NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Nigeria, Bichi.
ƙafafunsa suka hau kan step na ƙarshe na shiga cikin parlon, hannunsa ɗaya saƙale da waya ɗayan kuma na cikin aljihun rigarsa, yayinda pink lips ɗinsa na ƙasa ke cikin bakinsa yana tsotsa, yana mai sauraron maganar dake fita ta cikin wayar.
“Ummi da gaske nake miki”. ya faɗa muryasa ta fita da amon da ba zai bada tabbacin shaidar abinda ya faɗa ba. daga cikin wayar Akila tai murmushi sannan tace,”naji, amma sai na gani daga ƙwayar idonka zan gasgata hakan Kabir…yanzu ya jikin nata?”. ya ɗan rufe ido sannan yace,”nima ban sa ni ba, sai dai ki kira likitan nata ki tambaye shi”. “waye likitan nata?”. “shi Ahmad ɗin mana”. daga cikin jirgin da Akila ta ke tai dariya kaɗan kamin tace, “yaushe kuma Ahmad ya zama likita banda labari, naga ma karatunsa is not related to health taya zaai ya zama likita Kabir?”. “da a gabanki ya dinƙa rawar jikin checking ɗinta da zuba bayanan ciwon zaki kira shi da ƙwararran likita wanda ya amsa lambar yabo”. bai bari ta kai ga wata maganar ba yace,”yau ɗin za ki dawo?”. “kamar na fasa dai, tunda nasan zaka bawa Maryam duk wata kulawa da ta dace”. yay gajeran murmushi sannan yace,”Ummi ki dawo ki kula da ƴarki kawai, ni gobe ma zan bar ƙasar”.
murmushi Akila tai sannan taci gaba da masa bayani akan maganar da suke yi wadda ta zama musababbin kiran nasa. yay shiru na kusan minti biyar kamin ya amsa da,”tom shikenan sai kin dawo ɗin…hope jakar tsarabata daban da ta kowa?”. “kaima ka sa ni ai Kabir”. da haka suka yanke wayar. daga bayansa yaji Yagana na faɗin,”ai Zulai nafi ƙarfin awa biyar tsaye anan wurin tun kamin hudowar rana, ni da ƙofar wajena amma anyi bake-bake an hanani shiga, kinga fa yanda ya wani bubbuɗe hannu ya kankame ƙofar, ni dai Rakiya ina ganin ta kaina a gidan nan, wai sunan gidan ɗana. ko da yake dama duk abinda yake ba mallakin ubanka ba dole sai an nuna maka iko da shi, Allah dai ya jiƙan Babana Manniru, da yana raye duk wannan walaƙancin na jikoki ba zan fuskance shi ba”. girgiza kan Kabir ya haɗe da murmushin Zulai wadda tace. “ai Yagana bai san da zuwanki ba ne, baki kalla waya yake ba”. “a’a fa Zulai ko baida ido ta ƙeya ai yaji ajikinsa ina bayansa…ki bar mutum ɗan walaƙanci kawai, kuma wallah da Kabiru ba haka yake ba, ko dan yay kuɗi ne Allah masani…bai san ni bana maula ba”. sai taima Zulai nuni da kayan hannunta,”kuma fa kinga tsabagen ƙaunarsa da nake wallah ɗakinsa naje na ɗebo kayansa zan bawa Nawwara ta goge masa…amma sam baya ganin kyautawar da nake masa, ke dai ai kin auna arziƙi da kika haifi ɗan ƙwarai kamar Amadu”. Zulai ta sake girgiza kai tana riƙe dariyarta, kamar ba jiya ne ta gama cewa Amadu baida kyan hali ba amma yanzu shi ta ke cewa ɗan ƙwarai. ta karbi kayan hannunta suka nufi entrance ɗin parlon. “Baba Kabiru zan wuce dan Allah”. tai maganar da muryar ban tausayi. Kabir yana murmushi yasa kai cikin parlon, sai dai abinda idanuwansa suka fara tozali da shine yasa shi yin reverse ba shiri, ganin Ahmad da yay yana feeding Maryam harda wani goge ma ta baki. yana kuma juyowar ne Yagana na sako kai tasa hannu ta tura shi ciki,”koma ai dama ina so nai magana da kai…muje ka faɗa min wannan halin miskilanci daga ina ya samo asali, idan kuma a hatsarin ka samo shi muje asibiti yanzu a cire shi daga kanka dan ba zan ɗauka ba”.
ya cije fuska tare da dunƙule hannu kamar zai kai naushi. “ina da wurin zuwa ne fa Yagana”. Yagana ta ɓata fuska tace,”Kabiru ka kalleni a matsayin Hajara ba Rakiya ba”. maganar tata tasa ya koma ya zauna kan kujera ba tare daya ko ƙara kallon dining area ɗin ba. daɗin daya ji kuma earport ɗin dake kunnesa duka biyu, duk da ba komai yake saurara ba amma hakan ya taimake shi, dan yana jin Ahmad na masa magana yay tamkar baima san da shi a wajen ba.
sai da Basma tazo ta zare masa tana ƴar dariya tace,”Yaya anata magana”. yay kamar da gasken dama baiji ba, yace. “ban jiki ba Basma”. “ai ba ni ba, Ya Ahmad ne”. “ohh”. ya faɗa yana waigawa inda ta masa nuni da shi, ya ɗan saki fuskarsa kaɗan kafin yace,”kai dama kana nan kasa naketa zaryar nemanka”.

The Chapter goes to you Matar Yawale????????, thank you for disturbing my life akan new update ko ba komi na rage nauyi…aradun Allah ba dan kin hana wayata sakat da kira ba i will not be updating right know????, amma fa kika ƙara takura min idan ba i will maka you a black list????.

ku kuma ƴan team Kabir kuci gaba da cewa Ahmad me ƙaton kai kuga yanda zamu kwashe daku????

https://globalnews.com.ng/2022/01/13/sirrin-%c9%93oye-page-41-hausa-novel/
Please Vote, Comment& Share.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

(42)
“mantawa da Yagana kai ko shi yasa ka kasa nemana a ɓangarenta?”. “karta jika kaja min magana”. Kabir ya faɗa yana shafa wayarsa, shi kuma Ahmad ya ɗan dara. “to ya akai?, ai na shiga wajenka baka nan time ɗin…nace kura tai lafiya kenan”. “ka bari kawai, exams enn ce tasa na wartsake ba shiri”. bai san me yasa ba, amma a duk wani furuci na Ahmad wani haushinsa ne yake tsarga masa, abinda bai taɓa ji ba dangane da ɗan’uwansa, kai wani ma daban ba shi ba.
gashi yaƙi yardarwa kansa da hakan a matsayin kishi ne, gani yake tunda har yaywa kansa alƙawarin cire yarinyar daga ransa to babu wani abu da zai dameshi ga me da ita, zaici gaba da kallonta ne matsayi ɗaya da su Adawiyya, kuma matar ƙanensa.
“idan ka tafi motarka fa?”. ba tare da Kabir ya dube shi ba yace,”kai zan barwa ai, kaga ka rage yawan huzzeling da ita”. “amma kuma daka barta ba’a kawo ba saika dawo nan ɗin kawai”. “idan baka manta wane ni ba, ba zaka mance da rashin sauya ra’ayina dana tsara ba tun farko”. “to godiya nake, Allah ya ƙara buɗi…kaga saina ƙara tarin kuɗina yanda nima zan mallaki babbar kai”. da kai kawai Kabir ya bashi amsa. shi kuma ya maida hankalinsa kan Maryam, wadda kanta ke sunkwiye tana zane da yatsanta guda ɗaya akan dining ɗin.
tayi tagumi da ɗayan hannunta, fuskarta na haskawa da damuwar dake ƙasan zuciyarta, ayau kaɗai wani mugun haushin Ya Kabir ta ke ji, haushin da inda ta kai matsayin da zata saka masa duka babu abinda zai hanata. tun a daren jiya da ta dawo hayyacinta taga kowa akanta yana ma ta sannu shi bata gansa ba ta fara jin haushinsa matuƙa, amma kuma a yau da ta farka da sanyin safiya taji wai ya tafi kai Nawwara school sai haushinsa ya ninku a ranta, wai mutumin da baida cikakkiyar lafiyar ƙafa shine harda su driving, driving ɗinma ba nan kusa ba can da nisa. inda Nawwara ɗiyar wani ƙusance saita kira kulawar da taga ya fara bata a matsayin neman gindin zama, to ita ba kowan kowa bace, duk da dai shi ɗin me tausayi ne da son kyautatawa wanda ba shi da shi, ba ayanzu da yay kuɗi ba, tunda sanda baya samu a ko da yaushe.
ita bata damu da sannunsa agareta ba, tunda ko yayi ma ta ko baiba zata warke, amma ta damu da janye ma ta da yay, wannan kulawar tasa gareta, wannan soyayyar da yake ma ta, wannan fara’ar tasa akanta duk ya ɗauke ma ta kai da su, tsakani da Allah taya saida ya saba ma ta da hakan kuma sannan zai janye ma ta a lokacin da ta ke jin kamar tafi buƙatarsa fiye da lokacin baya.
ta shiga ƙifta idanu kamar zata fashe da kuka, sanyin hannun Ya Ahmad da naji a saman goshina yasa na ɗago na dube shi da raunannun idanuna. “kin daina jin zafin ƙirjin?”. nai masa knodding kaina kawai ba tare da nai magana ba. “to asha maganin?”. na ɗaga masa kai still ina kallon ƙwayar idonsa dake nuna tsantsar damuwa da ciwon nawa da kuma nuna kulawa. sai na kwaɓe fuska ina tura baki gaba na girgiza masa kai alaman bana so. murmushi yay cikin murya mai taushi yace,”kiyi haƙuri kisha magani kinji, kinga baki da lafiya, kuma rashin lafiyanki baya barin kowa ya sami natsuwar zuciya da ta ruhi…ko ba ki son hankalin Mami ya kwanta ne?”. tambayar ƙarshe tasa na kaɗa masa alaman a’a, sai ya ɗora tafin hannunsa ƙasan haɓata da faɗin,”to kiyi haƙuri kisha kinji ƴar lelen Mami da Ummi”. a karon farko tun tashina daga barci nai murmushi, na kuma ci gaba da kallon gefen fuskarsa da a yanzu ya karkata yanawa Basma magana. lallai sanadin cuta kana cin wani arziƙin, banda ciwon nan ya ɗaga hankalin kowa ina zan sami wannan tarairayar a wurin boss ɗin gidanmu, Ya Ahmad ɗin da ko kasha magani ko karka sha ko a kwalar rigarsa, bana mantawa da idan naƙi shan magani bulala yake sawa ya zaule min jiki, shi yasa idan ina gardama kan magani da Gwaggo tace ku kira min Amadu babu shiri nake sha.
kuma kawai sai naji wani abu mai sanyi ya tsarga ta jikina da ban san menene shi ba, naci gaba da kallon laɓɓansa dake motsawa suna magana da Basma, duk da cewan laɓɓansa ba su kai na Ya Kabir kyau da burgewa ba amma shima kyan nasa nada iya gwargwadonsa, ko da yake kyan Innah yayi, Inna Zulai tana da kyau sosai kawai dai dan batai kyan hali bane a baya, dan yanzu kam Alhamdulillah Innah ta sauya hali ƙwarai dalilin isharar da ta gani, kuma ba komai ya firgitata ba irin yanda rayuwar Inna Amarya ta koma, haka zalika da yanda taga ubangiji ya maidani, abunda ta faɗa da bakinta cewar bata taɓa zaton zan iya taka wani matsayi ba, ashema ni ɗin na wuce gaban hakan.
“Ya Ahmad gashi”. Basma tace da shi sanda ta miƙo masa ledar magungunan daya sa ta ɗauko a ɗaki.
“bamu ruwa mara sanyi”. yace da ita yana aje ledan ya fito da tarukan magungunan ciki harda inhaler, gabana ya faɗi, wato a rayuwa kowa da kalar jarabawarsa, kamar ni daga wannan sai wannan, wai yau nice da cutar asthma, cutar da ta ɗaure kaina dama kowa nawa.
ina ganin ya fara ɓallo tablet ɗin na miƙe tsaye zan bar wajen ya ɗago da kansa, idonsa akaina muryarsa na shaida izinin na koma na zauna. kamar nayi masa gardama saina tuna a gaban wanda nake, da ƙyar da siɗin goshi nasha maganin, dan saida ya cire tausayina, ya daina lallamina ya shiga zazaga min wannan faɗan nasa da babu wanda ke ƙaunarsa.
“kin san Allah kika dawo da maganin nan saina ɗauke fuskarki da mari”. na kalleshi da idanuna da suka cika da ruwan hawaye amma basu zubo ba, naga da gasken yake maganarsa, na sauke hannuna daga toshe bakin da nai, ta dole na tsaida aman dake neman taso min.
cikin fishi na miƙe zan bar wajen muryasa a ɗage yace da ni,”koma ki zauna”. ina zama ya kuma haɗawa da jan dogon tsaki fuskarsa na ƙara haɗo ɓacin rai ta bayyanar.
Sadiya da Adawiyya da Jamila suka shigo da sallama, suka gaidasu Yaya sannan suka gaida Yagana, kamin mu gaisa dasu suyi min sannu da jiki. ina dubansu da muryata da har yanzu bata saki ba nace,”ina zaku je?”. Adawiyya tace,”ɗinkunan Sadiya zamu kai”. da yake an kusa bikinta saura sati huɗu gaba ɗaya. na miƙe tsaye ina faɗin,”dan Allah ku tsayani mu tafi tare”. “lallaima ke ɗin nan, ke da ba ki da lafiya”. nace,”naji sauƙi ai…baku taɓa zuwa dani ko’ina ba fa tunda aka fara shirin bikin nan, kuma inata son zuwa, sai dai naji Inna tace kun fita”. Jamila tace,”to ba Yagana ce ke ƙunsheki a ɗaki ba ta hanaki fitowa wajenmu, kinga kam ai bama yi tunanin kina son zuwa ba”. karaf maganartata a kunnen Yagana dake fitowa daga ɗakinta.
“ba dan ance ba kyau idan mutum ya tuba daga wani saɓo da yake tafkawa ba a dinga taso da abubuwan da aikata a baya, Jamila ai dana yaɓa miki magana akan Uwarki…kuma kije dan kanki idan sharri abinyi ne karki fasa”. ta zauna akan kujera tana ci gaba da faɗin,”dama na jima da faɗa miki wannan zaman keɓa kan da kike sai ya jawo min magana, ace ina rabaki dasu saboda naga yanzu ke ƴar wasu ƙusoshinne…gashi nan yanzu ina zaman zamana kinja min zagi da sanyin safiyar nan”. Jamila tace,”Allah baki haƙuri Yagana ni ban faɗa da wata manufa ba”. ta taɓe baki bata ce ma ta komai ba, ta maida hankalinta gun Ya Kabir tana faɗin,”Ɗan Hajara aina muka kwana da kai?”.
“Yagana na shirya na bisu ɗin?”. bata dubi inda nake ba tace,”wallahi ba zakije ba…na gama magana Maryam”. tana faɗin hakan nai ɗakina a zuciye, ina shiga kuma na shiga tattara kayana ina zubawa a trolly, ko ina za ni dasu oho.
da yamma ina kwance akan gadona cikin nurƙufanci Inna ta shigo ɗakin, dama tun da safen nan dana shigo na gama haɗa kayana ban kuma fita ba, abincin rana ma da Yagana tazo tai maganar duniya nai ma ta shiru naƙi kulata, har taji haushi tace indai sunanta Rakiya ba zata ƙara min magana bare na wulaƙantata.
“Maryam jikinne?”. Inna ta faɗa a sanda ta ke zama gefen gadon tana taɓa jikina. zafin da taji yasa ta ɗauke hannu tana faɗin,”subhanallah, kin ko sha maganinki ɗazu?”. kai kawai na ɗaga ma ta. ta sake cewa,”Allah ya baki lafiya, tashi muje ga Mu’azzam can yazo zai miki alluranki”. “Inna dan Allah bana son wannan allurar”. ta ɗagani daga kwancen tana faɗin,”nasan baki son allura amma ya za ki, dole ce tasa…daure ki tashi kinji ƴar albarka, ina aka taɓa zama da ciwo a jiki ba tare da an magance shi ba, abinda ma Mu’azzam ba shi da zafin hannu”.
Yagana ta shigo ɗakin itama. “ke ki fito ai miki allurarki dan yau ban shirya hana idona yin bacci ba”. muryata kaman zanyi kuka na ɗan doki ƙafata a ƙasa nace,”nifa Yagana yau a ɗakina zan kwana Allah ba zan hanaki bacci ba”. ta ɓalla min harara sannan tace,”kin san Allah ba ki isa ba allurar nan sai anyita, jiya ni ɗaya nasan me naji a zaman jinyarki…kema Zulai kin wani zauna kin zuba ma ta ido tana abinda taga dama, ta bakin Amadu ki figo hannunta kawai”. na ƙara ɓata rai ina cewa,”to ni dai Yagana ki rabu dani mana tunda ba’a dole”. ina faɗin hakan tasa kai ta fita daga ɗakin tana jijjiga kai.
a parlon Yagana, Baba ne da Manyan Ƴaƴansa zaune, cikinsu Ya Kabir ne kawai babu. kuma ganinsu baisa na daina kukan karɓar allurar ba. Mu’azzam ya ɓare syringe ɗin yana zuƙar ruwan alluran, na tafi wurin Baba na ƙanƙame shi ina kukan ni ba za’a min ba, shi kuma Baban nata bani haƙuri.
“ashe ka shigo?”. Yagana tace da Baba tana zama a kan kujera. “Ehh Yagana…ina yini”. ta amsa masa,”lafiya lau, ya ka baro su Alhaji Ƙaramin?”. “suna lafiya duk suna agaisheku…ashe bikin ƴar gidan Baffayo ma sati guda ne dana Sadiya”. tace,”haka Nafisatu ke faɗa min sanda suka zo ganin gida, to mudai baza muje ba sai dai suzo nan a haɗe ayi tare, in ba haka ba kuma maje musu murna daga baya”. Baba ya kaɗa kai da rigimar da Yagana ke neman ja sannan yace,”jikarki dai har yanzu taƙi girma”. ya faɗa yana zolayata dana ƙanƙame hannayensa, kuma saina sadda kai a gefen hannunsa ina jin kunya.
Kamar jira dama ta ke yay magana akaina saita gyara zama ta fashe da kuka tana dafe goshi. gaba ɗaya idonmu yay kanta hankalin kowa a tashe, abinda ba’a taɓa ganin tayi ba, Baba yace,”Subhanallah Yagana me ya faru?”. bata bar kukan ba tace,”Adamu gidana zan koma tunda Allah baisa an siyar da shi ba, zanfi samun salama idan na koma can”. Baba ya ƙara cewa,”Yagana akan me? ko wani abu ya faru a gidan nanne?”. ta zuƙi hanci da faɗin,”to mene ma bai riga ya faru ba Adamu, kawai ni dai gwara aiwa tufkar hanci tun jinina bai hau ba, ga kayana canma na gama haɗawa tafiya kawai zanyi dama jiran isowarka nake, kar na bar gidan ban sanar maka ba kaga rashin kirkina”. wannan karan ba Baba ne kaɗai yay magana ba, kowa saida ya jefa ma ta tambayar,”wai Yagana me ya faru ne?”. ni kaɗai da banyi tambayar ba kallon Yagana nake da bugawar ƙirji, me yasa ta kuka? kuma me yasa ta ke maganar zata bar gidan?, nai tsilli-tsilli da idanu ina kallonta da jiran amsar da zata bayar.
kukanta ya ƙaru a sanda take cewa,”ni dai ba muguwa bace, kuma ba ƴar baƙin ciki ba ce. amma ban san me yasa ake min bahagon kallo ba, wallahi ni dai ko ƴaƴan kishiya ba zan iya cutarwa ba balle jikokin da nasan daga tsatsona suke…Adamu a rayuwa me naiwa ƴaƴanka da zasu dasawa zuciyata baƙin cikin da zai karni, idan wani abun nai musu tsakani da Allah ai saisu fito fili su faɗa min na basu haƙuri tunda ni ba baƙuwar zafi ba ce. amma haka kawai saisu ɗau karan tsana su ɗora min, su ɗaura gaba da ni, ɗabi’ar da ubangiji baya so”. tai shiru tana murza idanu, kowa ya sauke numfashi. Baba ya shiga kallonmu kamin ya kira sunan kowa, sannan ya kalli Inna ma yace,”Zulai meke faruwa acikin gidan nan da ban sa ni ba?, domin nasan indai fitina zata fito daga ɓangarenki ne, me Ƴaƴanki su kaiwa Mahaifiyata da baku ɗauketa a bakin komai ba”. yay maganar cikin faɗa da ɓacin rai…Yagana tai saurin cewa,”a’a karka ɗaukar hakkinta babu ruwanta babu ruwan ƴaƴanta acikin wannan lamarin…nifa ina maka magana ne akan Kabiru da Mairo”. Baba ya juyo yay min wani kallo da yasa na ƙara tsurewa dan ban san wani laifi da naiwa Yagana ba.
kuma maganar Yaganan ta katse shi daga abinda yake son cewa, a wannan karan kuka ta ke sosai wanda yafi na ɗazu. “kaga Adamu yaron nan Kabiru tunda uwarsa ta mutu ya ɗaukeni tamkar uwa, baya ɓoye min komai, halinsa me kyau, nima na ɗauke shi tamkar ɗa ba jika ba, tunda Allah ya sani kaf cikin jikokina nafi ƙaunarsa ba zan ɓoye ba…amma yanzu kashi ma ya fini mutunci a idon Kabiru, gaba ɗaya ya ɗauke min wuta baya kula ni, wannan shegiya abar banza gaisuwa Kabiru in zamu doki ƙirji da shi ba zai min ba, kai na taƙaice maka ma ɓangarena ya daina zuwansa…to ni duk ba wannan ya dameni ba, damuwar da nake gani a fuskarsa ita ke ci min tuwo a ƙwarya, juyin duniya nayi da shi ya faɗa min matsalar yaƙi, ƙarshe ɗazu da safe dana tsare shi da tsaki ya bini kafin ya tashi ya fita fuuuu kamar guguwa, to wannan halin kyautawa ne fisabilillah, ni ya riƙe maganarsa amma ka faɗa masa bana son ganinsa a damuwa”. Baba yay ƙasa da murya yace,”kiyi haƙuri Yagana, zan tuntuɓe shi naji meke faruwa”. tana shashsheƙa tace,”daka taimaka min, dan ni dai da wannan halin miskilanci da Amadu ya sauka akai shi kuma ya hau gwara kullum yazo ya dinga faffaleni da mari ko kuma yace na mutu kawai ya daina ganina, hakan zai fiye min da dai naci gaba da ganinsa da damuwa”. Baba ya ƙara bata haƙuri tace babu komai, ya kalli Lukman yace ya kira masa Kabiru, sannan yace da Yagana,”ita kuma Maryam me tayi”. ta goge fuska tace,”wannan abar ta kusa da kai ai fitina ce Adamu, shi yasa nace barin gidan nan zanyi tun bata ja ubanta yasa anmin ɗaurin rai da rai ba, ko kuma tasa uwarta ta maidani baiwar masarauta”. nai kicin-kicin da fuska nace,”Yagana nifa babu abinda nasan nayi miki”. tace da Baba,”kaga ni baa, duba fa a irin yanda ta ke min magana kamar zata dukeni, kasan kuwa ba ƙaramin haƙurin zama nake da ita ba. aini tunda ƴar nan ta balaga nasan zan fuskanci babban kalubale, to inda Allah ya taimaka ina kai lamarinta wurin Allah amma banda haka tuni tasa an ɗaureni”. Baba ya kalleni fuskarsa a ɗaure yace,”me kika ma ta?”. “yo ka tambayeta salon ta ƙaryata zancena Adamu, kaima kasan ba zata faɗi gaskiya ba sai dai tai ƙarya ta kare kanta”. Baba yace,”ki barni da ita”. nace,”Allah Baba ni dai nasan ban mata komai ba, kawai so ta ke taja min faɗa a wurinka”. sabon kukan da ta fashe da shi ya tari numfashina. “Adamu na faɗa maka yarinyar nan fitina ce, idan kaci gaba da tmbayarta ƙaryatani zatai tayi duk girman shekarun da nake da su.
abinda ya faru ɗazu fa daga ƴar ƙaramar magana nace ba zata bi waɗancan marasa kunyar unguwa ba shikenan saita ɗaura gaba dani, ta shiga ɗaki ta haɗa kayanta wai barin ƙasar za tai. na tsuguna na bata haƙuri amma duk bata ga wannan ba haka taƙi saukowa. abincin rana ma dana bita da shi ɗaki ƙinci tai tasa ƙafa tai fatali da kwanon”. ta dubi Nawwara tace,”ko ba haka akai ba ke?”. Nawwara dai tai shiru ita kuma taci gaba,”to ɗazu ma daga shiga ɗakin nace tazo ai ma ta allura saita balbaleni da masifa, wai na fita a lamarinta na daina shiga sabgarta ita bata son takura. jiya jiyan nan ma fa haka taje ta ƙala min sharri a wurin wancan ɗin, shi kuma sai ya turo ɗan’uwansa, haka Amadu yazo tsakiyar kaina kamar zai zaneni yayta banbami wai na daina takura ma ta…ka ga fa ba yau ta soma haɗani da mutane ba, kwanaki da nayi baƙi Allah yarinyar nan saita koma kamar marainiya a gidan nan, kaga waccan kujerar nan ta zauna ta dinga ɗacin rai da nurƙufanci tana kuka ba’a ma ta komai ba, duk dai dan taja min masifa, su kuma da gulma suka dameta da tambayar wai me aka ma ta, to ka faɗa min Adamu duk sanda tai irin haka agaban iyayenta me zasu ce tsakani da Allah, ai sai suce sun rufa mana asiri ni kuma ina tsangwamar ƴarsu kuma alhalin ba haka ba ne. ka tambayeta kaji wallah ko bacci bana iyayi sai naga sunyi ita da ƴar’uwarta, amma ta rasa da me zata dinga saka min saida mugun halinta, kuma da tayi abu nai ma ta gyara zata turo baki gaba kamar kuratandu, to ni dai na gaji gwara na bar ma ta gidan, tunda dama ba Ummana bace ta siya”.
Baba yace,”kiyi haƙuri Yagana ba zata ƙara ba daga yau”. tace,”hmm Adamu kenan baka san wace Mairo ba…to ka bar lallamata ina faɗa maka, dan kaima bata ƙi taja maka baƙin jini ba a wurin iyayenta, kaga dai fa ba lafiya gareta ba amma taƙi tsayawa ai ma ta maganin abin, alhalin tasan yau Akila zata dawo, to yanzu idan ta dawo taga ba’a bata magani ba’a ma ta alluran da likitoci suka bada me zata ɗaukemu tsakani fa da Allah?, to ni dai gaskiya asan abinyi, ko zamana a gidan nan ko barinta dan ni nagaji da halinta, ba zai yiwu ta dinƙa neman jefani a masifa ba”. “kiyi haƙuri dai Yagana”. “to haƙuri ai ya zama dole Adamu. kaga shi wancan ɗin daka aika a kira tun ɗazu har yanzu baizo ba, dama ni nasan ba zaizo ba indai yasan kana ɓangarena”. Baba yace,”to waishi da bashi da lafiya ma, yaushe ya tsiri wannan halin?”. maganar Baba yake ransa a ɓace. tace,”aini na gama magana, ga dai Zulai nan ka tambayeta kaji. Kabiru ai ya zama sai adu’a”. Zulai tace,”aini Yagana duk ban san hakan tana faruwa ba. amma komai zai daidaita”. tace,”uhmm daga jiya zuwa yau kawai Kabiru ya zama abinda ya zama, ki faɗa min idan akai gaba sai ya ya? aishi ice tun yana ɗanye ake taƙwarashi”.
Ya Kabiru da Lukman suka shigo, ya zauna a ƙasan carpet kansa a ƙasa. Baba ya shiga yi masa faɗa sosai shi kuma yana bada haƙuri. ya ɗaga kai ya kalli Yagana yace,”Yagana dan Allah kiyi haƙuri”. tace,”na haƙura na yafe maka. nima kayi haƙuri ka yafe min”. sannan Baba ya juyo kaina da nawa faɗan, faɗan da saida ya sa ni kuka, na bata haƙuri kuma saida ƙyar tace ta haƙura.
Baba zai fita nima na kai masa ƙarar Ya Kabiru, kuma bai tsaya ba yace,”wannan kuma laifina ne, may be rashin kunyar da nakewa Yagana nai masa”.
gaba ɗaya na manta da zancen zaa min allura sai bayan da taron kai ƙorafin Yagana ya ƙare, a rayuwata ganin allura na ɗaga min hankali, Ya Kabiru ya tashi zai fita nai jikinsa na ƙanƙame shi ina kuka, kamar zai janyeni kuma sai ya fasa. ya ɗaga wayarsa dake ƙara ya kara a kunne. daga yanda naji ya amsa maganar da aka masa daga cikin wayar na gane da ƙyar idan ba Ummina bace. “oak tom gani nan zuwa”. sai kawai naji ya ɗora min wayar a kunne, muryasa can ƙasa a hankali yace,”Ummi ce”. sai na shiga murna babu shiri, ina tambayarta yaushe zata dawo. abinda na sani kawai shine, naji sanda Ya Kabir ya karɓi allura daga hannun Mu’azzam amma ban sanda ya tsira min ba har ya zare saida Yagana tana lailaya min wurin. na kalli Yaganan nace,”allurar za’a min, nafa ji sauƙi”. ta taɓe baki bata ce da komai ba ta wuce ta bar wurin.
ina Kallon Ya Kabir da zai fita nace,”Yaya tun shekaranjiya fa Ummi tasa aka kawo driver, amma kanata driving da ƙafanka bai gama warkewa ba”. “who told you so?”. na ɗan haɗe fuska nace,”ɗazu ai ka kai Nawwara makaranta”. ya ɗaga kafaɗa sannan yace,”am well now. zaki je ɗauko Ummin?”. nai knodding kaina da cewan,”ehh”. na faɗi hakan cike da murna, dan sosai nai kewan Ummina. “to ki fito da sauri”. ya faɗi hakan yana sa kai ya fita daga parlon. dani da shi da Basma muka tafi ɗauko Ummi a airport.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button