NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Karna ji ƙorafi, ayi haƙuri da ɗan kaɗan ɗin da aka samu????.

Plss Comment&Share.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

Shafin Gaba Ɗaya Sadaukarwa Ne Ga Masu Sharing Wannan Book Ɗin, Alkhairin Allah ya isa gareku.

33)
Yagana ta gyara ɗaurin zane ta gyara zaman mayafi ta fuskanci Kabiru da kyau sannan tace,”Kabiru, ka buɗe min ɗakin nan yarinyar nan ta fito, shin da wanne kuke so taji?, memakonku ku lallasheta sai a ƙarke da kulleta, tsakani da Allah wannan ai ba kyautuwa bace…ka buɗe dan Allah”. ya kaɗa kansa ya juya ya fi ce baice da ita komai ba, tabbas ya riga ya sani a irin taurin kai na Mairo kamar kafirunal ula babu abinda zai dakatar da ita daga abinda tai niyya a wannan lokacin, shi yasa ba zai buɗeta ba ko da kuwa zata mutu aciki ne, indai taurin kaine ba ita kaɗai ta iya ba, shima ya iya, kuma zai iya rantsewa ya takata ya dame.
ganin ya fice Yagana ta juyo cikin gida jiki a mace kamar wadda akaiwa duka, ba don komai ba sai dan yanda cikin ƙanƙanen lokaci wai har wannan maganar ta baza gari dan abin takaici. ƙofar gidansu maƙil jama’a kowa na tofa albarkacin bakinsa, hatta Malam daya fito zuwa masallaci kasa fita yay sai dawowa yay.
“amma dai wallahi anji kunya, a haka kamar ta Allah ashe fir’auna a zuci ne. ni dai zaman haukar nan naki dama ba tun yau na dasa masa ayar tambaya ba. ai yanda Marigayiya ta dinƙa ƙumbiy ƙumbiya dake na soma shan jinin jikina, to tunda asiri ya tonu sai kizo ki fi ce ki bar mana gida ki koma inda aka koroki dan ba zakija sunan gidanmu ya ɓaci ba. ina dalili haka kawai babu dangin iya ba na Baba. dama Allah ba azzalumin bawansa bane, muna cikin gida an munafurcemu an ɓoye mana ai dole Allah ya saka mana”.
Kulu tai mutuwar tsaye tana duban Amarya da mamaki, sai dai ko kaɗan bataga laifinta ba. duk da cewar a zatonta ma ko Zulai ce zata tanka ma ta to amma ita batace komai ba sai ƴan habaice-habaice da ta hau yi, shima kuma da Malam ta ke.
Yagana ta kama hannunta suka wuce ɗakin Gwaggo, tare da cewa Amadu idan ya idar da sallah ya faɗawa Malam tana nemansa. Yagana tasa gefen mayafinta tana gogewa Kulu hawayenta, wacce zuciyarta ke gab da bugawa a halin yanzu saboda wani abu da ta ke ji yana taso ma ta. “ki bar kuka Kulu, ƙaddara ce a rubuce ta ke kuma babu wanda ya isa ya kauce ma ta, matuƙar kinyi imani to ki karɓeta a duk yanda tazo miki. Amadu ya sanar min da irin ɗibar albarkar da shashashar yarinyar can tayi, kiyi haƙuri ranta ne ya ɓaci kuma akwai ƙuruciya akanta dole ai ma ta uzuri, gani zatai koma mene laifinki ne kuma da gangan kika aikata, kafin ta fahimceki dole sai ki fuskanci ɓacin rai”. Kulu ta saka hannu ta goge hawaye kan tace,”Yagana ni yanzu tashin hankalina ɗaya ne, idan ba’a riƙeta ba tabbas saita aiwatar da abinda ta faɗa. wannan ƙazantar har ina…”. tai shiru na tsawon daƙiƙa saboda kukan daya ci ƙarfinta.”Allah ya jiƙan Yaya dama ta faɗa, sai abinda na gani. kuma tun farko laifinmu ne da bamu nuna mata cewar nima uwa ce ba wai abar ƙyama ba, ta yanda ko ƙaƙane zata ji ƙaina a zuciyarta”. Yagana ta shafa bayanta,”kinga komai fa zai zama da sauƙi, yanzu kawai dan tana kan dokin zuciya ne. da zarar ta huce shikenan zata tuna cewar ke ɗin nan kece dai Uwa, Uwar gaske da ake nufi bata wasa ba, Uwa me daraja”. Sallamar Malam da Amadu ta karkata hankalinsu garesu, Yagana ce kawai ta iya amsawa, suka nemi wuri suka zauna, daga baya kuma Kabiru ya shigo shima har lokacin jikinsa bai bar rawa ba saboda ɓacin ran dake tare da shi.
“ina Adamu”. Yagana ta kira sunan Malam. “na’am”. “yauwa kana jina ai, yanzu tunda anzo kan wannan gaɓar, to zaman Kulu a tare damu ya ƙare. dama duk dan wa akeyi?, dan ita wadda ba’aso ta sani ne, to ja’irar yanzu taji komai ta kuma san wace ita.
saboda haka kamar muka alƙawaranta cewar duk ranar da Mairo ta girma mukai ma ta aure to zaki faɗa mana inda iyayenki suke mu maidaki garesu, to kana taka Allah na tasa gashi yanda muka tsara ba hakan ce ta kasance ba. saboda ni anawa ganin tun wuri a gobe-goben nan ki shirya mu wuce mu tafi inda kika fito, dan ci gaba da zamanki anan babu abinda zai jawo miki fa ce tsangwama daga mutanen gidan nan dama jama’ar gari…Auwalu kana?”. Malam ya ƙara amsawa,”gani nan Yagana”. “to me kace?”. yace,”ehh hakan shine dai-dai, wannan shine ma abinda ya kamata ayi tuntuni”. Yagana ta kaɗa kai,”yauwa, to yanzu ke ina ne garinku?”. “ni ƴar ƙasar Qatar ce”. “ina ne kuma haka?”. Kabiru yace,”can ƙasar larabawa ce, daga inda nake zaune bamu da nisa”. Yagana ta wani zabura ta dafe ƙirji tare da waro ido,”kai dan manzon Allah?”. “ƙwarai kuwa Yagana”. Amadu ya faɗa. saita waiga ta dubi Kulu,”Kulu dama wannan hasken naki na larabawa ne?, kai jama’a ni Rakiya inda raina nata ganin abin mamaki, to garin ya haka ta kasance, me ya jefoki wannan ƙasar tamu?”. Malam dake gefe ya bata amsa da,”Qaddara”. Yagana ta jinjina kai da cewar,”ƙwarai sai ita ɗin kuwa, amma abin da mamaki, Kulu to dama kuna da ƴan’uwa ne anan ko kawai kurciyar da aka miki ne ta saukeki anan bichi?”. Malam ya ƙara ce ma ta,”ai Yagana wannan christan ɗin da Mairo ta faɗa hannunsu sanda ta ɓata shine yay ma ta cikin”. da Yagana ta doka wani uban salatin da sai da ƴan tsakar gida suka ji, ta zabura ta miƙe tsaye tana karkaɓe zane, “kirista, yo dama ke kirista ce shine harda danƙarawa kanki Hauwa saboda son zuciya. amma kuwa wannan mata baki ji daɗin halinki ba, yo nifa ince ya za’ai musulman ƙwarai suka kasa amsar ƙaddara dan ubangiji ya jarabci ƴarsu da yin cikin shege, wallahi tun a lokacin lissafina ne ya kunce amma nai ƙoƙarin ince muje gaban iyayen naki naji ko islamiya ce basu je ba, to ashema me ɗungurungun ɗinne ma musuluncinma babu bare har ai imani da ƙaddara, ashe jikar Yesu ce ke”. sai da tai shiru sannan Malam ya sami damar cewa,”Yagana bafa wai itace kirista ɗin ba, shi wanda yay ma ta fyaɗen shine kirista”. tai guntun tsaki,”to me maraba, kirista ai ɗan uwansa kirista kamar yanda musulmi sai ƴar’uwarsa musulma”. ta fuskanci Kulu da cewa,”to kinga Allah tunda dai anzo ga haka, ki tashi tun daren nan ki kama hannun ƴarki ku tafi, tun ubanta beji kuna nan ba, azo ai mana saukar aradu da ka muna cikin kwanciyr hankalinmu, ina mu ina jawa garin bichi faɗan arna”. ta faɗa tana kama haɓa, Kabiru yay guntun tsoki yace,”kefa matsala ce dake wallah”. tace,”Kabiru gidan haya ma nan ya ganni ya ƙyale”. yay kamar ya tashi ya bar wajen Amadu ya dakatar da shi.
“Yagana ki gane ma wai, itafa musulma ce shi kuma kirstan, anata miki magana da yarenki amma kin gagara ganewa”. ta harari Kabiru tace,”ubana ɗaga muryarka ai ba ita zata sa na fahimta ba”. sai kuma ta juyo ga Malam,”ka shiga tsakanina da Ɗanka”. Malam yace da Kabiru,”karna kuma jin bakinka”.
Yagana ta dubi Kulu tana rissinar da kai a gabanta tace,”ashe da gangan kika turata can wajen ubanta, kika tashi hankalinmu anan mu bayin Allah. Allah sarki Suwaiba Allah ya saka ma ta. da kika san lokacin komawarta wurin ubanta yayi ai saiki tattara ku tafi tare gaba ɗaya, mu san sallama kikai mana, amma kina ganin yacca baiwar Allah nan Suwaiba ta kasance duk akan ƴarki, kika kuma ja baki kikai gummm saboda mugun hali irin naku na arna, dama ance kasa mutum a inuwa ya saka a rana”. Kulu ta gigice tace,”wallahi Yagana bani na turata ba, ikon ubangiji ne kawai”. Yagana ta taɓe baki,”daga baya kenan ingozi…ni wallahi da nasan kema kafirar ce ba zamu taimaka miki ba, tunda dama ai kun saba iskanci a junanku, to sai me dan kin haifi shegu”. Kulu ta shiga kaɗa kanta,”a’a ni ba kafira ba ce musulma ce, ƙaddara ce ta haɗamu da shi”. Yagana ta ɗaga ma ta hannu, “kinga kar kiyiwa ƙaddara sharri, ina dalili, haka kawai da anyi abu saiku ƙalawa Ƙaddara dan kunga bata da baki”. Amadu yace,”ni dai gaba ɗayana kaina a ɗaure yake, dan komai ganinsa nake tamkar shirin film ko wani labarin littafi. dan Allah Baba wannan abinda ke faruwa da gaske ne?”. Malam yace,”Amadu ya za’ai muyi wasa da irin wannan al’amarin”. “to amma Baba taya akai Kabir ya san da hakan amma ni ban sani ba?”. “zaka san komai daga bakin Kulu, nima ita nake jira ta faɗa mana ainihin tarihin rayuwarta”.
Kulu ta fashe da kuka sosai sannan ta soma da cewa,”mu biyu ne kaɗai a wurin mahaifinmu sarkin Qatar, tagwaye ne mu Aaliya da Akila. ni Akila ni ce ƙarama Aaliya itace babba.
kamanninmu ɗaya tamkar an tsaga kara, hakan yasa ba’a iya banbacemu saita awarwaron zinaren da aka saka mana a hannu. a kaf duniya idan aka cire iyayenmu babu wani mahaluƙi da yake gane kamanninmu sai Major. mun girma a wurin kakarmu wadda ta haifi Mahaifiyarmu sarauniyar ƙasar ethiopia. acan muka girma dan bamu koma gaban iyayenmu dindin ba saida muka shekara shekara goma sha ɗaya. kasancewar muna da tsayi kuma Allah ya hore mana dirin jiki ga kyau yasa muke da farin jini a wurin duk wani ɗa namiji. a wata ziyara da shugaban ƙasar nigeria ya kaiwa mahaifinmu na fara ganin Major Tosin, sanda na fito zanje lambu shaƙatawa, ni macece mai tsananin son kyau, duk inda kyau yake ina wurin, kuma duk inda naga abu me kyau ina ƙoƙarin naga na mallake shi matuƙar baifi ƙarfina ba. hakan yasa Ammin’mu ke min adu’ar Allah ya rangwanta min gudun kar wataran wannan son kyau ɗin ya cutar da ni, ta inda muka banbata da Aaliya kenan a halayya bayan zafin rai.
Major Kirista ne shi to amma a acikin arnan ma shi na dabanne, yana tsarin halitta da kyau taimakar wanda Allah yaywa rahma da samun hasken musulunci, ga duk macen da ta ɗora ido akansa zata so ace ta mallake shi domin bashi da makusa saita ɓangaren addini, ta ko’ina Major yayi, kafin haɗuwata da shi fuskar Aaliya nake sawa a gaba naita kallo ina jin daɗi saboda nasan duk wanda abu da zan gani me kyau ya biyo bayan kyan halittar da muke da shi, to amma dana haɗu da Major sai lamarin yasha banban.
duk da irin ƙarancin shekaruna a lokacin amma nasan mene SO domin an rainemu ne a gidan da ake wanzar da So, hakan yasa a kallo ɗaya zuciyata ta tabbatar min da ta kamu da Son Major. har naje lambu na zauna ina shaƙatawa hoton Major bai bar haskawa acikin ƙwayar idona ba tamkar yana gabana, a sanda Aaliya tazo kirana cewar Abi yace muje zamu gaisa da abokansa ba ƙaramin daɗi naji ba, dan har kasa controlling kaina nayi har Aaliya ta gane ta ke tsokanata.
kwanansu Major biyu a gidanmu kuma a wannan kwanaki na sami shiga a wajensa, kasancewar duk safiya ya kan shigo ɗakin motsa jiki kuma muma muna kasancewa aciki a wannan lokacin tare da Abi.
nasan cewar Babban mutum ne dan ya ajiye kamata, amma ko kaɗan hakan bai haneni kwaɗaituwa da shi ba, kuma har na kanji zuciyata na kishi kamar zata pieces idan naji yana waya da iyalinsa, a yanda ya ɗaukeni yake kula dani har ya kan sumbaceni kamar yanda ya lura al’adar gidanmu ce hakan, yana minne duk a matsayin ƴa da yake kallona a wajensa, bai san a tawa zuciyar ba haka bane.
lokacin da su major zasu tafi harda ni aka rakasu airpot, dan maƙalewa Abi nai nace saina bisu, son samuna ma Major ya tafi dani, tsarabar da Major ya bar min itace kayan kakin soya da yasa aka kawo masa, bayan tafiyarsa wannan kaya sai da suka zame min tamkar uniform saboda kawai idan na saka ina jin kaman shine ajikina.
bayan tsawon wani lokaci sai na shiga ran Major fiye da yanda tunani ke hasaso min…hmm wato shi namiji ne da yake da baiwar sarrafa harshe ta ɓangaren soyayya, mutum ne shi me kyan hali da dattako, Major ya ƙara siye zuciyata da irin salon soyayyarsa, kulawarsa da kuma kyautatawarsa.
muka fara gudanar da soyayyarmu me tsafta acikin sirri ba tare da sanin kowa ba hatta Aaliya dan itama sai daga baya na sanar ma ta, bayan da soyayyarmu tayi nisa tsakanina da Major, ita ta goya min baya ga cewar mun san abune mai wuya al’amarin aure da muke burin cimma ya kasance. dan muna da ilimin addini cikakke tun muna shekara takwas muka sauke alƙur’ani, kuma mun sauke manya manyan littafan addinin tun muna shakara goma. nasan da cewar akwai haramcin aure tsakanina da Major amma hakan bai dakatar dani daga soyayyarsa ba, ƙoƙarin da nake a kullum shine naga na dasa masa son addinin da yake shine na gaskiya har Allah yasa yace zai karɓi musulunci.
na gama tsara sauran rayuwata ne da Major, hakan yasa nake lissafin cewar rayuwata babu shi tamkar mutuwa ce.
ana haka kwatsam sarkin garin bichi ya kai ziyara cikin masarautarmu ta harar wato a ethiopia, da zai dawo Abbu ya bashi kyautar auren ƴarsa Hauwa. ƙanwar Kakarmu me suna Bella ita ta riƙe Hauwa tun tana ƙarama, sanda Bella zata taho ƙasar nan wurin Addi Hauwa ta taho tare damu, mun sami kusan shekara guda a ƙasar nan kafin na sanarwa da Bella halin da muke ciki ni da Major, tun bayan titsiyeni da tai akan ita bata yarda da yanda alaƙarmu ke tafiya da wannan kafirin ba.
ni kaina nasan na tako abinda yake da wuyar kasancewa, dan Bella ce tai sam bata yarda ba, idan har ma ta kuma jin wannan shirmen maganar a bakina saita saɓa min. ni kuma a lokacin yarinya ce me taurin kai dake da wuyar tanƙwaruwa, ta inda muka banbanta da Aaliya kenan.
hakan yasa naga babu dalilin da zaisa Bella ta yanke alaƙar dake tsakanina da Major dan kawai tana kakata, ai bata kai wannan matsayin ba tunda aurena ba’a hannunta yake ba, mutum biyu nasan zasu iya zartar da maganar aure akaina na kasa ƙetarewa sune iyayen da suka kawoni duniya sai Jadda(Kakarmu da ta rainemu), bayansu ina ga babu me isa da iko akan aurena, haka zalika ba’a isa a hanani abinda nake so ba, bayan tunda nazo duniya ban taɓa son abu na rasa shi ba, ko menene shi Jadda sai tayi yanda akai muka same shi, hakama Abi, mutuwa ce kawai zamuce muna ya hanamu mallakarta itama kuma dan yana gudun karta rabamu da shi ne.
Yarinya ce ni da ban fiya jin shawara ba, hasalima me min magana naji Aaliya ce kawai, ba wai ina da ƙiriniya ko fitina ba, a’a abinda zuciyata tace shi kawai nake yi, ba kuma na abinda zaisa na kauce hanya ba. shi yasa ko a sanda Fadila ke ban shawara na nuna ban jita ba balle har nai tunanin ɗauka, tunda har Aaliya ta mara min baya magana ta ƙare.
ganin Bella da gasken gaske ta ke saita raba alaƙata da Major, hakan yasa na sanar masa da halin da ake ciki, shima ya nuna min cewar ba zai iya haƙura dani ba, nima kuma na nuna masa ba zan iya haƙura da shi ba. dan haka na yanke shawarar ya saya min ticket naje na sanar da Abi shi zai san abinyi, ai Bella ba ita ta isa dani ba, ko Aaliya bata sani ba muka wuce Qatar ni da Major, danma sai bayan mun sauka ne Bella ta kira Ammi tana tambayata tace ma ta ehh nazo ni da Uncle ɗina babu jimawa.
sanda na sanar da iyayena ba ƙaramin mamaki da kuma jinjinawa rashin hankali da kuma kunya irin tawa sukai ba. kuma Abbi ya sanar da Major wannan hanyar da aka ɗauko ba me ɓullewa bace, ya haƙura da ni tunda shi mutum ne babba daya san ya kamata, ni kuma ina da ƙuruciyar da ban gama haɗa hankalin kaina ba, ni kuwa a yanda nake jina zan iya rantsewa nafi kowa ma cikar hankali da sanin abinda ya kamata.
duk ta yanda naso abin ya faskara, kowa yaƙi goyan baya, ga Major da nake ganin yabi maganar Abi yana neman ya rabu dani, dalilin da yasa na shiga tashin hankali matuƙa a lokacin, ganin da gaske za’a rabani da abin so na, har na kamu da ciwon zuciya, ciwon zuciyar daya kaini ga kwanciyar asibiti.
kuma a lokacin kowa yay fushi dani, a asibiti ma Jadda da Ammi ne tare dani kawai, sai Jadd(mahaifin Abi) daya zo shima yay min kacakaca ba dan zuwa dubiya ba. Ammi ita ta kira Major yazo ya lallashe ni ya taushi zuciyata ko Allah zaisa a sami sauƙin abinda likitoci ke faɗa, shi kansa daya zo sai da hankalinsa ya tashi, hakan yasa shi yin alƙawarin da bai shirya ba, na cewar zai musulunta saboda ya aureni, kuma naji daɗin hakan matuƙa dan ko kwana biyu ban ƙara a asibitin ba na warware aka sallamemu.
a tunanina ƙarshen matsalar tazo, ashe sabon fegi ne za’a buɗe, dan da muka komawa da Abi maganar sai ya ce duk da haka ba zai aura min shi ba, sai in har zai musulunta ne domin Allah ba dan auran ƴarsa ba. shi kuma Major ya ce shi mutum ne da baya ƙarya balle yaudara, ya faɗa musu gaskiyar abinda ke zuciyarsa kuma wanda zai iya, amma duk da haka Abi da Abbu da Jadd suka ce a’a. ni kuma naga ina dalili tunda dai yace zai musulunta kuma sai a hana shi?, kawai saina yanke mana shawarar mu tafi wajen wani sarkin musulumin ya amsa musulunci a hannunsa sai kawai a ɗaura mana aure. nasan duk tsiya in har ya musulunta ɗin dole kowa ya haƙura. dan haka a ranar muka yiwa saudiya shigar dare, muka sauka a hotel da zummar da safe zamu isa wajen sarkin musulmai na ƙasar Major ya karɓi musulunci a hannunsa. ashe tsautsayi ne ya kirani wannan tafiyar, cikin dare ina cikin bacci sai ji nai Major na amfani da ni. sam ba’a hayyacinsa yay min fyaɗe ba, dan ya farka ne shan ruwan dare sai yasha barasa yay overdose har ya fita daga hankalinsa gaba ɗaya. nayi kuka, nayi kuka kamar raina zai fita, yanda nake kuka shima haka yake kuka a wannan lokacin, banda tsine masa babu abinda nake yi shi kuma yana bani haƙuri. nayi niyyar na kai Major kotu amma sai Aaliya ta hanani, amma duk da hakan ban haƙura ba na ƙudurta cewar sai nasa yayi nadamar da bai taɓa yi ba a rayuwarsa. babu wanda ya san da abinda ya faru dan mun rufe abinmu ni da ƴar’uwata, na koma gida naci gaba da rayuwata zuwa lokacin na cire Major a raina dan babu sbinda na tsana sama da shi.
rayuwata taci gaba da tafiya kamar ta ainihi kowa na murna, kuma har Abi ya haɗa min gagarumar walima dan jin daɗina. har sanda Bella ta dawo gida, kuma da zata dawo nigeria muka kuma biyota, bayan dawowarmu na fahimci cewar inada ciki.
na yanke shawarar zuwa nayi abortion Aaliya ta hanani, amma naƙi ji na kama hanya babu wanda ya sani na tafi asibiti, da naje likita ya tabbatar min in har akace za’ai abortion nasa zan sami matsala kasancewata ƙaramar yarinya mahaifata zata mutu gaba ɗaya, nace eh na amince, sai da akazo yi sai akaga ba zai yiwu ba saboda ƙunguna na maza ne, hasalima ko haihuwa zanyi sai dai ai min aiki.
na dawo gida cikin takaici da tunanin neman mafita, dan nasan duk ranar da aka gane inada ciki na gama kaɗewa, na ƙudurta barin gida na shiga duniya amma Aaliya ta dakatar dani, tace a’a mu zauna har zuwa lokacin da zai fito muga yanda ubangiji zaiyi hukuncinsa.
alƙalami yayi kaɗan ya faɗi irin tashin hankalin da nake ciki a wannan lokacin, kuma duk da abinda akaina yake amma tashin hankalin da ƴar’uwata ke ciki ya ninka nawa. na sha magungunan abortion sunfi kala a ƙirga dan har order na dingayi amma duka a banza, ga shi inata neman wayar Major na rasa, tsanarsa ta ƙara ninkuwa a saman ta da.
wani dare mun fito daga turakar me martaba mun an gama hira, zamu wuce ɗaki Bella ta kira sunana, tace da Aaliya ita ta wuce ta kwanta. gabana sai daya faɗi, dan ajikina na san maganar da zata fito daga bakin Bella, dan zuwa wannan lokacin cikina ya fara fitowa, maganar ma da Aaliya tai min a ɗazu kenan muka kasa samun solution.
“cikin wane ajikinki?”. tambayar da Bella ta jefo min kenan sanda na zauna kusa da ita akan kujera. naji wani ras, na kuma ji maganar da girma, to amma ɓoye-ɓoyen me zan tsaya yi?, ko nayi baida wani amfani dan shi ciki ba’a ɓoye shi, idanma na ɓoye akwai ranar da gaskiya zata fito, saboda haka ba kwane-kwance kai tsaye nace ma ta,”cikin Major”. amsar dana bata kenan, kuma cikin daƙiƙar dana bata amsar, cikin wannan daƙiƙar tasa aka watsomu daga cikin masarautar bichi.
haka ta ke, macece me alkhairi, macece da kaf dangi banga me mutuncinta ba, amma kuma daban ta ke da kowa a wajen yanke hukunci. na ciji yatsa har sai dana karya shi, dan ko kaɗan bamuyi tsammani ta yanda lamarin zai kasamce ba kenan. ko kaɗan banyi hawaye ba, amma kukan da Aaliya keyi a wannan lokacin zaks ce ne ma ko mutuwa ta rabamu da iyayenmu ne.
ba wai ban damu ba, zuciyata ce ta ke tafarfasa saboda baƙin cikin irin korar karen da akai mana, kamar mu ba jinin Bella bane, kuma kamar bata taɓa saninmu ba. irin tozarci da cin kashin da aka mana ba zai misaltu ba, hasalima Addi Hauwa cewa tai dama ai ta lura tunda nazo ƙasar nan nake bin maza, Bella kuwa ce tai babu mu babu ita ko a lahira kar mu nuna mun santa balle a wata ƙasa da t ke ƙasar haihuwarmu.
da Aaliya na musu magiya ji nai kamar nasa ƙafa na ta ke ta dan haushi, ehh nayi abun kunya, amma matsayinmu yafi ƙarfin mu tsuguna muna roƙo a gaban wata halittar. dan baƙin ciki ma da nace ma ta tashi mu tafi sai ce min tai wai na duba agogo sha ɗaya na dare ina muka dosa a wannan lokacin bayan bamu da kowa daya wuce nan, kuma ƙara roƙon Addi Hauwa ta ke akan su barmu zuwa safiya. ni kuwa nace sai dai ita ta koma ciki ta kwana, amma ni ko za’ai gunduwa-gunduwa da nama na babu abinda zai maida ƙafata cikin wannan wajen, masarautar da gaba ɗaya bata fi girman lambun gidanmu ba.
gaba da baya jinin sarauta ne mu, dan haka why Aaliya zata duƙa tana zubar mana da martabarmu da ƙasaitarmu, na ɗagota dan haushi na bata mari ko Allah zaisa ta saitu idanma barin hayyacinta tayi, naja hannunta muka bar ƙofar masarautar da ko a mafarki bana fatan na ƙara ganinta.
sarƙarta muka saida mukai kuɗin jirgi muka koma, sai dai ko da muka je ethiopia canma ba sauƙi, dan tuni har Bella ta kira waya ta sanar musu, suka ƙi amsata suka ce sai dai na koma wurin wanda yay min cikin muci gaba da rayuwa tare, Abbu yasa aka karɓe passport namu na shiga Qatar, Aaliya tace ba zata iya zama babu ni ba sai dai itama a koreta daga gidan.
dan haka bada saninta ba na gudu na bar ƙasar na koma london da zama har sanda cikina ya shiga wata tara, kwatsam watarana naje asibiti sai muka haɗu da Major shima yaje, an masa aiki an cire masa bullet dalilin wani harbi da ƴan bindiga sukai masa. har ga Allah soyayyar Major ta riga tayi ginuwar da ba zan iya kimantata acikin zuciyata ba, ina ganinsa saina manta da duk halin baƙin cikin da soyayyarsa ta jefani aciki, da baƙin tabon daya bar min.
shima cikin tsananin tausayina ya rungummeni yana ƙara bani haƙurin abinda ya faru, abinka da Mace raunin duk sai ya ban tausayi ganin Babban mutum kamarsa yana kuka da kuma tarin nadama ɓaro-ɓaro shimfiɗe akan fuskarsa.
tare muka dawo nigeria da shi inda ya sa ni a wani gidansa na nan kano, duk bayan kwana biyu yana zuwa wajena kasancewar shi yana zaune ne a abuja. ranar dana tashi da naƙuda baya garin, Aliya ta ɗaukeni muka tafi asibiti shi kuma yace gashi nan zaizo ya samemu, sai da na kwan ɗaya ina labour ƙarshe sai CS aka min aka ciro min twins, maimakon naji ina sonsu sai naji kaf duniya babu waɗanda nake ƙi sama da su, dan tunda Major ya damƙa min su a hannuna naji kamar na murɗe musu kai, dan ko nono da akai akai na basu nace wallahi ba zan bayar ba sai dai a yanke min nonon na zauna a haka, babu yanda ba’ai dani ba naƙi, ga kuma ruwan nonon na zuba amma na ƙwammaci na sakeshi yana jiƙa jikina, ƙarshe sai Aaliya ce ta ɗau kofi ta tara ta zuba a fida ta basu suka sha sannan suka daina tsanyara kukan da suke.
shi kansa Major da farko yana ta murna da ƴaƴan musamman macen kasancewar cikin ƴaƴansa kaf babu mace, amma daga baya sai murnar tasa ta ɗauke, yace shi ba zai iya karɓarsu ba yana gudun girmansa ya zube a idon duniya, nima nace masa bana ƙaunarsu tunda ban samesu ta hanyar da ta dace ba, saboda haka ya zubasu a leda kawai yaje ya yasar dasu, ko kuma ya zubasu a kwali yaje ya ajiye me so idan ya gani ya ɗauka…”.
tarin daya sarƙe Kulu shi ya dakatar da ita daga bada labarin, abu kuma kamar wasa sai aman jini, nan da nan hankali ya tashi Malam yace ai sauri a kira me chemist, ita kuma tana cikin wannan hali babu sunan wanda ta ke kira saina Mairo har bakinta ya ɗauke.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button