GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hakim ko yau ya sheda ya dawo dakin Hakima, dan yau Hakima ta sashi farin ciki sosai, bayan sun gama suka tashi sukayo wanka suka fara sallahr dare sai sukayi raka’atul fijir sannan Hakim yayi shirin massallaci ya biya room ɗin Hikimatu ya tada ta shima ya wuce sallah, bayan ya dawo sai da ya ƙara neman Hakima sannan yayi bacci koda gari ya fara haske tashi ta samu tayi wanka tayi ta shirya sannan ta wuce kitchen ta ɗaura sauwa, bayan ta gama sauwa ta dawo ta tada Hakim bacci yake yaji harshe yana yi mashi yawo cikin kunne tana fura mashi iskan bakinta tana cewa, “Angle wakeup tashi muyi wanka muje muyi breakfast.”

Janyo yayi yana mata kallon so dan ji yake kamar ya cinye ya huta, tashi yayi sukayi wanka suka shirya suka fito, lokacin da suka fito Hikimatu ma tana fitowa kamar buzurwar kura dan ko poder bata shafa ba ta fito haka ita ba wani kyaun kirki ba amman ta fito haka kamar wanda akayi ma baki, dan Hikimatu ƙazamaci sosai Hakim ma ya lura da haka, shiyasa yasama kanshi bai iya cin abin hannun Hikimatu, shi dan ba yanda zaiyi yake kusantar Hikimatu dan wani wari take marar dadin shaƙa.

(Hattara yan lesbians wallahi ku tuba ku koma ga Allah, wallahi duk mai lesbians idan ta zauna kusa dake sai kinji tana wari, to maiye amfanin neman jinshinki? Bayan kin san yin hakan babban zunubi ne, Allah yasa mudace Amin)

Bayan sun gama breakfast ɗin suka tashi, shi dai Hakim wajen aiki ya wuce, ita kuma Hakima shashen Gimbiya Fulani ta wuce dan ba ita zatayi abincin rana da dare ba Hikimatu zatayi shi, koda Hikimatu taga ba kowa gidan sai ita daya ta samu damar shiga kitchen tayi masu wata yagwalerlen taliya marar dadi ta zuba wannan maganin ta jera a dining tana gama jerawa Gimbiya Zulaha na shigowa da cooler din Abinci wai ta kawo mata abunka da kura uwar haɗama ga abincin da ta dafa amman sai da ta amshi na Gimbiya Zulaha, a gaban Gimbiya Zulaha ta zuba abincin taci mai isarsa dan sai da taji ba waje sannan ta tashi aiko Gimbiya Zulaha ta tafi tana farinciki da bukatar ta biya, Hakim na dawo shashen Fulani ya wuce bai san Hakima na can ba haɗawa sukayi abinci sukaci tare sannan suka dawo koda suka dawo suka wuto dining suna duba abincin da Hikimatu tayi sukace sun koshi dan ko sunci abinci sai dai aka ba bayi suka zubda dan ba mai iya cin abincin nan saboda rashin kyaun shi.

Raka Hakima yayi har room ɗin ta addu’a ya tofa mata sannan ya fita yana jin kamar ya dawo.

Koda yaje room ɗin shi ya tadda, Hikimatu har taje tana jiranshi wanka ya shiga ya fito ya kwanta, amman saboda da rashin class ɗin Hikimatu sai da ta nemaishi yace mata yau bai iya yi mata komai dan baida lafiya duk nacinta sai dai kyaleshi tayi ta kwanta tana tunanin Aziza dan ji take kamar tayi hauka dan tana bukatar ma taimaki,lura da yanayin da take ciki sai taba Hakim tausayi nan ya kusanceta ba dan dadi ba sai dan kawai ya fita hakinta, shi yanzun ma yake jin dadi ta dace kwana ɗaya dan bai iya yin kwanaki ba tare da yaji dumin Jewel ɗin shi ba.

Some days letter

Abubuwa da ma sun faru tsakanin Gimbiya Hakima da Gimbiya Hikimatu da kuma Yarima Hakim dan wani kallar kishi suke wanda wata rana yana ba Hakima tsoro tash kama Hikimatu tana yi masu barbaɗe cikin abinci daman saukinta Hakim baya cin abincin Hikimatu, taraiyar Hikimatu da Aziza abun gaba yake dan Aziza yanzun har gida take biyo Hikimatu suna shige ayarsu.

Bangaren su Gimbiya Zulaha kuwa suna ta zuba ido dan sauran sati shekara biyar ta cika su ga gawar Hakim, dan ko Gimbiya Zulaha ta fara shirin yanda zasu yi shagalin mutuwar Hakim da Sarki Abdulmalak.

Bangaren Gimbiya Kilishi itama tana nan tana bin boka yana yi mata wanka tana jiran sati ya cika taga gawar Hakim da Hamad….. Ita kuwa Gimbiya Fulani Kubrah bata damu da abunda akeyi ba duk da ta lura da Gimbiya Hikimatu halinsu ɗaya dasu Gimbiya Zulaha, shiyasa tasa ido akan Hakima tana bata kula ta musanman tana bata addu’oi tana sha tana wanka dasu sannan kuma tana ƙara ja mata kunne akan ta riƙe Allah, dan Allah yana tare da mai gaskiya.

Yau tunda Hakima ta tashi bata lafiya gashi Hakim ba ɗakinta ya kwana ba, koda yazo wajenta da safe bata nuna mashi bata lafiya ba dan tasan tana gaya mashi zaice baya zuwa aiki dan haka bata gaya mashi ba, sai bayan Tafiyarshi ciwon ya tashi sosai sanyi takeji duk da ta kashe duk wata na’auran sanyaya ɗaki, amman hakan baisa tta daina jin sanyi ba, koda Hakim ya dawo ya tadda bata lafiya ɗaukarta yayi ya kaita hospital ɗin Aliyu test Aliyu yayi mata koda result ya fito sai ga Hakima tana ɗauke da ƙaramin ciki dan wata hudu, murna wajen Hakim ba’a magana koda suka dawo gida shashen Fulani suka wuce suka gaya mata, nan Fulani tace bata ci su gaya ma kowa ba koda Hikimatu ce, haka ko akayi ba wanda suka gaya mawa suka cigaba da rainon cikinsu cikin sirin.

Yau tunda suka tashi sukaji Sarki Abdulmalak yana shela gidajen redio da television da masu shele yana gaiyatar ko wa gobe a fada zaiyi wani babban taro, ba wanda yasan da taron sai dai sukaji ana shele a cikin masarauta haka kuma a gidajen radio, koda Gimbiya Zulaha ta tambayeshi ce mata yayi idan gobe tayi sun gani,Rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya gobe shekara biyar take cika, gobe su Gimbiya Zulaha zasuga gawar Hakim…..

To FAN’S gobe ne fa????…. Shin gobe su Gimbiya Zulaha zasuga gawar Hakim kamar yanda suke faɗi.????

…… Gashi gobe kuma Sarki Abdulmalak yana neman duk wani bawa da hakimai da kuma iyalanshi a fada zaiyi wani abu wanda ba wanda ya sanshi sai dai gobe zasu gani????.

……… Komai ye wannan abun????

Wannan ansar ku jirata a page ɗin gobe????????????????????????????????

By Jameelah Jameey ✍????

Share

Comment

Vote

Like

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

97&98

Tunda safe Hakima ta tashi ta fara hidimar gabanta tunda ba ita zatayi break ba Hikimatu ce tunda room ɗinta Hakim ya kwana, daman ita ba komai take ci ba yanzun duk da cikin nata ya kai wata biyar yanzun bata da girman ciki shiyasa har yanzun ba wanda ya gane tana da ciki kuma bata shiga sabgar kowa, duk da fitinar da Hikimatu take janta, amman bata da lokacinta kuma komai Hikimatu zatayi mata bata taɓai gaya ma Hakim ba, amman ita Hikimatu komai Hakima tayi mata sai ta gaya ma Hakim, Hakim har mamaki yake dan baki ɗaya halin Hikimatu da Hakima ba ɗaya bane.

Bayan Hakim ya tashi daga bisa abin sallah azkar yayi dan yau tunda ya dawo sallahr asuba yaji bai iya komawa bacci ya cigaba da azkar ɗinshi yana gamawa yayi wanka ya shirya ya fita ya bar Hikimatu tana baccin asara, bacci take bata damu da ta tashi tayi masu break ba, daman shi tunda yake da Hikimatu bai taɓa shan koda ruwan hannun Hikimatu ba dan shi harga Allah ƙyamarta yake, bayan ya gama shiryawa ya tafi yaga ya sanyin idanuyanshi ta tashi ita da Babynshi, yana zuwa room ɗin Hakima suka cin karo da juna, ja da baya tayi sannan tayi hug ɗinshi tana cewa, “ina kwana mijina.”?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button