GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ƙara rungume ta yayi sannan yace, “lafiya lau My Jewel ya kuka kwana keda Babyn na.”?….. “Uhmm, abunda jiya Babyn ma hanani bacci yayi, sai dai na tashi nai ta sallah fa.”…. Ta ƙarasa maganar cikin yanga da shagwaɓa rungumeta ya ƙarayi sannan yace, “sorry Jewel ban sani ba ai da nazo munyi sallar tare ko.”?… “Aa ai inasan kayi bacci ka huta, kuma Hikimatu ba bari zatayi ba, ni yanzun bansan tashin hankali.”… “Ai ko da na sani da sai nazo munyi sallahr tare, amman ai yau zamuyi ko.”?…. “Eh insha Allah, Angle nifa hankalina tashe yake, bansan taron mai Abba zaiyi ba yau naji Baffah yace zasuzo dan suna hanya ma, Allah yasa ba wata matar zai sake baka ba.”…. Lakusar mata hanci yayi sannan yace, “Jewel bai dai tsoron kishiya kike ba.”?…. “Aa Angle ban tsoron kishiya amman kasani ina sonka ina kishinka.”….. “Nima ina sonki ina kishinki, insha Allah daga Hikimatu ba zan sake aure ba, kuma nasan Abba bai ƙara yi man aure tunda ga su Hamad nan, yanzun mu tafi shashen Fulani muyi breakfast kafin Yakumbo su iso ko.”?…. “To shikenan masoyina ilove with all my heart.”…. Love you too Jewel mu tafi karda muyi leting.”…. “Ok let go.”

Haka suka tafi shashen Fulani bayan sun gaidata suka fara yin breakfast.


“Gimbiya wai taron mai Abba zai yi kinga yanda akeyi ma wajen fada decoration kuwa.”?

“Wallahi ko Hamad bansan taron mai zaiyi ba, ni ba wannan ne gabana ba har yanzun banji anfasa ihu ba Hakim ya mutu kuma yau shekara biyar take cika amman shiru nike ji Hamad.”

“Wai daman yau shekara biyar take ciki? Kuma Hakim zai mutu Hakima ta zama tawa.”?

“Haka kaji nace amman shiru ka kakeji kamar mai, amman ila zuwa anjima zai mutun ko.”?

“Nima haka nike tunani Gimbiya, mu gama cin abincin muje wajen taron da nan naga manyan baƙin duk sun hallara harda sirikina ma Sarki Abdulhadi duk naga sun zo amman iyalanshi suna shashen Gimbiya Fulani.”

Hmmm! “Daman nasan ba Yakumbo bazata shigo sheshena ba, balle Fulani Aisha, amman ai yau Hakim yake mutuwa kuma gobe ubanku shima zai mutu jibi kuma a baka sarkin masarautar Zaria, gata kuma zan maida Fulani Kubrah baiwata, sai Gimbiya Fulani Kubrah tayi kuka da idanunwanta, sai idanunwanta sun tsiyaye saboda da kuka daga karshe kuma bakin ciki ya kasheta tana ganin ka ɗauro Hakima ta zama taka.”

Ikon Allah kunji Gimbiya Zulaha da wata magana, hmmm kudai muje zuwa muga wannan wani taro ne Sarki Abdulmalak ya haɗa wanda ba wanda ya san ni????.


“Hasiya.”

“Naam Allah ya taimaki Gimbiya Kilishi, Allah ya huci zuciyar Gimbiya Kilishi lafiya naganki cikin wannan yanayin? Banga kina niyar fita ba ma gashi wajen taro ya cika da bul’adama.”

“Hasiya ni wannan bai gabana, har yanzun baki ji kuka ya fito daga sheshen Fulani ko kuma Zulaha.”?

“Allah ya taimakeki banji kukan komai ba, sai busar da sarkin busa suke busawa da kuma sautin kiɗin da sarkin makaɗa yake bugawa, dan gaskiya daga gani wannan babban taro ne za’ayi na musamn… Tas! Tas! Tas!, ji kake Gimbiya Kilishi ta wanke Hasiya da marika guda uku lafiyaiyu dan ko maganar ma kasa idata Hasiya tayi ta dafe kunci tana kallon Gimbiya Kilishi da mamaki dan ita bata san abunda tayi ma Kilishi ba.

“Ke har kin isa, ina tambayarki kina yiman wani shiruntunki na banza da wofi, na tambayeki busa ko kiɗi? Amman zaki isheni da wani busa ta kiɗi, maza tashi ki ban waje ko nayi ball dake sakarar banza sakarar wofi.”

Haka Hasiya ta tafi tana sosa kunci dan mararin ya shige ta sosa.

NIKO NACE ALLAH YA KARA DAMAN DUK WANI MUNAFIKI MAGANINSHI KENAN, HASIYA KAƊAN KIKA GANI????

Tunda Hasiya ta tafi Kilishi take zagaya ɗaki tana mamakin yanda har yanzun bataji ankirata ba tazo Hakim da Hamad sun mutu, ba abun yana bata mamaki, amman sai tayi tunani ila da anjima zasu mutu wannan tunanin yasa taji sanyi ranta ta tashi ta tafi wajen taro kunyanganta suna take mata baya.


Bacci take taji ya faska mata bugu a baya ana cewa, “mai zangani haka? Hikimatu baccin mai kike har haka baki tashi an barki sheshe ki ɗaya kina baccin asara.”

Tashi tayi tana murtsuka idanu, tana kallon Gimbiya Binta dake gabanta tana mata wani kallo, tashi tayi tace, “laaa Mama yaushe kukazo.”?

“Bansani ba, abunda na tambayeki kenan? Nace daman haka kike wanann sakarcin gidan mijinki, nazo bakowa sai ɗaya gashi kuma har ana ta taharamar fara taron mu munsa ma mun makara amman Allah yasa ba mu makaraba ke ko shirya wa ma baki yi ba.”

“Haba Mama ni ai nasa bandamu ake wannan taron shiyasa ban tashi ba, kuma ko na tashi mak zanyi na gaya maki Hakim baya cin abincina daga na wacer munafikar matarshi sai kuma na uwarshi su kaɗai yake ci shiyasa yanzun na bar bama kaina wahalar tashi dafa mashi wani abinci, amman yanzun zan fito wanka Mama.”

“Sai kiyi sauri ki fito wankan inasan nayi magana dake kafin a fara taron, “to ni na shga.”

Tana shiga ta watsa ma jikinta ruwa ta fito, dan ni banzance tayi wanka ba tunda tana shiga tana fitowa, kuma ko sallahr asuba batayi ba amman kawai tana wanka ta fara shiryawa, bayan ta gama ta haɗa complex tasha sannan tace “Mama nagama ina sauraranki.”

“Hikimt kikace har yanzun Hakim baicin abincinki.”?

“Wallahi ko Mama, kona dafa bayaci.”

“Kiceman duk asirin dani yi mashi baya tasiri kanshi.”?

“Mama na fahimci Hakim asiri baya kamashi, saboda danaga baya cin abinci na sai nace ma boka yabar bani aikin da za’a samashi cikin abinci dan ba ci yake ba, amman duk da haka banga wani sauyi ba dan ko kusantata Hakim baisan yi sai na matsa mashi sannan.”

Hahahahaha! “Karki damu Hikimatu yaro baisan wuta ba sai ya taka, damu Hakima take zance, ai daman boka yace man komai muke Hakima take asiri tana karyashi amman ga wannan maganin zakiyi. Matsi dashi duk sanda jinin haila yazo maki kinayi matsi komai ya wuce Haka boka yace.”

“To shikenan Mama.”

“Amman yace idan kuma ki ka yarda kikayi ma’amala da wata mace maganin zai kare dan haka sai ki hakura da neman mata, dan nasan halinki yana nan na bin mata, idan baki koshi da Hakim ki sawo wannan abun na zamani mana kiyi amfani dashi amman sai kin yi hakuri da bin mace.”

“Amman… “Yi man shiru mutuniyar banza, tashi mu tafi karda mu makara.”

Haka suka tafi amman Hikimatu ta aiyanama kanta bata hakura da Azizarta dan tanajin dadi ma’amala da Aziza.


Suna cikin yin breakfast, su Gimbiya Yakumbo suka shigo bayan sun tarbesu suka zauna suka ida breakfast ɗin tare, sannan suka danyi firar yaushe gamo sannan suka ɗunguma suka tafi wajen taro.

Koda suka isa wajen taron sai da tsikar jikin Hakima ta tashi saboda mutanan da sukazo wajen baka ganin komai sai kwawuna, riƙe hannunta Hakim yayi sosai dan ya lura da Hakima ta tsorata da Mutanan wajen, yakan yi mamakin yanda Hakima take da tsoro har haka, dan shi a tunaninshi jarumace sosai.

Sarki Abdulmalak da Sarki Abdulhadi sai Sarki Abubakar sune bisa hight table ko wane matanshi a gefensu, daga ƙasa kuma Yarima Hakim ne dasu Gimbiya Hakima a gefensu, sai ƙasansu kuma Yarima Hamad ne da Yarima Humad sai Aliyu, suma daga ƙasansu Gimbiya Maryamace da Gimbiya Sadiya da Maryam, suma daga ƙasansu Wazirine da matanshi, sai sauran yan fada da kuma yan siyasa da manyan baƙi.

Tashi Sarki Abdulmalak yayi ya fara magana kamar haka, “Assalama Alaikun, ina godiya ga manyan baƙi da duk wani wannan ya hallaci wannan taro mai albarka taron da rabon da ayi shi yau kimanin shekara 40 kenan sai yau Allah ya yarda shekara ta zayo.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button