NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

shikenan komai yazo ƙarshe, sirrikan sun bayyana, komai ya warware, sabuwar rayuwa ta fara…
Bayan Wani Lokaci, Qatar, Turakar Mai Martaba.
Almustapha da Imam(Joseph) tare da Ibrahmin(Obi) suka shigo cikin turakar. suka ƙarasa har gaban Mai Martaba inda suka zube a ƙasa gaba ɗayansu suka kwashi gaisuwa, Mai Martaba ya amsa tare da sanya masu albarka, da kuma ƙarayi musu adu’ar tabbatuwa acikin musuluncin da suka karɓa a kwanakin baya da suka shuɗe, a wancan ranar da Almustapha da Major suka je asibiti, bayan dawowarsu gida ne an gama bikin mutuwar Madam Gloria da Madam Merry, Almustapha yazo har kano ya ɗauki Malam da Malam Liman suka je can abuja, suka riske Major inda Malam Liman yay masa wa’azi me ratsa jiki, kuma da yake yana da rabo, a washe gari ya kwashi ƴaƴansa da jagorancin Malam Liman suka zo har nan Qatar ya karɓi musulunci daga hannun Sarki Shaik Tamim bin Hamad wato sarkin Qatar mahaifi a wurin su Aaliya.
yanzu haka Major yaje ƙasa mai tsarki inda ya fara ɗaukan darasi na ilimin addini a wajen Shaik Mufti Mahek, sai muyi musu fatan Allah yasa rabon ya kaisu har aljannah.
Hirar da Mai Martaba keyi tasa ce shi da Almustapha, sai Ibrahim dake sako baki jefi-jefi, kuma suna tattaunawa ne musamman akan wata ma’aikata da Mai Martaba yake son mallakawa Alhassan ita, yake so Almustapha ya shige masa gaba a harkar, tunda shi Alhassan ƙaramin yaro ne, har yanzu da sauransa, duk da cewa idan ka ganshi ba zaka ce masa mai shekara goma sha bakwai ba, zaka ce ya bawa shekaru ashirin baya, kuma yaron akwai hankali dan halinsa ma na manya ne, zai iya yin abinda ba ma lallai wani babban yayi ba.
gaba ɗaya cikinmu babu wanda yasan da musuluntar Daddy da sauran ƴan’uwana, sai bayan da aka sallami Ya Kabiru daga asibiti, ranar da Mami da Ummi suka dawo Qatar, a wayar da suka yo ne suke shaida mana da duk abinda ya faru, daga baya kuma Alhassan ke tsugunta min zaman sulhun da Abi yaywa Mami da Daddy, sai dai ko kusa Mami tace ita dai abinda ake tunanin zai faru tsakaninsu ba zai taɓa yiwuwa ba. damuwa ta haska ƙarara a saman fuskata na buɗa baki nace da shi,”amma kai mene view ɗinka a akan hukuncin Mami na ƙin amincewa auren Daddy?, ni dai gaskiya zanso ace ta haƙura sunyi aurensu, ko dan Allah ya ƙara rufa mana asiri”.
da yake Alhassan A ne, ya saki wata siririyar dariya kamin yace,”ke ki kwantar da hankalinki, batun cewan ma Mami bata son auren Daddy daga baya ne, dan ba kya wurinne, amma da tsab idonki zai hango miki kwantacciyar soyayya a idanun junansu”. ban san lokacin da na saki dariya ba, har ina kifawa akan kafaɗar Yagana dake kusa da ni, nace da shi,”kai dai baka da kunya, iyayenka ma baka bari ba”.
dariyar yake shima yace,”hmm to ai bari kiji na baki labari, ni dai ɗansu nasa musu ido, dan ranar da Daddy zai tafi saudia ina kallonsa da yamma ya tarfa Mami yana lallashinta, na faɗa miki ya koma kaman ƙaramin yaro fa a gabanta, ita kuma sai wani yauƙi ta ke tana cewa wai ita saita rama wahalar da rayuwarta da yay, ke baki kalla a yanda ta ke maganar ba sak ke idan kina shagwaɓa, ni kuwa na riƙe haɓa nace ikon Allah, ni da Ummi da Akhy Almustapha muna gefe muna musu dariya”. a wannan karan dariyar da nai har da dukan Yagana, ba kuma wai ina sa ni ba, amma ƴar tahalikar nan sai ji nai ta ɗale min gadon baya babu shiri na miƙe daga kusa da ita.
still ban bar dariyar ba nace,”ina jinka ci gaba da bani ina sha”. yace,”gulmawuya to naƙi na ƙarasa”. “ah yi haƙuri Yayana na kaina”. a wannan lokacin murmushi yay mai sauti, yaci gaba da bani labari cikin nishaɗin da muke ciki.
“baki san me ba, da naga Mami na neman wahalar min da gyatumi ta sa shi kuka sai naje na kutsa a tsakaninsu, ke baki kalla wani abin dariya ba lokacin da suka ganni, ba sai ga Daddy na susar ƙeya ba wai naje na ɗauko clipper nayi masa aski ance masa na iya aski ni ke yiwa Abi ma, ni kuwa nace masa ai Mami ce uwar ɗakina, ita ta koya min dan haka idan da gaske me kyau yake so to su sulhunta kansu a daren nan gobe a ɗaura musu aure, a tare suka sakar min ranƙwashi fa, Mami harda murɗe min kunne saboda nace idan ba tsayuwar sulhu suke ba to a faɗa min gaskiya…ina faɗa maki ma Abi yace da Daddy ya dawo daga umara za’a ɗaura aurensu, ita kuma Mami tace bata yarda ba, ya za’ai sai da za’ai bikin ƴarta kuma ayi nata, Ammi kam tace to ki zauna idan anyi na ƴar taki ta sami ciki ta haihu ayi naki…ni dai ina cin dariyar drama, Malam ki baro wannan ƙauyen kawai kizo a dinƙa yi a gabanki ba kike kirana ina baki labari ba kuma ba kya biyana ko sisi”.
na kai hannu na goge ƙwallar dake neman sauko min kamin nace, “ka faɗawa Mami ramuwar gayya da ɗaukan fansa aiki ne na yahudu da nasara, saboda haka basu dace ɗan musulmi ba ko kaɗan, manzon Allah da kansa yace kada muyi koyi da su. saboda haka ina roƙonta da tayi haƙuri ta yafewa Daddy nah…ai abinda ya faru a tsakanin rayuwarsu zuwa rayuwar Alhassan da Maryam ɗin da suka haifa wannan tsananin rabo ne da ƙaddara, ƙaddarar da babu wanda ya isa ya kauce ma ta, amma dan Allah tai masa afuwa kar mu zama marayun ƙarfi da yaji”.
yay nisa sannan yace,”ke me zai hana ki kirata ki faɗa ma ta”. “Alhassan ni ban san me nai ma ta ba, tunda kuka koma bama wani long conversation da ita, kana kallo ma ai tun kamin ku tafi muka koma kamar wasu sirikai, duk yanda naso na keɓe da ita na ma ta magana bata bani dama”. “kunfi kusa, ni da Ummina ido ne namu”. ya faɗa, kuma kamin nace wani abu ya kuma cewa,”Ya sauƙin jikin Ya Kabir ɗin?”. na sauke wata doguwar ajiyar zuciya sannan nace,”da sauƙi, kawai dai har yanzu baya taka ɗaya ƙafarsa…shima yace na fita a sabgarsa babu ruwana da lamarinsa, jiya ma saura kaɗan ya mareni shi yasa nace insha’Allahu indai sunana Maryam tsakanina da shi ido”.
kuma da haka muka ɗauki hirar makarantar da Mami ke nema min addimission acan Qatar ɗin, dan sati biyu kenan da zan aprivate waec ɗin da ta biya min, tace wai idan nayi girma da yawa a secondry, kuma tunda ina da ƙoƙari sosai ƙwaƙwalwata naja to kawai da waec ɗin nafi dacewa…ni kam sam idan muna waya da ɗan’uwana kamar kar mu rabu nake ji, shi yasa duk na ƙagu Ummi ta dawo dag tafiyar da tai muma mu wuce Qatar din, dan Allah ya sa ni ina kewan kasancewa kusa da Mamina sosai.

03:00am.
“Yaya dan Allah ki saya min wannan takalmin”. Basma dake shigowa cikin ɗakina da nake kwance ta faɗa tun bata ƙaraso inda nake ba. na ɗago ido na dubeta ina kallon ikon Allah, ita dai kullum na siya ma ta na siya ma ta, ta maidani kamar wata asusun bankinta, gashi ni kuma ina bala’in son ƙanwata tilo ɗayan da Gwaggona ta tafi ta bar min. a yanzuma da ta ke shigowan kamanninta suka riƙiɗe suka koma min na Gwaggona, ban san lokacin da idona ya cika da ruwan hawaye ba, da kanta da ta lura da hakan tasa hannu ta goge min.
“Yaya za ki saya min ɗin?”. ta ƙara tambaya ta marairaicewa, nai ma ta shiru ina ci gaba da danna sabuwar wayar Mami dana karɓe ranar da zasu tafi. wadda babu komai acikinta sai tarin hotunanta, kuma su suka zame min abin kallo a kowanne lokaci da nake tare da wayar, ko ma bana tare da ita hoton surar Mamina baya barin haskawa a idona.
“shikenan tunda ba za ki saya min ba na fasa shiryaku ke da Ya Kabir”. ta faɗa tana ƙoƙarin sauka daga kan gadon ta fita, nai saurin kamota ina cewa,”haba mana my little Sis, kin kalla na taɓa ƙin saya miki abu?, Allah kam zan saya maki yi haƙuri kinji”.
sai ta noƙe ta juya min kai da cewan,”ni dai na fasa shiryaku, takalminma na fasa bana so”. sai kawai na marairaice ma ta ina cewa,”haba lil sis, Gwaggo fa tace mu zama masu kula da junanmu”. sai tai murmushi tana ce min, “to kije ki bashi abincinsa, na kalla yana jin yunwa kuma ya kasa ɗaga hannun”. maganarta tasa na zuro ƙafata ƙasa babu shiri nai waje, ina fitowa parlo na tarar da Ya Amadu da Yagana sai abokansu da suka zo yiwa Ya Kabiru sannu, na tsuguna na gaishesu sannan nai hanyar fita, kuma na sauka daga kan steps ɗin entrance ɗin parlonmu kenan sai naji Ya Amadu ya kirani.
kuma ko da na juyo sai na kalla kaman idonsa ba’a kaina yake ba, kiranma kaman ba shi yay ba, kawai sai na tsaya ina kallonsa, ya juyar da ƙwayar idonsa zuwa gefe tare da kasa tantance abinda yake kallo a wurin.
bata san ta ƙasan ido yake kallonta ba, gba ɗaya ya kasa tantancewa, bai sani ba kyau ta ƙarayi ko kuma akasin haka, idanuwansa na kalle masa ne kullum kamar ana sauya halittarta, abu guda ya sani shine kowanne lokaci tana canjawa, a kowanne sakan ya ɗora idonsa sai yaga ta sauya kamar wahainiya.
a yau da tai shigar english wears ɗin daya taho ma ta da su daga lagos, tabbas idan a hanya ne ya ganta zata wuce ya wuce ne ba tare daya shaidata ba, ya motsa leɓensa da murmushin da bata gane ba.
“Ya Ahmad”. na kira sunansa ba da irin wancan sunan ƙauyen dana saba kira ba, dan Ummi ta hanani, tace yanzu mu ƴan gayu ne, dan haka duka sunan ƴan gidan ya sauya a bakina daga ganda nake faɗarsu ada.
a tsakiyar fuskata ya sauke idonsa, yana ƙanƙance shi saboda hasken ranar dake dallare masa ido. “Ya kamar naji kayi kirana”. “ehh aiki zan sa ki ciki, kizo ki dafawa baƙin nan indomie, dukansu basa cin alala.”
“Ya Ahmad ai Nawwara(ƴar aikinmu) na ɗakinta, dan Allah ka kirata…ni zanje Ya Kabir na kirana ne”. wucewar daƙiƙa kamin ya gyaɗa min kansa, sannan na wuce na tafi zuwa part ɗin Ya Kabir, kuma ina shiga na tarar yana ƙoƙarin yanda zaiyi ya ɗauko spoon cikin ƙarfin hali, dan haka na ƙarasa gare shi da sauri, ba tare dana bari ya bani dama ba na tsaida hannunsa, sannan na matso da plate ɗin abincin da Basma tace min ta zuba masa, na kuma shiga ba shi abincin yana karɓa bisa dole, kuma cikin ɓacin rai dan ga hakan nan ya haska a fuskarsa.
abinda bata sa ni ba shine, ƙara maimitawa zuciyarsa yake cewar babu wani abu da zaiso a rayuwarsa ya kasa sadaukarwa da ɗan’uwansa, ƙanensa Ahmad, ko menene shi, kuma duk girman abin nan, sai dai idan Ahmad ɗinne da bakinsa ya furta masa cewar baya so ɗin ya haƙura.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button