GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Sofy, yanzun ni kike gayama haka, to nidai a matsayina na mahaifiyarki ba zan fasa gaya maki gaskiya ba, kuma tun wuri ki dawo cikin haiyacenki wallahi Sofy, haka za’ayi maki auren kina wanann MUMMUNAR DABI’AR , ai in ba shi Aliyun ba, ba wanda zai iya rayuwa da ke, dan haka ki tashi daga wannan dogon baccin naki, ina ma fatan kinyi sallahr isha’i? “Aah daman yanzun nike da niyar tashi nayi sallahr kike shigo, “Innalillahi yau naga ikon Allah ni Fiddausi yar-malan, yanzun Sofy har sai yaushe zaki ringa yin sallah kan lokaci? Ke kullun baki sallah sai nace maki kiyi, kinsan ko karfe nawa yanzun? “Eh duka yanzun karfe 10 fa Mami, kuma ai isha’i har gabannin asuba duk cikin lokacinta ne, “To shikenan tunda haka kika ce, tashi kiyi sallah, salan kuma inkin gama sallahr k ikoma bisa network din…

Hmmmmm wanan kenan Kadan daga litafin sanadin link yana hanya????????

Sai kuma IZZAH KO MULKI ????

Wannan labarin ba true life story bane,kirkirarran labarine,Amman yabambanta da sauran labaran da akasaba ji.....

IZZAH KO MULKI labarine mai cike da tuggu na sarauta ga kuma tsabagen mulki Mai cike da izza da kasaita sannnan kuma wannnan labari bana zamanin nambane labarine na DA,saboda baikunshi kayan zamaniba kamarsu,waya mota jirgi dasauransu.

Inafatan wannnan labari na izzah da mulki zaikayatar nishadantar da waazantar da alumma baki daya, dafatan Allah yasadamu da mafificin alkhairyn da ke cikin wannan littafi yarabamu da sharrin dake ciki.

*Masoyana kubiyoni acikin wannan kayataccen littafi mai taken *IZZAH* KO MULKI… muje zuwa masoyah fatan alkhairi inayinku……….

Tafe yake cikin takama da IZZAH ga kasaita kamar bayasan taka kasa ga bayinsa dake takemasa baya sunata kirarashi…

“Takawarka lfy Dan sarki jikan sarki taka a sannu Allah ya tsareka daga murmushin makiya,gaba sumul baya lafiya Allah yakara maka yawan rai.”

Amman dik wannan
kirari Kai kace ba dashi suke ba,duk inda suka wuce sai bayi sun zube sun kai gaisuwa ko kallon Inda suke bayayi a haka sukaci gaba da takemasa baya….

Da ya doso waje san yayyan kamshin tirarensa ke sanar da zuwansa…..

Babu inda suka tinkara sai wani hadaddan lambu,masu kula da lambun tin daga nesa suka ruga suna masa sannu da zuwa,nan yashiga cikin lambun….

Tin kafin ya isa wajen hutawarsa har an kayata wajen yasha kilissai ga kayan marmari Kala-Kala abun ba’acewa komai,Amman duk irin nau’in kayan itatuwan nan ko kalansu baiyi ba,saboda a wannan lokacin ba, abinda ya kawoshi kenan ba……

Kafin ma ya zauna wani aikin, kai kace bashi aka gyarawa wajenba,sai da ya ɗauki wajen kusan minti ukku sannan yayi yun kurin zama,nan fa bayi suka,fara cewa .

“Zaman ka lafiya magajin gobe Allah “Allah ya taimakeka…… “

Bayan ya zauna da minti biy, ya daga musu hannu atake kowa yawatse,
yabar wajen domin kobai magana ba sun gane abinda yake nufi.

Hakadai ya zauna yana ta yan’tinane tinane ba abinda yake tinawa sai irin kalubalen da yake fuskanta akan yanda kowa idonsa na kanshi kuma shi ba ma’abocin san mulki bane,duk da cewa mahaifinsa yana samasa ra’ayin hakan…..

Dan yasan masarautar su cike take da kalubale ga tuggu da makirci kala-kala……

Yana zaune yana wannan nazari sai ga babban bawansa na hannun damarsa,saminu yazo yasanar masa maga takarda nasan ganinshi.

Sai da yadauki yan dakikai sannan ya kalleshi hakan yabasa daman komawa yai masa iso har wajen hutawarsa…..

“Hutawarka lfy bango majinginar marayu magajin gobe, mai martaba yace in kawo maka wannan sakon…. “

Ya dago, ya daura masa wannan sexy eyes din nasa,sai yayi zaton kamar harararsa yayi take gabansa yafadi…..

“Tuba nake ranka shidaɗe Allah ya huce zuciyarka.”.. Nan ya kalli saminu,ya anshi takardar yamika masa,Kai kace bashi akamiko mawaba

“Allah yataimakeka gashi sannan yasa hannu ya’ansa…..”

Kamar bai san budawa yabuda yana tinanin me mahaifin nasa zaice a takarda yabude ta kamar haka….

_”Assalamu-alaikum,

dafatan ka riski sakona inasan ganinka yanzun a fada,bissalam”._

IZZAH KO MULKI KENAN, KUDAI KU CIGABA DA BIYOMI DOMIN SANIN YANDA WANNAN ABU DRAMAR ZATA KASANCE????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button