NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

***”magungunan da aka rubuta masa suna da tsada sosai, gasu nan ku hanzarta siyo su bada jimawa ba…karku ɗaga hankalinku da yawa saboda komai yazo da sauƙi…sai dai allurar da muka yi masa ce zata iya kaishi zuwa gobe, amma karku wani damu da rashin farkawarsa muna so ya sami hutu ne.”
duk wannan bayanin na fitowa ne daga bakin Dr ɗin daya gama duba Kabir a yanzu, yana isar da bayanan nasa ga Akila dake tsaye tana sauraronsa, yayin da Yagana ke zaune a kan wata kujera daga can gefe tayi jugum ƙirjinta na luguden fargabar abinda likitocin zasu ce a ga me da Kabir duba da mawuyacin halin da yake ciki, kuma a duk wani motsi na zuciyarta tsinewa Amarya ta ke.
Mairo kuwa na zaune akan kujerar da Akila ta tashi ta bata, idanunta na manne akan Kabir dake kwance kamar matacce, da kuma farar shaddar dake jikinsa wadda gaba ɗayanta ta ɓaci da jini kamar yanda shima fuskarsa ta ɓaci da jini a ɗazu kamin likitoci su gyara shi, su kuma nannaɗe wurin ciwukan da bandage.
a wannan lokacin zuciyarta na bugawa ne da motsin fargabar halin da Ya Kabiru ke ciki, yayin da a gefe guda kuma kalaman Ummi akan Amarya ke yawo a cikin kanta, wannan Amaryar da ta ɗauka tamkar Gwaggonta, ta kasa yarda da kowacce kalma ɗaya bayan ɗaya dake fitowa daga bakin Ummi akan ƙazaman abubuwan da Innarta ta aikata, amma kuma a sanda Baba ya kira yana tabbatarwa da Yagana gaskiyar lamarin sai taji kanta yay ma ta nauyi, komai na cikin kanta ya ɗaure.
ta sa ni, ba ita kaɗai ba, koma wane zai iya dafa Alƙur’ani ya rantse wajen ƙaryata duk wanda zai zo da shaidar maganar makamancin abinda Amaryar ta aikata, amma wai sai gashi ita da kanta tai silar ajalin Matar da ta ɗauketa ƴar’uwa, kuma ta jefa mutumin da akaf ƴaƴan gidan babu wanda ya kaishi bata girma, taɓa mata Gwaggo da tai shine babban zunubin da ta aikata, kuma a yanzu taɓa ma ta Ya Kabir ya zama mafi munin kuskuren abubuwan da ta aikata a rayuwarta, za kuma tayi dana sanin da zai zame ma ta mara amfani.
dan a yau tambarin laifinta ya kafu a zuciyarta ta hanyar da ba zai taɓa goguwa ba, tunda har ta haddasa faruwar wannan tashin hankalin, ta zama silar da Ya Kabir ɗinta ke kwance a gadon asibiti cikin wannan mawuyacin halin, ta zama sanadiyar fitar wannan jinin dake ɗaga hankalinta tun tana yarinya, ko ƙaƙa jini ya fita a jikinsa tana kasa samun natsuwa balle irin wannan jinin daya zubar.
sai kawai ta rufe idonta tare da kifa kanta a gefen gadon nasa, daidai hannunsa da drip ke shiga, ta kasa ganewa, ita bata san menene wannan dunƙulallan abin ba daya tsaya ma ta a zuciya ba na ga me da Ya Kabir, abu ɗaya kawai ta iya ganewa da fahimta shine ƙudurin da zuciyarta ta ɗauka akan Amarya, tabbas idan har ita ɗiyar Mami ce, wannan ƴar da ta ke da gata ta kowanne fanni, to sai tasa Amarya ta wulaƙanta, wannan alƙawarinta ne.
Shigowar Aaliya room ɗin yasa Yagana miƙewa da sauri tana tambayar yanda ake ciki ga me da binciken Amarya da akasa.
sai dai kuma Aaliyan ba jin me ta ke cewa ba balle ta bata amsa, sai Amadu dake shigowa daga baya ne yake ma ta bayanin komai, harda shaida ma ta sakin da Malam yay ma ta, wanda tace hakan shine dai-dai.
“wacce iriyar shaƙuwa ce ke tsakaninsu?”. “ina Alhassan?”. tambayoyi biyun suka fito a tare daga bakuna mabanbanta, suka kalla juna inda Aaliya ta ɗagawa ƴar’uwarta kai,”ki fara bani amsar tawa, wacce iriyar shaƙuwa ce ke a tsakaninsu?”. ta faɗa a sanda ta ƙara maida idonta kan Mairo da har yanzu bata ɗago daga kifa kanta da tai ba daga gefen hannun Kabir. “shaƙuwar me ƙarfi ce, kamar shaƙuwar hanta da jini…shi na zaɓa ma ta, kuma shi naiwa alƙawarinta in har muna raye, ina roƙon Allah da izininsa suka kasance a inuwa guda”. har yanzu idon Aaliyan na kansu biyun tace,”kenan da mun komai sai bikin aurensu?”. Akila ta dubeta da mamaki,”auren Maryam kuma very soon haka?.” “ƙwarai, domin a irin critical condition ɗin da yake ciki ya kamata su kasance a tare…inace kince min Mamansa ta rasu?”. “ehh baya da Mama a raye, amma ni kuma ai ba haka na tsara auren Maryam ba, so nake saita kammala karatunta tukunna”. “Kabir ɗin jahili ne?”. Aaliyan ta wurga ma ta tambayar sanda tai shiru. Akila na girgiza kai tace,”kaf gidansu ma ai babu me iliminsa”. “so me ilimi kamarsa kina tunanin zai hana mace yin karatu?, ko da bata so tayi ba dole zai tursasata, dan haka a irin shauƙin son da nagani a idanun Maryam kasancewarsu a tare shi zai wanzarwa da zuciyarta natsuwa…wanne time suka ce zai farka?”. “zuwa gobe suka ce”. “zuwa goben kenan zamu wuce gida, haka Ammi tace”. tai maganar sanda ta ke neman kujera ta zauna, tana kuma cewa da Akila,”Major ne yazo, Alhassan na tare da shi, tunda na gansa tafin hannuna ke ƙaiƙayi, kije kiji da shi.” fuskar Akila na haskawa da mamaki ƙarara tace,”Major kuma, me zuwan nasa ke nufi?, kar dai karɓan yarana zaiyi?.” Aaliya ta sauke jarkar ruwan faro ɗin da ta kai bakinta sannan tace,”ni na kawo shi?.” bata jira cewar wani abu daga bakin Akilan ba ta ƙara cewa,”tunda ba ni na kawo shi ba sai ki rabani da waɗannan tambayoyin naki”. Akila ta girgiza kai sannan ta fice daga ɗakin a zafafe.
kuma tun bayan fitar tata Aaliya ta maida kallonta kan Maryam da Kabir, kuma kamar yanda ta ƙura ido a kallon nasu haka Amadu ya zuba ido akan Mairo da wani irin kallo da fassararsa ke ga me yinsa shi kaɗai. a hankali Aaliyan ta sauke ajiyar zuciya sannan ta miƙe taja kujerar zuwa kusa da Mairon. duk da cewar bata leƙa taga yanayin fuskar Mairon ba, amma tasan da cewar idonta biyu ba bacci ta ke ba kamar yanda saukar numfashinta ke nunawa, haka kuma ta tabbatar hawaye ne ke bin kuncinta duk da bata kalla fuskarta ba, saboda haka cikin muryarta da ta bada wani irin amon sauti tace,”Ya Mutu”. kuma kalmar ta doka wani irin tartsatsa a zuciyar Mairo ta ɗago a rikice tana duban Mahaifiyartata, bakinta a buɗe yana rawa ta kasa cewa komai sai aikin girgiza kai da ta ke alamar,”a’a maganar ba haka ta ke ba”. da ta ga hakan saita kauda kanta daga barin kallonta tace,”ai bani na faɗa ba Maryam, ga file ɗinsa nan ki duba ki gani mana”. sai kawai Mairon ta fashe da wani kuka mai ƙarfin sauti ta faɗa jikin Aaliyan tana faɗin,”a’a Mami dan Allah, bana so ya mutu yanzu dan Allah Mami”.

Bari na dakata anan na miƙa sallama tare da ban haƙuri a gareku masoyana. kamin saƙon ban haƙuri i hope dai kowa yana cikin ƙoshin lafiya, if that so let thanks be to glory Almight Allah…Awwa my fans dan Allah kuyi haƙuri kunji ƴan albarka, wallahi i was extremely busy ne a kwanakin nan, ina ta ganin messages naku through inbox and whatsapp but i cant even respond ma saboda banda yanda na iya, even online enma da kuke ganina aiki ne me zaman kansa nake…so yanda abin yake for me dai nafi so idan zanyi rubutu ace a nutse nake gaskiya, idan ina busy tsakani da Allah bana iya typing even irin short ɗin nanne abinku da ƙaramar ƙwaƙwalwa, kai infact ma ba rubutu kaɗai ba komai ma na buƙatar natsuwa, buh insha’Allah when everything’s get settled zaku ci gaba da jina yanda ya kamata????…I Love You All????????…awwa kowacce na bata peck ɗin kulawa a gohi????…thanks to you all sai kun ƙara jina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button