GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiru kowa yayi yana jiran yaga ikon Allah tunda Gimbiya Zulaha taji Sarki Abdulmalak yace shekara 40 rabon da ayi kalar taron sai da gabanta ya faɗi amman sai ta dake tana kallon ikon Allah kamar yanda sauran keyi.
Cigaba da cewa yayi, ” Alhmdulillah, Allah na gode maka da kanuna man wanann ranar da ni Abdulmalak Muhammad zani yi murabus daga wannan mulkin danike sama zan ba ɗ’ana Hakim ya cigaba daga ida na tsaya, wannan abun babban abun farin cikine daga gareni.”
Hayaniya ce ta fara tashi wajen dan mutune sunga kokarin Sarki Abdulmalak suna jingina ma dantaku irin tashi, dan a wanann zamanin ba kowani sarki bane zaiyi murabus ya ba ɗanshi ba tare da yaji komai ba, tunda Gimbiya Zulaha taji Sarki yace yayi marabus ya ba Hakim mulki zufa ta jiƙeta sarkab haka ma Gimbiya Kilishi, shi ko Hakim tunda yaji wai yau shi a za’a ɗaura ma nauyi bisa kanshi ya fara kuka kamar ƙaramin yaro dan ji yake kamar ya tashi yace ma Abbanshi baya so wannan mulkin da yake niyar ɗauramai ya ba Hamad shi ko dai ya yafe, tunda Gimbiya Hakima da yanayin da mijinta ya shiga ta kama hannunta yana murzawa tana yi mashi nuni da yayi shiru, itako Gimbiya Hikimatu wata murnace ta kamata za’aba Hakim Mulki, Yanzun zata fara nuna wacece ita daman tana maganin da zatayi amfani dashi wanda Mamarta ta kawo mata bata damu da yanayin da mijin nata ya shiga ba, suna cikin wannan hali fadawa suka zo suka tafi da Hakim bisa munbari suna ta yi mashi kirari nan sarkin fada ya tashi ya fara naɗa Hakim mulki, ana naɗa mashi yana kuka dan yana tsoran masifar da ke cikin mulki, yana gama naɗashi kowa da kowa ya miƙe ya fara yi miƙa gaisuwa ga sabon sarkin su wato SARKI HAKIM ABDULMALAK MUHAMMAD, suna gamawa kowa ya tashi zai gama gabanshi ji mutane suke tum Gimbiya Zulaha ta yanke jiki ta faɗi sumaimiya, da gudu Hakim da Hamad sukayi kanta suna kiran “Gimbiya.”… Abun ya ba kowa mamaki yanda Hakim yake gudu dan chito da ran Gimbiya Zulaha, ɗaukarta yayi nisa kafaɗarshi yayi hanyar shashenta da ita dan Hamad kasa komai yayi sai aikin kuka yake dan bai san ya zaiyi ba idan ya rasa mahaifiyarshi da mai zaiji da rasa mulki da yayi ko kuwa rasa Hakima da yayi ko kuma rasha mahaifiyarshi?, haka suka ɗunguma su dukansu suka nufa shashen Gimbiya Zulaha, ita kuma Gimbiya Kilishi bata damu da yanayin da Gimbiya Zulaha ta shiga ba ta wuce wajen Turmursturs ranta ɓace.
????????????????????????????????????????????????????????????????Jama’a kunga yanda Shekara biyar ta yi dasu Gimbiya Zulaha????????????????????????????????????????.
????????????????????????????????
Komai Gimbiya Kilishi taje tayi ma Turmursturs ????????????????????????????????????????????????????????????????
Shin Gimbiya Hikimatu zata hakura da Aziza tayi aiki da maganin nan yanda ya dace????????????????????????????
Wai Allah na yau nagaji sosai wlh ????????
Much love my dear Fan❣️????
Masoyana duk mai bukatar karanta IZZAH KO MULKI yayi ma wannan num mgna 08160508316
By Jameelah jameey ✍????
Share
Comment
Vote
Like
Please
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
*M. W. A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
STORY AND WRITING BY
_Jameelah jameey ????_
*(Yar mutan kankia????????)*
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI
Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.
NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????
99&100
Tana zuwa ta iske Turmusturs kwance rai hannu ga Allah cewa take, “kan bala’i nan wallahi ko mutuwa kayi sai ka tashi ka gaya man abun mai ya hana Hakik da Hamad mutuwa a yau ɗin nan sai dai naga na naɗa Hakim mulki bayan kace mutuwa zaiyi.”?
Duk Turmusturs baijin dadin jikinshi hakan bai hanashi tashi ba yayi ma Kilishi bayani daman yana jiran zuwansu ita ko Zulaha yaji dadi da Kilishi tazo dan yafi bukatar ganinta, dariya ya farayi, sannan yace, ” Kilishi daman wannan ranar nike jira kuma ga tazo, hahahhahahah! Sakara kawai kinsa duk abunda ni Turmusturs nike gaya maku gaskiya ne.”?
“Ikon haka ne kun zama wawaye keda Zulaha, bari na baka labari dani Turmusturs baban bokane, amman daga baya nadaina bokanci tuni ina dai nan zaune ina cin kudin jahilai irinku wanda basu dogara ga Allah ba suka dogara da wani wanda bai iya yi maku maganin komai inba ba Allah ba, ina sane nace ku bari sai shekara biyar ta cika nasan duk masifa kafin shekara biyar Hakim yayi aure harma ya haihu idan da rabon haihuwar wayau nai ta yi maku na hanaku zuwa wajen ko wani boka kuka dogara dani dan ceton rayuwar bawan Allahn nan Hakim, Hakim baiyi maku komai ba kun sashi gaba saboda da neman duniya bayan kun manta barin duniyar zakuyi baki ɗaya ku koma ga Allah, amman idanuwanku sun kulle Kilishi.”
“Ina mai baki shawara kidaina duk abunda kike yi dan nima na daina harta zina duk na tuba na daina na koma ga Allah, to kema Kilishi ki koma dan shine tsaranki a gobe ƙiyama, kuma abu na biyu da zan gaya maki shine ki fara zuwa asibiti ansar maganin cutar ƙanjamau dan likitoci sun tabbatar man da ina ɗauke da ita sama da shekara 50 itace sillar kwantar dani dakika gan ni nan, ni dai abunda zan gaya maki kenan Kilishi, nima nan ƙarshe na nike jira kuma ban gajiya da neman yafiyar ubangijinmu Allah domin shi Allah gafurun rahim ne, dan haka bani da gurin komai sai na cikawa da imani kema ina maki fatan alkhari, kuma mu yafi… Gimbiya Kilishi ta cakama Turmusturs wuƙa a ciki, sake fiddo wukar tayi tfa sake caka mashi tana cewa, “Turmusturs Ni Gimbiya Kilishi ina iya kashe kowa a wanann lokacin duk munafintata da kayi har kake da bakin da zaka gaya man na tuba zuwa ga Allah, to na kasheka har lahira sai kayi tubar mai dalili, haka ta juyo ta bar gawar Turmusturs a dokar daji idan zakuna sun zo sunyi kalaci a cewarta daga wajen Turmusturs asibiti ta wuce nan aka gaya mata tana ɗauke da cutar H. I. V. AIDS, gaban Likitan ta fara ihu tana rawa tana cewa, “sai ni Kilishi, nice na kashe Ƙawata warda muke uwa ɗaya nazo na kashe boka Turmusturs sann… Likitan da sauri ya kulle mata baki yana kallonta dan ga dunkan alamu ta haukace, da yake babban asibiti ne direct wajen an gwajin ƙwakwalwa aka kaita bincike ya nuna Gimbiya Kilishi ta haukace, gashi basu san ko wacece ba, ana cikin Haka Aliyu ya shigo asibitin yana sauri dan wani abun awo yazo ɗauka a offices ɗinshi wanda zaiyi ma Gimbiya Zulaha gaji su gane abunda ke damunta, nan ya tadda an kulle Kilishi a bakin asibitin wai ko Allah zai jefo wanda ya santa, sai sub’batu take iri iri da har ya wuce yaji ana kiran “Shima Hakim ɗin sai na kasheshi.”…. Waigawar da zaiyi yaga Gimbiya Kilishi kallo ɗaya yayi mata yagane ta haukace wasu kwala ne masu zafi suka zubo mashi dan tausayinta ya kamashi, sawa yayi aka sata cikin motarta wani likita yayi driving suka ɗauki hanyar masarauta.
Tunda Hakim ya kai Gimbiya Zulaha shashenta ya kira Aliyu akan yazo ya muba masu lafiyarta, dafa Hamad yayi yana bashi hakuri dan sosai Hamad ya bashi tausayi dan ko shi ya san uwa daban take, bayan Aliyu yazo ya duba ta yayi mata duk abunda ya dace har ta farfaɗado nan yake shidamasu ta samu mutuwar rabin jiki(paralasis) sosai Hamad yake kuka dan ji yake kamar yayi hauka wai yau Gimbiya mafi soyuwa a zuciyarshi itace keda wanann cutata, sosai Hakim yake ba Hamad Hakuri dan shima abun ya girgizashi, suna haka Aliyu yace zashi ya ɗauko wata na’ura a hospital ɗinshi zai yi mata wani test anan ne yaga Gimbiya Kilishi.