GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yau biki saura sati, shiyasa masarautar zaria ta fara ansar baki daga kasa daban daban, haka suke ta ansar baki kullun ranar duniya, yau saura kwana uku biki dan ankawo laifen Maryama sannan itama Sadiya ankawo nata suma su Hamad ankai nasu, yau Yarima Annas ya sauka masarautar zaria domin ayi biki su koma da amaryarsu, anyi biki na gani na faɗa dan najeria baki ɗaya maganar bikin akeyi bayan angama aka kai ko wace amarya gidan mijinta sai dai muce Allah ya kawo daitin ɗaki????.

Bayan biki da sati biyu, yau su Gimbiya Kilishi suke dawowa daga kasar saudia, Alhmdullahi ta samu saukin haukan kuma an haɗo mata maganin H. I. V ɗin dake damunta dan idan ka kalleta ba zakace tayi ciwon hauka ko kuma tana ɗauke da cutar H. I. V ta kwantar da hankalinta tana shan magani kuma tayi nadamar abunda ta aika ta kanyin kuka idan ta tuna aika aikar da tayi a duniya dan tasan ita mai lefice da hannunta ta kashe ƙanwarta saboda soyayyar Sarki Abdulmalak ana sauran sati bikinsu aka wayi gari aka tadda gawarta aka maida biki da Gimbiya Kilishi, dan hannunta ta kashe boka Turmurtus kuma da kanta tayi ma Hamad asiri saboda da son duniya da bin zuciya gashi ta kaita ta baro ta, bayan sun huta suka haɗu a parlourn Sarki Abdulmalak bayan kowa ya zauna Sarki ya tashi ta fara magana yana cewa, “Alhmdullahi Ala’kulli hailin, Allah na gode maka da ka cika man gurina ka haɗa man kan iyalana, tabbas wannan yin Allah ne kuma ina ƙara gode maka ya Allah, kamar yanda kuka sani komai ya faru cikin masarautarnan mai dadi da marar dadi, wanda ba sai an tsaya gayashi ba kowa ya sani, tabbas Gimbiya Kilishi yana tayaki murnar dawowarki cikin hankalinki, sai wanann abun ya zama izina a gareki, ke bama ke ɗaya wannan abun zai ma izina ga duk wani mai kallar halinku keda Zulaha, domin ba hanya bace mai bullewa ba, Allah yasa mudace.”.. “Amin.”baki ɗayansu suka ansa, sannan ya cigaba da cewa, “Kilishi kinsan dacewa kina ɗauke da cutar H. I. V wanda kika kwasoma kanki saboda neman abun duniya, Allah cikin ikonsa mu nan ba mai ita dan haka idan kinji baki iya zama dani zakije ki nemo mai irin cutarki ki aura lafiya lau, idan kuma zaki zauna a haka shima lafiya lau, zaɓi ya zama naki.”

Shiru Gimbiya Kilishi tayi tana kuka tabbas Mijinta mutun ne mai adalci duk abunda ta yi mashi amman ita yake tambaya zabi, bayan ta cancanci ko wane irin hukunci, amman bayin Allahn nan basu yi mata ba, basu nuna ƙyama ko wani abu daga gareta ba sai ma janyo ta a jiki da suke, kallonsu tayi sannan tace, “ina godiya da hallacinku da kukayi man, sannan ina ƙara neman yafiyarku, ba kamar Maimartaba da Hamad ina neman afuwa ku ƙara ya feman, sannan na zaɓi zama dakai har mai rabawa tazo ta raba.”

Su duka wajen “Alhmdullahi.” suka ce dan sunji dadi da Gimbiya Kilishi ta zaɓi zama cikinsu, sannan suka ƙara cewa duk sun yafe mata sannan kowa ya wuce shashenshi cikin farinciki, Humad rungume mahaifiyar tashi yayi yana murnar samun saukin ta sanann suka wuce shashenta shida Amaryarshi Maryam ranar nan suka wuni sannan suka koma nasu shashen.

Bayan shekara uku

Abubuwa da dama sun faru ciki harda rasuwar Gimbiya Kilishi, sai dai muce Allah yayi mata rahma ya yafe mata zunubanta????, dan ko masarautar zaria sunyi babban rashi sosai, Allah ya ba Humad hakurin rashin mahaifiyarshi????.

Bayan rasuwar da sati biyu Maryam ta haihu ta yan biyu duk mace ranar suna yara suka ci suna KILISHI suna kiranta da MA’MA itace Hassana sai kuma HALIMATU suna kiranta da LEEMA sunan maman Maryam ce, su Humad anzama Daddy da Momy????.

Bayan sunan Maryam da wata ɗaya Gimbiya Maryama ta haihu itama ta haifi yan biyu duk maza, yara sukaci suna, ABDULHADI shine Hassan, sai kuma ABDULMALAK shine Husaini, ranar masarautar Kano ba ƙaramin shagali akayi ba, Gimbiya Maryama ta koma sheshen Gimbiya Fulani Aisha tana yi mata wankan jego, Sai dai muce Allah ya raya ma yan biyu, su Yarima Annas an zama Daddy ita kuma Maryama Momy????.

Bayan sunan Maryama itama da wata ɗaya Gimbiya Sadiya ta haifi yan biyu duk mata, aka sama su suna, ZULAHA ana kiranta da ANISY sai kuma ZAINAB suna kiranta da ZEE sunan maman Aliyu, su Aliyu sun zama Momy da Daddy ????.

Bayan sunan Sadiya da sati ɗaya Nana Aishatu ta haifi yan biyu mace da namiji ranar suna yara suka ci sunan MUHAMMAD suna kiranshi da MAN sai kuma KUBRAH suna kiranda da I’RA su Hamad an zama Daddy da Momy????.

Bayan duk angama wanann shegali wanda tsayawa na gaya maku zai cinye mana time sosai amman fa ankashe kudi, dan kudi sunyi kuka.

Bayan suna da shekara ɗaya Gimbiya Hakima ta haifi yan biyu mace da namiji lokacin su Jamel suna da sunada shekara Hudu a duniya, murna a wajen su Sarki Hakim abun ba’a maganar ranar suna yara sukaci sunan AMATALLAH da AMATAL RAHIR ranar sunan ne naga mutane dan can na hango GIMBIYA HAKIMA FAN’S 1&3 suna kwasar gara dan sune yan gaban goshin Gimbiya Hakima wurin suna????, waigawar da zanyi na hango yan MANAZARTA WRITER’S suda yan ZEE ABU group suna kwasher rahoto dan su barbaɗama duniya kallar farincikin da keyi wajen sunan nan.

Bayan kowa ya watsa dare Hakim yake cema Jewel ɗinsa, “gaskiya Jewel yau yan Gimbiya Hakima fan’s 2 sun bani dariya, kinga yanda na hangosu suna taka rawa dan anko ɗin da suka fidda wajen sunan nan yayi masu kyau sosai.”

“Hakane Jewel kaga yanda Bilkisu abukur da adije da Bilkisu d da Zulfa,da Sakina fago, da da da da da da duk wanda suke Gimbiya Hakima Fans 2 take taka rawa gaskiya abun yayi man dadi.”

“Nima haka Jewel dan sun nuna mana kara, ilove you more Jewel.”

“Ilove uh more my especially one.”….. Nan suka haɗa bakinsu wajen ɗaya suna kissing ɗin juna, kamar ba gobe, nan na haɗo yan ƙafafuna ina cewa Allah ya ƙara kawo yan hudu masoyan juna HAKIM DA HAKIMA ????❤️

ALHMDULILLAH, ALLAH ABUN GODIYA, ALLAH NA GODEMAKA DA KABANI DAMAR KAMMALA WANNAN LABARIN NAWA MAI TAKAN GIMBIYA HAKIMA, KURA KURAN DA NA AIKATA A CIKI ALLAH KA YAFEMAN, ABUNDA YAKE MAI ANFANI A CIKI ALLAH KA BANI LADARSHI AMIN YA ALLAH ????????

SAI MUN HADU A SABON BUK ƊIN NA MAI TAKEN SANADIN LINK GA KAƊAN DAGA CIKIN LABARIN????

Kwance take bisa makeken gadonta, tana sanye da ash colour night wear, earpiece ne manne a cikin kunnanta tana jin wakarasu DJ-AB mai taken DA SO SAMU NE, hankalin ta kwance babu abunda yake damunta a rayuwa,chatting take yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da alamu chatting din yayi mata dadi shiyasa hankalinta baki daya ya karkata agun chatting din, Allah sarki Safiya kenan…

“Sofy! Sofy!! Sofy!!!, oho ni Fiddausi wannan wata kalar rayuwace yarinyar nan ta daukarma kanta, ace shi mutun baida aikin da ya wuce jin wakokin sai kuma rige waya aikin kenan ba dare ba rana, ke Sofy wai baki jinane, ta buganmata baya sanna ta juyo cikin firgice da tsoro,”Mami, wallahi Mami kin bani tsoro sosai, bansan kin shigo ba sai kawai naji kin bigeni, “ai dole kice haka Sofy, yanzun sofy abunda kika daukarma kanki kena sabo da Allah, wannan ba hali bane mai kyau,”haba Mami, yanzun ke kullun saboda Allah ni mai laifi ce, baki san ki ganni cikin farin ciki, yanzun Mami maiye aibun chatting? Kuma ni yanzun ba yarinya bace tunda har degree nagama, haba Mami ai ya dace ki duba man mana…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button