NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Abuja, Nigeria.
acikin ƙaton falon gidan babu abinda kake ji sai sautin kukan dake tashi daga bakuna da dama. daga tsakiyar kujerun dake kewaye da wurin gawa biyu ce lulluɓe da jan ƙyalle, kuma daga gefen kan gawar Madam Gloria Joseph ne duƙe yana girgizata da kiran sunanta akan ta tashi.
Major ma na zaune kusa da gawar Granny hannunsa acikin nata yana kukan rashin mahaifiyarsa. mutuwar da sukai ta dalilin hatsarin motar da sukai akan hanyarsu ta dawowa daga Ibadan sunje taron buɗe wani flatfom da ita Madam Gloria ta buɗe.

Please Manage da wannan, Yau na tashi da idona a kumbure, kun san sanyi ya shigo, yanzu haka da ƙyar na iya maku typing ɗin wallahi saboda zugin da yake min.

Comment & Share.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

Avoid Error Mistake, ba’a nutse nai typing ɗin ba.

35)
Acikin bedroom ɗin, a bakin gadon, Al-Mustapha ne zaune ya dafe kansa da duka hannuwansa biyu, a gefe ɗaya kuma hawaye na sakkowa saman fuskarsa da yake jin zafinsu tamkar tartsatsin wuta ajikinsa.
ya miƙe a zafafe yay tattaki zuwa bakin ƙofa, ya murɗa handle ya fita, daga saman benen yake hango ƙasan parlon da jama’ar dake kukan mutuwar mahaifiyarsa da kakarsa, ya rumtse ido yay taku uku baya sai gashi ya komo cikin ɗakin, a saman gado ya zube tare da saurin dafe kansa dake barazanar rabewa gida biyu, kafin ya naushin gadon tare da faɗin,”Nooo!!”. amon muryar ya fita da wani irin ƙaraji, har saida ɗakin ya amsakuwa.
ya ƙara damƙe kansa sose yana me jijjiga shi kaman wanda zai yi hauka, ya zaiyi ne wai?, me yasa mutuwa zata yi masa haka?, sai kawai ya ƙara fashewa da kuka tare da kifa kansa akan ƙafafunsa.
Allah ya sa ni, tun bayan musuluntarsa yakewa ahalinsa kwaɗayin wannan addinin mai ni’imar gaske, tun a ranar daya musulunta ya fahimci akwai tarin ni’imomi dake cikin wannan addinin na gaskiya. zai iya rantsewa tun zuwansa duniya yana jin kansa da wani irin nauyi, nauyin da zai kimanta da wanda aka ɗorawa wani babban dutse, kuma kamar yana jinsa kamar yafi kowa matsala a duniya duk da cewar ba shi da ita ɗin, ya sami gata da dukkan komai na rayuwa da yafi ƙarfin yaji zuciyarsa na cunkushewa.
to amma tunda ya musulunta sai yaji komai ya sauya masa, wannan nauyin da yake jinsa da shi babu, haka wannan matsalar da yake jin kamar yana da ita itama babu, tun daga ranar daya musulunta sakayau yake jinsa, kuma zuciyarsa babu wannan cunkushewar da yake jinsa da ita ada.
idan ya tuna rayuwarsa ta baya sai yaji yana tausayawa kansa, matuƙar tausayi na wanda ya kauce hanyar dai-dai yabi ta gargada, gargadar da ba zata ɓullar da mutum ko’ina ba sai ga halaka. to amma idan ya tuna sabuwar rayuwar daya shiga a yanzu, ya kuma tuna Rahmar ubangiji ga bayinsa, sai yaji kamar yafi kowa sa’a da dacewa a duniya da Allah ya haska masa hasken musulunci tun kamin ƙurewar lokaci a gare shi. shi yasa yake roƙon ubangiji daya haskawa sauran ahalinsa wannan hasken suma, domin su samu su rabauta a duniyarsu da kuma lahirarsu.
sai ga shi a ranar daya ƙudurta zai fuskanci ahalin nasa da maganar da yake ganin zata iya zamowa ƙarshensa a wurinsu, sai ga shi mutuwa ta ɗauke masa mahaifiyarsa, ta ɗauketa ba tare da ta tuba ga mahaliccinta ba, ta mutu zata je ta tarar da wannan azabar da aka tanadarwa irinsu. sai kawai yasa hannu ya matse goshinsa, yana kuma ƙoƙarin tsaida hawayensa, babu wani abu da zai iya yi ma ta shi kam, tata ta ƙare.
“Ya Halatta Ka Halacci Jana’izarta Tunda Mahaifiyarka Ce Tana da Wannan Hakkin Akanka. A lokacin da Mahaifin Aliyu bn Abi Ɗalib Ya Rasu, Manzon Allah (SAW) Aliyu Ya Umurta da Yaje Ya Rufe Mahaifin Nasa, Duk da Mahaifin Nasa Ba Musulmi Bane. sai dai karkayi duk abinda Muslunci yace kar ayi wanda ya danganci jana’izar waɗanda ba musulmai ba kamar yi musu Addu’ar neman Rahama, da duk wani bukukuwan da ake yi, da raye-rayen da akeyi da sauransu. Allah Ubangiji Ya Baka Juriya da Haƙuri Ya Kuma Tabbatar da kai a Musulunci”.
maganar ta ƙara haskawa acikin kansa a karo na babu adadi tun bayan daya tabbatar da rasuwar mahaifiyarsa, amsar da Malam Liman ya ba shi kenan a sanda ya kirasa a waya yay masa tambayar,“Malam shin a addininmu ya halatta na halacci jana’izar mahaifiyata matsayina na musulmi ita kuma kiristan?”.
sai kawai ya kuma rumtse ido gam, tabbas shi yafi kowa rashin dacewa, zai iya kiran kansa da hakan. ganin cewar ba zai iya yiwa mahaifiyarsa wata adu’a ba, babu wani abu da zai iya yi ma ta domin ta dace da wannan Rahmar ta ubangiji, lokaci ya rigada ya ƙure ma ta, to amma kuma a ɗazu Liman yace da shi,”Kul ɗinka Al-Mustapha, karka ƙara cewa kai kafi kowa rashin dacewa, Allah yana sonka, domin da baya sonka da bai haska zuciyarka da hasken musulunci ba”. sai ya haɗiye wani abu da bai san mene ba a maƙoshinsa. kuma yana cikin wannan yanayinne Obi ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, ya ƙaraso bakin gadon ya tsaya, ganin yacca hawaye ke sunturin sauka ta gefen fuskar Yayan nasa sai shima yaji zuciyarsa ta ƙara tsinkewa, yasa handky ya goge nasa hawayen kafin ya buɗa baki yay masa magana.
“Bros Dad yace ka kira Michel ka sanar masa yaje Dunamis International Gospel Centre, acan za’ai bikin mutuwar. amma ya hanzarta wajen yin decoration ɗin wurin”. maganar ƙanen nasa tasa yaji zuciyarsa ta matse, bai motsa bai kuma amsa masa ba, bai kuma nuna yaji shi ba. tsawon daƙiƙa biyu Obi ya juya ya fita ya bar ɗakin, kuma babu jimawa da fitar tasa sai ga Dad ya shigo.
daga tsakin ɗakin ya tsaya yana saƙale da hannayensa ta baya, wanda hakan yake ɗabi’arsa, fuskantar ɗan nasa yake da tausayi, kamin ya kira sunansa,”Emanuel”. a can duniyar daya faɗa yaji sautin muryar mahaifin nasa, da sunan daya fara mancewa da nasa ne. ya buɗe idanuwansa a hankali kamin ya miƙe zaune ya amsa kiran Mahaifin nasa.
“ka bar kukan haka, ka tashi ka shirya zamu wuce chapel, Pastor yana jira karmu ɓata masa lokaci, zai bar ƙasar ne yanzu”. kansa a ƙasa yaji maƙogoransa ya bushe, da ƙyar ya iya tattaro wata jarumta da yake ganin kamar bai da ita yace,”Dad ni ba zan sami damar zuwa chapel ba don bikin mutuwar Mom da Granny…”. bai kai ga ƙarasa zancen nasa ba Dad ɗin yace,”what! are you mad?”. ya miƙe tsaye ya fuskanci Dad ɗin sannan yace,”Dad i am not a christian now since last three days past, i am now a muslim…”. tamkar saukar tsawa acikin duhun dare, tamkar ƙarar bindiga acikin tarzoma, haka maganar ta sauka a kunnen Major, ya waro dukkan idanuwansa waje yana duban ɗan nasa da ɗumbin mamaki.
bai ga wani abu related to kayan maye a ɗakinsa ba balle yace shi Emanuel ya sha ya samu gushewar hankali, haka kuma bai yi masa kama da mahaukaci ba balle yace ciwon ya kama shi ne babu jimawa, to amma me ya shiga ƙwaƙwalwar yaron?, kan ya jefa wata tambaya ga Emanuel ɗin sai ya tsinci kansa da haska masa cewar tabbas zai iya zama ya musulunta, kuma ya musulunta ne ata dalilin yarinyar nan da aka ƙi bashi aurenta, ya yarda ba zai ƙaryata ɗan nasa ba, tunda ga shi nan babu wannan sarƙar cross ɗin da baya taɓa rabuwa da ita.
gaskiya ne! yanzu ya yarda da cewar so yana sawa mutum ya zare ya zama taɓaɓɓe, gashi ya gani akan ɗansa, sai dai shi ba zai lamunci wannan haukan ba, dole zai yi masa maganin abin, dama shi ba me tolerating wani iskanci daga yaro ba ne, bare kuma yaron yazo masa da maganar da kansa ma ba zai ɗauka ba, yana jin zai iya ɗaukan ciwon haukan Emanuel kowanne iri ne, amma banda wanda ya shafi wulaƙanta addininsu, how comes ma zai fuskance shi kai tsaye yace masa ya musulunta, ina ya samu wannan ƙwarin gwiwar?, ko kuma shine dai ya rasa wannan girman kwarjinin da yake da shi ba tare daya sa ni ba?, ƙwarai zai yiwa tufkar hanci, yanzu kuwa bada jimawa ba.
to amma sai dai me? kamin ya kai ga ɗaukar matakin ɓulan kan Emanuel da bindigar daya zaro a gefen wandonsa, sai yaji Emanuel ɗin na magana, maganar da zai iya cewa tasa yayi suman tsaye saboda tsantsar mamaki, babu tsoro balle shakkarsa a idon ɗan nasa, illama shi da yake ganin yau ɗan nasa ne yake masa kwarjinin, da kuma shakkar aikata masa abinda yake niyyar yi.
“Dad kuje kuyi gaggawar abinda ya kamata ga gawar tasu, sannan kuma ku dawo ku karɓi addinin da nake acikinsa yanzu tun kamin ƙurewar lokaci, domin ita mutuwa bata da notice, ni kuma ba zanso ace duk na rasaku a wannan addini na ƙarya da kuke ciki ba”. Dad ya ɗaga hannu zai kai masa mari sai ƙarar wayarsa ya dakatar da shi, ya zura hannu a aljihu ya ɗaukota kuma dai-dai lokacin da kiran wayar ya katse, sai dai saƙon daya biyo bayan wayar shi ya ɗan dakatar da shi yana kallon lambar wayar da ta turo saƙon da mamaki, da kuma abinda saƙon ke ɗauke da shi, “Akila bint Tamim”. gajeren saƙon ne, kuma gajeren saƙon daya girgiza duniyarsa gaba ɗaya, a fili ya maimaita sunan ba tare daya sa ni ba.
kenan mafarkinsa zai tabbata?, idan bai manta sau uku kenan yana mafarkin sun ƙara gauraya da su a wata duniyar, ai shi a tunaninsa tunda ya binne wannan hotunan nasu kamar ya rabu da ƙayar tunaninsu ne, amma ya akai haka?, lambar nigera!, kenan tun sanda suka raba da Akila tana ƙasar nan bata koma gida ba kamar yanda ta faɗa musu?.
sai ya lumshe ido ya shaƙi wata iska me zafi, kuma ƙarar saƙon daya kuma shigo masa shi yasa shi buɗe ido zuciyarsa na me wani irin harbi. yay swapping ɗin wayar ya shiga whatsapp account nasa, ya duba lambar farko da saƙon ya shigo masa, ya kuma buɗe hoton da tun kamin ƙarasa buɗewarsa zuciyarsa ta raya masa hoton ƴarsa ce.
kuma kamar yanda ya zata, hoton na gama buɗewa sai ga hoton Akila da Mairo, hoton Mairo shi ya girgiza shi, kuma saƙon daya biyo ƙasan hoton a yanzu ya kuma girgiza shi.
“tsawon shekara goma sha bakwai kayi biris damu. naso ace na ɓoye amma hakan sai ya faskara, a yanzu ƴarka ta buƙaci sanin wane ubanta, kuma na faɗa ma ta, ta kuma ce sai tayi shari’a da kai, dan haka Major ka shiryawa abinda zai biyo baya. Ƴata zata ɗaukar min fansa, zata lalata duniyarka kamar yanda ka lalata mana tamu”.
sai yasa yatsansa ɗaya tun daga kan goshinsa har kan hancinsa, shikenan abinda yake gudu zai faru, komai ya zo ƙarshe, girmansa! mutuncinsa! ƙimarsa!, shikenan zasu zube ƙasa wanwar kamar yanda yake ta jimamin faruwar hakan tuntuni. shi yasa tun a wancan lokacin, yay yay da Akila ta haƙura su kai yaran marayu, ta yanda ko da sun girma ba zasu nemi iyayensu ba, tun san san cewar rashin gata ne ya kaisu wurin, kuma ko da watarana sun buƙaci iyayensu, amsa ɗaya za’a basu itace ba’a sansu ba, shikenan asirin kowa ya rufu, ko kuma kaman yanda Aaliya tace ma ta a yasar da su.
to amma da yake ita tafi Aaliya kafiya, sai taƙi, tace sam ita ba zata iya ɗaukarwa kanta wannan babban zunubin ba, wannan rashin imani har ina, a haifi jarirai sannan a zubasu a leda aje a watsar.
ya ƙara kallon lambar wayar da kyau, sai yabi bayanta da kira, sai dai daga can kamfanin layin MTN maimaita masa suke da cewar babu network, saboda haka yace da Al-Mustapha ya bashi wayarsa, ya miƙo masa.
sai dai ga tsananin mamakinsa ko da ya rubuta numbar a wayar, sai yaga sunan Sectary ya bayyana, wato Ahmad Adam Bichi. aikin Amadu ne, dan tun bayan da suka kawo Kulu asibiti, ya kuma tuna labarin da ta basu, ya ɗau aniyar sai ya girgiza Major, sai ya saka masa tsoro a wannan zuciyar tasa ta rashin imani.
dalilin daya sa ya ɗauki hoton Kulu kenan da Mairo ya turo masa, tre kuma da wannan saƙon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button