NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Manage Please.

Please Comment, Share&Vote.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

(40)
“ke kuma Yagana gaki da kambaba zance”. tai lakato tana duban Ahmad da yay zancen kamin tace. “dama tunda ba Zulai akaiwa sharrin ba ai ba zai dameka ba, ni kuwa da nake abar banza da wofi a wurinka Amadu ina nake da darajar da zaka ɗaukar min mataki…to ko ba komai ka tuna ni na haifi Adamu kuma na shayar da shi”. tai hanyar kitching tana ci gaba da faɗin,”ni dai na faɗa maka karka dawo min da wannan abar, dan ba zan iya zama da masharranciya acikin gida ba, Allah yaso ba wani nake aure ba da yau tasa an damƙa min farar takarda”. daidai fitowata daga ɗaki nace,”wai ni Yagana da kike ta faman wannan sababin sharrin me na miki ne?”. maimakon ta ban amsa sai ta juyo ta banka min harara sannan ta ƙwalawa Nawwara kira tace tazo ta rufe ma ta ƙofarta idan mun fita.
kuma har kitchen na bita ina ce mata bata yi min adu’an fita ba tai min shiru kamar wadda ke magana da kurma, sai da zan fita ne tace,”wanda yafi ƙarfinka ai yafi ƙarfin adu’arka”. siriryar dariya kawai nai kamin nasa kai na fice ina jin ƙara son Yagana a raina, da roƙon Allah ya daɗa ja min da ranta.
“jiya naji wancan abin yana cewa tuwon dawa yake sonci, je ki tambayi Zulai idan ta sami dawar ta bani, in ba’a samu ba kuma na kira ubansa ya taho da ita”. Yagana dake wanke nama tana tsiyaye ruwan acikin sink ta faɗa. Nawwara tace,”Yagana wane waccan abin?”. cikin ƙufula Yagana tace,”Ubana da waccan abar ta kai ƙarata wurinsa mana”. Nawwara ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa,”Hajiya Yagana ikon Allah, yau kuma Ya Kabir ɗinne wancan abin”. Yagana ta wurga ma ta mugun kallo da faɗin,”kin wuce kinje min aiken ko sai kin gama ɗaukar maganar taki”. Nawwara ta fito a kitchen ɗin still da dariya a saman face ɗinta, kuma tana jin Yagana na faɗin,”ƴan aiki da yawa suke a ƙauyen nan, dan haka zan koreki na nemi wata tunda naga kema kin fara shigar min hanci”.
Yagana ta idar da sallar la’asar Adawiyya tai sallama cikin ɗakinta, ko da Yagana ta ganta sai ta ɗauki lazimin da batai niyya ba, shiru shiru sama da minti ashirin bata katse ba, kuma dama taja musu kunne kar wanda ya ƙara zuwa ya ganta tana lazimi ya dameta da magana, shi yasa ko da Adawiyyan ta shigo sai ta nemi waje ta zauna zaman jiran idarwarta. Yagana kuma na sane taƙi sallamewar, sai can tai gyaran murya ta kalli Adawiyya da cewa,”irin haka sai ki haƙura kije kya dawo, ba wai ki tasani a gaba ba kamar wadda tazo ɗaukar fansar bashin dana ci ma ta na hana.” “ai naga dole za ki idar ne ba kwana za kiyi a hakan ba shi yasa na kafa na tsare ina jiran sallamewarki”. “au toh, da wacce tsiyar kika zo?.” “tsiyar arziƙi”. “to ina sauraronki, mene dama?.” Adawiyya ta sauko daga bakin drower ɗin da ta zauna ta dawo kusa da Yagana ta zauna, sannan tai ƙasa da murya ta fara magana. “Yagana dan Allah dama akan maganar Ya Suhail ne. na rasa yanda zanyi da shi a zuciyata, duk da cewar na nemi yafiyar Mairo kuma ta yafe min amma wallahi ina mugun jin kunyarta, Yagana dan Allah ki taimaka min ki shige min gaba”. ta faɗa tana kama hannun Yagana ta riƙe acikin nata. “to inace shima Suhail ai kun nemi yafiyarsa ɗin kuma yace ya yafe muku ko, to mene kuma ya dami zuciyarki da shi?”. Adawiyya ta karayar da kai tare da sake matsowa kusa da Yagana tace,”Yagana ki gane mana, har yanzu ina sonsa fa…”. bata ƙarasa ba Yagana ta katseta,”kai amma dai duk inda ɗan iska yake yafita daban, yanzu ke Adawiyya saboda babu tsoron Allah babu kunya a ranki shine kike maganar Suhail…to yanzu ni ko shegiya ce Adawiyya ai bana shige miki gaba ba akan wannan zancen sai dai na shige miki baya, to bada ni ba gaɗa a kabari, ni rashin hankalina bai kai intaha ba, kuma wallahi bari kiji yau ko Suhail ne yazo da batun aurenki gidan nan sai na shiga na fita al’amarin ya tarwatse, sai dai nima ku biyo min ta ƙarƙashin ƙasar amma wallahi ba zan bari wannan mai farar zuciyar ya auri macen da ta cutar da shi ba.”
ta ke ruwan hawaye ya cika idon Adawiyya tace,”haba Yagana karki manta fa ni wace ɗinki, kuma abunda ya faru ya rigada ya faru sai dai a kiyaye gaba, nayi nadamar abinda na aikata kuma har yanzu dana sa ni nake…duk da cewar sun yafe mana amma wallahi har yanzu zuciyata ta kasa samun natsuwa, tabbas yanzu na yarda cewan duk wanda yay ƙudurin hana wani bacci to shine zai kwana bai bacci ba, dan Allah ki taimaka min, wallahi da tsarkakkar zuciya nake sonsa tun farko…kuma na rantse miki da Allah yanzu zuciyata fess ta ke akan kowa, Allah ya shiryeni ya ganar dani”.
“to Allah yasa anyi taubatun nasuha, amma wancan zancen naki kam tun muna ta daɗi dake ki barni da shi, ki nemi wani acikin manemanki kawai.”
Adawiyya tai shiru tana hawaye, Yagana ta miƙe ta fita ta barta a wurin bata kuma tanka ma ta ba.
a ɗaki ta sami Kabir zaune yana kallo shi da Aminu, ta kalleshi tana aikin taɓe baki for a while kamin ta juya ga Aminu ta amsa gaisuwarsa da cewar. “kai kuma yaushe kazo gidan?.” “tun ɗazu na shigo Yagana.” sai ta ƙara gwame baki tace,”yayi kyau, lokacin da Hajara ta rasu ta bar Yaranta ababen tausayi kishiyarta bugar ƙirji tai tace babu ɗan da zata riƙe, sai ni Rakiya ce na raini Kabiru da Aminu da ƙarfina da jinina, yo a rayuwa kuwa ai bana zama abar a wulaƙanta ba tunda ance wanda yay maka alkhairi karka manta da shi…amma da yake Aminu kai ɗan halak ne har ka iya shigowa cikin gidan nan baka fara zuwa ka gaishe da ni ba, kai ai ga me ɗan’uwa tunda ba Uwarka a gidan ba wurin wanda zaka, wato da banzo nan ɗin ba ma ba zamu sami ganawa ba.”
Aminu ya girgiza kai da cewar,”Yagana ni ɗin banzana in shigo gidan nan banje wurinki ba, wannan ma ai zance ne.” tace,”haka ne, to ya wurin su Zannirar?.”

if i could remember tun muna page 20 something na fara maku kawaici akan rashin wadataccen comment daga gareku, amma kuka kasa sauyawa har zuwa yanzu da muka zo gaɓar da muke page 40, so wannan dalilinne yasa na sauya shawarar inda zanke yin posting daga yanzu har zuwa time ɗin da zamu kammala novel ɗin nan…waɗanda suke Wattpad ku neme ni a wattpad handle ena Oum_Ramadhan, wanda kuma basu da wattpad kuna iya zuwa kusha karatunku a website ena globalnews.com.ng, ko kuma a arewabooks, amma idan kuka je okada ana kuɗi zaku same shi but the rest of the handles duka free yake…amma whatsapp kam dai na bar tura maku update.

website????:- https://globalnews.com.ng/2022/01/10/sirrin-%c9%93oye-page-40-hausa-novel/
wattpad????:- https://www.wattpad.com/story/285058837?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_reading&wp_page=reading_part_end&wp_uname=Oum_Ramadhan&wp_originator=GkxVt8VQgcSiEHeCfcEYx0PMM1kJSZh1Oblc16%2FzlTZnFl9PCXi2qgnCNgxowh75vsHgS0uWdk6eWCYvnD4zCwTRX0Fu5tOIplreNO8pb9gvDXKR4zRs07qApBIAZbWa

Plss vote,share&comment.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

Continuetion of page 40…

Aminu ya girgiza kai da cewar,”Yagana ni ɗin banzana in shigo gidan nan banje wurinki ba, wannan ma ai zance ne.” tace,”haka ne, to ya wurin su Zannirar?.” “suna lafiya.” “to ka gaidasu idan kaje, ranar nan ai dana shiga wajejen naku na biya ta wurinta gidan a rufe, sai maƙwabciyarku ke ce min taje asibiti, to Allah ya raba lafiya”. ya amsa da,”amin Yagana”. Nawwara ta shigo parlon hannunta riƙe da kwandon abinci, Yagana tai ma ta nuni da inda zata ajiye, bayan ta aje ta gaida Aminu sannan ta gaida Kabiru tare da yi masa sannu da jiki, ya amsa ma ta yana bin bayanta da kallo har ta fice daga ɗakin. daga inda ya jiyo ƙwafar Yagana ya karkatar da kai kaɗan ya dubeta yanda ba zata gane ba, yana kallon yanda ta ke aikin jijjiga kai sai kawai ya motsala leɓensa yaci gaba da sauraron labarai.
sai da Yagana da Aminu suka gama hira sannan ta dawo kansa da cewar,”Baba kayi haƙuri ni bana gaba, ƴarka ce dai insha’Allahu ba zan kuma taɓa maka ba, dan haka ka sauka daga wannan dokin zuciyar ina mai bada haƙuri…ina yini, ya sauƙin jiki”. ya gimtse dariyar dake neman kubce masa. “Baba magana nake, kayi haƙuri dan Allah, a wannan halin da kake ciki ba zan iya ɗaukar shariyarka ba…kuma na maka alƙawarin Ƴarka Mairo ba zan ƙara takura ma ta balle har ta kuma ƙala min sharri akan abinda banji ba ban gani ba”. tana yin shiru yace,”Yagana dan Allah Maryam ba Mairo ba”. tace,”to Baba naji na ɗauka…yanzu dai ka haƙura ɗin ko?”. ya kalleta yace,”na haƙura tsohuwa”. “yauwa Baba Kabiru Allah ƙara maka haƙuri. ban sami leƙowa ba tun safe, sai nace Zulai tazo tai maka gashin ai anyi ko?”. “ehh anyi, yau ina jin daɗin jikin sosai…Ahmad ma nake jira ya dawo mu ɗan zagaya”.
“ehh ai da yake ya fita kai Ƴar taka yawon shaƙatawa, amma nasan duk inda suke suna kan hanya, Allah dai ya ƙara lafiya…ga tuwan dawar nan nayi maka lafiyayye, har man shanu nasa Mujibu ya aiko min, kaci sosai kaji ɗan albarka, bana son wannan rashin cin naka”. “zanci Yagana bari ayi sallar magriba tukunna…tun yaushe suka fita?”. yay tambayar yana jin wani abu na tokare masa ƙirji. “ah tun ga kamin azahar suka fita”. sai ta karkata ga Aminu tace, “Aminu ai yau Allah ne yay da sauran kwanana a gidan nan”. daga Aminun har Kabiru sai suka waro ido waje suna dubanta da son jin sauran bayani. Aminu yace,”Yagana me ya faru?, ba dai matsalar gas ɗin bace kumawa?”.
tace,”a’a wannan matsalar ai tafi ta gas.
to kaga ina zaune ina kallon tashar saudiya sai ga Alhaji Amadu yazo kaina yay zandardar kamar sandar ba’are, fuskar nan a murtuke ya hauni da masifa kace Allah ya jiƙan rai Baba Manniru, wai dan me zan hana akai su waccan abar Shufin, na daina yi masa irin haka baya jin daɗin, ai ko babu komai arziƙinta ake ci a gidan nan…wallahi saboda ban san zancen ba sai na riƙe baki ina dubansa, yace min ai ƴar da nake riƙo ne ta kai ƙarata wurin Baba Kabiru to su basa son haka na daina…maganin a zauna lafiya saina basu haƙuri, amma ai akwai Allah, gidan wani zata je idan sharri abinyi ne taci gaba ba”.
Aminu yace,”Allah sarki, haƙuri zaki amma ɗan riƙo yana da wuyar sha’ani”. “ka bari kai dai yau ai nai dana sa ni, ni tsorona ma maganar taje kunnen Uwarta ko Ubanta, dukansu kasan zuciyarsu a wuya ta ke yanzu sa saka a far min”.
Kabiru ya katse mitar da cewar ta miƙo masa abincin yaci, kuma ta ɗauko sai ga Zubaida ta shiga tana sanar ma ta tayi baƙuwa, nan ta tashi ta fita.
“ke ki kira min Nawwara”. Kabir yace da Zubaida. sai bayan ya idar da sallar magriba ne Nawwara ta shigo ɗakin, lokacin Aminu ya har ya tafi, ta sa me shi yana kaiwa da komowa daga bango zuwa bango, yana taka ƙafa ɗaya da ƙyar. ta cikin madubin dake kafe a bangon ɗakin da yake fuskanta yake hangota ta bayansa, tun lokacin da ta shigo ta tsaya har sanda ta ke ce masa gata, amma kuma bai amsa ma ta ba kuma bai juyo ba yana dai ta kallonta ta cikin madubin da irin kallon daya kasa fassara ma’anarsa a tare da shi.
maganar da ta ƙarayi ne yasa ya haɗiye wani guntun yawu a maƙogoronsa sannan ya juyo yana fuskantarta, sannan yay tattaki ya ƙarasa zuwa inda ta ke, inda tazarar dake tsakaninsu bata wuce inci huɗu ba. “Maryam fa?”. har yanzu kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace,”Ya basu dawo ba har yanzu”. sai kawai ya rumtse idonsa gam tare da ɗaga kansa sama yana jin wani abu me zafi na tsargawa ajikinsa. wucewar daƙiƙa biyu sannan yace da ita,”zuba min abinci”. yana faɗa ya koma ya zauna kan kujera, ita kuma ta ɗauki plate ta zuba abincin kaman yanda yace sannan ta kawo ta ɗora akan table ɗin dake gabansa. “Yaya shikenan?”. yay shiru baice ma ta komai ba, itama kuma bata miƙe daga duƙen da ta ke ba, ya ɗauki spoon ya fara kai lomar ruwan bakinsa, duk zumuɗinsa na son yaci tuwon memakon yaji daɗinsa sai yaji wani ɗaci ya ziyarci saman harshensa, dan haka yay saurin maida spoon ɗin ya ajiye ya sauke ƙwayar idonsa biyu a tsakiyar kan Nawwara. “wa ya dafa abincin nan?”. ta ɗago ta dubi yanda yake yatsine fuska kamin tace,”Yagana ce, wani abu kaji aciki?”. “ɗaci naji, may be ta haɗa da wani abun bata sa ni ba”. “aiko sai dai idan daga bakinka ne, tunda har baƙi ma sunci kuma basu yi ƙorafi ba”. “ci mu gani”. ya faɗa yana mai ma ta nuni da plate ɗin da idonsa. “Yaya bakinka ne kam, ni banji komai ba”. ta faɗa bayan tayi spoon ɗaya. hannunta taji ya kamo wanda yasa tai saurin ɗora ƙwayar idonta akan babban yatsansa dake shafa kan fatarta, kuma kamin ta kai ga haɗiye yawun dake maƙogoronta taji yace,”wannan ƙonuwar fa?”. “jiya ne manja ya zubo min”. “kuma shine ba’ai treating ɗinta ba”. a shirun da tai kawai ya fahimci bata gane me yake nufi da treating ba, dan haka ya ɗaga ma ta gira,”ina nufin me yasa ba kuje chemist ba”. “ai naga kaɗan ne bada yawa ba, kuma ma Anty Maryam ta min tofi a wurin”. ya saki hannun nata yana jinginar da kansa jikin kujera sannan yace,”shiga bedroom ena wajen gado ki ɗauko box ɗin first-aid”. ta inda tasan first-aid box ranar da Maryam taji ciwo Ahmad ya naɗe ma ta hannun da bandage, dan haka ko da ta shiga ɗakin bata jima ba ta fito ta kawo masa. “zo ki cire min wannan”. yace da ita yana ma ta nuni da zaren da aka naɗo hannunsa zuwa wuyansa, ta miƙe ta cire sannan ya miƙar da hannun nasa a hankali cikin ƙarfin hali da dauriya sai rumtse ido yake saboda zafi. ya matsa ma ta gefensa yace ta zauna, ta zauna a ɗarɗarce saboda wani baƙon al’amari da ta ke jin kanta aciki, kuma har ya fasa ƙunar ya shafa magani ya naɗe ma ta wurin bata sa ni ba, sai da yay magana tukunna tai firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta faɗo a lokaci ƙanƙane, kuma sai a sannan ta ke jin zafin ciwo.
“ki shirya gobe za ki fara zuwa school, da safe Mu’azzam zai kai sai kiyi ƙoƙarin kammala ayyukanki da wuri”. bata san lokacin da ta silalo daga kan kujerar ba ta zube gwiwoyinta biyu a ƙasa ta shiga yi masa godiya babu ƙaƙƙautawa har sai daya dakatar da ita, tukunna ta miƙe ta bar ɗakin cike da farin cikin da ta ke jin tamkar an ma ta albishir da gidan Aljannah, Allah ya sani ita ma’abociyar son karatun boko ce amma iyayenta basu da halin da zasu kaita boko, domin a samu a sakata a makatantar boko zuwanta aikatau na daga cikin dalilin amincewar mahaifinta, kuma gashi yau Allah ya cika ma ta burinta tun ba ai nisa ba, dan haka har mutuwarta ba zata fasa saka Ya Kabiru acikin adu’arta ba kuma ba zata taɓa mantawa da shi ba.
tun bayan fitarta yake jinsa wani iri, gashi natsuwar da yake neman yasamu ta gagara, ya ɗauki waya yafi sau goma zai kira Ahmad amma sai ya mayar ya ajiye ya fasa kiran, dan haka domin ya sami sauƙin abinda yake yaji ya ɗingiso ya fito dan shaƙar iskar waje, kuma yana fitowa harabar gidan ya tarar da Mu’azzam da Lukman suna shigowa gidan, ya buƙaci dasu zauna anan kan kujerar dake compound ɗin suyi hira ko ya samu ya ɗebe kewa. kuma da suka zauna hirar tasu duk akan kasuwancinsu ne, inda yake daɗa basu shawarwari akan harkar business. hirar suke amma gaba ɗaya hankalinsa ba’a kansu yake ba yana bakin gate, yana jiran shigowar motar Ahmad amma shiru shiru gashi har ƙarfe takwas da rabi saura.
ya buɗe baki zaice da Lukman ya kira shi a waya kenan sai ga horn ɗin motar, kuma har motar ta shigo ta faka bai sami natsuwa sai daya ga Basma ta fito daga motar, tukunna ya haɗe murfin idonsa ya rufe yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya. ta cikin hoton abinda ke haskawa acikin duhun idonsa yaji Basma a kusa da shi tana kamo hannunsa da faɗin,”Ya Kabir yau kaji sauƙi ka fito?”. ya buɗe idonsa ya sauke akanta da murmushin da a kallo ɗaya zaka gane da wani ɓoyayyan abu a tattare da shi. “na sami lafiya Basma…ya akai kuka daɗe?”. “Yaya ce bata da lafiya muka wuce asibiti”. da mamaki yake dubanta da tambayarta,”rashin lafiya kuma? ina ce lafiya ƙalau kuka fita?”. “ehh Yaya ai ko acan ma sai a hanyarmu ta dawowa ne ƙirjinta ya fara ciwo, kuma da muka je asibiti likita yace asthma ce”. “what?”. yay tambayar muryarsa na amayar da tashin hankalin acikinta. kuma kafin Basma ta kuma cewa wani abu sai ga Ahmad yazo ya wuce da Maryam ya ɗaukota a hannunsa.
da lokacin da yay azamar miƙewa tsaye zuwa sanda ya faɗa part ɗin Yagana har yay tsaye a bakin gadon da Maryam ke kwance duk bai sa ni ba. kuma tunda yay tsaye a bakin gadon kallon fuskarta yake da wani abu dake tsargawa ajikinsa from head to toe. bacci ta ke peacefully, sai numfashinta dake up and down da sauri sauri, yana kallon laɓɓan Ahmad dake yiwa Yagana bayanin abinda ya faru amma baya jin maganar da yake acikin kansa, da ƙarfi kuma ya cije leɓensa na ƙasa ganin yanda hannun Ahmad ɗin ke cikin nata yana murza ma ta tafin hannu a hankali. sai ya rumtse idonsa da ƙarfin gaske ba tare da sanin lokacin daya ɗauko wayarsa daga aljihu ba ya dannawa Abdurrahim kira ba, kuma bugu 1,2,3 ya ɗaga. daga can ɓangaren Abdurrahim ya shiga yi masa tsiya yay saurin dakatar da shi. “Abdurrahim ya isheka”. “to sarkin matsifa ya akai?”. “Abdurrahim bana so tafiyata ta wuce tsakanin gobe da jibi”. abinda yace da shi kenan ya kashe wayar, sannan ya ɗora ƙwayar idonsa akan Ahmad da fuskarsa ke nuna tsantsar damuwa.
da sassarfa yasa kai ya fice daga ɗakin, halin daya ke ciki a yanzu ya mantar da shi ciwon da ƙafafunsa ke masa, sai dai yana zuwa parlo bugawar da zuciyarsa keyi ta tsaya cak ganin Nawwara, bata lura da shi ba a sanda tazo wucewa ta gabansa sai ji tai an fizgo hannunta da ƙarfi ta dawo gaban mutum ta tsaya, hucin zafin numfashinsa na sauka saman fuskarta, inda shi kuma idonsa ke kulle yana ƙara matse hannunta da ƙarfin gaske tamkar zai ɓalla ma ta ƙashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button