NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Ethiopia, Masarautar Baharar.
acikin tangamemen parlon, wasu tsaffi ne su huɗu zaune a ƙasan carpet ɗin da aka malale a saman tiles ɗin parlon, sun ɗora hannayensu akan tumtum ɗin dake aje a gefensu, yayin da wasu dattijawan Mata guda uku ke daga kan kujera a zaune, sai Suhail dake kan tashi kujerar shima yana mai kaɗa ƙafarsa guda ɗaya, idanuwansa a kulle yana ci gaba da sauraron abinda Bella ke faɗa masa na ga me da saƙon mai Martaba akan aurensa da Maryam.

Ya na iya da halin magiyarku, amma please and please you people should change, i need comment not sticker or thank you, iya bakin ƙoƙari ina faranta maku but i don know why ku kuke discouraging ena…anyway kusha karatu lafiya amma f ba wai na sakko ba ne, if ban kalla enogh comment ba whatsapp people ba xaku kalla next page ba….

Maman Islam na gode, Allah tunjimaki a gidan aljannah????.

Plss vote,share&comment.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

(41)
“Aure! Aure dai! ana nufin babu aure tsakanina da Maryam?, yarinyar daya saka a ransa tun bayan rasuwar matarsa Sanah, to me yasa ma za ai masa haka?”. zancen zucin da Suhail keyi kenan tun a lokacin daya kai maganar yana son ya auri Maryam gaban Mai Martaba, kuma har zuwa yanzu da Bella ke ƙara isar masa da saƙon Mai Martaba ɗin na cewar dole ne ya haƙura da batun auren Maryam saboda ƙarfaffan dalili.
“Suhail ko kana sonji ko baka sonji babu aure tsakaninku, ka zama uba a gareta wajan shayarwa tunda har kunsha nono ɗaya kai da mahaifiyarta…dan haka the charpter close kar na ƙara jin zancenta daga bakinka…ka nemi wata matar kawai”. Bella ke maganar cikin ɗaga murya me fitar da sautin faɗa.
ya buɗe ido ya kalleta haɗe da sauke dogon numfashi. maganar mahaifiyarsa ta ratsa ta cikin baƙin cikin da yake ji a zuciyarsa. “ni ban san ma dalilin daya sa baka son Zeenatu ba wallahi, yarinya me hankali da tarbiyya, ga ilimi, tana sonka ba wai bata sonka ba amma sai watsi kake da lamuranta…tukunna ma kana tunin zaka sami macen da zata iya riƙe maka ɗanka da amana ne sama da Zeenatu?”. ya mayar da ƙwayar idonsa kan Hajiya, murya a ƙasa yace. “dan Allah Hajjah ki bar min zancen wannan yarinyar, mene haɗin daddawa da kunu…ni ko banyi wani auren ba zan iya kula da Arif, dan shi ɗaya dai Allah na tuba”. Hajjah ta bishi da harara, Bibi(Kakarsu Akila) tace da shi. “ai ni yanda na fahimci take-takenka Suhail so kake kaje ka auro wacce ba jinin sarauta ba. ba kuma zamu lamunta ba, kasan da wannan”. “amma Bibi fisabilillahi shikenan sai ace dan kai ɗan sarauta ne auren bare ya haramta a gareka, a wanne hadisin ko ayar aka ce haka?…magana ta gaskiya ni bana son Zeenatu ba kuma zan aureta ba, kuma ni ba ƙaramin yaro bane da za’a min dole awajen aure, like i said zanyi breaking record for sure”.
yana faɗin hakan ɗacin dake ƙasan zuciyarsa na haskawa a saman fuskarsa.
“to in haka ne ka koma ka nemi auren ita yarinyar da ta asirceka mana…”. Maama tai maganar, kuma bata kai ga ƙarasawa ba yay saurin cewa,”wa ɗin?”. tai guntun murmushi,”ah tou Suhail wadda tai asiri akan samun soyayyarka ai masoyiya ce ta haƙiƙa, dan haka a shawarance kawai kaje ka nemi aurenta yanzu tunda ta tuba, kuma ina baka tabbacin zaka sami tsantsar soyayya daga gareta kamar yanda ta nuna maka, ni naga hakan a ƙwayar idonta ta cikin vedio call ɗin da akai da su, kuna ƙwarai haƙiƙa zata kula da Arif”. “ko matan duniya sun ƙare babu abinda zanyi da wannan abar kam, kima daina wannan zancen Maama, haƙurin da nai ma ban hukuntata ba wallahi darajar Maryam taci”.
“to yanzu dai ai an faɗa maka kuma kaji, wata ɗaya kacal Mai Martaba ya baka…kuma Suhail Zeenatu kawai zaka aura muyi farinciki da aurenka”. ya dubi Bella da kyau sannan ya taje gemunsa da yatsunsa, kana ya miƙe tsaye yana zira hannu a aljihu da nufar hanyar fita yana faɗin, “ni dai na faɗa zanyi breaking record, kamar yanda ba zanyi auren zumunci ba haka matar da zan auro bata da alaƙa da sarauta, idan ta zama mallakina ta sami wannan jinin”.
Bella ta bishi da faɗin,”ka jima ba kai breaking record ba Suhail…ma gani mu dai kai waya isa da wani”.
a hanyar lambu ya tarar da Jawad, suka wuce ɓangrensa tare. inda yana shiga ya sami kuyangar dake aiki a ɓangarensa tana jera kayan abinci a saman dining. tana ganinsa ta zube ƙasa tana miƙa gaisuwa, ya amsa ma ta fuska a sake sannan ya wuce bedroom nasa ya bar Jawad anan parlo. ya ɗau kusan minti goma sha biyar kamin ya fito, a parlon ya sami Jawad nama Arif wasa wanda aka ɗauko shi daga makaranta, ganin ɗan nasa yay smiling ɗin da haƙoransa suka ƙi rufuwa, dan matuƙa yana son Arif da tausayinsa. Mamansa ta rasu tun a ranar da ta haife shi dan ko ganinsa ba tai ba ta amsa kiran ubangijinta. shekaru huɗu kenan da rasuwarta har yau kuma ya kasa ƙara aure saboda Arif, ya kasa mantawa da ita, gani yake tamkar yaci amanarta ne idan yay tarayya da wata macen, kuma yana ganin kaman duk wadda zai aura ba zata riƙe masa ɗa da amana ba, haka ɗan ba zaiji daɗin zama da ita ba…tun bayan rasuwar matarsa Sanah bai ƙara jin son wata ƴa mace ba sai akan Maryam, wadda kawai yaji yana kwaɗayin ya mallaketa kuma zuciyarsa tai masa amanna da cewar yarinyar zata iya kula masa da Arif gwargwadon yanda yake buƙata, duk da yasan cewar itama Maryam ɗin rainonta ne zaiyi, to ashe ita ɗin ba rabonsa ba ce, a hankali ya rufe idonsa for a while sannan ya buɗe ya kira sunan Arif din, Arif ya sakko daga kan cinyar Jawad ya tafi wurin mahaifinsa da gudu shi kuma ya ɗauke shi ya rungume shi ajikinsa yana ta sumbatar fuskar yaron.
kuma sai hoton lokacin da Maryam ke yiwa Arif wasa ta cikin vedio call ya haska masa acikin kai, ya rumtse idonsa sosai yana mai jin wani abu na taso masa. “muje ayi wanka sai ai lunch ko?”. yace da yaron yana shafa kwantacciyar sumar kansa, Arif ɗin ya ɗaga masa kai. “ehh Abbi ina jin yunwa dama”. “baka ci abinci a school ba”. “ba zan iya ci ba idan babu kai”. ya faɗa yana shagwaɓe fuska. nan Suhail ya juya zuwa bedroom ɗinsa yana cewa da Jawad. “Yaro kai aure ka haifa kaima kaji irin abinda akeji”. Jawad ɗin na shafa wayarsa yace,”me akeji dama?”. “Jawad wani irin abu ne da ba zai fasaltu ba”. murmushi Jawad ɗin yay sannan yace,”soon nima zanyi, Maryam nake jira…ina so tai hankali ne kamin nai requesting ma ta abinda ke zuciyata”. Suhail ya waigo ya dube shi da tambayar. “me kake nufi da tai hankali?, kana nufin zaka ce Maryam bata haɗa hankalin da zaace wani ya mallaketa ba?”. “no ba haka nake nufi ba, just i can’t take her bulshit. you know well an raini yarinyar nan da shagwaɓa, kuma har yanzu ban manta da abinda ta min ba wancan ranar…”. “ohh idan na fahimci inda zancenka ya dosa zama ka aureta ne saboda kai ramuwar gayya”. Jawad ya murmusa yana miƙewa. “ko kaɗan, kawai dai”. “kawai dai me Jawad?”. “Suhail you will not understand so faɗa maka ma baya da amfani”. “shikenan, amma ka sa ni, aurenka da ita sai dai idan babu numfashi ajikin Suhail tunda har na gane manufarka…ka gama tsara shirinka ni kuma na maka alƙawarin saina lalata shi”.
Jawad ɗin ya motsa laɓɓansa yana wani killer smiling sannan ya fice bayan yace da Suhail ɗin,”na barka lafiya”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button