NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Dare.
“Kulu zoki ɗorani a fo zanyi fitsari”. Gwaggo dake daga kishingiɗe ajikin filo ta faɗa. Kulu ta bar inda take zaune ta taso, ta ɗauko fo ɗin sannan ta ɗauro Gwaggon akai, bayan ta gama kuma ta taimaka mata wurin yin tsarki.
bayan ta sauketa taje ta zubar da fitsarin, ta ɗauko kofin silba mai ɗauke da koko ta kawo mata.
“Dan Allah Yaya kisha kokon nan, yau gaba ɗaya babu abinda kika saka acikinki, Yaya yanda kike ƙara ramewar nan yana ɗaga hankalina, rashin cin abincinki ba shi zai dawo mana da ita ba, sai dai ya haifar da wata matsalar”. Kulun ta faɗa a sanda ta miƙa kofin ga bakin Gwaggon, a gefe ɗaya kuma tana saka hannu ta goge hawayenta, Allah ya sani wannan rashin lafiyar ta Gwaggo shine dalilin daya hanata bin sahun ƴarta, duk kuwa da bata san inda take ba, to amma ai tana zaune a gidan saboda rufin asirin ƴarta ya rufu, yanzu kuma da babu ita mene amfani zaman, zata tafi ne kawai, tayi rayuwar da take ganin itace mafita a gareta.
“Hauwa bakina bashi da wani ɗanɗano, duk abunda kuka bani ina ƙarfin halin cinsa ɗura ne kawai kuke min, an riga anzo gaɓar da ba zan iya ƙara saka komai a bakina ba”. kuka takeyi a sanda tayi maganar, ta kamo hannun Kulun ta riƙe tana ci gaba da cewa, “Hauwa ki yafe min, ki yafe min dan girman Allah, ban cika alƙawarin dana ɗaukar miki ba, naci amanarki, ban san wannan ranar zata zo ba, ban san da zuwanta ba, da ban ɗaukar miki alƙawarin dana saɓa ba, da ban ɗaukar miki alƙawarin zan kula miki da Maryam ba kamar ƴar dana haifa acikina, da ban ɗaukar miki alƙawarin zanga rayuwarta ta inganta ba, da ban ɗaukar miki alƙawarin halin ƙuncin da kike gudun zata shiga ba ba zan bari ta shige shi ba, da banyi miki alƙawarin Malam zai riƙe ta ba, zai mata riƙon da uba ke yiwa ƴarsa ba. yanzu Maryam ta ɓata, ban san a wanne hali take ciki ba, da ace gawarta na gani da nafi samun lafiya da kwanciyar hankali, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”.
da ita da Kulun sai aka rasa wane zai taushi wani ya bar kukan, Kuka suke sosai, kukan da idan ka gansu kaima saika zubar da hawaye. sai can ne Kulu tayi nisa tace,”haƙiƙa har mutuwa ba zan taɓa mantawa dake da alkhairanki ba, bani da bakin yi miki godiya, alaƙawari ɗaya, alƙawarin nan guda dana ɗauka nayi miki adua a koda yaushe zan cika shi har ranar da ƙasa zata cika min baki…Yaya ki daina ɗorawa kanki laifin ɓatan Hussaina dan Allah, ba kece sila ba kuma ba kece sanadi ba, ƙaddara ce, ƙaddararta ce, Allah ya shirya hakan tuntuni, Allah ya rubuta a lauhul mahfuz hakan zata faru da ita, ko kaɗan bana ganin laifinki, kuma hakan ba zaisa na ƙulle ciki ba, baki sanni ba, baki san wace ni ba, baki san daga inda na fito ba, kuma tsawon shekara goma shida baki taɓa tambayata daga wanne ahali nake ba, taimakona kawai kikai, taimakona kawai kike da kyakykyawar zuciyarki wacce babu tsatsa acikinta, biki taɓa goranta min ba, biki taɓa hantarata ba, biki taɓa ƙyamatata ba, sai ganin kin ƙara ɓoye sirrin dake lulluɓe dani, abunda ko jinina ba zai iya min ba…ni kaina zanfi farinciki da samun natsuwar zuciya data ruhi da ace gawar Hussaina na gani, domin bana so tarihi ya maimaita kansa…”. kukan daya ci ƙarfinta a wannan lokacin shi yasa ta yin shiru.
“mutuwa zanyi, mutuwa zanyi Hauwa, ina jin ajikina lokacina yayi, ƙarshen rayuwata yazo, domin Allah yaji ya gani zuciyata ba zata taɓa iya ci gaba da ɗaukan rashin Maryam a kusa dani ba, ina sonta, ina tsananin ƙaunarta fiye da Basma, ji nake ajiki da ruhina tamkar ni nayi naƙudarta bake ba, Ya Allah ka dubemu, ubangiji ka dubi halin da muke ciki, ya zuljalalu ka kawo mana ɗauki, Allah kai kasan komai, kai kasan abunda ke faruwa da wanda zai kasance, ya Rahmanu ka sauya wannan ƙaddarar, Allah a duk inda Maryam take ka kula da rayuwarta”. ta kalli Kulu da hawaye ya gama wanke mata fuska, “idan na mutu ki bar gidan nan karki zauna, kuma dan Allah karki dawo cikinsa, kiyi nesa da shi kiyi nesa da abunda zaisa ki tuna shi, inaji ajikina kamar Maryam zata dawo wataran, Allah zai kuɓutar da ita, a wannan lokacin kuma da zatayi rashina nasan ba zaki juri ganin halin da zata shiga ba, ni kuma bana so, bana so tayi wani kukan daya fi na mutuwata ciwo…kiyi min wannan alfarmar Hauwa”.
Sallamar da ake ta kwaɗawa daga ƙofar ɗaki tasa sukayi shiru, Kulu ta shiga goge hawayen nata dana Gwaggo, Zannira ce matar Aminu da akayi auren sati uku da suka wuce, ƙanen Kabiru ne da suke ciki guda, wanda yake zaune acan Lokoja yana bugabugar kasuwanci tsawon shekaru uku, ana tsaka da alhinin ɓatan Mairo ya dawo kamar wanda aka aikawa da saƙon ɓatan nata, ya tafi can Lokoja ɗinne ba tare daya san kowa ba, sai kuma Allah ya haɗa shi da uban gida na gari, mutumin da baya da ƙyashi, ya samu ya nuna masa kasuwanci har Allah ya buɗa masa bayan yanke tsammani da Aminun ya farayi, Allah ya saka masa albarka ya fara samun abin hannunsa, dan ɗan ƙaramin shagon daya buɗe acan Lokoja ɗin na sayar da kayan electronics nasa ne wanda ya mallaka bayan sun haɗa hannun jari da uban gidan nasa, daya ga samun nasa yana faɗa-ɗa sai ya sayar da shagon ya dawo gida, ya kuma buɗe sabon shago anan kasuwar singa ta cikin garin kano, kuma da ike da albarkar iyaye sai shagon nasa ayanzu ya daɗa bunƙasa fiye dana lokacin da yake can Lokoja, domin dai-dai gwargwado yana samu. a yanzu haka ya ɗaukewa Baba duk wani abincin da za’a ci a gida, daman kuma Ahmadu yana aikowa da kuɗin abinci duk wata, wannan yasa babu matsalar abinci a gidansu Mairo a halin yanzu, akwai abinci wadatacce dan hatta gidan kansa ma gyara shi ake, shi da Amadu sukai haɗakar kuɗi akayi face-facen inda ya lalace, dan kowanne ɗaki yanzu da fenti, gidan ya koma kamar bashi ba, banɗaki ma kansa shi Aminun yasa an maida masan zamani.
“shigo mana Zannira”. Gwaggo tace, da ike har a wannan halin Gwaggo dai bata bari Kulu ta nuna tana magana ba, duk da taso yin hakan a sanda wani Malami yace da wuya Gwaggo ta kuma takawa da ƙafarta sai dai wani ikon Allah, to Gwaggonce ta hanata da ce mata da hakan kaɗai zaki biyani da abunda nayi miki.
“Gwaggo sannu da jiki”. Zanniran ta faɗa tana zama. “Yauwa Zannira sannunmu dai, ya ɗawainiyarku to Allah ubangiji yay muku albarka, an gode Allah ya ƙara arziƙi”. “Amin ya Allah Gwaggo, kema kuma Allah ya baki lafiya”. ta faɗa tana duban Kulu tace,”sannu Kulu kina ƙoƙari kema mun gode Allah ya baki lada ya kuma baki lafiya”. Kulu dai kallonta tayi tai murmushi kawai.
“Gwaggo dama ganda ne yazo da shi, to yayi niyyar kawo miki da kansa kuma sai Baba ya kira shi yaje masallaci ya same shi, shine yace na kawo miki, idan baiyi dare ba zai shigo”. ta faɗa a sanda take buɗe kwanon tana saka cokali aciki ta miƙawa Gwaggon. “Allah dai yayi muku albarka”. Zannira ta buɗe jaka ta ciro magani a ƴar kwalaba shima tace,”magani yaji wani malami ya faɗa a radio shine ya taho da shi, Malamin yace za a dinga shafa shi lokaci zuwa lokaci insha’Allahu za’a dace”. ta buɗe ta lakuto tana fara shafa mata.
Amarya ta shigo itama hannu ɗauke da kwanon abinci, ta ƙaraso tana faɗin,”aini nayi zatonma ko bacci kukai da naji Zannira nata kwaɗa sallama, ni kuma ina banɗaki a sa’ilin”.
Gwaggo dake ta ƙarfin halin magana tace,”gyangyaɗin dai muka fara, banma san Kulu itama ta kwanta ba”.
“to ga abincin, tuwon semovita ne da kuɓewa ɗanya”. Gwaggo tace,”aina kuma kika sami semovita?”. Amarya na murmushi tace,”ai biki ji daɗinsa da naji ba, kuma wallahi musamman danke na tuƙa shi tunda lokacin da muke je gidan Gwarzo naga kinyi santinsa. a kayan da Amadu yayo aike jiya ya sako, bamu lura da shi bama duka saida Zulai take ɗiban wake take ce min laa kinga ashe Amadu harda semo ya haɗo”.
“amma kuwa Allah yaywa yaron nan albarka. mu dai mun zama ƴan gata yara nata samun buɗi”. cewar Gwaggo.
“ai dama ance komai lokaci ne, Allah dai ya ƙara sanya albarka a cikin dukkan lamiransu”.
Zulai ta shigo ita da Sadiya da aka tsaida bikinta jiya watan mauludi. tun daga bakin ƙofa Sadiya ta hango gandar dake gaban Gwaggo cikin kwano, ta ƙaraso ciki tana cewa,”Allah ya kawoni a sa’a, ke dai Gwaggo ubangiji ya ƙara miki lafiya”. tai maganar tana zama tasa hannu ta ciro nama ɗaya ta kai baki.
“ɗakinki na leƙa ai ba kya nan”. cewar Zulai ga Amarya. “kuma fa shigowata kenan”.inji Amarya.
“hala kin manta zamu shiga gaisuwar gidan Hajiya Fatsima, ɗazu ma saida Yagana tayo aiken tuni, tace maƙota nata shiga mu muna ɗinke a gida babu wacce ta leƙa, to tace dai karmu wuce daren nan bamuje ba”.
“bari na ɗauko gyale na, dama tunani na Gwaggo, ba’a fita a barta ita kaɗai ba, to tunda Zannira ta shigo shikenan sai mu tafi…ni wannan ƴar ƙaniyar ma ai ban san ta dawo ba”. Amarya ta ƙarasa maganar da kaiwa Sadiya duka da ƙafa dake ta kai lomar nama baki.
Gwaggo tace da Zulai,”wato dai da gaske Adawiyya take ta koma gidan Yagana, yaufa gaba ɗaya ban sata a idona ba, to wallah kice mata ta dawo inba so take kuma na ƙarasa ba, ina zan iya zama babu Mairo itama kuma babu ita”.
Zulai na gyara zaman mayafi tace,”ai sai dai ki aika Saleh gashi can a tsakar gida, idan taji saƙon daga bakinki tafi ɗaukansa da muhimmanci…ɗazu ƙememai tazo tayi dakan yaji babu kowa a gidan amma ƙi tayi, saima ɗan aiken da tacewa a faɗa mana Baba Mujibu ya bada garin kunu ta shiga banɗaki awakin Yagana sunbi ta kansa”.
Saleh yay caraf ya amshe da faɗin,”ce tayi ma ba zata dawo ba saita gama hukunta awakin, yanzu ma dana baro su sai yi suke da Yaganar wai Adawiyya ta karya mata ƙafar tinkiya”.
duka akai dariya. kuma daidai lokacin Malam ya leƙo ɗakin, duk suka haɗa baki wajen yi masa sannu da zuwa. “baku tafi gidan gaisuwar ba?”. Zulai tace,”tafiyar zamu yi”. yace,”to kuma zaman me kuke yi bayan kun san dare ne, zaku haƙura yanzu fa ku jira safiya”. Amarya tayi saurin amsawa,”rufa mana asiri da faɗan Yagana”. ta dubi Zannira tace,”ki shirya gobe kema Sadiya ta rakaki kiyi musu gaisuwa, mijin gidanne ya rasu”.
sannan suka fita. haka suke yanzu a ɗakin Gwaggo ake yini jiddan walahairan, aita hira ana shafta saboda su ɗebe mata kewa, kuma hakan kanyi tasiri wataran.
ƙarfe biyu da rabi na dare.
Kulu ce a kwance kusa da Gwaggo, ba bacci take ba, a kwance take kawai, tana tunanin rayuwarta, tana tunanin irin yadda rayuwa ke gara mata.
ZANEN ƘADDARA, gani take kamar rayuwarta ce kaɗai mai ɗauke da ZANEN ƘADDARA, rayuwarta na haskawa ne da ƙaddarori mabanbanta tun a sanda suka shiga shekara goma sha huɗu a duniya, yanzu tana shekara talatin da ɗaya cif, kuma ƙaddara bata fasa binta ba, bata sauya ba, saima tarihi da take ganin kamar zai maimaita kansa, a tunaninta haɗuwarta dasu Gwaggo rayuwar zata dai-daita ko da ba kamar a baya ba, ƙaddarar ta sauya kuma ta tsaya, to amma me! tunda irin shekarun suka kama, shekara goma sha biyar, sai rayuwar take nema ta koma irinta farko.
tunda shekaru goma sha biyar suka kama a rayuwarsu ta duniya suka fara kallon ƙaddara, ƙaddarar data fara binsu a koda yaushe tana bin takunsu, tun suna guje mata har ta kamasu ita da ƴar’uwarta, ƴar’uwarta da suka zo a mahaifa ɗaya, Hassanarta, Hassanarta da suka zo duniya tare. ashe dai da gaske ne rayuwa bata taɓa biyewa muradin zuciya, a baya bata yarda ba, amma a yanzu ta yarda da hakan, ta kuma gasgata, dan hakan ta faru dasu ita da Hassanarta, sam rayuwa bata biyewa muradin zuciyarsu ba.
tunaninta ya katse a sanda wayar dake jikinta ta shiga Vibration, tayi sauri ta jawo wayar daga jikin zanenta data soke gudan kar Gwaggo taji ta farka, ta damƙeta a hannu sannan a hankali kuma ta sakko daga gadon ta fita tsakar gida, cikin sanɗa ta ƙarasa ɗakin girki ta ɗaga wayar a sanda kira na biyu daya shigo ke ƙoƙarin yankewa.
“Kabir”. ta kira sunan nasa a hankali, bai amsa ba sai data ƙara maimaita sunan,”Kabir”. sannan ya amsa. “ina jinki fa”. ta sauke numfashi,”to ya kake ya wajen naku?”. “muna lafiya”. muryar Kabiru na fita ne da sautin fushi, tasan fushin yake tun daga yanda yake bata short amsa.
shiru daga shi har ita babu wanda yay magana sai can ta katse shirun da faɗin,”har yanzu baka sami shiga cikin masarautar ba?”. yay gajeren murmushin data ji sautinsa,”Har yanzu kema baki nemi dabarar da za kiyi ki saka min muryar Maryam naji a kunnena ba?”. ya tari numfashinta, “aina faɗa miki ba zan kuma baki wani information ba har sai kin jiyar da kunnuwana muryar da take so”.
“to ai yanzu bacci take”. ya ɗan daga sautin murya kamar wanda zaiyi faɗa yace,”kullum abunda kike ce min kenan, bata nan, tayi bacci, zancen kenan kullum. ina so naji muryarta amma kun hanani, duk ranar dana kira kowa da uzurin da yake bani tsakanin ke da Amadu, shi zaice min idan yazo gida zai haɗani da ita, amma sai dai naji batun yazo ya koma, ke kuma da dabara kawai za kiyi ba wai ki bata wayar ba amma kin gagara… na fara tantama da wannan yawo da hankalin da kuke min tsawon wata shida, Amadu baya saɓa maganar da mukai da shi, ku daina ɓoye min ku faɗa min gaskiya idan Baba ya aurar da ita ne”.
ba wai dan ya gama magar da yake ba, ta katse shi da faɗin,”ko ɗaya ba haka bane, ba’a aurar da Hussaina ba, aina maka alƙawarin taka ce, taya zan yarda a gaban idona a bawa wani ita, Kabir zan yarda Sirrin dake ɓoye tsawon shekaru ya bayyana, amma ba dai ka rasa Ƴata ba”.
daga inda yake ya wani zuƙi numfashi, tabbas ya manta da wadda yake magana, dan ɗaga murya sama yay yana magana a zafafe, “kin san kuwa irin zafin da zuciyata ke min?, kin san irin yanda kunnuwana ke bala’in son jin muryarta?, kin san yanda idanuwana ke kewar ganinta?, kuka nake kullum, kuka bana fili ba na zuciya saboda tsananin kewa, kewa ta Maryam. duk safiya, duk rana, duk dare, duk baccina, wannan harufan guda ashirin da shida da suka bada kalmomi bakwai da suka fita daga bakinta zuwa gareni amsakuwa suke a kunnena, Ya Kabiru dan Allah ka tafi dani., kin san yanda naji a lokacin?, idona sai daya cika da ruwa, bugun zuciyata sai daya sauya, haƙiƙa a lokacin banda Sirrin dake Ɓoye babu abunda zai min shamaki da kama hannun abata na tafi da ita…har yau idanuna hoton wannan lokacin da take kukan tafiyata ne ke haskawa acikinsu, kunnuwana kuma amon sautin kukanta ne aciki”. Yay shiru, yay ƙasa da murya, muryar data raunana, muryarsan nan mai taushi, ta koma tamkar ta ƙaramin yaron dake tsananin buƙatar ai masa abu, ta tabbata a wannan lokacin tsugune yake akan gwiwoyinsa, kuma zata iya rantsewa hawaye yake. “dan Allah, dan girman Allah ki taimaka min, ki taimakawa kunnawa da saka musu muryar Maryam a sanda take cikin farinciki, ki kuma goge min hoton Kukanta dake haskawa a idona, na koma ganin fuskarta a sanda take murmushin nan nata mai sanyi, ki min hakan tun kamin zuciyata ta taɓu…dan Allah, dan Allah, na roƙeƙi nima ki taimaka min kamar yanda nake taimaka miki akan halin da ahalinki suke ciki…wallahi tallahi ina son Maryam, ina sonta, ina sonta da dukkan gangar jiki da ruhi, karki hanani ƴarki dan Allah”.
ɗiff ya kashe wayar, tabi screen ɗin wayar da kallo, ya zatayi?, ya zatayi ta sanar da Kabiru cewar Mairo ta ɓata ba’a ganta ba?, ba zata iya ba, ba zata iya wannan kasassaɓar ba, haka kawai! iyayensa da ƴan uwansa sun ɓoye masa sai itace zata sanar masa. har yau bai san da ɓatan Mairo ba, domin Baba yace kar wanda yayi gangancin faɗa masa, duk da dama ba samun damar wayar suke da shi ba, sai idan Amadu yazo ne zaice musu Kabiru yana gaishesu.
ta fito daga kitchen ɗinne sai taga kamar giftawar mutum dan haka tayi saurin nufar hanyar banɗaki, daga wajen banɗaki kana hango ƙofar ɗakin Gwaggo, mutum tagani ya shiga ɗakin, babu jimawa kuma aka fito, ba zatace waye ba ko kuma wanda take tunani, tunda lulluɓe yake da babban zane hatta kansa baka gani. to waye?, ta fara tsorata fa! wancan satinma ta tashi sallar dare ta shiga uwar ɗaki, fitowar da zatayi taga kamar mutum ya laɓe a bayan ƙofa, saboda sallar da zatayi sai batabi takan ta duba ba, dan lokacin gab ake da ai kiran farko, kasancewar bata farka da wuri ba, kuma tana cikin sallar zata tafi sujjada sai inuwar mutum ta gani ta fita, abun ya ɗaure mata kai a sanda ta sallame tana dube-dube bata ga komai ba. sai ta barshi a cewar idonta ne ya haska mata hakan, gizou kawai take, shaiɗanne ke so ya sanya mata wasi wasi, ai dama taji wani Malami ya faɗi hakan, idan shaiɗan baya so kayi ibadar cikin dare sai ya dinga sanya maka tsoro.
to amma ayau dai tabbas mutum ɗin ta gani, idonta ba gizou yake ba, kuma koma wane shi ɗin me cutarwa ne, gabanta ya faɗi, tai ɗakin da gudu, tana zuwa ta ƙaro hasken fitila, a sa’ilin data kuma ganin inuwar mutum ta gimla ta jikin labule, ba so take ta san wannan ba, lafiyar Gwaggo, dan haka tayi kan Gwaggo da sauri tana taɓata har ta farka, Gwaggo ta bita da ido ganin duk ta rikice, kuma yanda take dudduba jikinta kamar me neman wani abu.
Gwaggo ta farka, “Hauwa lafiya?”. “kina jin wani abune ajikinki?”. itama ta jefa mata tata tambayar ba tre data amsa mata ba. “babu abunda nake ji, wai menene hala?”. Kulu ta haɗiyi wani yawu a maƙoshi tana aikin sauke numfashi da sauri sauri. “kuma da kina bacci baki ji wani abu ya taɓaki ba?”. “ke ko dai mafarki kika yi ne daya tsorata ki kika tashi a hargitse haka?”. bata so ta ɗaga mata hankali, dan haka dole ta ɓoye mata ainihin abunda ta gani, kuma idanma tace zata faɗi hakan babu mai yarda da ita. “mafarki nayi mara daɗi, kiyi haƙuri na tasheki”.
Gwaggo kallonta take da rashin yardar abunda ta faɗa, tace, “fuskarki bata bani tabbacin abunda kika faɗa ba Hauwa, gaya min gaskiya”. “babu komai fa Yaya, ance baa son faɗar mummunan mafarki”. a yanda take maganar a tsorace da kuma nuna rashin gaskiya sai tayi mata saka Mairo. kai ta gyaɗa,”to Allah ya sauya shi ya koma mai kyau…kinyi sallah ne?”.
“a’a, yanzu dai zanyi”. “to kiyi adua sosai, ni bana jin ma zan iya yi saboda ƙafata tana min zafi, kamar ana caccaka allura nake ji”. Kulu ta tsareta da ido, “to ko kiyi sallar ƙila ta daina ciwon”. “ba zan iya ba, ki dai ƙara shafa min maganin da Aminu ya siyo, dan naji daɗinsa ɗazu, harna kwanta ba irinma tsamin da take yi, sai yanzu”. hannu na rawa Kulu ta ɗauko maganin, ta kwalɓato shi sai data kusan juye mata rabi sannan ta bari dan a sami na gaba, saboda taji Zannira tace maganin da tsada ɗari takwas aka siyo.
sanda ta idar da sallah ta jima zaune akan sallaya, hankalinta ya karkata gaba ɗaya kan mutumin da ta gani a ɗazu, waye?, waye?, so take tasan waye?, macece ko kuma namiji?, daga ina yake?, kuma tana da tabbacin koma wanene Gwaggo yake son cutarwa, aina zata ganshi ta faɗa masa da kakkausar murya matsawar tana tare da Gwaggo yayi kaɗan ya cutar da ita, saboda haka ya sake sheƙa, ba anan ba, ba anan inda take tare da ita ba, cutarwarsa ba zatayi tasiri akan Gwaggo ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button