NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Pls Comment&Share.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

34)
“Uwa da Uba suna da girma da daraja, Alƙur’ani ya fito fili ƙarara ya nuna mana mu kula da su. wajibi ne ƴaƴa su ɗaukin nauyin yin magana ta mutuntawa da darajartawa ga iyayensu. Allah SWT yana cewa,”wala taƙul lahuma uffin”. ana so ɗa ya zama me kyakykyawan saurare ga iyayensa. bima’ana idan suna magana karka katsesu ko da kuwa faɗa ne suke maka. ka zama me ladabi, haka kuma ya zamana kana tare dasu ko da yaushe kar mutum yace zai gujesu, haka zalika ka da kayi abinda za ka jawa iyayenka magana.
Abudarda yana cewa naji Manzon Allah yana cewa, “mahaifi shine ƙofa ta tsakiya cikin ƙofofin Aljannah,(uwa ko uba), wanda yake so ya shiga Aljannah, to ƙofar tsakiya wadda daka shiga tsakiyar aljannah zata kaika ba gefe ba to mahaifi shine wannan ƙofar, mahaifiya itace wannan ƙofar”. saboda haka in har mutum naso ya shiga aljannah to idan yaga dama ya kula da wannan ƙofar idan kuma yaga dama ya jefar da maƙullin wannan ruwansa ne.
hakana kada ka sake ka taɓa yin magana me tsauri ga iyayenka, su iyaye kullum so ake ka zama kana saka su cikin farinciki. kuma wallahi duk lalacewar iyaye sunfi ƙarfin ai ramuwar gayya akansu, haka kuma ba’a yin jayayya da su. saboda haka ina me horanku akan saɓawa iyayenku ko kuma ɓata musu domin Allah na fushi da wanda iyayensa sukai fushi da shi”.
maganganun dake yawo acikin kaina kenan tun baya shigowata cikin wannan motar, tunasarwar da Malamin makarantar allonmu yay mana kenan a ranar da Mahaifiyar wani yaro ta kawo ƙararsa makaranta. to amma ban san dalilin kutsowar wannan magana cikin kaina ba ayanzu, bayan an ɗauki tsawon shekaru da yinta.
naja dogon numfashi sanyayyan ƙamshin daya cika cikin motar yabi bayan iskar dana zuƙa. “wallahi matsawar mutum yana so ya samu rahmar ubangiji, yaji daɗi duniya da lahira to yabi iyayensa, iyaye duk yanda suke iyayenka ne, balle Uwa da hadisi ya tabbatar da ma’aiki ya faɗeta sau uku”. maganar Malamin ta ƙarshe ta kuma haskawa acikin kannawa, nai saurin saka duka hannayena biyu na toshe kunnuwana, dan sam zuciyata na faɗa min kamar bata so wata magana makamanciyar wannan zancen a halin yanzu, dan ko kaɗan bana so gwiwata ta raunana akan ƙudurinta na ɗaukan fansa akan Akila da Major, shi kansa tunanin rashin kyautuwar abinda nai da wanda nake shirin yin tun a sanda na baro gida nai watsi da shi, wataƙila zuwa sanda na ɗauki fansa tukunna.
saboda haka sai na san yanda nai na ture hakan daga cikin kaina, sannan na dawo da ruɗani dana shiga a ɗazu, wannan Matar dake zaune kusa dani, wannan matar da nasan Akila ce ita kuma tana ƙaryata hakan, to dama ubangiji na halittar surar mutum a guda biyu ne?, tambayar da naiwa kaina kenan, kuma amsar da zuciyata ta bani itace a’a, babu ta yanda za’ai hakan ta kasance, ita ɗin ba kowa bace fa ce Kulun da kika sani, tana so tayi wasa da hankalinki ne.
sai naji zuciyata ta matse, saboda tunawa da nai da marukan da ta sharara min a ɗazu, to a bisa wanne dalili?, ita fa ta zalunce ni. ta ke na saki wata gajeriyar ƙwafa acikin raina, ƙwafa me tarin ma’anoni a wajena. zan gani idan da gasken najeriyar zamu je, zanga iya gudun ruwanta a wajen rainin hankalin da ta ke neman yi min, idan har naga saɓanin abinda ta faɗa to tabbas zan nuna ma ta bata ga komai a ɗayan kaina ba, hasalima abinda taga na ma ta ban ko buɗe shafin farko ba.
acikin wannan duniyar saƙe-saƙen nawa, acikinsa ne muryar Aaliyan dake kusa da ni ta kutso ta cikin tunanina, amon muryarta ya fita da wani irin sauti acikin shirun daya ratsa cikin motar tun bayan shigowarmu, kuma sautin muryar da saida ya girgiza allon ƙirjina.
“kince a jiya kika san komai, aina kika sami visa na shigowa ƙasar nan cikin lokaci kaɗan haka?”.
simple tambaya ce tayi min, amma saida zuciyata tai wani irin duka acikin ƙirjina, wani tsoro na daban ya dirar min, duk da irin daɗin sanyin ac’n dake busawa acikin motar, amma maganar tata sai tasa ni shaƙar wata busashshiyar iska ta daban a maƙogarona, na kuma haɗiye wani wahaltaccen yawu da zance ya wuce da ƙyar, ofcourse zuciyata na faɗa min Akila ɗaya ce, to amma na rasa dalilin daya sa nake shakka da tsoron wannan dake kusa dani a yanzu saɓanin wadda na baro acan, na tattaro yawun bakina na bata amsar tambayarta cikin sanyin murya.
“babu buƙatar da kuɗi basa biya maka a duniya in har kana da su”.
“yi min dalla dalla”. sai kawai na karkato da kaina ga barin kallon titi da nake na dubeta, kamar ba ita tai maganar ba, dan kanta na kan wata ƙatuwar tab dake saman cinyarta, kuma zan iya cewa hankalinta ba akaina yake ba, tana tattaro shi ne a sanda zata min magana. kaman nai shiru naƙi bata sauran amsar, amma tunawa da wannan zafin dake jinin jikinta yasa ni babu shiri nace.
“na biya adadin wasu charges da suka nema bayan na nemi alfamar su barni na fita…”. ban kai ƙarashen zancen ba ta jefo wata tambayar acikin maganar tawa. “aikin me kike?, ko kuma sana’ar me kike?”. tambayar tasa na ɗora ganina akanta da har yanzu fuskarta na kan tab, kuma ata gefen fuskartata na hango tambayar da tai min cike ta ke da tuhuma da kuma mamakin kuɗin dana bayar, duk da ban faɗa ma ta yawansu ba, amma tasan bill ne da ba kaɗan ba.
a wannan karon yawun dana haɗiya yafi na ɗazu zafi, to amma sai na noƙe naƙi bata amsar, nima na kauda kaina gefe nai kamar ban jita ba, ina dalilin da zata tsareni da waɗannan tambayoyin, ai karma ta bari mu isa nigeria na tabbatar da itace ainihin Akilan dana sa ni, dan ina tantama akan maganganun da ta faɗa min, domin basu kama da magana ta hankali ba.
kuma ajikina naji shigar kallonta, dana tabbatar da kallon nata gareni ta gefen ido sai naji jikina ya hau tsuma na tarin tsoron abinda zai biyo baya.
“yanayin da nagani a tare dake ya shaida min cewar Akila bata karya alƙawarin da tasa muka ɗaukarwa juna ba. hakan yasa bata taɓa baki labarin cewa Uwarki Aaliya bata maimaita magana sau biyu ba, kuma idan har ta jefa tambaya da gaske tayi tambayar dan haka amsa kawai ta ke buƙata”.
shirunta yay daidai da shigar leɓena na ƙasa cikin bakina na ɗan tsotsa sannan na bata amsa da,”bana aikin komai kuma bana sana’ar komai. lokacin da gaskiyar ta shiga kunnena zuciyata ta yanke shawarar barin kusa da duk wanda ya sanni na koma inda babu wanda ya sanni, domin zuciyata ba zata iya naɗar baƙin cikin rayuwar shegantani da jama’ar garin bichi zasu dinƙa min ba, dan ko na tambayi Ummi dailin daya sa tayi zina ta haifeni bata da wata ƙwaƙwarar hujjar da zata bani wacce zata wanke laifinta a gareni.
shi yasa da zan taho na ɗauko wallet ɗin Ya Kabiru na taho da ita, da ATM ɗinsa na biya kuɗin komai tun daga kan Passport har kan ticket…”. yanda na lura kamar tana da azarɓaɓi kome zance?, dan a wannan karanta ma ban idasa zancena ba ta jefo wata tambayar acikin maganata.
“dama ke ɓarauniya ce?”. tambayar da tasa babu shiri na ɗago kaina na dubeta kenan, sai dai tsoron wannan manyan idanuwan nata masu kama dana zakanya basu barni naci gaba da kallonta ba, nai saurin sauke kai ƙasa ina girgiza ma ta kai da cewar,”a’a ni ba ɓarauniya bace. wallahi ban taɓa sata ba, Gwaggona da Babana basu ɗorani akan wannan bigiren ba, sun bani kyakykyawar tarbiyar da zan nisanci duk abinda yake ba mallakina ba…”.
yanzunma dai ban ƙarasa ba ta kuma katseni,”kin taho ne bada sanin kowa ba, haka zuciyata ta faɗa min a sanda kike furta kalaman rashin ɗa’arki gareni a ɗazu…shi yasa yanzu a maganarki na tsinci cewar bada sanin Kabiru kika ɗauki wallet ɗinsa ba, me hakan ke nufi kenan?”. na haɗiye wani yawu na daban, na bata amsa da,”sata”. na faɗa muryata na rawa.
saita jijjiga kanta kamin tace,”da kyau! saboda haka da mun sauka a nigeria kanki tsaye ki wuce police station ki miƙa musu kanki, ki sanar musu kin saci wallet kin kuma yi amfani da kuɗin mamallakinta da suka fi ƙarfin riƙewarki. na san zasu nemi Kabir, idan Kabir yace ya yafe miki shikenan, idan yace kuma bai yafe ba ni zan shige masa gaba wajen ganin yayi shari’a dake kin biyasa kuɗaɗensa da kika satar masa kika biya buƙatar kanki”.
tai shiru da maganartata, kuma tare da ɗauke tab ɗin dake saman cinyarta ta zira cikin aljihun jakar kujerar motar, sannan ta zira hannu a jakarta ta ɗauko wayarta dake ringing ta kara a kunne, da larabci ta shiga magana saɓanin turancin da muke a ɗazu. kuma har lokacin idona bai bar kallonta ba da dukkanin iyaka adadin tsoron dake cikin duniyata, tsoronta da tsoron abinda zata iya aikatawa dana tsinci tabbacinsa acikin furucinta da kuma saman fuskarta.
a yanzu zan iya cewa da gaske wannan ba Akilan dana baro bace, da gaske zai iya zama wannan dabance, me daban ɗin da komai na duniyarta yake daban. sam babu sanyi acikin al’amuranta, tun daga kan furucinta zaka shaida ita ɗin me zafi ce, ga wani kwarjini na daban da Allah ya bata, irin kwarjin da zaka ji kana shakkar yin magana a gaban mutum balle kuma haɗa ido da shi, ni dai nasan waccan dana baro ina iya kallon ƙwayar idonta, amma wannan sai dai ma na kalli fuskarta a sace, balle ta kai ga na iya saka idona cikin nata na faɗa ma ta abinda naga dama.
abu ɗaya na sani idan har da gaske ya zama ba itace Akilan da na sani ba, to kuwa in har zan miƙa ƙarar kaina, to itama zan miƙa tata, shari’ar saita zama guda biyu, na miƙa ƙararta akan haifata da tayi ba da aure ba, danni ba zan ɗauki wata kalma ta ƙaddara acikin wannan lamarin ba.
tunanina ya katse a sanda muka iso filin jirgi, kuma maganar drivern ita ta katseni, dan ko dana dawo duniyar da nake rayuwa aciki naga sai ni kaɗai a motar, ita ta fice tuni, na zuro ƙafata waje ina duban drivern daya buɗen ƙofar da girgimamawa.
“ga ta can tare da Al-Hassan”. drivern yace da ni a sanda ya lura da kalle-kallen da nake na nemanta ne. na taka ƙafata ina tafiya kamar me ciwon cinya, sai ƙudundune hannayena nake ajikina har sanda na ƙaraso inda suke tsaye. kuma da alama magana suke da me tattare da nishaɗi duba da yanda haƙorin makka ɗinta ya bayyana a waje dalilin dariyar da tai.
nai tsaye kamar wata munafuka a kusa da wanda ban san kowane shi ba, naji dai sunansa daga bakin direba.
tare dai suke da shi, kaina a ƙasa ina wasa da zip ɗin rigar sanyin dake jikina, ba zan iya kwatanta abinda nake ji atare dani ba, amma dai ina jin wani abu me kama da tsoro, taraddadi da kuma fargaba, ta ƙasan ido na hango ta ɗaga ƙafarta da zummar tafiya bayan tai magana da Al-Hassan ɗin, amma ban san me tace masa ba, kasancewar da larabci ta faɗa, ita kuma ta tafi tana nufar wurin da jirgi yake.
wucewar daƙiƙa biyu na ɗago da ganina ga mutumin da tun zuwana wajen tsayinsa ya bani tsoro, mutumin da Aaliya ta tafi ta barni da shi, Al-Hassan! kuma tsoron dake cikin zuciyata ya ninku a sanda idona ya sauka akan fuskarsa, nai wata muguwar razana naja da baya, ina kallonsa da maɗaukakin mamaki da al’ajabi gami da ruɗani.
me ya kawo Emanuel nan?, kuma mene haɗinsa da ita?, tambayar da naiwa kaina kenan, sai dai kuma abinda ya gilma ta cikin idona shi ya bani tabbacin ba Emanuel bane me kama da shi ne, wanda zan iya kiransa photocopy of Emanuel.
na haɗiye wani abu a maƙoshina da ban san ko mene ba, ya ƙara tabbata Major Tosin shine mahaifinmu, kuma ko ba’a faɗa min ba wannan shine wanda aka haifemu tare, duk da bama kama da shi amma kuma ga kama ta jini nan ina kallo ɓaro ɓaro a tare da shi. na buɗi baki zanyi masa magana sai naga ya zabga min wata uwar harara da tasa na ɓata rai kamar yanda shima nasa yake, na kuma bishi da tawa harar nima.
cikin ɗagin murya yay min maganar da ban san me ya faɗa ba, dan haka ina zumɓuro baki nace da shi bana jin yaren da yake ya faɗa da turanci. sai kawai yaja tsaki yay gaba abinsa ya barni a wurin, nabi bayansa da ido cike da haushi, wannan miskilinne Yaya na?, tabɗi lallai ma.
kamar Aaliya tasan meke faruwa sai ta datakata da tafiyarta ta juyo, ban san me tace da shi ba, kuma shima ban san abinda ya mayar ma ta ba, amma dai a maganar da ta ƙara yi masa da turanci cewa tai,”eh mana bata jin larabci, ka ma ta yaran da ta iya…kuma nima har muje mu dawo da english ɗin zamu ke magana kaji me nace ai”. shima cikin harshen turancin yace,”to amma Mami wace ita?”. daga inda nake na hangi irin kallon da tai masa kamin ta bashi amsa da cewar,”uban ƴan kishi, to ƙanwarka ce Hussainarka da aka haifeku tare”. “Hussainata dai Mami?, da gaske kike?”. tace masa,”ban san lokacin dana fara maka ƙarya ba balle na dinƙa shigar da rantsuwata cikin maganarmu kamin ka yarda da ni”. da alama suna ɗasawa da shi, dan maganar tayi masa ne fuskarta tana washewa da annuri.
sai ya sake tambayarta da cewa,”to Mami ba ki faɗa min abinda zai kaimu nigeria ba”. sai naji tace masa,”Mai Martaba Abi kayi haƙuri muyi tafiyar nan, idan muka je can duk zan amsa maka tarin tambayoyinka ranka ya daɗe, yanzu duk a matse nake da naje inda zan isa”. sai ya juyo yana min harar ƙasan ido, kuma kaman wanda aka tursasawa yin maganar yace da ni,”zo ki wuce”. ina ƙunƙuni da mummurguɗa baki na fara tafiya zuwa inda yake, har yanzu kuma Aaliya na tsaye tana kallonmu da jiran tahowarmu.
tace da shi,”ka bata jakar ta riƙe, kai ka huta”. maimakon ya bani kamar yanda ta ce sai kawai ya jefo min ajikina, kuma sai naji nai saurin tarota ajikina gudun karta faɗi ƙasa, dan nasan akwai muhimman abubuwa a ciki.
kamar daga sama naji yace,”gaba nake dake, so ki biyoni a baya”. na ɗago na harare shi da kyau kamin nace,”ba haka Ya Kabiru yake min ba”. “Al-Hassan nake ba Kabir ba”. abinda yace dani kenan yay gaba, ni kuma nabi bayansa.
duk sun rigani shiga jirgin, kuma sai dana iso gaban jirgin naga a jikinsa an rubuta EMIRATE AIRLINE da manyan baƙi, a ƙasansa kuma an rubuta Shaik Tamin Bin Hamad Al Thani da ƙanan baƙi. nasa ƙafa na shiga ciki kuma daga can gaba na hangosu kowa kujerarsa daban, na wuce nima dan neman wurin zama sai naji Aaliya tace,”ki zauna kusa da Al-Hassan”.
na zauna a kujerar kusa da shi, kuma sai naji duk na takura, gashi bini bini sai yay tawani ja min tsaki, yana harata ta gefen ido, kamar ma me shirin rufeni da duka.
ban san lokacin da bakina ya furta,”Mami ni bana son zaman nan”. tace,”halin ku ɗaya. tashi ki dawo kujerar gabansa”.
sai yay karaf yace,”Mami ta dai koma ta bayana, ni ne fa babba”. kafin tace da shi wani abu nace,”ai sai ka bari ka tabbatar da ni ƙanwar taka ce kafin ka yanke hukuncin kaine Babba”. sautin murmushinta kawai muka jiyo, kuma tai shiru bata ce damu komai ba, shi kuma sai yay guntun tsoki ya miƙe daga kujerar tasa gaba ɗaya ya koma kusa da ita.
na taɓe baki kamin na nemi wata kujerar na zauna, kuma duk da hakan a kujerar gabansu na zauna, ina sane dan naga shi ɗan rainin hankali ne, bai san duk tsiyar da yake ji da ita ba na fi shi. ina jinsa yana cewa da ita,”Mami da kika tsintota ba ki faɗa ma ta ni jinin sarauta bane, izzata ba zata bari na ɗauki rashin kunyarta ba. please Mami idan taimaka ma ta bai zama dole ba ki yasar da ita, dan bana sonta”. amsar da ta bashi itace,”to sai ka fara koyawa zuciyarka sonta tun wuri”.
kuma maganar Aaliya ta shiga kunnena a sanda na kwantar da kaina jikin kujerar na rufe ido.
“a irin furucinki na rashin hankali a ɗazu, na tabbatar da cewa ba ƙaramin ɗibar albarka ki kaiwa Akila ba kamin gudowarki. to umarnin da zan ba ki da zarar mun isa ki duƙa a gabanta, ki zube gwiwoyinki a ƙasa, ki tattaro yawun baki da dukkan wasu tarin kalamai na ban haƙuri da suke cikin kanki ki bata haƙuri, ki nemi yafiyarta, ki bata haƙuri ki nemi yafiyarta…umarni nake ba ki Maryam, domin akan Akila bani da kyau ko kaɗan, wallahi summa tallahi in har ta nuna min rashin jin daɗin rashin kyautawar da kika ma ta, na rantse da Allah zan manta da zafin naƙudarki, na saɓa miki kamanni ta yacca ba zaki taɓa ganuwa ba a idon duniya…furucina ne wannan, kuma alƙawari ne saina cika shi”.
shirunta yay daidai da tambayar da Al-Hassan ya jefa ma ta,”Mami wacce iriyar magana naji kina yi, wace me irin sunanki haka, kuma me kike nufi da abinda kike faɗa?”. duk da bana kallonta amma nasan tayi murmushin da ya tsaya ne iyakar leɓenta, kuma sai naji ta bashi amsa da cewar,”kamar yanda ta ke acikin duhu, kaima acikin duhun kake, haɗuwata da ƴar’uwata ne zai haska muku hanka, har ku sami amsar tambayar dake saƙe acikin zuciyoyinku…bana son wata tambayar Al-Hassan”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button