NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

2)
Safiyar yau zaune nake kan kujera ina wanke-wake, yayin da Adawiyya kuma ke shara tsakar gida bayan kammala wankin bayi da tayi, can gefe kuma Inna Zulai ce tana lissafa mafitai da take sayarwa, sai Gwaggona dake kai da komowa zuwa madafa kasancewar yauma girki a hannunta yake. Inna Amarya kuwa na ɗaki bata fito ba, dan dama ita uwar ɗaka ce da wuya ka ganta a waje, indai ba wai ranar girkinta ba ko kuma ya kasance duka iyalan gidan ana zaune a tsakar gida. Baba ne ya fito daga ɗakinsa yana gyara zaman hularsa yake cewa da Adawiyya,”kira min Kabiru”. Ta ajiye tsinstiyar da take shara ta fita cikin hanzari domin cika umarnin Baba. Ni kuma na dubi mahaifin nawa da kyau ina yaba kyawunsa da kuma jin ƙaunarsa na ƙara fizgar duk wasu hudoji na jikina, ban ankare ba sai ji nayi hawaye sun cika min ido saboda tausayinsa, na lumshesu zuciyata na daɗa bugawa da sonsa da ƙaunarsa.
“Baba Sannu da fitowa”.
Nace da shi ina miƙewa na ƙarasa inda yake na karɓi buhun hannunsa da zai fita da shi, ba komai bane acikin buhun sai kayan faskaran ice.
Babana Adamu Hashimu asalin mutumin garin bichi ne dake cikin jihar kano, kuma sannane ne aciki da wajen ƙauyen bichi saboda sana’arsa ta siyar da itace wadda ya gada a wurin mahaifinsa Malam Hashimu, babu inda zaka shiga ka fita acikin ƙauyen bichi ka tambayi Malam Adamu me faskare ace maka ba’a sansa ba, ko kuma ka tambayi gidansa ba’a kawoka har dakalin gidanmu ba, Haka zalika shi ɗin manomi ne domin kuwa yana da gonaki har guda biyu a fagolo, sai dai a sakamakon ƙwacen gonakin da gwamnati tayi Babana ya rasasu dan ciki har da nasa guda biyun, haka yanaji yana gani babu yanda ya iya dole ya haƙura dasu dan bashi da inda zai kai kukansa a karɓar masa hakkinsa, sai dai ya kai kukansa ga sarki Rabba adalin shugaba, dan yace ba zai yafe musu ba, domin da albarkar wannan gonaki biyunne Baba ke noma abincin da za’aci a gidansa har na tsawon shekara, shinkafa, wanke, gero, masara, dawo, maiwa, waken suya da barkono duka suna daga cikin abinda Baba ke Nomawa.
Malam Adamu mutum ne mai mutumci da tsananin kyautatawa, kamilin dattijo mai wadatar zuci, bashi da kwaɗayin abin duniya ko kaɗan, hakan yasa girmansa da ƙimarsa ke ƙara yawaita a wurin jama’ar garin bichi, matan Malam Adamu huɗu, Hajiya Hajara itace matarsa ta farko wadda ya kaita saudiya tun silalla nada daraja, ayanda tarihi ya nuna Hajiya itace jarumar matarsa dan babu ruwanta da duk wata harkar fitintinu na kishiya ko kuma dangin miji, matar rufin asiri domin ko a wancan zamanin da Baba ke da ƙarfinsa Hajiya ta ɗauke masa nauyin karatun yaransu uku, Ƴaƴan wurinta biyu dana abokiyar zamanta ɗaya, wanda kaf cikin yaran gidanmu su kaɗai ne suka sami ilimin zamani na boko har matakin da suke akai yanzu na diploma, ƴaƴanta uku Kabiru, Aminu sai autarsu Safiya wadda a lokacin haihuwarta ne Hajiya ta rasu, itama kuma ranar data cika sati a duniya tabi bayan mahaifiyarta.
Inna Zulai itace matar Baba ta biyu, kuma itace sukai zama tare da Hajiya, fitinanniyar mata ce, dan ko da yaushe tana kan hanyar zuwa wurin bokaye a burinta na a lalata zamantakewar dake tsakanin Baba da Hajiya, sai dai har Hajiya ta rasu burinta bai cika ba Allah bai sa tayi nasara ba, akaf Matan Baba itace wadda taci gida domin ta tara Ƴaƴa da yawa, Amadu shine Babba, Sunusi, Mu’azzam, Lukman, Sadiya, Adawiyya, Mubarak, Saleh, Jamila da Habiba sai auta Zubaida.
Sai Gwaggona Suwaiba data zo mata ta uku, Mace mai sanyin hali dan bata faɗa ko kaɗan, sai dai akwai miskilanci, idan Inna Zulai zata zo tsakiyar kanta sau dubu ta sauke buyaginta Gwaggona ba zata ce mata kanzil ba, kuma mutane suna ta faɗin daga Hajiya sai Gwaggona a matan da Baba yayi sa’ar samu, saboda Gwaggo da Hajiya halinsu kusan ɗaya ne, banbacinsu Gwaggona miskila ce bata kuma ɗaukan rainin dangin miji ko kaɗan, Gwaggona ni ta fara haifa kuma sai dana shekara goma ciff a duniya sannan ta ƙara samun arziƙin haihuwa ta haifi Basma, Gwaggo da kanta ta shawarci Baba ya ƙaro aure, dan tun bayan haifata data yi taga haihuwa ta tsaya mata tsawon shekaru daga ita har Inna Zulai, ga Baba da son ƴaƴa dan kullum a adu’arsa Allah ya ƙara azurta shi da ƴaƴa na gari yake duk damu goma sha biyar da Allah ya bashi.
Aisha itace mata ta hudu a wurin Baba wadda muke kira da Inna Amarya ƴar gidan sarkin noman garinmu, Tsakanin Inna Amarya da Gwaggona sam babu wani abu waishi kishi, illa iyaka mutunta juna da suke. shekaru kusan goma sha biyu da Inna Amarya ta shafe a gidanmu bata taɓa haihuwa ba har yau, ko ɓarin ciki wannan, kuma dama tun bayan aurota babu jimawa na koma wajenta da zama, a ganina ba jin daɗin zaman wurin Gwaggona nake ba, dan ita takan hantare ni a wasu abubuwan da nake ko tayi min faɗa, amma ita kuwa Inna Amarya zallar gata ne take nuna min da sangarta, dama tun a lokacin data cewa Gwaggona zan koma wajenta Gwaggo tace mata ai gani nan indai zata iya da halina ta ɗauka.
bayan auro Innata Inna Zulai taci gaba da haihuwa dan yanzu haka ma wani cikin gareta, duk da ƴaƴa goma sha ɗaya data mallaka tace har yanzu bataci gida ba.
To tsakanin Inna Amarya ne ma da Inna Zulai ake samun ƴar tsama, dan ita Inna Amarya bata barin ta kwana, ko ba ita aka taɓa ba in har za’a taɓa Gwaggo to sai inda ƙarfinta ya ƙare, ita kuma Inna Zulai da shegen habaicin bala’i da bata gajiya da yinsa, martani kuma sai dai idan Inna Amarya bata ji ba, darajar Ya Amadu kaɗai Inna Zulai keci wataran har Inna Amarya ta ɗaga mata ƙafa, dan Ya Amadu mutum ne, idan baka sani ba ma zaka rantse kace Gwaggona ita ta tsuguna ta haife shi har Ya Kabiru, Ya Amadu sam bai ɗauko baƙin halin uwarsa ba, kuma baya goyon bayanta akan abubuwa marasa kyau da take, hasalima shi mai yawan yi mata nasiha ne wataran har ya tarasu duka uku yay musu nasiha, idan ya gama ta kaɗe zane tace ita dama ai ta jima da sallama shi, dan ba tun yau ba ta gama gane Gwaggo ta shanye mata ɗa, to saboda haka yaje gashi ga Gwaggon nan, da ace shi ɗaya ta haifa sai tayi kuka, to amma Allah ya bata da yawa, dan haka ba zata bari takaicinsa ya kasheta ba. Ya Amadu yana kuka da wannan halin na mahaifiyarsa sosai, dan sau tari yakan zubar da hawaye agaban Gwaggo sai dai Gwaggo ta lallashe shi ta ƙara bashi haƙuri, tace masa yaci gaba da haƙuri duk lalacewarta uwa ce, yaci gaba dayi mata adu’a Allah ya ganar da ita.
Gidamu ginin ƙasa ne daga ciki, daga waje kuma ginin bulo wanda babu ko fulasta ajikinsa, shima ginin bulo ɗin anyi shine babu jimawa, dan waccen shekarar ne lokacin da Ya Amadu yabi Yayan abokinsa lagos ya tayashi aikin company ɗin mahaifinsa acan, to a wannan lokacinne Ya Amadu ya dawo da shatara ta arziƙi da Baban Joseph ya haɗa masa, Kuma ko daya tashi dawowa Obi abokinsa shi ya dawo da shi ya kawo shi har ƙofar gida a danƙareriyar motar gidansu, shine har aka rushe ginin ƙasar ƙofar gidanmu aka tada na bulo, da shi dasu Ya Kabiru suka yi aikin dan ko ƙwandalarsu basu kashe ba a wurin neman me aiki, Sannan ni da Sadiya da Adawiyya da Lukman ya kaimu makarantar boko Government Secondary School Bichi, ya kuma ƙarawa Baba jarin itace, itama mahaifiyarsa ya ƙara mata jarin Mafitai da take siyarwa, sannan ya sarowa Gwaggona kwalaben manja yace take saidawa, sauran abunda ya rage masa kuma ya biya kuɗin koyan ɗinkin daya ke zuwa.
A wannan lokacin dai gidanmu an godewa Baban Joseph da kuma yi musu adu’ar samun hasken musulunci, ko ni idan naje makarantar boko sai na shiwa kafirin nan albarka, na kuma yi masa adu’ar Allah yasa ya musulunta, domin ta silarsa yau gani a makarantar boko da naketa fatan kasancewata aciki.
To ita dai Gwaggona da Yagana(Kakarmu ta wurin Uba) sam basa son hulɗar Ya Amadu da Obi kai harma da shi Joseph ɗin daya ke ɗauka matsayin uban gidansa, ayanda take nunawa ta tsani ahalinsu gaba ɗaya dukkuwa da basu taɓa ganin ko mutum ɗaya daga cikinsu ba, acewarta Obi ba abokin hulɗa bane karya dulmiyar mata da ɗa, ko kuma shi Joseph ɗin ya cutar da shi, dan arna abun tsoro ne, Baba ya kan fahimtar da ita akan alaƙar tasu ba wani aibu bane, ta dalilin hakan ma sai shi Amadu ya zama silar jawosu cikin musulunci, Gwaggo dai ba zata tanka ba illa iyaka taɓe baki da takeyi, kusan kuma duk sanda Ya Amadu zaice mata Oga Joseph na gaisheta sai tayi kunnen uwar shegu da shi, idan ya kuma magana tace ai taji, ranar nan kuma tace masa ita dai wannan gaisuwa da ake kawo mata kusan kullum tunda babu tsiyar da take ƙara mata a ƙyaleta, ko shi Joseph ɗin ya riƙe gaisuwarsa ko kuma shi Ya Amadu yake riƙe aiken saƙon iyaka shi, wani lokaci da sukayi waya da Oga Joseph tana zaune a wurin sai Ya Amadu yake ce masa itama Gwaggo na gaida shi, da alama shi Joseph ɗinne ya fara tambayarta, Ya Amadu na gama wayar ta dube shi tace ni Amadu a tarbiyar da nayi maka ban koya maka ƙarya ba, kuma daga yau idan ka ƙara cewa wannan zindiƙin kafirin ina gaisheshi wallahi sai ƙaga yanda zamu kwashe da kai acikin gidan nan, to fa daga wannan lokacin Gwaggo ta fara share Ya Amadu, ta koma kome zatayi sai dai Ya Kabiru, dan ko gaisuwar Ya Amadu sama-sama take amsa masa, babu shiri kuwa ya fara janyewa daga Oga Joseph koma nace ya janye gaba ɗaya, yana tare da shine dama saboda a rufawa kai asiri, tunda duk sanda ya buƙaci yay masa rakiya zuwa Lagos yana samun kuɗi sosai a wajensa, harma yayi masa alƙawarin zai yiwa Daddynsu magana a nema masa gurbin karatu a jami’a dan ya ɗora degree nasa tunda yana da diploma.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button