GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Dan haka Hakima umirnin zan baki amman idan kin ɗauki a matsayin da na ɗaukike wato ɗiyata,”Fulani keɗin mahaifiyatace bani da kowa a garin nan sai ke dasu Maryama na ɗauki a matsayin mahaifiyata ba sarakuwa ba, zan iya gaya maki ko wace matsala ta idan ta samaini dan haka yanda zaki ba su Maryama umirnin nima haka zaki bani dan keɗin uwatace banda kamarki a garin nan.”

Wannan maganar, da Hakima tayi ba Fulani kaɗai ba harta Hakim tayi mashi dadi dan daman yana fatan Allah ya bashi mata ta gari wanda zata ɗauki mahaifiyarshi kamar mahaifiyarta, ta maida ƙannanshi kamar nata kuma baida abunda zayi sai dai godiya ga Allah da kuma mahaifinshi daya haɗasu aure da Hakima tabbas ya yarda duk wanda yayi biyaiya ga iyayenshi bazai taɓa yin da yasani ba kuma gashi ta kasance a kan su shida Hakima insha Allah ba zaisa masoyiyarshi kuka ba.

“Allah yayi maku albarka gaba ɗayanku, “Amin ya Allah.”suka ansa su dukansu, sannan ta numfasa tana kallon Hakima, babu shakka abu ne mai wuya zama da kishiya a wannan zamanin,abu ne da har yau yaqi dadi a cikin gidajen aurenmu,amma duk da haka ta sani ba duka aka taru aka zama daya ba,duk abinda zata gaya mata a yanzu shi zai zame mata madubin dubawarta.

Murmushi Fulani tayi sannan tace
“abinda nake son gaya miki kawai shine kada ki soma cewa zaki tada hankalinki ko ki daga hankalin mijinki,ki zauna da ita tsakani da Allah,ki sauke duk wani haqqi nata dake wuyanki,Hakima kada ki sake kice zaki cuceta,idan kika cuceta Allah yana nan bazai taɓa yafemaki ba, sannan karki sake kice zaki shiga neman bokaye da malamai saboda da neman duniya Hakima ki miƙe lamarinki ga Allah dan kuwa Allah yana tare da mai gaskiya kinji dai ko.”?

Kai ta gyada tace”insha Allah Falani zanyi duk abinda kika ce,da ikon Allah bazan zama mai sabawa maganarki ba.”

A hankali Fulani ta dinga kwantar mata da hankali haka har Sadiya ta kawo mata breakfast saukowa Hakim yayi suka ci tara dan shima bai samu yace komai ba dan tunda yaga Hakima ta shiga damuwa ya kasa cin komai dan baisan abunda zai tada hankalin Hakima ko ya yake, amman yanzun har hankalinshi ya kwanta tunda yaga har dariya take idan Fulani tayi wata magana, har yaji karfin jikinshi ya dawo da ta da walwalarta, bata san sun cinye abicin ba sai da tasa hannu zata ebo taji suna yi mata dariya wai abinci yayi dadi bata san ta cinye ba, “Fulani kinganshi ko yana yi man dariya bayan duk shi ya cinye abincin ba ni ba.”… Ta ƙarashe maganar cin shagwaba, “rabu dashi Daughter ina ganinku ai yanda kukaci abincin duk shi ya cinyeshi.”

“Ful… “Yi man shiru Hakim tashaa ka bamu waje, “to shikenan na zan wuce.”.. Waigowar da zaiyi yaga Hakima tana yi mashi gwalo, nuni yayi mata da gira zasu haɗe anjima, duk abunda suke su Fulani na kallonsu sai sukayi kamar basu ganinsu, abun yana yi ma Fulani dadi yanda suke zamansu cikin soyayya abun burgewa, sai da la’asar ta koma shashensu ta ɗaura masu abincin dare, bayan ta gama wanka ta shiga ta shirya Hakim ba dawowa abincin sukaci sannan ko ya wuce room ɗinsu.


Garin katsina……

By Jameelah Jameey ✍????

Share

Comment

Vote

Like

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

91&92

“Mama wai ya maganar auren na da Abbu yace, zaiyi man har yanzun ango bai zo ba kuma bikin saura sati haka za’a kaini gidan miji bai ɗoukin gani na.”?

“Hikimatu ina sane da haka, karki damu Hikimatu dole Hakim ya soki ko ta wace hanyane, kedai ba gurinki ya cika ba, ko kin manta bakoye nawa muka bi kafin mu samu asiri ya hau Abbunki ya yarda da zaije ya nema maki auren Hakim.”?

“Mama wallahi ina san Hakim kan Hakim ina iya kashe mutu, wallahi sai na raba Hakim da Hakima ai boka yace man Hakima ita ta ɗauke man hankali shiyasa baiyi ma ko wace mace kallon arziki, to wallahi Mama ina shiga gidan Hakim zani rabashi da matarshi ba ma matarshi ba harta uwarshi sai na rabasu, dan Hakim nawa ne ni ɗaya, dan haka ni GIMBIYA HIKIMATU na dauki alkwarin raba Hakim da kowa nashi nayi wannan alkwarin Mama.”

“Tabbas Hikimatu kinsha Nonona, naji dadin maganarki ina san naga mutun mai zuciya dan haka karki kuskura ki ɗaga ma kowa, duk Wanda ya nuna mako yatsa kema Ki nuna mashi ban yarda Ki zauna lafiya da Gimbiya Hakima ba, Ki fidda ta a gidan wannan shawarace na baki ni GIMBIYA BINTA, karki manta Hikimatu ni nan baiwace a gidan nan, Amman bala’i na sai da na shiga na fita na zama matar Sarki Abubakar gashi har na haifeki, kuma na rabashi da kowa nashi dan haka inasan kema idan kika shiga masarautar zaria Ki raba Hakim da kowa nashi sannan ki haifamai magaji haka nike bukata daga gareki.”

“Shiyasa nike sanki Mama, Ina alfahari da kika zamo mahaifiya a gareki, Mamana kwantar da hankali koda na taida Hakima tana ɗauke da cikin Hakim ni Gimbiya Hikimatu sai na zubda shi har lahira dan ni yafi dacewa da na haifama Hakim ɗ’a wanda nan gaba zai gaji masarautar zaria, nayi wannan alkwarin Mamana.”

(Wata sabuwa ???? ita kuma Gimbiya Hikimatu da da salon da zata shiga gidan Hakim kenan????????)


“Maryam wallahi nagaji da magangunan da Fulani take bani, baki ji yanda nike jin kaina ba, wallahi jiya kasa bacci nayi wani magani da Fulani ta bani dan wallahi har sai da nasha kuka na kafin na samu bacci ya kwasheni.”

Hahhahhha! “Hakima wallahi ki bada kai bori ya hau, dan wallahi idan baki ba Yaya Hakim hanya ba akayi komai aka wuce wajen amaryashi na shigowa za ta bashi abunda ke kika hanashi tunda ke baki so ai ita naso.”

“Maryam kin san bani boye maki komai nawa, keɗin ƙawatace kin san nasa gaya maki a da bani son Hakim na tsaneshi ko.”?… “Eh hakane Hakima bani ɗaya had ta su Maryama sun san baki san Yaya Hakim baki kaunarshi.”

“Hakane ko gaskiya Maryam.”.. Hakima tace tashi tayi tana zagaya bedroom ɗin ta ruwa ta ɗauka tasha sannan ta numfasa tace, “Maryam yanzun ina son Hakim ina kaunarshi, amman bansan ya zanyi ba duk da ina iyakar kokarina na ganin na shawo da hankalinshi a kaina.”

“Alhmdulillah, Allah nagode maka Hakima da gaske kina son Yaya Hakim.”?

“Wallahi Maryam inasan Hakim sosai maiye mafita Maryam.”?

“Mafita ɗaya ce Hakima ai yanzun gobe ne za’a kawo Amarya ko.”?

“Eh gobe ne ɗaurin aure Hakim, Maryam wallahi ji nike kamar nayi hauka.”… “To shikenan idan kin yarda yau za’ayi komai a wuce wajen amman idan kin bani haɗin kai daman dare yayi.”

“Eh na yarda Maryam.”…. Magana ta raɗama koni bansan mai tace ma Hakima ba naga kawai suna dariya sannan suka tashi su duga biyun suka shiga kitchen suka fara girki Hakima ita ke sauwa ita kuma Maryam tana haɗa juices, haka suka gama sannna suka fito, tare suka ci da Maryam sannan ta tafi gida ita kuma Hakima ta shiga wanka ta shirya cikin ƙananan kaya masu kyau doguwar rigace tasa iyakarta cinya sannan ta baza gashinta baya, ɗakin Hakim ta shiga ta haɗa mashi ruwan ka sannan ta fito, tana fitowa yana dawowa bata kyaleshi ba tadai ce mashi sannu da zuwa sannan ta shiga kitchen ta cigaba da fiddo abinci shi kuma Hakim ya shiga room ɗin shi wanka yayi ya shirya sannan ya fito cin abinci zuba mashi tayi sannan itama ta zuba suka fara ci bayan sun gama ta wuce room ɗin ta ta sake wanka dan wanka tayi na mutuncin ta fito ta fara shiryawa tana cikin shiryawa taga Hakim ya shigo room ɗinta direct wajenta ya nufo fisgota yayi yana manna mata kiss ta ko ina, cewa take “Hakim maiye haka baka laf…. Taji ya haɗa bakin su waje guda yana yi mata wani irin kiss wanda take ya mantar da Hakima duniyar da take ciki daman abunka da tana hannu sai ta fara biyema Hakim, murzata yake san ranshi itama baye mashi tayi suna ta murzar juna wani kallar numfashi suna fitar da sauti, tun suna tsaye har Hakim ya ɗauke ta ya sauketa bisa gado rumfa yayi mata da faɗanɗan girjinshi nan ya cigaba da murzata tun Hakima najin dadin abun har ta fara yi ma Hakim nisa dan Hakim yayi nisa bayajin kira ni Jameey da naga abun ya girmi tunani na kulle masu kofar na haɗo yan tarkacena na kama gabana nace masu asuba ta gari????????‍♀️????????‍♀️.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button