NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Qatar, A wannan ranar.

Comment&Share.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

27)
“me muka zo yi anan?”. Abdurrahim ya tambaya a sanda ya waigo baya yana duban Kabir, yaji tambayar tasa amma sai dai bai amsa masa ba, dan ya tattara hankalinsa gaba ɗaya zuwa ga fuskar masarautar dake fuskantarsu, ba komai yake kallo ba illa hoton dake ajikin ƙatuwar fastar da aka manna daga wajen ginin.
ya sani akwai identical twins, amma shi tunda yake a rayuwarsa bai taɓa ganin twins ɗin da sukai tsananin kama da juna ba irinsu, kai ko a labari ma bai taɓa ji ba, duk kamannin da suke dasu dole akwai ta hanyar da ake gane su, amma su waɗannan kamanninsu ya zarce tunanin mutum ko hasashensa, idan har ba sani kayi ba to zaka rantse da Allah mutum ɗaya ne shege editing ya maida shi biyu.
gaba ɗaya ya rasa wacce aciki zai nuna ya kirata da sunan Kulu, to ko dan ba’a kusa da hoton yake sosai bane yake ganin hakan?. ya ɗauke kallonsa daga barin kallon hoton fastar ya dawo da kallonsa ga hoton Kulu dake cikin wayarsa, ya jijjiga kai yana mai ƙara jinjinawa sarautar ubangiji, a sannan kuma hoton Mairo ya haska a cikin idonsa, lallai ne maganar hausawa da suka ce sai kasa aka sannan kake ɗauka, in ba haka ba ai akwai tsananin kama a tsakanin Mairo da Kulu, ana sakata a tsakiyar hoton nan zasu tashi a sahun identical twins su koma identical triplet, banbancinta dasu ɗan kaɗan ne fuskarta tafi tasu siranta sun kuma fita hasken fata, amma daga wannan ba zai iya kawo wani abu da zaice ya banbanta kamanninsu ba.
kunna datar wayarsa yayi ya shiga goggle inda ya tafi kan map yana duban ta yanda zai tsarawa shiga gidan ba tare da tambaye tambaye ba har ya isa ga inda Kulu ke so ya isa, wato turakar mahaifiyarta. yana shafa wayar yana dariya ƙasa ƙasa saboda mitar da Abdurrahim keta zabgawa, shirun da yay masa kuma na ƙara hasala shi harda buɗe motar ma ya fice ya tsaya daga waje, Abdurrahim ɗin faɗi yake,”Kabir inda nasan da wannan walaƙancin naka wallahi da ban biyoka ba, kazo ka shanyamu a waje kamar waɗanda aka sassaƙa, ana tambayarka kuma ka share mutane saboda rashin mutunci”. bakinsa kuma ya ɗauke da maganar a sanda idanunsa suka kai masa kan fastar hoton kyawawan ƴan matan su biyu, kana ganinsu kaga larabawan asali, ga shigar da suka yi ta abaya ta ɗaukesu.
ya murza hannayensa yana me leƙo da kai ta glass yay knocking Kabir ya zuge, “Kabir kaga wasu zuƙa-zuƙan ƴan mata anan, la’ila ha’illallahu ka fito malami ka gani mu san yanda za ai”. Kabir na jinsa yay masa banza bai tanka shi ba, shi kuma bai fasa surutan da yake ba, har tambayar me taxi ɗin daya ɗaukosu yake wai ya bashi shawarar da zai shigar da kansa cikin masarautar ko kuma inda zai sami numbar ɗaya daga cikinsu, shima Babansa na da kuɗi dan haka Al’amarin aurensu ba zaiyi wuya ba, Me taxi ɗin dai murmusawa kawai yay.
Kabir daya jishi yay tsaki da cewar,”ashe dai bani kaɗai ne mahaukacin ba kaima shine”. “Malam ban sa da kai ba, kai sabgarka nayi tawa”. Kabir ya ƙyalƙyale da dariyar da ta ƙular da shi ya ƙara hawa sama da mitarsa.
“yallaɓai akwai tsaro sosai a wannan masarautar, indai ba kana da alaƙa da ita ba to ƙofar wajen ma baka zuwa dan hakan zai iya jefa aka a haɗari…yanzu ma ko da munje daga tsallaken titi zamu tsaya saboda ba’a parking a wajejen”.
maganar mai taxi ɗin daya ɗaukosu daga airpot ta haska masa acikin ka, ehh tabbas kamar yanda ya faɗa akwai tsaro me tsauri ma kuwa…baya jin akwai ta yanda zaiyi ya sami shiga cikinta, saboda haka zai haƙura ne kawai ya koma, tunda in har ba shiga ɗin yay ba, ba zai sami abinda yazo nema ba, kuma idanma zai sami bayanin daya ke so ɗin daga wajen wani to dole sai wanda yake mazaunin cikin masarautar ne.
ya buɗe murfin motar ya fito ya jingina da jikin motar, hannayensa harɗe a ƙirjinsa yake kallon masarautar da tunaninka mabanbanta acikin kansa. fitowar wata farar mota ƙirar BMW daga cikin masarautar ya ɗauki hankalinsa, bin motar yake da ido har sanda ta hau kan titi idonsa ya sauka akan lambar motar da ke ɗauke da rubutun sunan Al-Hassan Bin Hamad Al-Thani da manyan baƙi, ta ke anan maganar Kulu ta gifta acikin kansa. “inaji ajikina Al-Hassan yana tare da ahalina, duk da cewar mahaifinsa ya ƙwace shi daga hannuna, amma nasan ba zai iya ɗaukar nauyin riƙe shi ba, so dole ne ma cikin biyun ɗaya, ko ya salwantar da rayuwarsa ko kuma idan da sauran wannan ɗison imanin dana fara saninsa da shi a zuciyarsa to zai miƙa shi gidanmu, zuciyata na cikin zullumin son sanin a wane irin hali Al-Hassan ke ciki, wallahi bana iya bacci saboda tunaninsa, ka taimaka min Kabiru”. bai san ata yanda zai kwatanta yanda yaji ba da ganin wannan motar, suna kawai ya gani bashi da tabbacin wanda ke cikin motar, dan haka dole ma yay binciken wanda ya wuce acikin motar.
“Driver kabi min bayan waccen motar”. abinda yace da me taxi kenan a sanda suka shigo ciki shida Abdurrahim. Driver faɗi yake,”Yallaɓai ina fatan dai silar hakan ba zaisa na shiga wata matsala ba, domin na lura kai ɗin kamar ɗan bincike ne”. “karka damu babu wata matsala da zata gifta, ni ɗin ba ɗan bincike bane akwai abinda nake nema dai…ka ƙara speed dan Allah karsu ɓace mana”. me motar ya ƙara gudu yana bin bayan motar da irin dabarar da baza’a gane binta yake ba.
kuma motar bata tsaya ba sai a wani ƙaton building dake ɗauke da rubutun Qatar Charity. su kuma tasu motar ta tsaya daga baya, Kabir ya rufe ido yana roƙon Allah akan Allah yasa kar motar tasu ta shiga cikin gidan marayun ba tare daya ga Al-Hassan ɗin da zuciyarsa ke tunanin shine aciki ba, gashi shi ba irin shigar da zata nuna shi ɗin me tsananin buƙatar taimako bane balle yayi amfani da damar hakan a dabarar dake kansa, yasa yatsunsa cikin sumar kansa ya yamutsa gashinsa yana cije leɓensa na ƙasa. kuma kamar ance buɗe idonka, yana buɗewa yaga motar na bakin gate ɗin bata kai ga shiga ciki ba, sai kuma biyu daga cikin security ɗin dake tsaron wajen suka zo suka buɗe murfin motar na ɓarin dama da hagun.
Kabir ya buɗe motar ya fito ya tsaya daga gefe kamar wanda hankalinsa ba’a wurinsu yake ba, ta gefen idonsa yake kallon matar da ta fito daga cikin motar sanye da baƙar abaya, fara ƙal da ita wadda zai iya kira da potocopy ɗin Mairo ta yanda take takun tafiyarta, fuskarta cike da annuri idanunta kuma na ɗauke da gilashin da zai baka tabbacin medical ne. yes! bashi da haufin cewa wannan itace mahaifiyar su Kulu dan ga kamanni nan sun bayyana, ya leƙa cikin motar yana tambayar me taxi, “dan Allah wace ita ɗin?”. ya bashi amsa da,”Yallaɓai wannan itace Sarauniya Asma matar Mai Martaba”. kuma maida dubansa gareta da zaiyi sai yaga wani ɗan saurayi tsaye a kusa da ita tana mishi bayani yana kaɗa kai alamar yana sauraronta, shima fari ne ƙal kyakykyawa, dogo, siriri, gefen idonsa akwai abar da ake kira da tusar jaki, akwai kama ta jini sosai a tsakaninsu, baiyi tambayar da zai sake yiwa me taxi ɗin ba ya sami amsarta daga Umm da sautin muryartata ya sauka a kunnensa tana faɗin,”Al-Hassan”. ta kira sunan ɗan saurayin daya juya zai shiga cikin gidan marayun. anan Kabir ya sami damar ƙare masa kallo, sam basa ma kama da Kulu bama zaka ce ɗanta bane indai ba ka lura da kama ta jini ba, kawai dai a surar jikinsa ne suka yi yanayi da Mairo da idan ka gansu tare zaka iya cewa Yaya da Ƙanwa ne.
yay wani sanyayyan murmushi na nuna jin daɗi, sannan ya lalubo wayarsa daga aljihu ya danna kiran lambar Kulu amma sai dai yana ta kiran bata shiga ba, sai can kuma ta shiga a bugun farko kuwa muryarta ta shiga kunnensa.
“Salamu Alaikum Kabir”.
sai ya lumshe idonsa ya jingina daga jikin motar, ƙarshen aikinsa yazo, haka kuma ƙarshen komai yazo.
ya amsa sallamartata,”wa alaiki salamu da Aaliyah, barkanki da wannan lokaci”. batayi mamaki ba domin tasan dole ayanzu zai san asalin sunanta in har yay binciken da tasa shi, saboda haka ta amsa masa da,”wane tarihi ka samu ga me da wannan sunan?”. har yanzu wannan murmushin na jin daɗi bai bar fuskarsa ba yace, “duk wani bayani ki bari ba yanzu ba sai zuwa anjima…yanzu dai babban albishir zan miki”.
cike da zumuɗi me ɗauke da fargaba tace, “Allah yasa albishir ɗin da zai yaye min wani kaso na cikin damuwata ne, ina sauraronka ɗan halak”. Ya shafi goshinsa a sanda yake cewa,”gani a kusa da Umm da Al-Hassan”. sunayen daya ambata suka daki zuciyarta bugunta ya sauya,”Kabir kasan waɗannan sunayen a bakina, saboda haka karka yi wasa dani dan wanzar min da farincikin da ba zai ɗore ba”. “wallahi da gaske nake miki, tsakanina da Al-Hassan ma bamu da tazara, gashi nan ya girma ya zama saurayi kamar yanda Maryam ɗita ta zama budurwa”. a ɗan shiru data yi zai iya rantsewa hawayen farin ciki take, kuma bakinta yaƙi rufuwa saboda farincikin daya lulluɓeta, ya katse wannan shirun nata da tambayar,”amma ko kusa ko alama babu kamanninki a tare da shi, banda kamanni ta jini da kuma kasancewarsa tare da Umm da zan rantse nace ba shine Al-Hassan ɗinki ba”. ta bashi a amsa da,”ai shi kamar mahaifinsa yayi tun a ranar farko daya zo duniya…Kabir ina so na dawo cikin ahalina sai dai ban san ya zanyi ba, ubansu ya zama silar tarwatsewar duk wani farinciki nawa”. ya sauke numfashi yana faɗin,”karki damu in Allah yarda komai zai warware acikin sauƙi”.
ta amsa da,”Allah ya yarda”. sannan ta kuma ce masa,”to baka sami labarin Hussainar ba?”. yace da ita, “yanzu tunda na gama da nan da zarar na sauka a Ethiopia wurinta zan fara sauka, itama zan gano miki ita da lafiyarta, karki damu”. ta sauke numfashi sannan tace,”to baka ce min komai ga me da Abi”. “nace miki saina tattara dukkan bayanan komai sannan zan sanar miki, nan Qatar dai na gama da ita, Hussainarki ce kawai tayi saura acan ethiopian ma”. kamar tana gabansa a lokacin ta gyaɗa masa kai, “to shikenan na gode Kabir”. ta tari numfashinsa akan maganar da zaiyi da faɗin,”ina ɗaga wayarka kenan Malam ya aiki su Hussaina, sai dai idan ta dawo zuwa anjima zan kiraka”.a sannan wani annuri na fuskarsa ya ƙaru yace da ita,”tom sai na jiki…amma nan da 3hours dai ina jirgi”. daga haka kuma suka yi sallama.
ya koma mota drivern yaja su zuwa airport, a duniyar tunaninsa ta yau gaba ɗaya cike take da tausayin Kulu, in banda ƙaddara me tsanani me zai baro Kulu daga cikin daularsu ta koma rayuwar ɗan akurkin gidansu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button