga shi sai towel ƙara Hakima ta saki yana juya mashi baya dan bata taɓa ganin namiji haka ba daga shi sai towel, shi ko Hakim ko a jikinshi dan ma matsawa yayi kusa da ita tana tambayarta abunda ya kawo ta room ɗinshi, idonta rintse take ce mashi zuwa tayi ta ce mashi ya fito yaci abinci ta gama haɗawa, yaji dadi sosai shiyasa yayi huging ɗinta yana manna mata kiss a koshi daman tayi mashi kyau sosai ce mata yayi ta shirya mashi sai su fita tare, cewa tayi bata yarda ba sai dai ya shirya ya fito matsa mata yayi ba yanda ta iya ta fara shafa mashi mai tana yi mashi Allah ya isa cikin zuciya, komai take Hakim yana kallon ta ta mirror dan hakan ma da take kyau take ƙara yi mashi sosai, bayan ta gama shafa mashi mai ta ɗauko wani jean da T-shirt masu kyau tace yasa amman sai yace duka ita zata sanya mashi nan fa suka fara drama dan ko boxer bai sa ba wai duk ita zata sanya mashi ita ko tace bai isa, daman yasan bazata saba kawai dai shi yana son yaga tana magana dan ƙaramin bikin nan nata yana motsawa kamar anayi mata dole, sai da ya gama kallonta san ranshi sannan ya cire towel ɗin a gabanta dukewa tayi tana salati dan Hakim ya girmi tunaninta ko kunyarta baijinya tsaya a gabanta haihuwar uwarshi, bai damu da abunda take ba ya gama shiryawarshi yayi gaba abunda shi ya barta tsugune sai da ta tabarta da ya fita sannan ta bi bayanshi, bata yarda suka haɗa ido ba ta zuba mashi abincin ta tura mashi gabanshi sanan ta zuba nata nan suka fara ci, shi abun dariya yaso ya bashi wai Hakima ce batasan haɗa ido dashi duk tsiwar da rashin kunyar sun gudu dan ya cire towel a gabanta yana sane yayi haka dan ya dasa mata tsoranshi cikin zuciya.
NIKO NACE MALAN HAKIM AI KO BUKATAR KA TA BIYA DAN NAGA ALAMA HAKIMA TA TSORATA SOSAI ????
Haka wunin ranar Hakima a tsorace take da Hakim dan bata yarda ta biye mashi sukayi faɗa ba duk da shi yana jan ta faɗan take kyaleshi.
Gimbiya Zulaha ta shirya ma su Hakima abinci mai rai da lafiya wanda yasha magani dan da kanta ta ɗauki hanyar shashen Hakim dan kaima Hakima abinci.
By Jameelah Jameey ✍????
share
comment
vote
like
please
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
*M. W. A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa