GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari Hakim da kanshi ya taimaka ma Hakima tayi wanka ta gasa jikinta sosai yanda ya kamata dan bata sa san jiki ba ta gasa jikinta sosai sannan ta fito tayi sallah tana bisa abun sallah tana azkar Hakim ya shigo ji tayi anyi sama da ita cewa tayi, “wai maiye haka haba mana duk cin zalin ɗina da kayi bai isheka ba har sai ka dawo kasake cucata.”

Tunda take maganar yake kallonta, dariya yake yi mata sai da ya gama dariyar shi sannan yace, “haba Jewel yanzun ni zaki cema naci zalin ɗinki bayan haƙina nazo na ansa.”

“Ya isa haka.”… Hakima ta faɗa cikin kukan wasa dan ita kaɗai tasan yanda take jin jikinta gashi kuma yazo yana niyar ɓatama rai, dariya ya cigaba da yi sannan yace, “wallahi Hakima ina sonki, ina kaunarki please i beg you Hakima ki soni ko da kadan ne, ki taimaki dan almajiri.”… Yace yana langwabar mata dakai alamun ban tausayi, wani dadi ne ya ziyarci Hakima wai Hakim ne yake gaya mata kalmar so, Hakim ɗin da tasan baisan ta bai kaunarta amman yau ita yake roƙar ta soshi, Allah kenan tana cikin wannan tunanin taji yace, “Hakima gani gaban na duge ina neman soyayyarki Hakima please Hakima duk abunda ya faruna tsakani na dake a baya muyi fecing abunda zai faru gaba amman karki manta Hakima ina sonki kuma ba sai wannan abun ya faru a tsakaninmu ba a jiya naji ina sonki Aa na fara sonki tun randa idanuna sukayi gamo dake, amman na kasa gane hakan sai daga baya, baki ce komai ba.”

Kallonshi ta kama yi sai da tayi kusan 6min tana kallonshi sannan ta kwanciyar ta, ta kyaleshi ba ta ce mashi komai ba, cewa yayi, “please Jewel ibeg uh karki hukanta da laifin da nayi maki a baya na roƙeki zan jure ko wani hukunci daga gareki amman karki juya man baya karki kujeni domin kece rayuwata Jewel.”

Sai da ta numfasa sanann tace, “naji Hakim ka tashi ka tafi please ina bukatar na huta, kuma ko ka manta yau ake kawo maka sabuwar amarya kaga ba abunda zanyi maka tunda yau za’a kawo maka sabuwar amarya dan haka dan Allah nima na roƙeka ka tashi ka fita ina bukatar hutu.”

“Naji zan barki ki huta nima ai ina bukatar na huta dan haka tare zamu kwanta dake kuma kisani ina sonki ina kaunarki ba zan daina sonki ba har abada.”…. Bude baki tayi zatayi magana yayi saurin haɗe bakinsu waje ɗaya yana aika mata da wasu hotskiss, nidai Jameey da naga lamarin yana neman ya wuce kiss na kulle masu kofa na nace dai Prof Hakim karda ka manta yau ake kawo maka sabuwar amarya ????.


Yau aka ɗaura auren HAKIM ABDULMALAK DA AMARYARSHI HIKIMATU ABUBAKAR, akan sadaki naira dubu ɗari da hamsin, ango Hakim shi dai bai san wani yanayi zaice yake ciki ba, dan shi ba farin ciki ba kuma ba baƙin ciki ba, bayan angama ɗaura auren suka ɗauko amaryarsu sai gidan mijin ta, bayan angama komai kowa ya watsi ya kama gabanshi, kamar yanda al’adarsu take haka ta kasance sai da Hakim ya ɗauki Hikimatu suka je gaida kowa shashen sannan suka dawo gida.

Tunda Hakim ya fita Hakima take kwance bata lafiya dan bata fita ko da aka kawo Amarya kwance suka iske ta hakanan ta tashi ta anshi Amarya ita dasu Maryama, waya Maryama ta kirashi ta gaya mashi Hakima bata lafiya shiyasa hankalin shi yana kan Hakima kawai dai ganinshi suke, bayan sun dawo shashen su sakin hannun Hikimatu yayi ya wuce room ɗin Hakima bai ce mata komai ba, tsaye tayi tana kallonshi tsaki tayi sannan itama ta shige room ɗin ta itama.

By Jameelah Jameey ✍????

Comment

Share

Like

Vote

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

93&94

Yana shigowa ya isketa ɗaure da towel tana tsane ruwan jikinta da alamu fitowarta kenan daga wanka, ba taji shigowarshi ba sai dai ji tayi anyi hunging ɗinta ajiyar zuciya yai tayi dan ganin ta kawai da yayi yaji natsuwa ta samaishi hankalinshi ya kwanta yarda da ba tun yau ba yake son Hakima, yaa yarda duk abunda yake yi ma Hakima da take A. B. U duk sonta ne sanadi, yana sonta har bai san wani irin so ne yake yi mata dan haka shire yake da duk wanda yake shirin rabashi da rayuwarshi, raɗa ya hau yi mata cikin kunnanta harshenshi ya tura ciki yana cewa, “Jewel ya jikin naki, fatan kin samu lafiya? Dan bansan wajen ya daɗe bai samu sauki ba saboda shine rayuwar Hakim, Ilove with all my heart, kece bugun numfashi na Jewel, kice komai nawa dan Allah ki soni ko ya yake, ki furtaman kalma so yau ɗin nan ba sai gobe ba Jewel.”….. Ya ƙarashe maganar cikin fuskar ban tausayi, dan ji yake kamar ha haɗiye ya huta saboda tsananin sonta da yake fusgishi.

Hakima ita bata san wani kallar farin ciki take ciki ba, ita kanta tasan tana son mijinta kuma tana kishinshi sannan zata gaya mashi kalmar so kafin a rigita dan ta lura Amaryar tashi da rawar kai ta shigo cikin gidan nasu, tana son mijinta kamar ranta bata iya jure rabuwa dashi kona minti ɗaya ne amman ba yanda zatayi dole ta koyi hakuri da juriya na wasu lokaci kafin ya dawo gare ta, shi dai Hakim yana riƙe da yatsan hannunta yana murzasu cikin sauƙin so da kaunarta kana kallonsu a lokacin kasan masoya ne masu shirin sadaukar da rayuwar su a kan ɗayansu, ji yayi ta rungumeshi tana kuka, shima ƙara rungumota yayi yana aikin lailashi sai da tayi kuka mai isarta sannan tace, “nima inasonka mijina ina kaunar ina yi maka so na Amana da babu algunshin a cikinshi kaine rayuwata, masoyina dan Allah inasan kayi mana adalci a zaman nan da zamuyi da wannan baiwar Allah kayi iyakar yinka sai Allah ya dafa mana baki ɗaya.”

Kiss ya fara yi mata yana sama mata albarka sai da ta hanashi dan taga yana san ja mata matsala wajen amarya dan har sha ɗayan dare yayi bai fito ba kuma tun goma ya shigo room ɗinta, ce mashi tayi, “tashi ka shiga wanka masoyina daman na haɗa maka karma ya huce ni kuma na samu na shirya sai in kai ka wajen Amarya nasan tana can tana jiranka.”

Ɓata fuska yayi dan shi ya manta da wata Amarya dan so samu ne da zuwa zaiyi yace ta saida ma Hakima kwanta dan wallahi shi gani ɗaya yayi mata yaji bata yi mashi ba, dire-dire ta fara yi mashi tana cewa, “ni wallahi ka tashi ka shiga wanka kana ɓata lokaci kuma kasan akwai mai jiranka ko.”?…. Ta ƙarasa maganar ta kama hannunshi wai ita a dole tada shi zatayi, fisgota yayi ta faɗo jikinshi kallon juna suke ido cikin ido kamar zasu cinye junansu, sun kusa 6min a haka sannan Hakima tayi janye fuskarta dan bata iya jurar kallon nashi ce mata yayi, “Jewel korata ma kike ko.”?

“My Angle kasan kaine rayuwata ican’t live with out you, but ina san itama ka bata haƙinta dan haka please ka tashi ka shiga wanka nima na shirya kafin ka fito.”

“Naji amman ke dai zakiyi man wankan inba haka ba ba idan zani nan zan kwana muyin amarcinmu wanda bamuyi ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button