GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Tare fa kace Angle? Kuma ni zan maka wanka.”?

“Uhm, idan bakiyi kisa a ranki nan zan kwana.”yana faɗin haka ya yi hanyar bathroom kasancewar zamanan da sukayi da shi tasan halinshi ta bi bayan shi suka shiga bathroom , koda ta shiga kulle idonta tayi wai ita bazata kalleshi a haka ba ba kaya daman ai haka ya taɓa yi mata ya cire towel ɗin shi a gabanta yanzu kuma rashin Kunyar tayi gaba wai ita zatayi ma Hakim wanka, ji tayi an saka ta cikin bahun wanka daga ita har towel ɗin shima ya shiga cikin firgigi tayi ta bude idonta tana ganin ikon Allah, saurin rungumeshi tayi ita wai karda ya kallan mata boos, bai damu ba ya fara yi mata wanka ƙyaleshi tayi ya gama yi mata sannan itama ya matsa mata sai da ta yi mashi dan yace bai sake wanka shi ɗaya mudun yana ɗakinta bayan sun fito suka shirya a gurguje sannan ta suka fito parlour Hakim ya zauna sannan Hakima ta wuce ɗakin Hikimatu zatayi mata magana ta fito Hakim yana san magana dasu.

Da Sallama Hakima ta shiga duk da Hikimat bata ansa mata sallamar ba, cewa tayi, “sannu Amaryarmu, na samaiki lafiya.”?

Wani kallon banza Hikimatu tayi ma Hakima sannan ta matsar dan daman cike take fam fashewa ne kawai bata kai dayi ba????, sannna tace ma Hakima, “da ban lafiya ai a gadon asibiti zaki iskeni ko kuma ina kwance ina saman ruwa, kuma kice ma shi mijin naki bani fitowa, dan haka ina mai ja maki kunne daga yau karki sake ki sake shigo man room banza maiyar miji.”

Duk da Hakima taji haushin kalman da Hikimatu ta gaya mata amman sai ta ɗaure kuma suke da laifi dan Hakim ya daɗe a room ɗin ta, bayan yasan Amarya na jiranshi cewa tayi, “Allah ya baki hakuri Amaryarmu ni zan wuce.”

“A gayas dagin tsiya.”… Waigowa Hakima tayi ta kalleta sai ta girgiza kai tayi murmushin ta wuce, wai ita ce dagin tsiya tayi mamakin yanda ta kyale Hikimatu har haka amman ita tasan da da yanzun ba ɗaya ba da dane Hikimatu ta gaya mata wannan maganar da basu kwashi yan kallo da ita ba, amman ita yanzun bata iya kallar rayuwar dan ta fahimci duk masu kallar rayuwar ganewa ne kawai basuyi ba amman rayuwar dabbobi suke bata mutane ba, dan haka ita yanzun bata iya faɗa dab faɗa karnuka ke yinshi ba dai mutane ba.

Haka Hakima ta shi iso parlour ta samu waje ta zauna tana kallon shihabin nata, ce mata yayi, “ina ita Hikimatun na ganki ke ɗaya Jewel.”?

Shagwaɓe mashi fuskar tayi tana kisisina sannan ta bude baki tace, “tace gata nan zuwa Angle.”ta ƙarashe cikin yanga, ai oga Hakim shagala yayi da kallonta dan sai da yayi suma ta wucen gadi sannan ya dawo, tashi yayi daga kujerar da yake ya koma wanda ta zauna ka mota yayi yana wasa da yatsanta sannnan yace, “idan kina yi man kallar wannnan salon naki mantawa nike dani waye Jewel ba tun yau ba, Jewel keɗin ta daban ce, kuma ke ɗin tawace bata kowa ba, mutuwace kawai zata rabamu, kuma ina fatan mu mutu tare Jewel idan ba hali ina rokan Allah na rigaki mutuwa, Allah na tuba karnayi sabo da nace ban iya jurar ganin gawarki a shinfiɗe kasa baki numfashi Jewel nasan nima binki zanyi a ranar, shiyasa nike rokan Allah yasa mu mutu tare masoyiyata.”

Kamo kanshi tayi suka haɗa goshi wajen ɗaya suna shakwar numfashin juna sannan tace, “Angle ban taman ka mutu kabarni idan ka mutu kabarni ya zanyi da rayuwata? Nidai Allah yasa sai mun haihu munga jikokinmu sanann mu mutu, amman dan Allah daga yau kabar yi man kallar wannan maganar.”… Ta ƙarasa maganar tana hawaye, lashe hawayen yayi duka a bisa fuskarta sannan yace, “Sorry Jewel na daina, amman kisani mutuwa ta zama dole sai dai muyi fatan cika da kyau da imani.”

“Amin.”tace sannan tace, “Angle dare keyi fa ka wuce wajen Amarya basai mun zauna ba insha Allah gobe sai mu zauna ko.”?

“Aa bari na tashi dai na kirata.”… Abunda su Hakim basu sani ba duk abunda sukayi a parlour a kan idon Hikimatu sukayi shi, tana ganin Hakim ya tashi tayi sauri ta koma room ɗin ta tana goge hawaye tana guɗirinma kanta ko ta wani hali sai ta raba Hakim da Hakima dan ta lura idan Hakima nanan to Hakim ba wani rawar kai zaiyi kanta ba, shigowa yayi yace, “wai mai kika tsaya yi ne Hikimatu muna jiranki fa dare yayi.”?

“Yi hakuri mijina yanzun nike shirin fitowa, “ok let go.”tare suka fito parlourn suka zauna a kujera ɗaya sai wani shige ma Hakim take a jiki shi kuma yana dan ja baya dan wani bashi bashi yaji ta nayi duk abunda suke Hakima tana kallonsu sai ta nuna bata san anayi ba, dan take mulkin da sarautar ya taso mata, addu’a Hakim ya bude taron sanann ya fara magana, “Alhmdulillahi Allah abun godiya da ya bamu rai da lafiya har mukaga wannan ranar, ke Hakima kece babba dan haka inason ki rige girmanki ki zauna lafiya ke da ƙanwarki, ke kuma Hikimatu kice ƙarama inasan kiyi mata biyaiya ku had’a kanku ku zauna lafiya karku biye ma yan tashi zaune, ina fatan zaku zamo masu biyaiya a gareni.”

“Insha Allah zaka samaimu masu bin umirnin ka a kowani lokaci.”cewar Hakima, itadai Hikimatu bata ce komai ba sai fusgar iska dakeyi, cewa yayi, “masha Allah , sannan maganar raba kwana uwar’gida ya kika ga za’ayi.”?

“Aa Amarya ta faɗi yanda tace haka za’ayi.”…. Koda Hikimatu taji ance ta faɗi sai taji farin ciki dan ta lura ji suke kamar su cinye junansu, dan haka tasan abunda zatayi masu dan daman da shirin ta tazo dan haka sai tace, “nidai a gani nina kwana ɗaya yayi ko Yaya.”?… Ta jefama Hakima question ɗin tana kashe mata ido, Hakima tasan san zuciya yasa Hikimatu sa masu kwana ɗaya bayan tasan ko wani gida idan akwai kishiya kwana biyu akeyi ma ko wace idan kwananta ya zagayo amman su naso daban yake da na kingin, Hakim addu’a yake Allah yasa Hakima tace yayi kaɗan dan ba zai iya juran kwana ɗaya kawai zaiji dumin Jewel ɗin shi , amman sai yaji Hakima tace, “eh haka yayi kanwata, Allah ya bamu ikon yin biyaiya ga mijin mu, “Amin tace tana shi’umin murmushi dan gani take tana gama amarci ya koma ɗakin Hakima zai dai dawo nata tunda kwana ɗaya ne ba biyu ba ko hudu, bayan sun gama Hakima ta rakasu har room ɗin shi sannan ta dawo nata duk da Hakim yaso ya rakota amman tace ya barshi itako ta hutar dashi.

Haka ta kwanta ta gama juyi danji take kamar ta fasa ihu, tashi tayi ta ɗauro alwallah ta fara sallah, bayan ta gama sallah ta fara karatun al’quri’ani mai girma.

Bangaren Amarya Hikimatu ko taji maza dan Hakim ba tausaya mata yayi ba balle daman yanajin haushinta ta sa masu kwana ɗaya ko wani ɗaki shiyasa ya fidda tausayinta jiya ya murjeta sosai yanda zataji abun ya fita ranta, kawai dan haka yayi ma’amila da ita ba dan dadi ba dan wani wari ma take wanda shi baisan ina ta samo shi ba, duk da sau daya yayi sex da Hakima amman Hakima tafi Hikimatu komai harda dadi ma dan duk wani abu da ake bukata a jikin mace, kuma Hakima tafi Hikimatu budurci dan cikarkar budurwa ya samu Hakima, amman ita Hikimatu bai san wani layi zai saba wanda ta kawo budurci ko akasin haka shi dai bai sani ba, bayan ya gama yi mata abunda ya gadama ya sauka samanta ya shiga wanka, wankan tsarki yayi sannan ya ɗauro alwallah ta fara sallah shima.

By Jameelah Jameey ✍????

Share

Comment

Vote

Like

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button