GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan tafiyar Aliyu Yarima Hamad ya kama hannun Gimbiya Zulaha sai kuka yake itama kukan take tana girgiza mashi kai alamar yayi shiru, kunyar haɗa ido take Hakim dan tasan komai ya samaita alhakin Hakim ne amman sai gashi ya damu da lalurarta anbashi sarki amman bai damu da yaje fada ba ya tsaya na jinyarta, lokacin sallah yayi yace ma su Hamad su taso suje sallah sai su Hakima su cigaba da kula da ita kafin su dawo suma sai suyi tasu sallahr haka akayi kuwa dan su dukansu suka tafi harda Hamad.

(????????????Hamad yau zaiyi alwallah yayi sallah jama’a karku manta fa tun tuni na gaya maku Hamad na shiga massalaci da sunan sallah asirin da Kilishi tayi mashi zai ƙarye domin daman duk tsanar da Hamad yayi ma Hakim da san sarautar da yake ba yin kanshi bane duk aikin Gimbiya Kilishi ne har shaye shayen da yake duk yin Gimbiya Kilishi ne to yau dai Hamad ya shiga massallaci????????????????)

Suna shiga aka fara kiran sallah yaji kasanshi yana juya mashi yace yayi, “INNALILLAHI WA’INNA’ALAI HIRAJIUN.”… Yana faɗan haka da ƙarfin tsaya yana faduwa ƙasa, nan wani abu kamar hayaƙi ya kama fita daga cikin hancinshi, Sarki Abdulmalak da Sarki Abdulhadi da Sarki Abubakar sai Hakim da Annas da Humad sai Liman suka ɗauki Hamad suka kanshi fada, har suka kanshi fada hayaƙin nan bai bar fita daga hancinshi ba, hankalin Sarki Abdulmalak ne ya tashi ya sa aka kira mashi wani babban malami a garin zaria nan fa ya fara yi mashi rukiya Aliyu ya shigo da Gimbiya Kilishi a ɗaure kamar an kama biri nan kallo ya koma wajensu dan sai da Hakim ya kama Humad, dan Humad kuka ya fashe dashi da yaga mahaifiyarshi cikin wannan hali daman wannan ranar yake kujemata amman bata jin maganarshi gashi wa gari ya waya, gaban Malan aka ajiye Gimbiya Kilishi sai surutu take kala kala, nan shi dai Malan sai yi ma Hamad rukiya yake nan ya samu suka fara magana aljanun suka gaya masu Gimbiya Kilishi ta turosu jikin Hamad sama da shekara 20 domin su ɓata mashi rayuwa yana bin mata da shaye shaye sannann su dasa mashi son sarauta a cikin zuciyarshi kuma su dasa mashi tsanar Hakim a zuciyarshi dan haka komai suka ga Hamad nayi duk bai san yana yi ba sune suke tashi, nan fada tahau salati kowa yana mamakin bakin hali irin na Kilishi, nan Malan ya ya fidda ma Hamad wannan baƙaƙan aljanun, yanan Hamad ya tashi yana cewa, “AUZUBILLAHI MINAI SHEƊANIN RAJIN.”… Nan kowa yace, “ALLAHU AKBAR KABARIN.”

Kallonsu yake ɗaya bayan ɗaya yana mamakin abunda ya kawoshi fada, Hakim da Humad suka rungumeshi suna kuka dan ba ƙaramin tausayi Hamad ya basu ba, ace mutun sama da shekara 20 baya cikin yaiyacinshi komai yayi baisan yayi, Hakim godema Allah yayi cikin zuciya da bai taɓa sa yaji haushin Hamad ko dai dai da kwana ɗaya ne, Sarki Abdulmalak ta tashi yayi godiya da Allah da nuna mashi wanann ranar sannan yayi tir da mai hali irin nasu Gimbiya Kilishi da Zulaha, sannan ya tambayi Malan haukan Kilishi mai warkewa ne ko? Nan malamin yace ba mai warkewa bane sai dai shi Hamad ya yaye mata abunda tayi mashi nan Hamad yace ya yafe mata, nan Aliyu yake gaya ma Sarki Abdulmalak Doctor yace Gimbiya Kilishi tana ɗauke da cutar ƙanjamau nan hankalin kowa ya tashi, Sarki da Gimbiya Zulaha da Gimbiya Fulani Aliyu ya ibi jininsu ya wuce hospital dashi test yasa akayi masu Allah ya sosu ba mai ɗauke da ita dan rabon da Sarki Abdulmalak ya kusanci Gimbiya Kilishi har mantuwarshi ta manta, nan aka ɗauki Gimbiya Kilishi aka kaita shashenta aka cigaba da kula da ita ana bata maganin H. I. V, ita kuma Gimbiya Zulaha taji duk abunda Kilishi tayi ma Hamad tayi kuka sosai ta nemi tuba wajen Allah tayi mamaki yanda Kilishi taci amanarta har haka, itama kullun sai Aliyu yazo yayi mata gashin ƙashi yana bata magani Alhmdulh dan jiki da sauki tunda ta fara magana tana ɗaga hannunta Kuma tana zama tafiya ce kawai ta rage a fara koya mata.


Some days letter

Abubuwa da dama sun faru har da ta samun saukin Gimbiya Zulaha dan yanzun ba abunda batayi da kanta kamar take da, komai ya wuce dan sun yafi juna ita da Gimbiya Fulani suna zaman lafiyarsu kamar wani abu bai taɓa haɗasu ba, Hakim ya ba Hamad waziri shi kuma Aliyu shine sarkin fada, Humad da kanshi yace yana san a bashi Galadima kuma aka bashi, ansa ranar bikinsu su dukansu, WAZIRI HAMAD shida wata ƙawar su Hakima NANA AISHA sai GALADIMA HUMAD shida MARYAM sai SARKIN FADA ALIYU shida GIMBIYA SADIYA sai GIMBIYA MARYAMA ita da YARIMA ANNAS, rayuwarsu suke cikin aminci da yarda juna dan soyayya suke nuna ma junansu, Gimbiya Kilishi tana nan ana kula da ita yanda ya kamata dan baka cewa tana da matsalar hauka ma idan ba gaya maka akayi ba.


Yau tun safe Sarki Hakim ya tafi fada ita ko Gimbiya Hakima ta koma da zama shashen Gimbiya Zulaha saboda tsufan da cikin ta yayi haihuwa ko yau ko gobe gashi lokaci guda cikin nata yayi wani irin girma abun har tsoro yake ba Hakima.

Tunda Gimbiya Hikimatu taga ba ba kowa shashen nata ta kira Aziza tazo su dan huta ta rage mata zafi, aiko haka akayi dan tinda Aziza ta zo suke abu ɗaya ko gajiya ba suyi, suna cikin wannan aika aika Hakim ya shigo shida Gimbiya Zulaha da Gimbiya Fulani da Sarki Abdulmalak zasu bashi shawara akan a fidda Gimbiya Kilishi waje a samarmata magani domin ba cutarda bata da magani in ba ikon Allah.

Shigarsu suka wannan ikon Allah koda Gimbiya Hikimatu taga Hakim harda su Sarki nan ta tafasa ihu, tana neman abunda da zata boye jikinta dan a parlour suka taddatasu suna wanann abun, shi Hakim dafe kanshi yayi baice mata komai ba Sarki Abdulmalak da kanshi ya ba Hakim umirnin ya saki Gimbiya Hikimatu, kuma ya kira Sarki Abubakar ya gaya mashi duk abunda ya faru, haka Hikimatu ta haɗa kayan ta sai gida, koda taje gida kashe tane kawai Sarki Abubakar bai yi kuma a ranar ya saki uwarta Gimbiya Binta, daman baiwace bata da kowa Allah ma ya sota tana da wani gida a cikin gari nan ta koma da zama.

Bayan Sakin Hikimatu da sati ɗaya Hakima ta tashi ta nakuɗa…..

By Jameelah Jameey✍????

Share

Comment

Vote

Like

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

ALHMDULILLAH ALLAH NAGODE MAKA DA KABANI LAFIYA HAR NA KAMMALA WANNAN LABARI MAI TAKEN GIMBIYA HAKIMA

TO JAMA’A ANCE LAIFIN DADI ƘAREWA TO GASHI TA KASANCE DAMU, YAU NA KAWO MAKU KARSHEN GIMBIYA HAKIMA, WANDA NA ƁATA MA RAI TA SANADIN WANANN LABARIN DAN ALLAH YA YAFEMAN NIMA NA YA FE MAKU ????

NAGA MASOYA SOSAI KUMA INA YI MAKU GODIYA DA WANDA NA SANI DA MA WANDA BAN SANI BA DUK INA GODIYA ALLAH YA BAR KAUNA DAN INAYIN DADIN KASANCEWARKU DANI INA GODIYA SOSAI????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button