GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Tuba muke nema Gimbiya Hakima, godiya muke, nan suka kwashe kaya suka fita dasu waje…

“Lantana fito ya wanku, yanzun, “to godiya nike Gimbiya Hakima, uwar marayu da gajiyaryun Kano..

Nan Ba’ba Bilkisu ta kama yima Gimbiya Hakima tausa, ita kuma lnna Lantana ta na bata labari haka suka kama yi mata har bacci ya kwasheta sannan suka fita waje..

“Wai Lantana yau su A’bu sunga masifara Gimbiya Hakima, “kedai bari Bilkisu ai halin Gimbiya Hakima sai mu kawai zamu iya dashi, yanzun muje muci abincin da tace bata ci, “aiko dai..

“Sannunku Murja, Allah ya baku hakuri, “Hmm! Ai yau Ba’ba Bilkisu munsha wulakanci baki ji kumatuna ba yanda suke yi mani zafi ba..

“Hmm! Ai Murja ki gode ma Allah da hukuncinku ya tsaya iyakar nan, ni daga ta kirani sau uku tasa Sarkin bulala yayi man bulala hamsin da kaini gidan horo..

“Hakane fa Inna Lantana, Allah yakara bamu hakuri, ga abincinku can kuma kuci tunda ita tace bata ci mun cika barkono da mai…

Nan suka ci abinci suna labari, sai da mangarid sanann kowace ta koma bakin aikinta, su kuma su Lantana sune basu bar shashen Gimbiya Hakima ba har sai da tayi bacci sanann suka dawo shashensu na bayi…

By jameelah jameey ✍????

Share and comment pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY
Jameelah jameey ????

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

07&08

“Ni wallahi Hakim kina bani mamaki, “mamaki name kenan Aliyu?

“Kai dai rayuwarka haka kake ba ruwanka kamar ba dan sarki ba.

“Hmmm Aliyu kenan to muye dan ina dan Sarki? Ai duk daya muke a wurin Allah banbancinmu shine wanda yafi bauta mashi..

“Hakane amman duk da haka maganar gaskiya kana bani mamaki ace dan sarki kamar kai dan Sarkin ma na Zaria amman kana rayuwa cikin tallakawa gaskiya ina mamaki ko ni da nike dan waziri ai bani kallar wannan sai dawowarka nike shiga cikin su…

“Kenan da baka shiga cikin tallakawa? “Gaskiya bani shiga ai sai su renani..

“Kaga niko ina shiga cikin tallakawana dan nasan mai suke bukata, sanann nasan maiye rayuwa, kasan ko saboda mai nake yin lectured a A. B. U?

“Aa nidai nayi mamaki ace kamar ka kake wani lectured a wata A. B. U, da daman ina san nayi maka maganar kawai fuskace ban gani ba…

“To na zabe yin lectured saboda nasan wani hali al’ummar kasar Zaria ke ciki, san nasan wani hali tallakawa ke ciki, mai suke bukata ayi masu, mai ake yi masu wanda basu jin dadinshi, sai kuma ina kara yin expressed akan halin mutane..

“Kaji dalili, Alhmdulh naji ance ankusa koma wa hutun Season kaga za’a kawo new inters student kuma ni zan dauki yan Chemistry..

“Gaskiya kaji dadi halinka yana bugerni, wanda bai san halinka ba sai yace baka da tausayi balle imani..

“Amman Hakim maiyasa baka dariya cikin tallakawa? Kuma kana san shiga cikin su dan kaga matsalarsu..

“Dan ina shiga cikin su shine zai sa nayi masu dariya ko sakin fuska sosai, ko ka manta nidain Yarima ne?

“ai naga tunda kana ma’amula dasu sosai ya dace ka zama mai sakin fuska garesu sosai..

“Hmmm! Ai ni kai kasani haka Allah ya hallicine ban cika magana ba, ko da ko ina gaban Gimbiya Fulani, dan haka ba laifina bane yin Allah ne..

Hmmmm! YARIMA HAKIM kenan, dan sarkin Zaria matashi maiji da samartaka ga kuma haiba da kyau da jinin sarauta dake yawo jikinshi..

Yarima Hakim, missikiline na ajin karshe dan bada kowa yake magana ba, inka ga maganar shi to shida mutun uku ne, daga Fulani mahaifiyarshi kenan sai kuma Maimartaba sannan abokinshi tun na yarinta Aliyu haidar, da wannan mutanan biyu suke ganin maganar shi mai tsawo, ko kannanshi Gimbiya Maryama da Gimbiya Sadiya basu ganin maganar shi balle dariyarshi abunda ke hadasu shine kawai su gaisa, ba wai wulakanci ke sashi haka ba Aa halinshi daga Allah ne wannan kenan….


Washe gari tun da asuba Kuyangan Gimbiya Hakima suka fara aiki, kamar yanda ta bukata..

“Ladi, “Naam Larai..

“A gaskiya Ladi muna bautuwa a gidan nan, muna yi ma Gimbiya Hakima bauta amman bata gani, yanzun ji yanda muke ta wanann wahalar tun da asuba muke abu daya yanzun har bakwai tayi kuma tace kafin karfe takwas mun gama komai..

“To ya zamuyi Larai tunda munfito a bayi? Ai hakuri ya zama dolenmu, kuma ai daga wannan mopping din mugama sai mu jira fitowarta ta bamu umirnin mu tafiyarmu..

“Aiko dai Ladi, ai mu mungode Allah da ta fidda mu a madafa da Jiya mu zata wanka ma mari taci mana mutunci kamar yanda ta saba…

“Eh mana, da man su A’bu basu cika haduwa da itaba tunda gyaran gida kawai suke suna gamawa kuma inta gani zasu kama gabansu ba kamar muba dasu Inna Lantana da ba mu rabuwa sai dare, kinga ai munfisu shan wahalarta..

“Sosai ma, su daga Jiya kawai fa har sun fara koke-koke sun bani su ya zasuyi basu iyawa da aikin madafa, shine nace masu muma haka muka sha wuya har Allah yasa ta chanza mana aiki…

“Ku ina fatan kun gama ga maigirma Gimbiya Hakima nan fitowa, “mun gama yanzun muka gama, sai yanzun kenan Allah yayi zata fito yar-mulkin!

“Ke Larai ba ruwa, ki gyara kalamanki yanzun indan tajiki kiyi ya?

“Sai tasa a hukuntani, kuma hukunci na nawa ne bangani ba indai na Gimbiya Hakima ne..

“Nidai ba ruwana kunga tafiya wajen masu madafa naga har yanzun basu fara fito da abincin ba ga shi har Gimbiya Hakima ta tashi na niyar fitowa ma…

“To Ba’ba Bilkisu a dawo lafiya, “Allah yasa Ladi ni na barku lafiya..

“Ku yan madafa Ina fatan kungama dai ko?

“Eh mun gama yanzun muke shirin kai abincin wajen cin shi..

“To barkan ku, kutaso mu tafi kawo na taya ku dauka A’bu..

“To Ba’ba Bilkisu mungode, ni tunda dazun rabon da naga Inna Lantana, “kin san aikin Gimbiya Hakima ba karewa yake ba, tana can ta shafa mata mai..

“Allah sarki Inna Lantana, duk dai sannunmu da bauta, “yauwa kunga har mun iso, nan suka jera abinci a bisa dining table bayan duk kowace ta gama abunda take suka zauna zaman jiran fitowar Gimbiya Hakima…

Gimbiya Hakima itace bata fito ba sai karfe goma, bayan su kuma tun karfe takwas kowace ta gama aikinta…

“Takawarki lafiya yar’masu gida, Gimbiya Hakima uwar marayu, tar sarki jikar sarki..

“Bilkisu! “Naam Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima anfito lafiya?

Gimbiya Hakima bata ansa ba sai da tayi kusan ten minutes sannan tace “Lau, Ina fatan kowa ya gama aikin shi?

“Eh Alhmdulh duk sungama umirnin Gimbiya kawai suke jira ta aiwatar a garesu..

Sai da ta mula tasha iska sannan ta tashi Bilkisu da Lantana suna biye da ita suka duba masu shara, sai dai suka gama zagaye sannan suka dawo ta zauna wajen abinci..

“Ace ma masu Shara su tafi su ban waje, “angama Uwargijiyata, nan Ba’ba Bilkisu ta fito main parlour inda suke tsugune tace..

“Ku su Larai, Gimbiya Hakima tace ku tashi ku tafi aikin ku yayi kyau, “godiya muke, nan suka tashi suka tafi suna Alhmdala cikin zuciyarsu sun rabu da Gimbiya Hakima lafiya ba tare da ta ci masu mutunci ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button