SIRRIN ƁOYE COMPLETE

1hour pass.
Ta cikin Kamfutar dake aje saman table Emanuel ke Vedio call da ƙanensa Obi, tambayarsa yake dangane da halayyar abokinsa ɗan arewa da sukai aiki shekaran baya. Obi ya buɗi baki yace,”Brother kana da study of psychology, dan haka a ɗan iya zaman da mukai last time da Ahmed na san ka gama karantar halayensa”. Emanuel ya kaɗa masa kai alaman haka ne sannan yace masa,”kuyi magana da shi kaji idan zai iya zaman Lagos, ina so zan ɗauke shi aiki matsayin sakatare mai kula da harkar shige da fice na office ɗina”. Obi yay tsalle a saman royal bed ɗin da yake kwance, “what a great news, amma gaskiya brother naji daɗi sosai akan wannan tunanin da kayi na ɗaukan Ahmed aiki domin shi ɗin mutumin kirki ne, sam bashi da mugunta acikin zuciyarsa, ni shaidansa ne a zaman da mukayi na karatu da shi”. Emanuel ya ƙara tambayarsa da cewar, “mene full name nasa?”. “Ahmedu Adamu Bichi”. “is he single or married?”. “no he is single, amma ban sani ba ko zuwa yanzu yayi aure dan mun ɗau tsawon lokaci ba muyi waya ba since time ɗin dana bar nigeria”.
“i hope ya iya turanci tunda kaga mu nan ba jin hausa ake ba”. “ehh bross yana da speech me kyau, shifa kawai dan dai yazo a mutumin karkara ne”.
Emanuel yace da shi,”to kayi gaggawan sanar da shi yau, becouse within next tomorrow nake so ya fara gudanar da aiki, idan yana da iyali yana tunanin ba zai iya barinsu ba you should let me know za’a samar masa gida cikin gidajen Dad na GRA”.
“okay bross”. “ina Mommy?”. Emanuel ya tambaya a sanda ya kai apple baki ya gutsira. Obi yace, “Mommy sunje church ana bikin ƴar gidan Pastor Eze”. “what about Dad?”. “yana ɗakinsa, na fuskanci yau mood ɗinsa is not good, dan ko da naje gaishe shi bai amsa min ba kai ya ɗaga min kawai, kuma har na fito idonsa a rufe yake”. Lokaci ɗaya hankalin Emanuel ya tashi, yay decline call ɗin ya ɗau wayansa ƙarama yay dialling numba ɗin mahaifinsa, har sai data yi ringing biyu ta katse sannan mahaifin nasa ya kira shi, ya ɗauki wayar murya ɗauke da damuwa ya shiga jerawa mahaifin nasa tambaya ba tare daya ko amsa gaisuwar da Dad ɗin nasa ke masa ba.
“Dad meke faruwa da kai? Baka da lafiya ne?”. Daga can ɓangaren General Tosin Afafa yace da ɗan nasa,”babu Wata matsala Son, ya office naka?”. Emanuel bai yadda da maganar mahaifin nasa ba, ya dai ji shine kawai, saboda daga yanayin muryarsa zaka fahimci akwai damuwa tattare da shi. “Dad komai lafiya, sai dai ina so zan biyo jirgi gobe nazo na ganku”. “no ba sai kazo ba muma ending this month zamu dawo, na gama gudanar da aikin daya kawoni, ni kaina na gaji da zaman ƙasar nan…i dont know what is exactly happening to me amma hankalina gaba ɗaya yayo nigeria”. Emanuel zai kuma magana Dad ya tari numfashinsa da cewa,”Son ka bar kallon news ne?”. “a’a Dad, jiya ne dai da yau ban kalla ba saboda aiki daya min yawa a office…yauwa Dad ko Md ya sanar da kai yanda ake ciki game da Contract ɗinmu da NDBH?”. Dad yace da shi,”Son for now ka mant da wannan tukunna, ɗazu ina kallon news akwai yaran da akayi kidnapping from university, and the kidnappers are talking about 4millon kana su bada su, iyayen yaran kuma basu da kuɗin karɓo su, infact ma suna maganar cewar idan gwamnati ba zata taimaka masu ba zasu bar musu ƴaƴan tunda basu da yanda zasuyi, so ina so ka fitar da wannan kuɗi aje a amso yaran daga nan zuwa yamma kaji ko…and dont let your Mum know about this issue kaji ko”. Emanuel ya amsa da karɓar umarnin mahaifin nasa kamin kiran wayar nasu ya katse.
Kano, Masarautar Bichi.
Zaune muke a wani tamfatsetsen falo na gidan saurauta wanda aka ƙawata shi da kayan alatu iri-iri na more rayuwa, ni dai tun shigowarmu bin ko’ina nake da kallo ina jin dama ace mune acikin wannan daular, Adawiyya dake kusa dani ta zungureni na juyo na dubeta, tana wani yatsine fuska tace,”Wai ke sai ance mana ƴan ƙauye”. Na harareta nace,”to da su wane? Kinga ki rabu dani na kashe kwarkwatar idona yanda zanji daɗin bada labari wataran, kuma sarai kin sani daga yau ba kuma shigowa zamu yi ba”. Tasa hannu ta toshe dariyar da take ƙoƙarin yi, saboda ina nunawa Habiba wani abu kamar bal yana juyawa ta saman cikin ƙwai yana fesar da hayaƙi dake bada daddaɗan ƙamshin acikin falon. Ni tun ina jin dadin zaman ma har na fara gajiya na fara jan tsaki, ga shi Ya Kabiru daya kawomu yasa ƙafa yay tafiyarsa tun ɗazu da shi da Suhail. Na miƙe tsaye saboda yanda na gaji da zaman, baiwar da akasa tsaronmu ta doka min tsawa akan na koma na zauna, nayi firr da idona nai mata banza kamar ban jita ba. Sai gata ta taso daga inda take cikin sassarfa tayo kaina, dukana zatayi kone oho mata, nasa hannu na dakatar da ita da cewar, “ke ni ba ɓarauniya bace balle kiyi zaton ko sata zanyi muku, ki bar ganin girman masarautar nan taku da daular dake ciki to wallahi ba ku da abunda zan sata, dan ina da godiyar Allah da matsayin da ubangiji ya ajeni aciki, tashin da kika ga nayi tafiyata zanyi na gaji da wannan zaman shanyamu da akai kamar ba mutane ba”. Zatayi magana sai ga Jawad ya fito daga saitin ƙofar da muke tsaye, kunnensa sanye da abun jin kiɗa hannunsa kuma riƙe da waya yana dannawa, tafiya yake ko kallon gabansa bai yi, baiwar ta zube ƙasa tana jera masa kirari irin nasu na ƴan maula wanda har haushi saida ta bani naji kamar nasa ƙafa na mangareta gefe. Bai ko bi ta kanta ba yazo wucewa ta kusa dani na taɓe baki naja ƙaramin tsaki wanda shi kaɗai ya iya jinsa, nan ya dakata da tafiyar ya ziro hannunsa ta wuyana ya ɗalle min baki, acikin kunnena yake faɗin,”yarinya idan tace zata min rashin kunya acikin gidanmu wallaAh sanyawa zanyi fadawa su zane min ita, koma nasa a maida ita tarihi sai naga da wanda zata kuma yi”. Idan ya barni ma da jin zafin ɗallemin laɓɓa da yayi kaɗai ya isheni, banda kuma take ƙafa da yay min da wani shegen takalmi dake ƙafarsa irin na ƴan sarauta, ya san da cewar naji zafi tunda yaji bakina ya ɗinke, amma duk da hakan bai ƙyaleni ba saida ya kuma sa yatse ya ɗalle min laɓɓana, zafin da naji a wannan karan yafi na ɗazu, idona ya cicciko cikin zafin nama na ɗauke hannunsa daga saman wuyana na wurgar da irin yanda shima zaiji zafi, na jiyo na fuskance shi da ƙarfi nace,”Allah ya isa mugu azzalumi, kuma wallahi nima sai dai idan baka shigo ƙauyenmu dan saina rama”. Ya kuma kawo hannunsa zai gwaɓe min baki maganar dattijuwar dake shigowa ta dakatar da shi. “Jawad me nake gani haka?, yara na wajenma kai ba zaka ƙyale ba”. Yay min duba kaɗan sannan yace da ita, “Ammi bata da kunya ne, baki kalla yanda take zumɓurowa mutane baki ba”. Ta nufi kujera tana zama tace,”wani abun kayi mata shi yasa, ya kamata ka rage zafin zuciya, haka kawai dai yarinya ba zata zumɓura maka baki ba babu abunda kayi mata, wuce ka bamu wuri”. Maimakon ya wuce kamar yanda ta umarce shi sai ya nemi ɗaya daga cikin wasu tsinannun kujeru na alfarma ya zauna akai, ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yaci gaba da danna wayarsa. Ni kuma na tsuguna na gaida matar, ban san ya akai ta lura da goge ƙwallar da nayi ba sai ji nayi tana cewa,”ka kalla har kuka sai daka sata tsabar mugunta irin taka Jawad, yarinya taso kizo nan kinji, ya sunanki?”. Nace da ita, “Mairo”. Kan tace komai Jawad ya bushe da dariya yana cewa, “ji wani suna wai Mairo, kai ƴan ƙauye ma da kayan haushi suke”. Na ɗago kai na dube shi nace, “kaima ai sunan naka ba daɗi ne da shi ba, mene wani Jawad ko daɗin ji babu suna sai kace za’ai amai”. Wata tsohuwar mata data shigo ta doka min tsawa da cewar ya isheni haka ko yanzu asa bayi su sokeni tunda ina yiwa Yarima rashin kunya. Na harareta ta ƙasan ido sannan nayi tattaki zuwa gaban dattijuwar kamar yanda ta umarce ni, kuma har na ƙarasa gabanta kaina na ƙasa ban ɗago ba dan tun shigowarta ma ni ban kalleta ba, sai a yanzu data sa yatsunta ta ɗago da haɓata tana cewa, “ba kyau yiwa Babba rashin kunya karki ƙara kinji Maryama, idan kuma ba haka ba zansa a cire sunanki daga waɗanda za’a kai makaranta, kina so nayi hakan?”. Na kaɗa mata alaman a’a, take kuma Yawun bakina ne ya ƙafe da amsar da zan bata, sakamakon kallon fuskarta da nayi wanda ta sani faɗuwar gaba da ban da taɓa jin irinta ba. Kallon fuskarta nake da ɗumbin mamaki da al’ajabin kamannin da nagani a fuskarta, kamannin da suka so ruɗar dani suka kuma nemi zautar dani. Na rumtse idona sosai ina jin shigar wani abu ajikina dalilin kamo hannuna da tayi ta zaunar kusa da ita, in banda kar nayi saurin rantsuwa zan rantse nace hannun nan ya taɓa riƙeni, Na ƙara kallonta kamin na lumshe ido, idanuna dake rufe na hasko min hoton halittar dana jima da sani a saman fuskar wannan matar, yanda zuciyata ke ayyana min shine kawai mafarki nake, dan haka na buɗe idona a zabure na saukesu akan manyan akwatuna guda uku da aka aje agaban Ammi, tare da jakar bakko guda uku suma shaƙe da kaya, hakan ya kuma tabbatar min dai da ba mafarki nake ba, ta gefen ido nake bin Ammi da kallo ta yanda ba zata gane ba har sanda na sauke idona kan zarazaran yatsun hannunta, ni dai tabbas idan ba tunanin daya cika min kai a kwanakin nan bane ke neman zarar dani ba, to babu tantama akan abunda idanuwana suke gane min.
Ya Kabiru da shi da Suhail sukai sallama a falon, hankalin kowa ya tattara kansu banda ni, wacce na zuba idanu a wuyan Ammi da son gano abunda nake zargi, sai dai har na gama ƙare mata kallo ban hasko komai ba. Na maida hankalina ga maganar da ake wacce ta shafi tafiya makarantarmu, Suhail ke cewa da Ammi, “Ammi ba dai Mairo har ta zama ƴar gidanki ba”. Tai murmushin manyace kana tace masa,”ka bari Suhail, yaron nan Jawad ne daga shigowarsa ya sata kuka, ko ce masa akai su Ziyan e daya saba cin zalinsu”. Wanda ya shigo bayan shigowar Ya Kabiru yana zama kan kujera yace,”to ai yarinyar ce kamar su Ziyan ɗin, gata nan kamar a hure ta faɗi, kuma da alama abunda ya tsana tayi masa na turo baki dan gashi nan na gani da idona, kinga ko Ammi ai dole ya sata kuka”. Na ɗago ido na kalle shi ina daɗa turo bakina gaba nace,”nifa bakina ne a haka”. Kowa na gurin ya dara har da Ya Kabiru, shi kuma wanda naji Ammin ta kira da Ashraf ya daɗa cewa, “A’a Mairo wannan ɗan ƙaramin bakin naki kam da gani da gan-gan kike turo shi”. Sai kuma ya gyara zama yana fuskantar Ammi wacce ke complain ɗin wai Suhail ya cire mata hoto. Shi kuma yana cewa ba yin kansa bane Mai Martaba ne yasa shi, ta ɗan kaɗa kai kaɗan kana tace, “ai shikenan, amma sanin Mai Martaba ne hoton nan shi nake gani naji daɗi a ƙasar nan…amma ba komai Suhail kai da ka biye masa naka laifin zanta gani”. Ta ƙarashe maganar da murya mai ban tausai wadda har saida na juyo na dubeta, dan a yanda muryar tata taso sarƙewa sai tai min kama da sautin dana taɓa ji, sai dai ba zan tantance sautin wane bane. Ashraf yace,”Ammi mun gama komai dangane da tafiyar yaran nan, sai dai fa da ƙyar muka shawo kan Baba ya amince, dan haka Gwaggonsu da kuma Inna Amarya suna miƙo tarin godiyarsu ga wannan masarauta da kuma shi Suhail daya zama sila, irin tarin adu’oin da sukai sai da nace kema ki bisu da irinsu kawai”. Ammi ta gyaɗa kai sannan ta mayar masa da magana acikin wani yare na daban wanda ba hausa ba, hakan yasa ban fahimci mai suka ce ba, sai dai naga ta miƙe ta wuce ciki ta barmu da Jakadiyar dake mana bayani da kyautar kayan tafiya makaranta da Ammi tayi mana.