NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Ayi haƙuri ni ban san ta yanda zanyi ya zama yanda kuke so ba, so please and please kuyi haƙuri muci gaba da tafiya a yanda aka tsara labarin tun farko….and again kuyi haƙuri muna hidimar biki ne shi yasa ban samu damar yi muku da yawa ba.

Assalamu Alaikum
jama’a na tallatamuku hajarmu ta online/offline business ɗina wanda zan ringa sayar muku da data ta mtn a sassauƙan farashi Kamar haka*
I sell MTN data with this cheap price:
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Whatsapp OR Call 08066268951

Comment&Share.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

29)
nabi ɗakin asibitin da nake ciki a kwance da kallo ɗaya, kafin na haɗe murfin idona na maida na rufe, wasu tafasassun hawaye kuma suka shiga bi ta gefen idona, a yayin da hoton lokacin da aka ɗauki gawar Gwaggona aka fita da ita ya shiga haskawa a idanuna, maganar Baba Mujibu dake faɗin an tafi kaita itama ta kutso cikin hoton, na buɗe idanuna a zabure na saukesu akan Basma dake gefena a zaune, tana goge hawayen fuskarta a hankali.
zuciya da ruhi suka ƙara tabbatar min da Gwaggona ta rasu, kuma ni da Basma mun zama marayu, bamu da kowa sai Baba. na mayar da idona na rufe ina ambaton kalamar innalillahi wa’inna ilahi raji’un, faɗa nake ina ƙara maimaita yayin da zuciyata kuma ke min wani irin zafi. kafin can kuma naji shigar wani sanyayyan ƙamshin turare acikin hancina, sannan wani sanyayyan hannu me taushi ya shiga cikin nawa, ban dai buɗe idon nawa ba, sai zuciyata dake bugawa fat fat.
“musulmi na ƙwarai me cikakken imani shine wanda ya yarda da Allah ɗaya ne, me bayarwa kuma ya karɓa, wanda ke yin dukkan yanda yaso akan bayinsa, a gare shi muke kuma gare shi zamu koma, gaba ɗayanmu da muke rayuwa cikin ƙunci ko jin daɗi cikin jiran mutuwa muke…saboda haka kiyi haƙuri, ki zama me tawassali ki zama me dangana, ki kuma bi Gwaggo da adu’a domin ita tafi buƙata daga gareki, ba wannan kukan ba, yanzu ne lokacin da zaki nunawa Gwaggonki ƙaunar na kike ikirarin kina ma ta da gaske, ta hanyar yi ma ta adu’a da roƙa ma ta gafarar ubangiji”. muryar nan me zurfi da kauri ta shiga kunnena da wannan tausasan kalaman nasihar tasa, muryar nan ta Ya Kabiruna da ko mutuwa nayi na dawo zan shaidata, ada ina jin kamar Baba ne kawai ya rage min, ashe ina da Ya Kabiru wanda nasan duk tsanani yana tare dani, duk da ban kalle shi ba amma shima nasan kukan yake yi ƙarfin hali da dakiya kawai yake yana faɗin wannan maganar.
na buɗe baki cikin murya dake harɗewa da kuka nace,”Ya Kabiru kaga Gwaggona ta tafi ta barni ko, Mahaifiyata me tsananin so na, me kowa me komai ya amsa abarsa, shikenan yanzu bani da Uwa sai dai na kalli ta wasu”. idona a rufe suke nayi maganar, ajikina naji sanda yasa hannu ya goge hawayensa sannan yace da ni. “ban isa na hanaki kuka ba domin nima haka nayi a sanda na rasa tawa mahaifiyar, amma zan roƙeki da Allah da Annabi karki ƙara min magana da wannan sautin idan har ba so kike zuciyata ta tarwatse ba, kukanki na karya zuciyata, yana raunanata, bana son kukanki Mairo, bana sonsa ko kaɗan…”. ya damƙe hannuna dake cikin nasa, ni kuma na buɗe idanuwana na yunƙura na miƙe zaune, na samu na tsayar da hawayena tukunna na tsayar da idona akansa, cikin ƙwayar idonsa, kan fuskarsa, akansa da girmansa da cikar haibarsa suka cika min ido.
gaba ɗaya ya sauya kamar ba shi ba, kamar ba Ya Kabiruna, ya ƙara yin kyau dan hasken da ya har cika min ido yake, yanayin tashin hankalin da nake ciki ne kawai zai hanani fassara abinda nakeji a ga me da shi. shima ɗin tun a sanda na ɗora idona a nasa ni yake kallo, ban san me yake tunani ba, amma kallon da yake min kallo ne na kamar wanda yaga sabuwar halitta a gabansa. na sauke kaina ƙasa ina motsa yatsun hannuna, murya a hankali nace,”kuma mutuwar bata tashi ɗaukanta ba sai a sanda na dawo, ko ta bari mu gana da ita tsawon lokaci bama tare, da saita bari muyi sallama ai”. magana nake cikin ƙarfin halin riƙe kukan dake neman kubce min.
a tunaninta ya san komai, bata san daga ɓatan nata har ciwon Gwaggon duk bai sani ba, mutuwar ma banda ya kira Kulu yaji tana kuka ba zai sani ba, ba wai kuma dan ta sanar masa ba, a jikinsa yaji wannan kukan nata da kuma jiyo hayaniya ta cikin wayar ya tabbatar masa da babu lafiya, hakan yasa ba shiri ya yanki ticket ya taho, kuma da zuwansa tun a hanya aka shaida masa Gwaggo ta mutu, kuma acikin gida daya shigo yake jin suna batun ciwon nata wai har da ƙafa ma saida aka yanke ma ta saboda wani ruwa me wari dake fitowa, Adawiyya kuma ta tare shi da albishir ɗin wai Mairo ta dawo, ta dawo daga ina?, alokaci ɗaya yaywa zuciyarsa da ita Adawiyyan tambayar mamaki kwance a fuskarsa, kuma sai yaji tana sanar masa da abinda zuciyarsa da gangar jikinsa suka kasa ɗauka, har sai daya sami tabbacin hakan daga bakin Amarya kafin ya yarda ya amince da abinda ya faru kamar a mafarki.
kuma wai Inna Amarya faɗa masa ta kr sun ɓoye masa ne gudun karya shiga tashin hankali acan har yace zai taho, Mutuwar Gwaggo ta dake shi, amma ɓatan Mairo ya shafe kaso 99 na cikin dukan, banda ana cikin jimamin mutuwa da babu abinda zai hana shi zazzagin Amadu inta kama ma harda duka ya haɗa masa, Allah ne da kullum sai sunyi waya da shi amma bai taɓa nuna masa da alamar wata matsala dake faruwa acikin gidan ba, ɓatan ɗan Mutum! ɓatan ma kuma na Maironsa!, kuma kowa yake rayuwa hankali kwance, sam shi baima yarda da batunsu na cewar har hukuma ma tayi iya nata wajen binciken nemanta ba, ya ƙaryata hakan, ya ƙaryata hakan daga bakin Amadu daya kusa kaiwa naushi a sanda yake rantse masa, har a ƙarshe suka fusata dukansu.
kuma kafin ya taho asibitin sai da yaywa Sadiya da Ƙawarta dukan mutuwa, yaji su ne a sanda suke tattaunawar wai Mairo da kanta ta ɓata ba saceta akayi ba, yawon iskanci ta tafi, Adawiyya ta karɓe zancen nasu da cewar,”nima haka nake zato dan duk wanda ya kalli Mairo sai ya zargi wani abu dan batayi kama da wadda ta ɓata ba, ai wanda ya ɓace a firgice yake dawowa ,kun tuna Sahura ƙanwar su Zailani?, ita ai kamarma haukacewa tayi, amma ita fa ras da ita, na rantse ma aka bibiya ciki gareta dan irin wannan hasken da tai bana lafiya bane, dana rungumeta ma wani irin wari na dinƙa ji irin na gidan karuwai”. shirunta ya haɗe da naushin da Kabiru ya baiwa bakinta har saida haƙori ɗaya ya fara lilo, kuma baiyi wata wata ba ya shiga fatali dasu gaba ɗaya, ƙwallo yake da Adawiyya tun daga Zaure har cikin tsakar gida, da ƙyar aka ƙwacesu daga hannunsa, babu yanda ba’ai ba ya faɗi me suka aikata ba yace su tsumayi dawowarsa bai gama dasu ba.
ya cije laɓensa na ƙasa da ƙarfi, tsakanin Amadu da Kulu waya kamata yafi jin haushi ne?, ya wani jijjiga kai a hankali kafin ya ɗago ya dubeta yace, “ina yi mana ta’aziyya”. na amsa masa da kai kawai, shiru kuma ya gimla, kafin wucewar wasu daƙiƙu na ƙara cewa da shi,”ya akai nazo nan?”. ya bata amsa da, “nima sanda na dawo akace an kawo ki asibiti, kinyi dogon suma ana tsoron ma Allah sa ba haɗiyar zuciya kika yi ba…Hajiya Hinde tana daga waje, taje alwala”. nai wani guntun murmushin daya tsaya iyaka laɓɓana, zanso ace haɗiyar zuciyar nai nabi bayan Gwaggona, dan gani nake kamar ba zan iya wannan rayuwar babu ita ba, gani nake a yanzu duniyata zata sauya ne ta shiga cikin tsananin ƙunci, gani nake kamar wani babban al’amari me cike da ruɗani na shirin tunkaro ni, gani nake tamkar watan zubar da hawayena ne ya tsaya, ji nake kama na rasa dukkan gata.
a wannan daren ƙarfen goma saura muka koma gida, na shigo ciki bayan munyi sallama da Ya Kabiru, Hajiya Hinde na biye damu, muka ratsa ta cunkoson matan da har yanzu basu ragu ba, kaman gidan da ake shirin yin biki, dan ƴan’uwan Gwaggo da Ƴan’uwa Baba yawancinsu duk sun hallara, haka ma ƴan’uwan Inna Amarya ƙwansu da kwarkwatarsu. idanun kowa akanmu cike da tausayawa muka shige ɗakin Gwaggo, kuma tunda na shiga sai mutuwar tata ta dawo min sabuwa, Gwaggona yau ta wuni a makwancinta sai mu kaɗai zamu ci gaba da rayuwa a wannan ɗakin, na ƙyalla idona kan gadonta, idanuna ita suke hasko min a kwance tana baccin nan nata wanda da safe ne kaɗai ta ke samun damar yinsa, dan raya dare ta ke tana ibada bata bacci, idan da rana nace ta kwanta ta huta sai tace min a’a, ai ba zata iya baccin da nutsuwa ba, hankalinta akaina yake.
na ƙarasa ƙafafuna na rawa na ɗauki filonta da zanen rufarta na rungume a ƙirjina, wani sabon hawaye na daban masu ɗumin gaske suka shiga malalo min, a yanzu kam na gama tabbatarwa Gwaggo tayi mana nisan zango.
ban san da shigowa wani cikin ɗakin ba, sai ji nai Inna Amarya ta kamoni ta miƙar dani tsaye, wacce sam na manta da ita, itama idanunta sun kaɗa sunyi jazur da alama har yanzu itama kukan nata bai gama tsayawa ba. “kije Babanku na kiranki”. ta faɗa a sanda ta kama hannuna muka nufa ƙofa, kuma har lokacin ban ajiye filo da zanen rufar Gwaggo ba, a tsakar gida muka same shi inda yake cewa a wuce damu ɗakinsa mu kwana acan, shi kansa Baban tausayinsa nake ji, dan yana tsananin son matarsa, amma ayau mutuwar nan da bata barin wani dan wani yaji daɗi ta raba shi da matarsa kamar yanda ta rabamu da ita.
na juya na riƙo hannun Basma ƴar’uwata da idan na kalleta nake jin zuciyata ta kuma tsinkewa da tausayin kanmu a dalilin rashin mahaifiyarmu. Mama Hadiza ita ta zauna damu a ɗakin tana ta lallashinmu da bamu haƙuri, kowa yazo cemin yake na daina yi ma ta kuka nayi ma ta adu’a, kuma duk yanda naso na tsayar da kukan saina ji wani sabo ya ƙara tahowa, Basma ma harta fini haƙuri da dangana, dan ita zuwa yanzu ta bar yin kukan saima idan taga inayi ne ta ke tausata.
Baba ya dawo ɗakin ya tasamu a gaba muka ci abinci, dan kowa nata fama damu muci abinci munƙi ci, haka na dinƙa tura abincin babu wani ɗanɗano, kuma sai daya tabbatar munci da yawa sannan ya ƙyalemu yace zai tafi gidan Yagana acan zasu kwana su da ƴan’uwan Gwaggo na nesa da suka zo, mu tashi cikin dare muyi mayi sallah muyi ma ta adu’a da samun dacewa da Rahma ubangiji, duk da cewar shi baya kokoton Suwaiba ƴar aljannah ce, muka amsa masa da to kuma bayan fitarsa babu jimawa saiga Kulu ta shigo, ta shiga tsakiyarmu ta zauna sannan ta kwanto da kanmu jikin kafaɗunta, kusan kowa na gidan yayi bacci a lokacin.
itama da tata dasashshiyar muryar da ta sha kuka ta ƙoshi ta ke ce mana, “baku kaɗai akayiwa mutuwa ba harda ni, nima na rasa ƴar’uwar da ta fi min ƴan’uwana da suka kasa riƙeni a lokacin dana shiga cikin tsanani, haƙiƙa ba zan taɓa mantawa da alkhairin Gwaggonku a gareni ba, saboda haka ina mana ta’aziyya gabaki ɗayanmu…kuma karku taɓa saka cewa a ranku rashinta zaisa ku zama marayu, kuna dani, zan maye muku gurbin Gwaggonku, zan tsaya tsayin daka wajen ganin cewar na zame muku Uwa ta gari, zan kwantanta kamar yanda Gwaggonku ta ke dan nasan ba zan taɓa zama irinta ba gaba ɗaya ba, domin ita ta dabance”. ta shafo kaina tana ɗago da fuskata na dubeta, bata taɓa kiran sunana ba, kuma ko a yanzuma da yanayinta suka nuna maganar da zatayi tawa ce shima bata faɗi sunana ba, illa iyaka kafeni da ido da tayi masu cike da tarin ruwan hawaye acikinsu tace,”Gwaggonki har ta rasu sunanki ta ke ta ambata, tana binki da tarin adu’oin da baki bai isa ya faɗi adadinsu ba, har numfashinta ya ɗauke faɗa ta ke Allah yayiwa rayuwarki albarka, Allah ubangiji ya shiga dukkan lamuranki, Allah ya dafa miki, ya tsareki daga dukkan sharrin masu sharri, ubangiji yasa kiyi kyakykyawan ƙarshe, ubangiji ya bayyanaki cikin amincinsa ya dawo dake gida…adu’ar da ta dinƙa yi muku kenan kafin yankewar numfashinta, saboda haka ku sha re hawayenku Gwaggo bata cancanci mu dinga yi ma ta kuka ba, fa ce mu bita da tarin adu’oin dake cikin kanmu”.
ta ƙarasa maganar harafan bakinta na karyewa, tana kuma saka hannu wajen sha re mana hawaye, amma inaa nawa sai suka ƙi tsayawa, na kifa kaina a tsakanin cinyoyina na kuma fashewa da sabon kukan da nake yi babu ƙaƙƙautawa, domin har yanzu na kasa amincewa raina Gwaggona ta rasu, komai ganinsa nake kamar a mafarki, Kulu haƙuri ta ke ta bani da dukkan wasu kalamai da ta san zasusa zuciyata tayi sanyi, kuma da karatun alƙur’anin da ta kama a bakinta cikin ƙira’arta me daɗin sauraro, da wannane bacci ɓarawo ya saceni.
Kulu kam wannan daren ba ta yi bacci ba, Basma da Mairo na kwance akan cinyoyinta, tausayinta kanta da su na sukar kowanne lungu da saƙo na zuciyarta, tana kuma taraddadin abinda zai iya faruwa bayan gama zaman makokin Gwaggo. kuma a lokacinne ƙwaƙwalwarta ta shiga tariyo ma ta da zantukan da suka shafe yinin dare suna yi da Gwaggon kamin ta rasu, ganin ciwonta ya tsananta tana ta faɗa ma ta cewar ita ta tabbata lokacinta yayi mutuwa tunkararta ta ke, kuma Gwaggon ta roƙeta akan ta faɗa ma ta asalinta.
a sannan ta kwashe dukkan tarihin rayuwarta dana ahalinta ta bayyanawa Gwaggon, ta kuma shaida ma ta abinda bata sani ba na cewar Kabiru ya san komai, Gwaggon tayi mamaki da jin hakan, don duk da cewar da ƙyar ta ke iya magana hakan baisa muryarta ta fito tar ba a sanda ta tambayeta, “ya akayi Kabiru ya san komai Hauwa’u?”. “Yaya akwai ranar da muke ɗakin Malam ni dake muna tattaunawa akan yanda za’ai na koma cikin ahalina, ku kuma kuci gaba da riƙe Mairo, to dana fito lokacin na tarar da Kabiru a tsaye wanda ya fito daga banɗaki, yanayinsa kuma ya tabbatar min daya ji dukkan zancen da muke, shi yasa ko a lokacin dana ji cewar zai wuce karatun can ethiopia nasa shi bincika min yanda labarin rayuwata yake yanzu acikin ahalina…kuma Yaya ita kanta Hussaina ta san da ina yin magana”. Gwaggo ta dubeta a firgice da ɗunbin mamaki, mamaki me haɗe da tsoron daya fallasa firgitar da zuciyarta tayi, ta zabura ta yunƙura zata miƙe amma ta kasa saboda tsananin azabar da ciwon da ƙafarta keyi ma ta. tashin hankali a muryata tace da ita,”ya akai Maryam tasan kina magana?, ta ya ya Hauwa?, duk ta yanda naso na ɓoye komai ashe ke kin kasa wannan dauriyar da kika ce min zaki iya”. Kulun ta shiga girgiza ma ta kai tana faɗin, “wallahi ba haka bane Yaya, kamawa tayi yasa dolen nayi ma ta magana a lokacin…saboda na tsinci agogon da nasan a masarautarmu ne kaɗai ake sa shi, kuma ko da na tambayeta sai ta ke shaida min Suhail ne ya bata, shi yasa na buɗi baki na zaburar da ita akan tai sauri ta dawo, idan mu’amalarta da shi tai nisa zai iya ganowa cewa ita jininmu ce, idanunsa na ƙyallawa kan azurfar hannunta shikenan komai ya bayyana, ni kuma ban shiryawa su san cewa har yanzu ina ƙasar nan ba, dan bana fata ko da gawata ta ƙara shiga masarautar bichi, kuma bana fatan na ƙara yin ido huɗu da Didi, duk da cewar ita ɗin Ƴar’uwata ce, amma ta kasa karɓar ƙaddarar da ta shato mana layi ni da Hassana muka biyota ta kawomu cikin ƙasar nan”.
“to amma dai bakiyi wata maganar da zata fahimtar da ita Sirrin da ake Ɓoye ma ta ba ko?, Hauwa koma dai kece silar barinta gidan nanne? domin yanzu zuciyata ta fara kokonta akan lamarinki?, in har zaki ce min Maryam tasan kina magana to ban san iya tsawon adadin lokutan da kuka shafe kuna hira ba”. Kulun ta zuƙi wani nunfashi kan tace,”a’a Yaya wallahi bata san komai ba, bamu ma taɓa yin doguwar hira da ita ba”. Gwaggon ta rumtse idanunta hawaye na silalowa a kumatunta. “ni dama wannan hukuncin da muka yanke nasan babu inda zaije muddin muna rayuwa a doron ƙasa, kuma muddin kina kusa da ƴarki, dole wataran gaskiya saita bayyana, ba zaki iya ci gaba da jurewa ba har ƙarshen rayuwa, dole sai kin fallasa ma ta ke ɗin ke kika haifeta, kamar yanda bamu isa mu binne gaskiya ba muce zamu fito da ƙarya…ko ajiya nayi mafarkin Maryam na kan hanyar dawowarta, kuma ajikina ina jin mafarkina zai zama gaskiya. kuma Alhamdulillahi na godewa Allah da zai kansace bana raye Maryam zata san gaskiyar komai, na kuma gode masa da sai bayan raina zata san da cewar bani na haifeta ba, na gode masa da sai bayan raina ne zata ɗanɗani wannan baƙin ciki da takaicin rayuwarta, na kuma godewa Allah da yasa bana raye zata zubar da hawayen da babu me iya tsayar ma ta da shi…Allah na gode maka da zaka ɗauki numfashina a yanzu, Allah na gode maka da ba zaka barni naga hawayen Maryam ba, wannan hawayen da nake jinsu tamkar ɗigar dalma a jikina a duk sanda naga ƙwalla a idonta”. muryatarta ta dakushe da matsanancin kukan da yaci ƙarfinta, taci gaba da faɗin,”ni nasan daga ranar da Maryam tasan komai ni kaina saita tsaneni, zataji haushina, zata ji takaicina fiye da jin takaicin komai, ba don komai ba sai dan ƙunshe ma ta mahaifiya da nayi a wuri ɗaya na hanata raɓarta, har nake hantararta idan ta kusanceta, nake ma ta tsawa a duk sanda suka kasance da juna, na sani, na sani wallahi saita ji haushina…amma dan Allah dan Annabi Kulu ki faɗa ma ta karta ƙullaceni a ranta ta yafe min, ban raba tsakaninta da mahaifiyarta ba saboda biyan buƙatar kaina ba, nayi hakanne dan sama ma ta rayuwa me ƴanci, nayi hakanne dan bana so ta koka a rayuwa, shi yasa na maye gurbin mahaifiyarta Malam kuma ya maye gurbin Mahaifinta daya ƙi amsarta a sanda tazo duniya, domin daga lokacin da ta gane kece kika haifeta, Malam kuma ba shi ne mahaifinta ba, abinda zata fara tambayarki shine ina nata mahafin?, waccen amsa zaki bata?, amsar cewa mahaifinta yaƙi karɓarta ya gudu daga gareki da mahaifiyarki shine abinda bama so ki sani…amma dan Allah dan Annabi ta yafe min, daidai da rana ɗaya ban taɓa jin cewa ita ɗin ba tawa bace”. ta tsagaita da maganar sannan ta ɗauko wasu ɗan kunnen yari da sarƙa na daham ta damƙawa Kulu a hannu. “Hauwa wannan sune kaɗai kadarar dana mallaka me tsada da daraja, yayin dana mutu Basma ita zata ci gadon komai nawa, to na bawa Maryam wannan halak malak, ki damƙa ma ta a hannunta kice tayi yanda taga dama da shi. kuma kema Kulu sai kinyi haƙuri da ita a sanda ta san cewar kece mahaifiyarta, zata ɓauɗe ne ta juya zuwa asalin Maryam ɗinta da ta ke tun farko, Maryam ɗin da babu mahaluƙin dake iya tausasar zuciyarta a sanda ta ke tafarfasa, sai kinyi haƙuri da dukkannin abinda zata aiwatar”. daga hakan kuma maganarta ta tsaya cak sai wata shaƙuwa da ta sarƙeta, kuma a wannan daren suka wuce asibiti da ita saboda yanda ƙafarta ta kumbura kamar an hura balan balan, tana kuma tsiyayar da wani irin ruwa me wari, ana zuwa kuma asibitin akace sai an yanke ƙafar, ƴan’uwanta su suka harhaɗo kuɗi Baba kuma ya siyar da rumfar da yake zuba itacensa aka haɗa kuɗi aka biya kuɗin akai ma ta aikin, kuma dama tunda aka yanke tace ita a dawo da ita gida ta mutu a ɗakin aurenta, mutuwa zata yi rayuwarta ta ƙare.
kuma a yau ɗin da aka sallamosu, lokacin da suka gama waya da Kabiru tana fitowa daga banɗaki ta jiyo salatin Yagana da Amarya kafin su fashe da kuka, ta ɗaga labule ta leƙa ɗakin ta tarar ashe Gwaggon ce ta rasu.
kuma ta ke maganarsu ta ƙarshe da ita ta haska ma ta acikin kanta,”Hauwa ƙwarai kina da kyakykyawar zuciya, babu makawa ke ɗin ƴar aljannah ce, domin ba kowa ne zai iya yin sadaukarwar da kika yi ba, ashe ni ba komai nayi ba acikin sadaukarwar da kike ikirarin nayi miki, lallai ke ɗin ta dabance, ubangiji ya faranta miki…idan Allah ya bayyana Maryam a duk sanda gaskiyar da muke ɓoyewa ta bayyana ki faɗa ma ta, tayi haƙuri ta barwa Allah komai, Allah shi kaɗai yasan dalilin da yasa zanen ƙaddararta ya kasance a haka…kuma ki faɗa ma ta wasiyyata agareta itave ta ɗauki fansa akan mahaifinta, ko da Allah bai cika min burina akanta na zama lauya ba, tayi shari’a da shi, ta tozarta shi kamar yanda ya tozarta rayuwarku”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button