NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

what am i going to say???????, well, to all of you that commented on the last chapter, i say a big thank you????…i enjoyed some of the conversation i heard from you guyz…please keep the votes and comments comming oak…

and what do you think would happen? surely za’a ɗaura auren Maryam a gobe, but dawa za’a ɗaura?, Maryam tawa zata tabbata?, don’t you think everyone acikinsu ukun deserves to marry her?, how do you think Kabir’s plan will be akan Nawwara?….Jawad! Ahmad! Kabir! kowa fa son gaskiya yake ma ta and kowa kuma ɗin ya taka wani muhimmin abu a rayuwarta. wait, let make a decison! ko dai ta zama bata kowa ba acikinsu a raba sa’insar da zata iya shiga tsakani! dan idan Kabir ya iya haƙuri, do you think Ahmad zai iya haƙura?, kuma ya ɓangaren su Hajjah Nashwa(Maman Jawad) zai kasance?…abunda bamu sa ni ba shine, zaren wata ƙaddarar da bamu san da shi ba zai iya warwarewa a gobe, wata ƙila before the wedding Fatiha takes place or after, WATA ƘADDARAR TAMKAR ZANEN DUNTSE TAKE….an interesting Chapter coming next insha’Allah.

One Love Guyz❤

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

(48)
“menene?”. tambayar tasa ta fito daga bakinsa kai tsaye zuwa cikin kunnuwanta, kuma yanayin yanda yay maganar ɗumin iskar bakinsa na fita ta sauka a wuyanta ya ƙara haifar mata da kasala. ta buɗe lumsassun idanunta ta zubesu akan hannunta da har yanzu ke kan ƙirjinsa riƙe da gaban rigarsa, wata uwar kunya ta lulluɓeta har tana neman nutsar da ita acikin ƙasa, yayin da bugun zuciyarta ya ƙaru wanda tana da yaƙinin yana iya jin sautinsa dum-dum!. a hankali ta shiga ɗauke hannun nata akansa, shi kuwa yana lure da yanda hannayenta ke rawa kamar ana girgizasu. ya fahimta a tsorace ta ke, tsoron da shi kuma baya so yake ganinsa a tare da ita. sai kawai shima ya saketa ya matsa baya da ita yana kallon yanda hatta ƙafafuwanta rawa suke, hakan yasa yace da ita,”zauna”. kuma yanayin muryar tasa da ta fito fayau tasa ta saurin ɗago kai ta dube shi, a lokacin har ya zauna kan kujera yana tattara wasu takardu dake gabansa.
ta silale ƙafafuwanta zuwa ƙasa ta durƙushe akan carpet ɗin, har yanzu hannunta bai bar rawa ba, kuma tambayar daya jefo ma ta ne yasa gaba ɗayanta ta girgiza a lokaci ɗaya. “kinyi wanka?”. sai ta shiga girgiza masa kanta dake ƙasa ba tare da ta amsa masa da baki ba. kuma a wannan karon daya ƙara jefa ma ta tambayar taji yanda amon muryarsa ya sauya daga na ɗazu. “me yasa to ba kiyi ba?”. tai shiru ta kasa cewa komai, sai taji ya ƙara cewa. “daga wannan lokacin har zuwa gobe kar wadda ta ƙara saki aiki acikin gidan nan kika yi, kinji na faɗa maki, kuma duk yaron da naga kin ƙara goyawa abunda zanwa goyon yaron kaɗai zaisa ki shiga hankalinki…”. sai tai yunƙurin katse maganarsa da cewan,”ai…”. kuma bai bari ta ƙarasa ba shima ya tari numfashinta,”ai me? ke baiwar kowa ce? ko su suka ɗauko ki aikin?”. yanda yake maganar cikin ɗagawa sai ya tsoratata, bata san sanda bakinta ya buɗe da ce masa,”a’a Ya Kabir duk ba haka bane”. muryartata ta fito a karkarye. kallonta kawai yake yi kamin yaja tsaki ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihun wando. sai daya zo saitinta sannan yace,”minti goma na baki kiyi wanka ki shirya”. ta miƙe da azama zata bar ɗakin ƙwayar idanunsu ta gauraya, ya wurga ma ta wani kallo daya tsaida tafiyarta yace,”ina nufin ki shiga wannan toilet ɗin kiyi wanka”. ta haɗiye wani guntun yawu sannan tace,”zan ɗauko kayana ne, kuma Innah zata nemeni zamu yi yankan albasa”.
kai tsaye bakinsa ya fito da furucin,”ba zaki yi ba. ko ɗazu da nace karki ƙara aikin komai kunnenki a toshe yake?”. “a’a”. baice komai ba ya juya zai fice yaji tana binsa a baya, bai tsaya daga tafiyar ba taji yace,”karki ja na sauke duk fushina akanki…ina nufin kiyi wanka anan, ga kaya can a leda ki sakasu, idan kin gama ki sameni a parlo”. abinda yace kenan ya fice gaba ɗaya daga ɗakin cikin taku biyu. tabi bayansa da kallo tana haɗiye wani ƙullutun abu da bata san ko menene ba, wucewar sakanni uku ta ɗaga ƙafarta da ta ke tunanin ta maƙale a wurin ta ƙarasa ta rufe ƙofar ɗakin, sannan ta juyo ta nufi inda toilet ɗin nasa yake ta buɗe ta shiga, bata da natsuwa sam, hakan yasa ta gaggauta yin wankan ta fito, ƙamshin shower gel ɗin da tai wankan da shi ya baɗe ɗakin, hatta ita kanta lumshe ido ta ke tana zuƙar ƙamshin saboda daɗinsa.
a ƙasa ta tsuguna ta jira har ruwan jikinta ya gama tsanewa gaba ɗaya, kuma ta miƙe kenan sai gani tai ƙofar ɗakin ta buɗe a lokaci guda, kuma ƙofar ta gaya ma ta wane tun kamin taga ƙafafuwansa ds suka shigo a yanzu, kuma ba tare da ta shirya ba sai jinta tai a tsaye akan ƙafafunta duk a rikice, ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi.
sam bai lura da ita ba sai da yaje ya kwashi takardunsa ya dawo zai fita tukunna ya lura da ita a tsaye sai ƙudundune jiki ta ke, kallo ɗaya yaywa gashin daya kwanto saman goshinta yasan zai iya cewa jikinta yaga ruwa, amma yanayinta sam baiyi kama dana wadda tai wanka ba. dan yanda ya fita ya barta da kayan jikinta haka ya dawo ya sameta da kayan jikinta. kallon hannayenta dake aikin rawa yake yana jin kamar ya kamo su ya riƙe acikin nasa har sai sun tsaya, to amma hakan da zaiyi dai-dai yake da ƙara rikita yanayin tsoron da yake gani tare da ita, ƙwaƙwalwarsa na gaya masa cewa bayan ihun da yake ganin bakinta zai iyayi wannan siraran ƙafafun nata har kwasa da gudu ma zasuyi su fita su bar ɗakin. kawai sai ya kaɗai kansa yace da ita,”har yanzu ba ki wankan ba?”. kamar jira ta ke yay maganar da sauri kuma cikin saurin murya tace, “nayi tun ɗazu ma na fito, kayan da zan saka ne ban san inda suke ba”. abinda tace ɗin ya fito tare da tsayawarsa a gabanta, kuma wannan dunƙulallan abun dake maƙogwaronta yaƙi wucewa a sanda tai ƙoƙarin kora shi da yawu. a yanzu da ta ke jin saukar numfashinsa a jikinta ji ta ke kamar zai ɗaga hannu ya duketa ne. dan haka bakinta yay saurin furta,”kayi haƙuri yanzu zan shirya”. “why are you afraid of me?”. bata iya kallonsa ba kuma bata iya bashi amsa ba, kuma taji me yace ɗin. “wannan wankan da kikai sunansa wankan ƙazanta”. ya miƙa hannunsa yana haska ma ta agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa yana ci gaba da cewa,”ko da saɓi ɗaya ki kaiwa jikinki baici ace kin fito a minti biyu ba balle har ki ƙara da cewar tun ɗazu kika fito”. sai yasa hannu ya ɗago haɓarta,”ki nutsu Nawwara babu abinda zanyi miki, ba zan cutar dake ba, ni ba mugu bane…kawai ina so ne naga kema kin zama kamar kowa ba yanda kowa ke son ganinki kina kai komon aiki ba…ki koma ki sake wannan wankan, akwai towel aciki ki ɗaura shi karki mayar da kayan jikinki dan wata dauɗar ce zata kuma hawa jikinki…idan ma ba za ki iya ɗaura nawa ba to akwai sabo daga ɗayar hanger ɗin yana nan ki saka shi”. sai kuma ya saki haɓar tata yay ma ta nuni da bakin gadonsa,”kayan da za kisa suna cikin waccan ledar, dan Allah Nawwara karki ɓata lokaci, jiranki nake yi, kuma nima jirana ake”. sai tai masa knooding kanta kawai, ya juya ya fita sannan ta koma toilet ɗin ta sake yin wani wankan, sai dai bata sako sabon towel ɗin ba kaman yanda yace, nasan ta saka ba tare da tasan me yasa zuciyarta ta sauya ra’ayi ba a sanda zata saka sabon.
atamfa ce sky blue da kwalliyar flowers dark blue acikin ledar da ta buɗe, anyi ɗinki jiki da dark blue ɗin net less, daga atamfar har ɗinki sun bugu, tana iya tuna inda ta taɓa ganin irin atamfar da kuma kuɗinta da taji an ambata, ranar da su Ummi suka je store sukai sayayya, acikin kayan taga atamfar har Ummi tace ta bawa Sadiya ita a gudunmawar bikinta, atamfar nada tsada dan dubu sha biyar taji Ummi na cewa Yagana ta siyo, har Yagana ke cewa ana almubazzaranci dai da kuɗi, ta ke ta mitar mene zaisa a sayo atamfa harta wannan kuɗin, a sayo ta ƙasa da hakanma sauran kuɗin kuma ai sadaƙa dasu tunda an lissafa dole sai an kashe su.
sai ta ke ganin kamar zata yi kuskuren saka kayanne, wata ƙila yayi mantuwar nuna ma ta sune, amma wannan kayan sunfi ƙarfinta, sun girmi matsayinta, ba ta kai ba, kuma bata isa ta saka sutturar da ta kai waɗannan kuɗin ba, abunda ta sani shine kuɗin suttirarta baya wuce sama da dubu ɗaya da ɗari biyar, atamfa leda kenan itama kuma sai sallah ne Baba ke siya musu, amma yawancin kayanta kwance ne suke samu a basu. saboda haka sai ta zaro mayafin ciki ta yafa shi akanta, duk da cewar ba wani babba bane amma yazo ma ta har kusan cikinta, ta ɗauki kayan ta riƙe ta nufi ƙofa ta fita, daga bakin ƙofar ta tsaya kanta a ƙasa, sannan ta buɗe ba ki, ta ɗan ɗaga muryarta yanda zai jiyota tace,”wanne ne kayan?”. idonsa ya ɗauke daga kan tvn dake manne a bango, ya juyo zuwa inda yaji sautin muryarta da tambayartata, kuma idonsa ya fara sauka akan ƙafafunta da suka bayyana ta ƙasan towel ɗin, kamin ya maida ganin nasa ga kayan da ta ke nuna masa. “ehh su ne”. yana faɗin hakan ta juya ta koma, kayan kaman an auna da jikinta, dai-dai ita ciff.
tunaninta bana yadda zata fita gare shi acikin kayan ba ne, ta yanda zata fita ta dinga ratsawa ta cikin mutanen gida suna ganinta. saboda haka saita yafa mayafin a kafaɗa, shi kuma ɗankwalin ta ɗora shi a saman kanta ta rufe fuskarta da shi, sannan ta fita daga ɗakin.
kuma abunda ya bashi tabbacin fitowarta ƙamshin man da ta shafa, dan haka ya ɗago yana kallonta a inda ta ke tsaye daga bakin kujerar dake kusa da shi. kamin ta silale ta duƙa ƙasa, wannan hannayen naci gaba da rawa kamar yanda suke yi tun a ɗazu, ba dukan fuskarta ya gani ba amma yasan tayi kyau, gefen leɓensa ya tale da murmushi sannan yace da ita. “ga abinci can kije ki zuba”. “zanci idan na koma ɗaki”. shi ɗin kawai ta gani a gabanta sanda tai shiru da maganar, kuma kamin tai wani yunƙuri taji ya sunkoyo ya kamo hannunta guda ya ɗagota, sannan yajata suka fara tafiya zuwa inda dining ɗinsa yake daga can baki-bakin ƙofar shigowa, Allah ya sani a wannan halin da take ciki babu abinda ta ke so tayi irin ta kurma ihu ta ambaci ta shiga da tara, dan halin da yake sata aciki tun daga ɗazu zuwa yanzu yafi gaban ta shiga uku, ta lura ya kasa fahimtar cewar yana neman ya zautar da yanayinta musamman a yanzu daya ƙara sa ɗaya hannunsa ya kamo ɗayan nata ta bayansa, ya damƙe a nasa hannun, kuma abinda ta fahimta so yake ya dakatar da duka hannayen nata daga rawar da suke yi.
“haka nacewa telan ɗinkin na ƴar siririya ne, siririyar fa irin firit ɗin nan, dan ƙafafunta yawo suke acikin zane duk sanda tasa kaya, kaman yanda hannunta yake yawo acikin duk hannun rigar da tasa, tsayinta kuma gaba ɗaya a ƙasan ƙirjina yake saman cikina kenan. amma karka yi awon daidai da yanda ƙaƙafunta da hannunta zasu yi yawo a kayan, kayi daidai da yanda kayan zasu zauna ajikinta”. abinda yake ce ma ta kenan lokacin da suka ƙaraso bakin dining ɗin, yace taja kujera ta zauna sannan ta zuba musu abincin. ta zuba abincin amma ta kasa ci sai tunanin maganar awon ɗinkin ta ke acikin kanta. “na bada awon dai-dai ko?”. taji ya tambaya a sanda ya kai spoon bakinsa, sai ta ɗago kanta a yanzu ta kalle shi sau ɗaya sannan ta maida kanta ƙasa. “ba ki ban amsa ba”. “Ya Kabir amsar me?”. “surutun da na gama yi miki a yanzu, indai bai bi iska ba to akansa nake magana, in kuma yabi iska to kici abincinki kawai”. kuma haka kawai maganar tasa yasa murmushi suɓucewa a fuskarta kamin tace da shi. “Ya Kabir to ai ban san wace siririyar ba”. kuma sai kawai taga shima yay murmushi yace,”ki ƙaddara a matsayin kece, kuma acikin ɗinkin awon yanda aka bada”. bata san lokacin da ta fara cin abinci ba tun daga lokacin nan daya ce in maganarsa bata bi ta iska ne, dan haka a yanzu da ta haɗiye abincin dake bakinta cikin jin kunya sai tace da shi,”ehh yayi daidai amma ni nafi waccan tsayi”. so yake ta sake taci abincin dalilin daya sa yake janta da zancen kenan. dan haka ya ƙara cewa,”kenan idan naki ne anyi kuskuren bada awon kenan?, in aka kawo maki tsayinsu zasu yi maki kaɗan”. kuma kawai sai yaji tace,”aini Ya Kabir na taddoka a kafaɗa ita kuma kaga a cikinka kace”. ya gyaɗa kansa har sau biyu a sanda ya kai kofin lemu bakinsa, bai sake cewa da ita komai ba sai daya lura ta gama cin abincin tukunna ya miƙe yace ta tashi. “zan kwashe kwanukan…”. wani kallo da yay ma ta shi ya dakatar da sauran furucinta, hakan yasa ta tura kujerar baya ta isko zuwa inda yake ta tsaya, kuma tsayuwarta kenan taji ya janyota ta tsaya ajikinsa. “banbance min wannan tsayuwar da maganarki ta ɗazu”. a hankali saita buɗe idonta dake rumtse, kafin ta kelleta gaba ɗayanta akan cikinsa. kuma maganarsa saita katse tunaninta a sanda yace,”kin ƙara faɗa min kin kerewa kafaɗata ko sai na kaiki asibitin wanke ido”. “na kere maka”. ta faɗa a sanyaye shi kuma yana sakinta a hankali ta bar jikin nasa, kafin yayi gaba ya barta a baya, sanda ta ƙaraso bakin motar tasa har ta buɗe zata shiga baya cikin ɗagin murya yace da ita,”drivernki ne ni”. da sauri ta maida murfin motar ta rufe ta dawo gaba ta shiga, ta tsorata sosai da shi ɗin da yanda yay ma ta maganar, dan bata mantawa da kwanaki can kamin Yaya Maryam ta bar gidan ta taɓa yi masa irin hakan, kuma ƙiris ya rage ya kaiwa fuskarta mari tai saurin kauce ma sa, shi yasa ko a yanzu da yace ma ta shi drivernta ne ta fuskanci me yake nufi.
da gudu yaja motar ya bar harabar gidan sanda mai gadi ya buɗe masa gate, ko gaisawa bai tsaya yi da mai gadin ba kamar yanda suka saba da shi a duk sanda zai fita, kuma tunda ya hau titi magana bata shiga tsakaninsa da ita ba har suka baro bichi ya shigo kano, kuma har zuwa sanda yay parking motar tasa a bakin S. FARI BEAUTY PALACE, COURT ROAD.
maganar da zata iya tunawa kawai ta shiga tsakaninsu a awa ɗaya da suka ɗauka suna tafiya akan titi yace da ita,”kina jin yunwa?”. kuma a wannan lokacin da yay tambayar girgiza masa kai kawai tayi alaman a’a, kuma bai ɗauki a’a ɗin tata a ya yarda ba sai daya tsaya a wani restaurant yay takeaway tukunna suka ci gaba da tafiya.
a yanzu da suke bakin wurin da ta lura wajen gyaran gashi da jiki da ƙunshi ne, waya taga ya ɗauko ya kira wata lamba kuma babu jimawa wata bayerabiyar budurwa ta fito, bata san maganar da sukai da ita ba tunda cikin harshen turanci ne, kamin budurwar ta juya ta koma ciki shi kuma ya juyo gareta yace da ita. “idan an gama ki kirani da wannan wayar”. ya faɗa yana miƙa ma ta ƙaramar wayar dake hannunsa, ta ɗago ido ta kalle shi kamin tasa hannu biyu ta amsa. sannan ya ƙara miƙo ma ta card ɗin da taji Ya Maryam na kiransa da ATM ya bata yace,”6915″. sai daya maimaita ma ta lambobin sau biyu kan ya ɗora ma ta da cewar,”lambobin sirrin banki ne. idan kika bari wani ya gani zaki ja a yasheni gaba ɗaya, kuma aka yasheni kamar an yasheki ne”.
“a dawo lafiya”. shine abinda tce da shi sanda tasa ƙafa ta fita daga motar, ta rufo ƙofar a sanda taji ya kira sunanta,”Nawwara”. hakan yasa ta dakata daga tafiyar ta leƙo ta glass ɗin tana amsawa,”na’am Ya Kabir”. “ai miki mai kyau, haka zaki ce da su duk dana faɗawa incharge ɗin wurin”. “to Ya Kabir, na gode”. ta faɗa tana juyawa ta nufi inda ƙofar shagon ta ke, bai kuma bar wurin ba sai daya tabbatar da shigarta wurin har ya ƙara kiran matar ya tambayeta ta shigo tace masa ehh sannan ya baɗe wurin da ƙura.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button