NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE


anyi sallar isha’i ina zaune kan sallayan ban miƙe ba inata tunanin Mamina, sai ga Nawwara ta shigo hannunta riƙe da tray na kayan abinci, na amsa sallamarta ta nemi kan ƙaramin table ɗin dake ɗakin ta ɗora akai, sannan ta dawo tace da ni. “Yaya abinci ne Yagana tace na kawo nan, wai ki shirya yanzun Ya Kabir ɗin zai shigo”. nai saurin ɗagowa nai ma ta wani duba tare da cewa,”zai shigo yayi me?”. sai tai shiru kan tace,”ance dai zaa kai muku abincin ɗakinsa yace a kawo nan”. ban ƙara ma ta magana ba ta miƙe ta fita ina bin bayanta da harara kamar wadda tai min laifi. kuma na miƙe ina ninke hijab ɗin Yagana da nai sallah sai ga shi ya shigo, ni dai banji sallamarsa ba ƙamshin tararansa ne kawai ya sanar dani shi ɗin. ya shigo cikin wannan takun nasa da bana iya ɗauke idona akai amma ta yanda ba zai lura ba, ya ƙaraso har gabana sannan ya miƙo min baƙar leda yana faɗin. “ƴar gidan Ummi gashi inji Umminki”. nasa hannu na amsa ina turɓune fuska, na taka zan ƙarasa ga wadrobe ɗin Yagana naji yana tambayata wai menene a ledan, dan tunda aka bashi yake jin ƙamshi, motarsa ma duk ta cika da ƙamshinsa, nai kaman ba zance komai ba sai can nace. “me yasa ita da ta baka baka tambayeta ba tun acan”. “ke naga damar tambaya ai”. na juyo ina masa kallon ƙasan ido sannan nace,”to nima ban sa ni ba”. sai kawai ya saki murmushi tare da cewan. “bari naje nai wanka, yanzu zan dawo muci abincin…visa ɗinmu ya kammala amma goben a abuja zamu kwana sai washegari zamu wuce”. ni dai bance masa komai ba har ya juya ya fice. yana fita Yagana ta shigo tana ta maganganunta, itama bance ma ta ƙala ba saida ta gama abinda zatai zata fita sannan nace,”Yagana kice da wancan jikan naki ya dawo ya ɗauki abincinsa, zan rufe ƙofa ina jin bacci”. sai ta dakata ta juyo ta dubeni da kyau sannan tace,”sannu sara mai baƙar takashi, ai mai hali ba zai taɓa fasa halinsa ba. to da za ki rufe ɗaki naki ne dama zaƙwaƙura?…ai sai ki bari ni da nake da iko da abinda in gama abunda nake idan na shigo kya rufe…”. ban jira ta kai ƙarshen zancenta ba nace,”to ai dai naga da aka kawoni ke kika kawo ni ɗakin naki ko…to kije kiyi abinda za ki da sauri ki dawo zan kwanta”. ta saki baki galala sannan tace,”to Uwar Yagana naji”. ta juya ta fita tana faɗin,”ni dama da Amadun aka barki ya saita miki hali bada wannan sanyi ƙalau ɗin ba…da sonki zai hana shi hukunta ki”.
na zauna bakin gado ina jiran Nawwara dana kira a waya tazo ta ɗauke abincin da ba cinsa zan ba ta fita da shi. sai kawai ganinsa nai ya shigo sanye cikin ƙananun kayan da idan nace bai yi kyau acikinsu ba ma nai ƙarya, muna haɗa ido kuma na ɓata rai. ya ƙarasa bakin table ɗin ya zubo abinci a plate sannan ya ijje akan carpet ya umarceni dana sakko muci. nai masa shiru na kauda kai. ya ƙara cewa,”yanzu fa Ummi ta kirani tana tambayan kinci abinci”. nace,”to ni ba zanci ba na ƙoshi…kuma ka gama ka bani takardata na tafi gidanmu yanzu, dan naga da gaske ne kai ɗin aka aura min kuma ni ba zan zauna da wanda baya so na ba”. sai ya sa ki wani killer smiling mai ƙarfin sauti da cewan. “ahh tunda ma dai ke kina sona ai da sauƙi, a hankali kya koya min son naki”. da sauri nace,”ni nace maka ina sonka, Allah sauƙa na so wanda baya so na, yake ƙaurace min saboda ƙaddarar da ta samar da ni”. yay shiru baice min komai ba, sai na ɗago ido ina dubansa da yanda ya tsareni da ido, na tsuke baki na murguɗa shi gefe sannan nace masa. “ko baka ji ba, nace bana sonka, idan kaji haushi ka ɗauka mataki”. ai rufe bakina ke da wuya sai jin hannunsa nai saman bakina ya matse da ƙarfi, kamin nan yasa haƙori ya gantsara min cizo a leɓe, na kuwa daddage na kurma uban ihu, ihun daya ja Yagana zambaɗa salatin da ta bata shirya ba.
a lokacin kaman na fita parlon na sameta na bibbigeta dan takaici, salati ta ke zabgawa tana faɗin wai. “shikenan Abunda nake gudu ya faru…yanzu Kabiru haƙurin da nace maka shine ka gaza yinsa, yanzu shikenan akan gadon nawa…ni Rakiya naga ta kaina, haihuwar ƴaƴa da jikoki iya shegen da ba’a taɓa min ba sai akanku”. ihun dana kuma saki ya ƙara sakata zabga salati tana cewa,”Kabiru kana jina ina salati da salallami shine ba zaka barta haka ba, dole dai sai an fara lissafin kwanakin ciki daga ɗakina…Kabiru nace ka ƙyaleta haka kuzo ku wuce Habujan a yanzu ku ƙarasa acan, ko kuma ga ɗakinka can ku ƙarata amma ni wannan ihu ƙarasa shi ba a ɗakina ba”.

ina godiya sosai ga tarin adu’oinku ga Yayana kuma Angonmu na wannan week ɗin, Allah ya amsa ya kuma bar zumunci a tsakaninmu….masu cewa na aiko masu da kayan gara to ku biyoni bodar niger ku amsa????.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

(52)
Yagana na tsaye na sababi Zulai ta faɗo parlon da sauri, tambayarta ta ke lapia amma ko sauraronta bata yi ba, salati kawai ta ke zabgawa tana kambaba zancen da ba shikenan ba. Zulai ta juya ga su Basma dake zaune kan kujera hankulansu na kan tv suna kallo, ta kira sunan Sadiya, ta juyo a sanda ta ke kai mango baki tana sha. “wannan ai shashashanci ne Sadiya, kuna jin Yagana na salati baku tashi kuga meke faruwa da ita”. kamar Sadiya ba zata ce komai ba can ta nisa sannan tace. “Inna ki yiwa Allah ki ƙyale wannan rikitacciyar tsohuwar”. kuma lokacin Yagana ta juyo tace da Sadiyan. “wannan kuma da wadda ke tsaye kusa da ni kike ba ni ba”. Sadiya ta ƙara kaiwa wuya amma bata ce ma ta komai ba. Zulai ta maida hankalinta ga Yagana dake faɗin,”ki kalle min nan fa Uwar Amadu, wai yaron nan Kabiru daga yi masa halacci nace ya shiga suci abinci da matarsa shikenan sai ya tafi aikata abunda ba haka mukai da shi ba”. Zulai tace,”me ya faru Yagana”. Yagana tai guntun tsaki sannan tace,”kema Zulai wataran dai akwai ki da duhun kai…matsa ki ban wuri nan kiga na shiga na fito da shi”. sai a yanzu Zulai ta fuskaci inda maganar Yagana ta dosa, dan haka ta dakatar da ita daga shiga ɗakin tana cewa,”yi haƙuri Yagana”. “nayi haƙuri kamar ya Uwar Amadu…ba ki lura da ta’asa ake aikawa ba akan gadona ba ne”. “bai zama lallai hakan ba Yagana”. “ke kinji uban ihun da yarinyar nan ta kurma kuwa da kike faɗar wai ba farketa yay ba…ta ina za ki sa ni, haka fa yaron can Lamiɗo yay mana da bikinsa, daga shiga ɗaki a barsa ya keɓe da matarsa sai fito mana yay kayan jikinsa duk sun ɓaci da dilkar da ake shafa ma ta, to yanzu tsakani da Allah ki faɗa min a wanne irin yanayi Kabiru zai fito, kai kai ni Rakiya ina ganin abinda ya isheni bai ishi Allah ba….akan gadona, kan gadona fa akai kwanciyar aure, wannan ɗiban alhaki da me yay kama”. tai zancen tana neman kujera ta zauna haɗe da rafka tagumi. Sadiya taja dogon tsaki tace,”wallah Yagana kayan haushinki da yawa yake…taya mutumin da baifi minti biyar da shiga ɗaki ba za ki ce ya farke matarsa?, sai kace wanda zai yi fyaɗe ko kuma wanda aka aura masa wacce baya so…dan Allah ki rage zuzuta abu”. Yagana dai bata ce ma ta kanzil ba tai kunnen uwar shegu da ita.
ni kuwa tunda Ya Kabir ya sakar min baki daga matsar da yay masa nake aikin matsar hawaye, naja hancina daya cika da majina ina ƙara kumbura da irin tunanin sharrin da zan ƙala masa wurin Daddy a raba wannan auren. yasa hannu ya gyarani akan cinyarsa da nake a zaune, zaman da yay min ta dole dan kawai zaiyi forcing ɗina naci abinci. ya kawo spoon bakina wanda ya ɗebo eba daya sha miyan egusi busashshen kifi. “oya haa”. na kasa yi masa garda saboda yanda nnaga ya ɓata rai, irin ɓacin ran da tun tasowarmu tare ban taɓa gani a fuskarsa ba, haka ya dinƙa feeding nawa har sai daya tabbatar da cikina ya cika kamin ya ƙyaleni.
kuma abunda nake ta tsoro tun shigowarsa shi ya faru, idonsa ya ƙyalla kan wedding card gift ɗin dake aje gefen pillow ɗin dana ɓoye. a ɗazu da ina sallar isha’i Ya Ahmad ya shigo, lokacin tayarwata kenan dan haka bai iya zaman jiran na idar ba ya sunkuya har ƙasa ya aje min card ɗin sannan ya juya ya fita, ya fita ya barni da bugun zuciyar da har yanzu bai tsaya ba, kuma harga Allah a lokacin ko da ace nayi sallama ne ba zan iya ɗaga kai na dube shi ba balle na iya yi masa magana, dan ban san da me zance masa ba.
“wancan card ɗin fa?”. tambayar Ya Kabir ta katse min gajeran tunanin da nake, ƙirjina ya fara yin fat-fat, ban san me aka rubuta ajikin card ɗin ba, dan tunda na ɗauko aje shi kawai nayi da zummar idan zan kwanta zan karanta, abu ɗaya kawai da nake tunani nasan ba zai wuce marriage wish ba. ban san me zance masa dan haka nayi tsilli tsilli da idanuwa bakina a gimtse. hannunsa na zagayowa kan cikina ya ƙara tambayata, da irin sautin da ayanzu na gagara yin shiru na amsa masa da. “Card ne”. “ehh ai nasan card ɗin ne…na mene shine abunda nake tambaya”. na haɗiye wani guntun yawu sannan nace. “nima ban sa ni ba”. na amsa mishi a ɗarɗarce saboda yanda yake tambayar cike da tuhuma, cikin kausashshiyar muryarsa yace,”tashi ki ɗauko min”. nai ƙumm na kasa tashi, a tsawace ya ƙara cewa,”nace ki tashi ki ɗauko min ko”. muryana a ƙasa nace,”to ai ka matse ƙafan nawa”. sai a yanzu ma ya tuna da cewar ƙafafuna na tsakanin cinyarsa ne daya maƙalesu, ya ware ƙafar na miƙe kamar munafuka naje na ɗauko, kuma abunda ya ban mamaki ina miƙe masa kallo ɗaya yaywa card ɗin sannan ya ɗago ya dubeni fuska babu annuri yace,”me ya kawo Ahmad wurinki”. sai nai kamna ban gane me yake nufi ba. “wai ba za ki bar min shiru ba idan ina tambayarki”. “to ai kaine da wata negative tambaya, me zai kawo Ya Ahmad ɗakin nan bayan yasan ni matar wani ce”. a harzuƙe cikin tsananin ɓacin rai yace,”zan ɗaukeki da mari wallah, ni za ki rainawa hankali…ƙamshin turarensa da naji shigowata naki ne? ko kuma wannan hand writing ɗin naki ne?…kin faɗa uban me ya kawo shi wurinki ko saina miƙe kinga ainihin tsayina tukunna”. jikina na shaking nace,”wallah ni ban san me yazo yi ba, kawai ya shigo ya aje min wannan ya fita amma Allah ka yards dani ko kallonsa ban ba”. ya galla min wani banzan kallo kamin yasa hannu ya keta card ɗin, sai da yayi gutsi gutsi da shi tukunna yay watsi dasu gefe sai wani irin huci yake. sannan ya miƙe tsaye ya tsaya a tsakiyar kaina yana cewa,”daga yau ko wuta Ahmad ya aje kikai gigin ɗauketa gudun karta ƙona ki Maryam abinda zan miki sai kin ƙwammaci mutuwa ki kai…stupid kawai”. yay maganar kamar zai rufeni da duka sannan ya bar ɗakin fuuuu kawa guguwa. sanda ya fita ina jiyo Yagana na cewa da shi,”Ta faru ta ƙare, da gasken dai lissafin daga ɗakina zai soma…ai shikenan Kabiru kanka kayiwa”. kuma abinda yasa ta faɗa masa haka ganin yana gyara zaman belt ɗin dake jikinsa ne, dan da kamar zai cire belt ɗin ne ya dukeni sai kuma yay saurin ficewa.
na miƙe ƙafafuna a sanyaye na shiga toilet ɗin Yagana na wanko fuskata na dawo na kwanta ko cire kayan jikina banyi ba, kuma bacci yay ƙaura daga idona tunda na kwanta, tunaninsa da tunanin abunda yay min kawai nake, sai ƙwafa nake saki a raina. haka har Yagana ta shigo ɗakin, ina jinta sanda ta kunna fitila ta kashe tana faɗin,”ni Rakiya Allah yasa bai jiwa ƴar mutane ciwo ba…dan yanda naga ya fito fuskar nan kamar hadarin daya haɗe a gabas nasan bata daɗin rai akai ba, ni dai Kabiru bai kyautan ba, dan daya san amana na karɓa ba zai aikata hakan ba”. ta hayo gadon tana taɓa jikina, cikin fushi na bige hannun nata. ta hau surutanta har taga ji kuma ta dawo tana yabona da yabon Ya Kabir, harda kukanta na zata rabu da shi gobe, wai tasan yanda yay auren nan in ya tafi sai ranar da ta ganshi…ina kallonta tana haɗa wasu kayansa da ta ke faɗin ta wanke masa tasa an goge, tana haɗawa kuma tana goge hawaye, duk sai naji ta bani tausayi, na sauko na ɗora kaina saman cinyarta, nan ta shiga yi min kalar nata nasihar da faɗan duk akan zamantakewar aure.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button