NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

“Baba to kaje a aske maka gemun mana tunda naga yana damunka”.
Na faɗa idanuna ƙyar akan haɓarsa da yake sosawa, ya bani amsa da cewa, “yau insha’Allahu zani a aske, ni nafi ganewa askin wanzamai su kuma su Amadu sai suce ba haka ba”. Ina murmushi nace, “to Baba ai na kilifa ɗin yafi yin kyau, kuma kaga shi ance ba’a fiye ɗaukan cutukan zamani ba”.
Kafin ya bani amsa Ya Kabiru ya shigo, ya tsuguna yana cewa da Baba gashi.
“Yauwa Kabiru nace ya za’ai anjima dan Allah ka nemo mota ƴar ƙurƙura akai itace gidan galadima”. “babu damuwa Baba sai a nemo, zanwa Hamisu magana idan baza shi cikin gari ba saina karɓi tasa”. “to Na gode Allah yayi muku albarka. Ina Amadu yana nan ko ya wuce makaranta?”. “ehh naji dai ya fita ɗazu to amma ban sani ba ko makarantar ya wuce tunda banji ya min sallama ba”.
Baba yasa hannu a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa mishi,”Dubu huɗu ce ka bashi ya auno masara da shinkafa ya kawowa Suwaiba”. Yasa hannu biyu ya amsa tukunna ya fice shima Baba yay sallama da Matansa ya fita, mu kuma yaran mukabi shi da adawo lafiya.
Da yamma muna zaune ƙarƙashin rufin kwanon ƙofar ɗakinsu Lukman wanda yake kallon ɗakin Baba, Inna Amarya ce ta gama yi min yankan farce take kuma saka min lalle kasancewar gobe zamu koma makarantar boko hutu ya ƙare, an gama sawa Adawiyya nata tun ɗazu, Adawiyya itace sakuwata dan tsakaninmu shakara guda ne ta bani, komai namu tare Inna Amarya take haɗamu tayi mana mun zama tamkar ƴan biyu duk da cewar uwarta ba son hakan take ba, dan wani lokacin Inna Zulai har kulleta take a ɗaki ta zaneta akan shige mana da take, haka zataci kukanta ta gama, data buɗeta kuma ta kuma dawowa wurinmu, burinta ma bai wuce ta koma wurin Gwaggona da zama ba dan kayanta da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai ta kwaso ta maida su can, shi yasa abinda ke shiga tsakaninta da uwarta harara da hantara.
Ya Kabiru ne ya shigo hannunsa riƙe da baƙar leda, yasa Zubaida ta miƙo masa kujera ya zauna gefe kusa damu, fuskar nan tasa ɗauke da murmushin da baya rabo da shi, marabar shi da Ya Amadu kenan, Shi mai fara’a ne da son mutane saɓanin Ya Amadu da baya son mutane kuma miskili ne na ƙin ƙarawa, shi idan ka ganshi a gidan yana hira to da Baba ne ko Gwaggo ko Ya Kabiru wanda suke tamkar ƴan biyu dan tsiransu shekara ɗaya ne a haihuwa.
Ina bala’in son duka yayyuna biyun nan saboda kyawawan halayensu dake burge kowa, da kuma yanda suke nuna min tsananin so, dan komai suka rakiito da tsarabarsu nawa ne nida Adawiyya, Ni yarinyace me data san kyau kuma nnake son kyau, saboda hakane na gane duka yayuna biyun da nake matuƙar so kyawawan gaske ne, hancinsu har baka irin na Baba, ga fararen idanu da dogon gashin ido, na kan kasa tantance acikinsu waya fi wani kyau, idan na tambayi Adawiyya sai tace ai Ya Kabiru yafi kyau tunda yafi Ya Amadu haske kuma yana da wushirya, sai nace mata a’a shifa Ya Amadu har dimple ne da shi kuma bakinsa yafi na Ya Kabiru ƙanƙanta, haka muke zama muyita wannan musun da junanmu, ƙarshe sai Yagana ce ta raba mana gardama tace ai Ya Kabiru yafi kyau tunda shi ingarman namiji ne, Kalar mazan da mata suka fi so, ba ƙaramin daɗi naji ba da batun Yagana domin akomai ina so naji ance Ya Kabiruna yafi, haka itama Adawiyya akomai tafi so ace Ya Amadu yafi.
“Sannu da dawowa”. Inna Amarya tace da Ya Kabiru wanda yake latsa ƴar ƙaramar wayarsa. “yauwa Inna Amarya”. Ya amsa mata yana buɗe kwanon abincin da Basma ta ajiye masa agabansa yanzu.
Gwaggo ta fito tana ce mishi, “Kabiru kuma saina jiku shiru daga kai har Amadu baku kawo cefane ba. Shine kawai saina bada aka siyo taliya ƴar murji akayi jalof, Allah yasa dai zaka iyaci”. Tun shigowarsa idona yake akansa na kasa ko da ƙiftawa, babu wanda ya lura dani harta shi ɗin dana ke ta aikin kallo, gani nayi ya ɗan yatsine fuska kaɗan kamin yace, “zanci mana Gwaggo, ba dai abinci bane kuma duka kowa yaci ya rayu lafiya. To ni wane da bazanci ba”. Ya numfasa bayan ya sosa girarsa sannan yace, “Gwaggo kiyi haƙuri da mukaje kai itacen gidan Galadima ne bamu dawo da wuri ba, sai yanzu ne dana dawo na miƙa mishi kuɗin”.
“ai tunda ansamu wanda za’aci ɗin shikenan, dama bana son yin abinda ba kwa son ci ne, saina bada a siyo ƴar gwamnati naji tayi tsada shine nace to kawai a karɓo taliyar murji.
Allah sa shi wancan ɗin idan yazo ya iyaci”. “zaici mana Gwaggo, yanzu ma na baro shi shagon ɗinki yana nan tafe”.
Gwaggo ta wuce dan ci gaba da sabgarta, shi kuma ya buɗe kwanon abincin bayan ya wanko hannu ya fara ci da bismillah, ba ma’abocin cin abinci bane shi dan haka kaɗan yaci ya aje gefe kusa da shi yay masa adani mai kyau yanda wani ba zai shigo yagga saura ba yace masa zaici, domin nawa ne ya ajiye min, haka muke da shi a gidan, idan banci sauran abincinsa ba to zamuci tare.
Ɗagowar da zaiyi muka haɗa ido sai nayi saurin saka hannu na rufe bakina zuwa hancina, murmushi me bayyanar da haƙora yayi ya ƙura min ido yana kallona tare da min nuni da ƙunshina da idonsa da kuma ledar dake hannunsa.
SIRRIN ƁOYE

3)
Inna Amarya na ƙoƙarin saka min leda kawai na miƙe, ƙafar da akasa lallen a ɗage, na taka da wadda ba’a saka ba, na nufin wurin Ya Kabiru da ƙaguwar son ganin tsarabar daya taho min da ita.
Tangal-tangal nayi zan faɗi, Kulu da ake gefe ta miƙe da sauri dan zuwa ta tareni amma sai Gwaggo ta dakatar da ita da riƙe hannunta, sai Ya Kabiru ne wanda ya taso cikin azama ya riƙoni jikinsa, ya sunkuya ya ɗaukeni ya ajeni kan kujerar daya tashi, Gwaggo cikin faɗa tace masa.
“wai Kabiru sai yaushe zaka gane wannan yarinyar ta girma ne, shekara goma sha uku fa ba wai shekara uku bane”. Yana ɗora ƙafar da aka samin lalle saman kwano yace, “ni Gwaggo wannan girman da kuke ta faɗa ne har yanzu ban gani ba”. Gwaggo taja tsaki tana ƙara cewa, “Ai shikenan sai kayita biye mata. ke kuma Amarya da kikaga ta tashi ai sai ki taɗo ƙafarta ta koma ta zauna, ni bana son wannan rashin natsuwar tata”.
“yoni inama nasan zata miƙe ɗin, kamar fa wacce aka fincika haka ta miƙe”.
Ya Kabiru na dubana yace,”yanzu Mairo da ƙunshin ya dagulefa shikenan sai ƙafarki ta koma ta tsaffi”. Ina dariya nace,”ba zan bari ai yayi kamawar da zai zama dungulmi ba, kana bani tsarabata zanje na wanke sai Inna ta kuma samin wani”. Inna Amarya ta sako baki da cewa, “Mairo yanzu ko ai sai dai ki tashi da ƙafa ɗaya, dan ba zan ƙarasa saka miki ba, kyata yawo da ƙafar haka ɗaya da lalle ɗaya babu”. Nayi shiru kawai dan nasan tunda tace haka ta zauna, na ɓata fuska ina cewa Ya Kabiru, “to ka bani tsaraban na gani sai naje na wanke lallan kar ya kama sosai”.
Ya miƙe daga tsugunon da yake yaje ya ɗauki leda kusa da Inna Amarya ya dawo yazo ya ɗaure min ƙafar. “ki saki ranki zansa miki na ɗaya ƙafar ai na iya. Kamin Hajiyarmu ta rasu ni nake saka mata indai na dare zatayi, lokacin ba’a haifi mace ko ɗaya ba a gidannan”. Ya buɗe baƙar ledar daya shigo da ita, takalmi ne ya fito da shi kambos na makaranta fari ƙal sai ɗaukan ido yake, mai kyau da adon fulawoyi ajikinsa, ban san lokacin dana saki wata ƙara ba saboda murna, tsananin farinciki ya kamani, ta ko’ina ni ƴar gata ce tunda Allah ya bani Yayyu masu sona, ya kuma bani Inna Amarya bayan kyauta mafi girma da darajar daya bani ta mahaifina ba.
ya kama ƙafata da babu lallai ya saka min, takalmi tamkar an auna da ƙafata tun kan a ƙera shi, adu’a na shiga kwaranyowa Ya Kabiru babu ƙaƙƙautawa, Domin ko a mafarki ban taɓa zaton ƙafata zataga irin wannan takalmin ba, dan nafi ganinsa a ƙafafun ƴaƴan masu kuɗin garinmu, ni ko a makarantarmu ma ban taɓa ganin mai irinsa ba, sai dai a ɗaliban makarantar kuɗi ta garin bichi. Ban gama wannan murnar ba ya kuma kasheni da wata murnar, ta hanyar ɗauko min dalleliyar jakar goyo ta makaranta mai bala’in kyau, itama dai nafi ganinta ajikin ɗaliban makarantar kuɗi, wayyo daɗi yanda kasan an tsundumani a aljannah, na tarairayo wuyan Ya Kabiru na ruƙnƙume shi ina daɗa masa godiya da adu’a, yana ta murmushi yace, “to Mairo acika min wuyan karya ɓalle”. “Ya Kabiruna farincikin da kake sani kaima Allah ya saka acikinsa, takalmin da jakar sunyi min kyau sosai, Allah ya biya maka karatunka yasa ka sami aikin gwamnati”. Na rungume kayana ajiki kamar wadda akace za’a ƙwacewa, har Allah Allah nake gari ya waye mu tafi makaranta.
Gwaggo da Inna Amarya suma sai godiya suke mishi da jerin adu’oi, Inna Amarya na cewa na kawo ta ɓoye min ina cewa ta bari zan adanasu a wajena kar wani abu ya tabasu, Adawiyya tace, “idan baki bata ba ai kya ɓata su da lallai”.
Sai Yamma sannan na cire ƙunshina, ina gama wankewa kuma Gwaggo tace mu shirya ta aikemu gidan Liman wajen Baba Lami, saƙon Nakiya ne ta bayar akai mata, Baba Lami ƙawar Hajjo ce mahaifiyar Gwaggo.
“Adawiyya ki riƙe min Langar nan da kyau kinga sabuwa ce, gadarta nayi a wajen Hajjo, bana son abunda zai taɓa lafiyarta, har kuje ku dawo ban yarda yaje hannun Mairo ba, dan zata iya salwanta, tunda ita abun ɗaukar magana ba wuya yake mata ba idan ta fita…kuce da Baba Lami ɗin ina gaisheta kuma ina yi mata sannu da ƙafa, insha’Allahu ina nan shigowa na dubata”.
Muka amsa da to, kafin ta juyo kaina da cewa,”saura ki tsaya siyan faɗan da banaki ba”. Na amsa da to sannan muka fice daga gidan muna riƙe da hannun juna.
Tafe muke ni da Adawiyya muna ƴar hirarmu ta rayuwa, hirar bata komai bace face wadda ta shafi cikin gidanmu da yanayin rayuwar yanzu dake sauyawa, harma da yanda zamu maida hankali sosai akan karatun boko wannan karon idan an koma, saboda wancan karan bamuci jarabawa ba, dan ni ta tara nazo Adawiyya kuma ta goma sha biyu, Ya Amadu kuma yace ta ɗaya kawai yake so, duk sanda muka wuce ta ɗaya la shakka zai ciremu a makarantar.
muna kan gangarawa kwanar gidan Liman Adawiyya tace, “Mairo zomu shiga gidansu Zainabu, rabona da ita tunda muka wanke Allo yau kusan wata guda kenan”. Nace mata, “ni kuwa kinga indai gidansu Zainabu ne ba zani ba, wai tana ƙawarki amma ita bata damu dake ba sai ke komai Zainabu Zainabu, ke kenan kullum kina kan hanyar zuwa gidansu, ita kuwa idan zan lissafa zuwanta gidanmu baifi sau ɗaya ba, to ni ba zani ba, zanyi gaba kya taho”.
Ban tsaya jin ta bakinta ba nayi gaba abuna, ita kuma ta shige gidansu Zainabu, a rayuwata Zainabu na bani haushi, ba wai dan wani saɓani ya taɓa shiga tsakaninmu ba, shegen son girmanta ne yake haɗani da ita da kuma faɗin rai, gata aba kamar guntun kashi.
A dai-dai lokacin dana iso ƙofar gidan Liman Naci karo da wata arniyar farar mota a bakin masallacin gidan, ban shiga gidan ba sai dana gama ƙarewa motar kallo, irin waɗannan motocin dana fi cin karo dasu a binni irinsu nakewa Ya Kabiru da Ya Amadu fatan mallaka, duk dana san mallakarsu sai mai shi, wanda ya tara ya ajiye, su kuwa basu ajiye ba basu bawa wani ajiya ba.
Har na shiga gidan Liman ban bar santin motar nan ba, dan harga Allah ta gama tafiya dani, zanso ace ko ɗana ni acikinta ne ayi. Na jima ina ƙwala sallama a tsakar gidan ba’a amsa ba, dana gaji sai nasa kai na wuce ɓangaren Baaba Lami, a falonta na sameta zaune tana shafa man zafi a ƙafa, na ƙarasa kan kujerarta na zauna, yanda naji iska na kaɗawa ta ko’ina a ɗakin yasa na miƙe akan doguwar kujerar tata ina lumshe ido tare da sauke nunfashi, lokaci ɗaya naji idanuna sun fara rurrufewa bacci na neman ɗaukata.
“Mairo ke har yau dai baki koyo yanda ake sallama ba ko?”. Na karkace na gyara kwanciyata ina wani daɗa lumshe ido. “Baaba ni kuwa sallama yau ai nayi harda ta siyarwa a gidan nan. Nayi sallama tafi biyar ba’a amsani ba, shi yasa koda nazo nan naga ba saina ƙara yin wata ba tunda duka na haɗa daga can…sai dai gaisuwa da banki ba, amma yanzu ina yini”.
Ta harareni da faɗin,”bana amsawa”. Sanannan ta hau mita akan lamarin Mama matar Liman kenan, saita shige can ƙuryar ɗaka a shigo gida aita ɗaka sallama shiru, wani lokacinma har ayi zaton ko basa nanne, a hakane kwanaki ma aka sacewa Isma’il sabon machine ɗinsa da Yayan Liman na binni yayi masa kyautarsa.
Barci harya fara ɗaukana kuma saina farka nace da ita,”Gwaggo na gaisheki da yi miki sannu da ƙafa, wai idan ta sami lokaci zata shigo ta gaisheki. Ta bada Nakiya akawo miki tana wurin Adawiyya zata ƙaraso da ita, tace ki adana mata langarta karki salwantar mata da ita”.
“amma dai saƙon ƙarshe naki ne ko Mairo?”. Idanuna a rufe nace,”bari Adawiyyan tazo kiji daga bakinta”. Daga haka bacci ya ɗaukeni, iskar fankar ɗakin na daɗa kashe min jiki.
Ban farka ba sai ana gab da sallar magriba, a firgice na tashi ina tambayar Baaba Lami ba dai Adawiyya har tazo ta tafi ba. Tace min ita ai ko inuwar Adawiyya ma bata gani ba, dama tasan ƙaryata ce na zancen Nakiya, nasa ta saka rai yawun bakinta harda tsinkewa.
Haushi ya gumeni akan Adawiyya, ni dama nasan idan taje gidan su Zainabu ba zata hankalta da lokaci ba, kuma yanzu da za’aje gida Gwaggo na tashi faɗanta akaina zata sauke, tace ai tasan nice. Banwa Baaba Lami sallama ba nai ficewata fuuuu, ina jinta tana agaida na gaba.
A bakin kwana na tarar da Adawiyya a tsaye ta ƙurawa wuri ɗaya ido, langar Gwaggo kuma a ƙasa, murfin langar yayi gefe guda, wanda ya bani tabbacin ɓari ne akayi. Na ɗau langar ina kallon Nakiyar da duk ƙasa ta buɗe samanta, sannan na ɗago na dubeta datayi tsaye ƙeƙam kamar wadda aka dasa, baki na taɓa na ɗau murfin na rufe, nace da ita mu tafi tunda an fasa zuwa kai aiken.
Sai naga ta juyo ta dubeni hawaye na sauka a fuskarta, na waro ido ina tambayarta lafiya? Me aka mata? Me ya faru?. Tasa hannu ta goge hawayen, batace min komai ba ta miƙo hannu dan karɓar langar, saina ƙi bata, nace wallahi saita faɗa min abunda ya faru, garinma ya akai langar da aka gama mana gargaɗi akanta ta fashe haka? Har ƙasa kuma ta shiga cikin nakiyar, ko tuntuɓe tayi?.
Ta kuma girgiza min kai akaro na ba adadi da naketa jero mata tambaya.
Bata bani amsa ba sai dataga ina shirin tafiya na barta sannan tace,”wanine mukayi karo da shi, kamin na ɗago na bashi haƙuri ya hauni da zagi iri-iri na cin mutunci wai ai da gangan na bige shi, harda cewa dama mu ƴan ƙauye bamu da ɗa’a, babu ilimin komai a tare damu sai jahilci, banda tsantsar jahilci me zai hanani kallon gabana ina tafiya, haka kawai nazo na goge shi da koɗaɗɗun kayana marasa tsarki.Shine Auwalu ɗan gidan Malam Ladan ya karɓe da cewa ai dama indai Ƴaƴan Matsiyacin mutumin nanne me farin gemu haka muke, sam ba mutumci a tare damu sai tsiya, an girkemu a gida anƙi aurarwa sai aikin yawon kwararo da mukeyi…”. Adawiyya bata ƙarasa min ba nasa hannu na toshe bakinta, domin ba zancen marasa mutuncin nake so naji ta ƙarasa min ba, martanin data maida musu nake so naji. Buɗar bakinta sai ce min tayi ai babu abunda tace musu, ita dama abunda yafi mata ciwo kalmar matsiyaci da Auwalu ya kira Baba da ita, Shi kuwa wanda ta buge dama laifinta ne tunda ita taho kai a sunkuye tana sosa ido abu ya faɗa mata.
Takaici ya cikani, naja tsaki ina jin kamar na rufe Adawiyya da duka, ta wannan fannin na rashin bakinta tana bani haushi, sai acuceta tace ba zata rama ba, tafi gane ta bar abun ya dameta ko kuma tace zatayi kuka ahakane zata huce.
“amma ke dai kuwa anyi shashasha, wawiya kuma doluwa. Ke yanzu har wannan ƙazamin yaron Auwalu ne zai tsaya yana gasa miki magana kiyi shiru baki mayar masa da wadda taci uwar tasa zafi ba, mtswww wallahi Adawiyya sam baki haɗu ba, ji nake kamar na zubar dake anan nayita dukanki har sai kin daina nunfashi, har ataɓa mutuncin mahaifinmu a taɓa mutuncin gidanmu kuma kija baki kiyi shiru…to naji sunan Auwalu, shi ɗayan wanda unguwar zoma bata gasa masa baki ba wanene shi?”.
Ta dubeni tana cewa, “kinga Mairo dan Allah mu bar zancen nan. Komai ya wuce kansu suka yiwa ai”. Na fizge daga riƙon data yi min, “kin san Allah ko ki faɗa min ko kuma na juya gidan Ladan ɗin na jira har shi Auwalun ya dawo, idan yaso shi sai ya faɗa min ɗaya ɗan iskan…”. Tasa hannu ta rufe min baki tana zaro ido, harda waige ta gani ko da wani a kusa, murya acan ƙasa tace min, “Mairo ki rufa mana asiri, ɗayan fa ɗan birni ne, ke bakiga yanda jini ke yawo ajikinsa ba kamar zai tsallo waje ya fito, inamu ina ja da wannan, Allah kuwa arniyar motar daya shiga kamar ta ƴan yan kan kai, wannan idan kika ce zakiyi masa rashin kunya ai sai yasa a kamamu, ina jinma ɗan sanda ne dan baƙaƙen ƙaya ne ajikinsa, dan Allah Mairo kiyi haƙuri ki ajiye wannan jin kan naki a gefe, ki wuce muje mu kai saƙon nan mu tafi gida a salama”.
Ban ƙara tabbatarwa da Adawiyya wawiya bace sai yau, a yau ɗinma yanzu da take ce min wai na ƙyale mutumin dayaci mutuncin mahaifinmu. Idanuna sukai jajur suka kuma yo waje kamar zasu fito, zuciyata tazo wuya, na kai hannu na maƙuro wuyan Adawiyya nace wallahi kota nuna min hanyar da tsinannan mutumin nan yabi ko kuma duk abunda nayi mata ita taja, dataji zafin shaƙar dana yi mata ba shiri tayi min nuni da hannu, na kalla gabanmu inda motar ɗazu dana gani ƙofar gidan Liman ke fake a bakin wani shago. “shine da wancan motar?”. Ta ɗaga min kai alamar ehh, na tambayeta shima Auwalun yana cikin motar? Tace min ehh tare taga sun shiga, na miƙa mata langar hannuna nace ta riƙe abarta, ta kuma wuce muje, zatayi min turjiyar tafiya na figi hannunta muka wuce, isarmu bakin motar na tsuguna na ɗauki dutse, da ƙarfi na shiga ƙwanƙwasa gilashin motar da yake a zuge yanda zasufi jina su buɗe, babu wanda kake ganowa daga ciki saboda duhunsa, acikin zafin nama aka zuge gilashin. Cikin wata kakkausar murya wanda ke zaune wajen matuƙi yace, “ke wace iriyar mahaukaciya ce zakizo kina dukan glass ɗin mota da dutse”. Ban kalle shi ba, dan gaba ɗaya na tattara hankalina ga leƙen cikin motar, idona babu wanda yake so yay tozali da shi inba Auwalu ba, Amma shima na bashi amsa da cewar mahaukaciya na gida ya barota.
SIRRIN ƁOYE

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button