GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Lantana! “Naam uwar marayu, “Uhmm, abunda Gimbiya Hakima tace kenan Amman har Inna Lantana ta gane abunda take nufi????

Wai ashe tace nufin ta tashi ta zuba abinci ta fara ba su A’bu suci sannan ta ci itama wai Gimbiya Hakima ba dai masifa ba????

“Ranki yadade angama zubawa, kallonta kawai Gimbiya tayi, nan take Inna Lantana ta shiga taitayinta..

“Murja bissimilla ga abinci, “to Inna Lantana, nan suka ansa suka ci sai da kowace tayi three spoon sannan suka ajiye..

Sai dai Gimbiya Hakima ta mula tasha iska sannan ta yi ma Lantana nuni da hannu..

“Gashi ranki yadade, nan Gimbiya ta fara cin abinci cikin natsuwa da kwanciyar hankali, sai da tayi two spoon sannan tace, “ku tashi ku tafi ku bani waje, “godiya muke Gimbiya Hakima…

Bayan Gimbiya Hakima ta gama cin abinci ta aika sako wajen jakkadiya tana san yin magana da Maimartaba..


“Hakim! “Naam Ranki yadade, “nifa Hakim ina mamakin yanda ka makale sai kayi wannan koyawar a jami’a..

“Fulani ya kamata ace yanzun kinyi hakura da wanann maganar dan Allah ki saman albarka cikin lamarin..

“Shikenan naji Allah yayi albarka, “Amin Fulani godiya nike, ni zan wuce massalaci, “to adawo lafiya…

Nan ya fitowa shashen Gimbiya Fulani dogarawa suka goya mashi baya sunata yi mashi kirari nan suka shiga massalaci sukayi sallah bayan sun fito yaga sun kara biyo shi nan ya tsaya.

“Wai dan Allah bana ce maku kubar yi man wannan abun kamar wani abu..

“Allah yaja da ran Yarima dan sarki jikan sarki, ka hanamu binka cikin gari nan ma kana cewa mubar binka, ai wannan shine aikinmu kare lafiyar Yarima sarkin gaba..

“To naji, amman ai ni nace na hutar daku ko? “Eh ranka dade, “to dan haka ku wucewarku nagode.

Haka suka tafi suna mamakin saukin hali irin na Yarima Hakim shi dai bai damu da mulki ba..

“Wai Kilishi ya ina maki magana kinyi shuru, tunanin mai kike?

“Hmmm! Kedai bari Zulaha, ina tunanin yanda zamu kauda wanann dan iskan yaron kullun da abun nike Kwana muke tashi, duk hanyar da muka bi bata bulewa, kullun sai fi yaran mu yake..

“Wannan abun nima yana damuna Kilishi, ban ki na bude idona naga Hakim baya numfashi a doran kasa…

“Baki daya Yaro shida uwarshi kallon banza suke ma kowa cikin gida, wato dan sun samu boka wanda yafi namu aiki shiyasa, sun mallake gida kina ga Maimartaba baya jin maganar kowa cikin gidan nan sai ta uwarshi..

“Kuma muma mun haifa cikin gidan nan fa, kuma nice babba cikin gidan nan, dan kawai an rigani haihuwa sai a daukeni sakara cikin gida ko magana ta ba’atsayawa a saurara..

“Karki damu Gimbiya Zulaha zan san abun yi, dole YARIMA HAMID zai gaji mulkin Maimartaba ba YARIMA HAKIM ba, dan Yarima Hakim da wata hudu ya girma Yarima Hamid kinga ko ya zama dole mulki ya fito dakin matar farko ba ta biyu ba..

“Aiko dai Gimbiya Kilishi, shiyasa nike sonki, dan kina gane gaskiya..

Haka sukai ta tautaunawa yanda zasu samu su kawarda Yarima Hakim a duniya duk saboda mulki..


“Ranki yadade Jakadiya ta aiko da sako, “mai tace Bilkisu?

“Cewa tayi Maimartaba yana san ganinki..

“To ace mata gani nan zuwa, “angama Uwargijiyata..

“Uwani kije kice tace gata nan zuwa, “to shikenan Lantana..

Nan Gimbiya Hakima ta shirya ta dauki hanyar shashen Maimartaba Sarki Abdulhadi..

By jameelah Jameey ????

Share and comment pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

09&10

Nan Gimbiya Hakima ta shirya ta dauki hanyar shashen Maimartaba ita da kuyanganta…

Bayan sun iso Jakkaddiya tayi mata iso har gaban sarki..

“Ranka yadade Allah ya ja da tsawancin kwana, na barku lafiya, “Uhmmm, abunda yayi mata kenan Jakkaddiya ta kama gabanta, ta koma bakin aikinta..

“Baffah ina kwana, “lafiya Lau Mamana,”Baffah da man nazo ne akan maganar makaranta, “to inajinki Mamana, mai kike so ayi maki?

“Da man ina neman Sausaci wajen Sarki mai adalci akan hukuncin da ya yanke man na yin karatu nan kasar Nigeria..

“Kin gama Hakima, sai da gaban Gimbiya Hakima ya tashi da taji yau Maimartaba ya kira sunanta ba tare da yace Mamana ba..

“Eh Baffah na gama!

“To daga yau karna sake jin kin zoman da maganar baki san karatu nan kasar, ya zamai maki dole kiyi karatu a kasar Zaria, can nike bukatar kiyi karatu, ko kuma na maidoki nan Kano kiyi karatun..

“Allah ya huci zuciyarka, Amman, “ya isa haka Hakima kinsan bani magana biyu, dan haka ki shirya nan da kwana biyu zaki wuce makaranta dan naji da zamanki gidan masarautarnan kina shiga hakin bayin Allah..

“Godiya nike Baffah, Amman ina neman alfarma ta biyu, “Uhmmm ina jinki, “da man nace ayi man adalci, adalin sarki, kar a barni na zauna hostel..

“Da man ba hostel zaki zauna ba, na sa ankama maki gida, dan ba zaki zauna gidan Sarkin Zaria ba, ki zunda man mutunci kina wulakanta masu bayi…

“Dan haka ina mai maimaita maki Hakima nan da kwana biyu zaki tafi makaranta, kije kiyi karatu nasan tarbiyar da muka baki, tashi ki tafi Allah yayi maki albarka..

“Amin, godiya nike Baffah, ni na wuce..

Haka Gimbiya Hakima ta fito turakar Maimartaba ranta bace tana mamakin yanda Fulani da Maimartaba basu ansar uzurinta a rayuwa su dai sunfi bayin gidan nan akanta…

Tana cikin tafiya wata baiwa daga shashen bayi tafito bata bata lura da Gimbiya Hakima ba ta shafen mata gefen alkelba..

Tas! Tas!! Tas!!! “Ke wata kalar kidahuma ce da zaki taho kamar wani doki kike san bankadeni?

“Inalillahi! Ranki yadade kiman rai, wallahi banga tahowarku ba uwar marayu..

“Ke Azima, “Naam Allah ya taimakike, “maza kije ki kira man Sarkin bulala, “ke kuma in samaiki bakin shashena, “to Allah ya taimaki Gimbiya Hakima..

Haka wannan baiwar take gudu-gudu sauri-sauri, jiki na rawa haka ta isa shashen Gimbiya Hakima, ita ko Gimbiya Hakima tafiya take cikin kwaciyar hankali har dai tayi kusan awa sannan ta iso shashenta dayake da dan nisa tsakaninta da shashen su Maimartaba..

“Sarkin bulala, Gimbiya Hakima na bukatar ganinka, “To Allah sa dai lafiya? “To kawai za’ace kaima kasan indan Gimbiya Hakima tayi kiranka ai hukunci zata yanke kaima kasani, “to ai laifinkune, tunda kunsan halinta ba tausayine da ita balle imani, to dan mai zaku kama yi mata laifi, nidai indan ta ban umirni dole na bi, dan haka mu tafi…

“Allah ya ja da ran Gimbiya Hakima, gani na ansa kiranki, “sarkin bulala, ina san kayi ma wannann kidahumar baiwar bulala Hamsin, indan tayi kuka ta zube ko kuma ta sosa balle motsawa..

“Angama uwar marayu, godiya take, nan Sarkin bulala ya tashi ya fara zula ma wanann baiwa bulala sai da yayi mata bulala hamsin sannan ya tsaya, “ranki ya dade nagama cika umirninki..

“Akaita gidan horo, ayi mata horo na tsawon sati, angama uwar marayu..

Kai kai kai!!! Gimbiya Hakima ya kamata ki tausaya bayin nan fa????, suna ce maki uwar marayu, Amman baki tausayinsu hukuncinki yayi tsanani fa????????‍♀️, kudai muje zuwa my fan????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button