NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Bichi.
Alhaji Adamu ne zaune a ƙaton parlonsa, tunda Malam yaje Umra ya dawo shikenan mutanen ƙauyen suka koma kiransa da Alhaji duk da cewar inkiyar mai faskare bata bar sunansa ba. ya ɗago da kansa ya dubi Kabir dake zaune a ƙasan carpet yana fuskantarsa yace,”Kabir wai meke damunka ne?, gaba ɗaya ka sauya kowa sai ƙorafi yake akanka, jiya a gidan nan tambayanka ake alhalin kana cikin gidan, keɓewa daga mutanen na mene Kabir?, wannan sabuwar ɗabi’ar taka ban yarda da ita ba”. muryarsa a ƙasa cike da girmamawa yace da Baban nasa,”kayi haƙuri Baba, ni kaina bana jin daɗin kaina a yanzu, kuma ba komai bane yajawo hakan sai yanayin karatuna, accounting akwai zafi sosai, ga yanayin yanda business ɗin nan ke neman wargajewa, company ɗin da muka haɗa hannun jari dasu naje nasa hannu a kuɗaɗen da basu kenan ba, hakan kuma na neman yaja min asarar da ba zan iya maida ita ba, shine duk al’amura suke neman dagule min”.
Malam ya numfasa yace,”to ya kuwa ba za kai wannan ta’asar ba ka koma wani kalar mutum na daban…mtswww”. tsakin da mahaifin nasa yaja ne yasa shi saurin ɗagowa ya dube shi, “dan Allah Baba kayi haƙuri, adu’arka kawai nake nema”. “Allah ya gyara lamarin…kuma jiya munyi magana da Gwaggo Azumi tace min kai kaɗai ne baka bada gudunmawar Amadu ba, me yasa? bayan kasan kaf ɗinku babu wanda aka ɗaukewa hakan”. Kabir ya ƙara yin ƙasa da kansa yana fitar da wata zazzafar iska daga bakinsa. “wallahi Baba gaba ɗaya na manta ne, ni da kaina ma na kira shi nace ya tura min account numberns to ban san me ya sha’afar dani ba. shi kuma bai tuna min ba ko a ɗazu”. Malam ya kuma jan tsaki,” ya za’ai ya tuna maka salon kai tunanin maula yake wurinka tunda ka fishi, kuma ai ba shi yace ku haɗa masa ba ni naga hakan ya kamata shi yasa nace ku haɗa masa, kake wani batun bai tuna maka ba. banda shirmen banza har akwai abinda zai ɗauke hankalinka akan abinda ya shafi ɗan’uwanka…to bari kaji na faɗa maka Kabir wallah dukiyarka a banza zata tafi muddin kace ba zaka taimaki ƴan’uwanka ba dan kwata-kwata ba zatai albarka ba. dan ubanka idan baka kyautata musu ba wa zaka kyatatawa, shirmen banza kawai, ashe a matsayinka na magajina ba zaka iya kula dasu ba a sanda na bar muku duniyar…”. yay saurin tarar nunfashin mahaifin nasa da faɗin,”a’a Baba ba haka bane wallahi ka daina wannan tunanin. na rantse ko kusa ko alama bani da zummar morar abinda yake mallakina ni ɗaya, duk wani faɗi tashi da nake dalilinsu na gaba gaba”. “shikenan ai. tashi kaje, ni dama wannan sabuwar halayyar taka ce bana so, dan Shatu ma ɗazu ta faɗa min kwata-kwata ma bata ganinka acikin sha’anin daya shafi bikin, shi Amadu da abokansa ne kawai suke komai”. a wannan karan baice komai ba, yay sallama ga Baban sannan ya miƙe ya fita, takaici duk ya cika shi, shi komai yana yi ne domin Allah, abinda Baban bai sani ba shine shi kansa gidan da Ahmad ɗin zai zauna shi ya bashi a matsayin gudunmawa tun ranar da aka kira shi akace an tsaida maganar aure, tunda yasan Ahmad ɗin baya da ƙarfin da zai iya mallakar gidan kansa a irin ƙurarran lokacin da akasa, yasan da cewar yafi ɗan’uwan nasa ƙarfi shi yasa yaga babu babban taimakon da zai yi masa sama da wannan, kuma yace da shi hakan ya zama sirri a tsakaninsu ko da Baba bai yarda ya faɗawa ba, dan zasu ga kaman baya wani samu da wurin aikinsa.
sanda zai nufi part ɗin Ahmad ɗin ya hango Nawwara, tana riƙe da wata ƙatuwar kular abinci data rinjayi hannunta, ga goyon wannan ƙaton yaron da taiwa wanka ɗazu, a kallo ɗaya yaywa goyon ya fahimci nauyin yaron yafi ƙarfin ƙirjinta. sai ya kulle idonsa ya buɗe, so yake ya kirata tazo gabansa yasa hannu ya kunce ɗaurin zanen, in yaso ma yaron ya faɗi ƙasa ko fasa kai ne yayi shi babu ruwansa, ko da yake bautar daga yau ne, matsayin da zata samu a gobe baya ƙara bawa kowacce ƴar banza damar sakata rainon yaronta ba. yay tattaki ya ƙarasa wurin cuncurundon iyayensa mata da suke tsaye ana lissafin yanda za’a ɗora tukunyar sanwar abincin yau…ta gefenta ya ratsa, amma bata san daya zo wurin ba, haka kuma bata san ya wuce ba, sai bayan wucewarsa ne ma ta tsinci maganarsa a iska dake shiga cikin kunnenta a yanzu. “karki sake kizo min da wannan goyon ɗakina”. abinda yace da ita kenan, kuma ta gane mai maganar tasa take nufi, taje ta same shi, ta same shi a ɗakinsa, kuma bada wannan goyon ba, hakan yake son ce mata amma sai ya dunƙule maganar. ta waiga tana kallonsa, kallon tafiyar nan tasa ta ke mai ɗaukar hankali, tafiyar da ba zata iya kwatantata ba, taji wucewar wani dunƙulallan abu ta wuyanta sannan ta ɗauke kanta daga inda yake. haka kawai ta tsinci hannunta na rawa, ta ɗan duƙa ta zurkuɗa goyan yaron ta gyara shi, sannan ta ɗauki kular abinci ta wuce babban store ɗin gidan dake bayan ɗakin da ake ajiye generator.


“zaka fita da motarka ne?”. Kabir ya kalli Ahmad da yay tambayar yace,”i dont think so, amma kai yanzu zaka fita da ita?”. Ahmad ɗin ya ƙara cewa,”zuwa 11 dai wancan ɗan rainin hankalin Abba telan bai ɗinka min babbar rigar da zan saka ba gobe…to zuwa zanyi na sa shi a gaba”. Kabir ya shafo wuyansa sannan yace,”kaima kasan halin wannan mashiri-rancin ina kai ina kai masa ɗinkin biki…idan bai ɗinka ba saika sa tawa kawai”. Ahmad ɗin ya kalla ɗan’uwan nasa cike da so da ƙauna yace,”kai kuma fa?”. “ai ka fini buƙatarta, kaine jigon saka babbar riga a gobe. kuma dama si ba kala ɗaya na ɗinka ba, akwai wadda zan saka a dinner, so saina fasa sakawa nasa goben”. Ahmad yace,”tom shikenan dan babu alamar ɗinkin nan zai gamu ayau wallahi, ya ɓatan rai sosai”. Kabir ya numfasa yace da shi,”wurin dinner ɗin ƙarfe nawa ne?”. “8”. “Allah ya kaimu”. yay shiru, a ɗaƙiƙa ɗayan da ta wuce Ahmad yace da shi,”kaje asibiti kuwa?”. “ni ba ciwo ba me zai kaini asibiti”. “baka da lafiya Kabir, kaga yanda kuwa ka rame, ai yanayinka kaɗai ma na nuna ƙarfin hali kake, shi yasa ban takura maka ma akan bikin nan”. Kabir baice komai ba, suka ɗora da wata hirar akan ziyarar da suke so su kai can dangin su Yagana bayan bikin.
daga bisani ya miƙe ya koma ɗakinsa, kuma yana shiga ya tarar da calender ɗin da Ahmad yace ya aje masa na abokansa daya gayyata. ya kai hannu ya ɗauki calendern, hoton Maryam ɗin kawai yake kallo, da wannan fararan idanuwan nata ƙal, ta saƙalo kanta ta gefen fuskar Ahmad din tana murmushi. ya lumshe ido ya aje calander sannan ya nemi kujera ya zauna ya jinginar da kansa jikin kujerar.
“Kabir ka daina forcing kanka akan son yarinyar nan, na faɗa maka sam ba sonta kake ba kaƙi ka yarda dani, kawai kana so ka huce takaicin rashin Maryam ne akanta, amma ba sonta kake ba, ko ka aureta ba zata samu soyayyarka ba tunda Maryam ta riga ta gama da zuciyarka…ka yarda dani ko karka yarda Nawwara tausayinta kawai kake, dan haka ka daina ƙoƙarin sauke zafinka akanta, karka je ka aikata wani abin da zaka zo kana regreting”.
abinda Abdurrahim yace da shi kenan a jiya kamin tahowarsa, bayan sun gama waya da Nawwara, kuma furucin daya haddasa faɗa a tsakaninsu, saboda haka ne ma Abdurrahim ko jiran tashin jirginsa bai ba ya tafi, bai sani ba ko daga baya ya koma ya ɗauki motar oho. ya fitar da iska a bakinsa yana kulle idanuwansa, a hankali kuma hoton kwanakin baya ya shiga haskawa cikin idonsa, wannan ranar daya je Qatar jin Akila ta sauka a ƙasar, yaje don su gaisa da ita sun jima basu haɗu ba sai dai a waya. kuma yana zuwanne ya tarar Ammi ta aiki Maryam store zata yo ma ta siyayya, sun kuma yi faɗa ita da Alhassan yace ba zaije aikin ba, zuwansa Ammi taji daɗi tace ya ɗauki Maryam ɗin dan Allah ya kaita tunda yau iskar kanta tace driver ba zai jata ba shi yasa ma ta liƙe sai dai su tafi da Alhassn ɗin. shi kansa a lokacin ganin idon Akila ne kaɗai yasa shi faɗin abinda bakinsa bai shiryawa ba,”tazo mu tafi”. amma da ace babu ita a wurin duk da cewan Aliya na nan tsab zaice da Ammi ba zai kaita ba…kuma duk da hakan darajan Akila dai Maryam ɗin taci har suka je suka dawo bai taɓa lafiyar jikinta ba, saboda irin maganganu masu ɗacin da ta dinga yaɓa masa har suka je suka dawo, amma ko abinda tai masa a parlo yaci ace ya manta da Aliya da Akila dake zaune a wurin yasa ƙafa ya fyaɗeta ta zube ƙasa, sannan ya ciro belt ya tafarfasa ma ta jiki, ta yanda gobe waninsa ma ba zata yi wannan rashin kunyartata ba.
ya buɗe idanuwansa a zafefe yay tattaki zuwa bangon gabas ya tsaya, ya harɗe hannayensa ta baya, kallon bangon kawai yake ba tare daya san me yake kalla ba ajiki, tsawon wucewar mintina goma ƙofar ɗakin tai ƙara.
a hankali hannun Nawwara dake riƙe da handle ɗin ke tura ƙofar, kuma muryarta acan ƙasa tayi sallama da kai tsaye da doka wani abu a zuciyoyin duka su biyun, ta rakuɓe tsaye daga bakin ƙofar kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta, wucewar sakan 1,2,3 taji saukar maganarsa a tsakaiyar kanta. “ni zanzo na ƙarasa shigo dake?”.
wannan siraran ƙafafuwan nata daya ƙurawa ido suka shiga takawa a hankali suna lumewa acikin tattausan carpet ɗin dake malale a bedroom ɗin, kuma bai san dalili ba sai yaji ba zai iya jira ta ƙaraso har zuwa inda ƙafafun nata da zuciyarta zasu iya tsayar da ita ba. dan haka acikin shirin da bai ba yaji ya ƙarasa inda ta ke ya kamo hannunta, kuma ƙafafunsu suka tsaya a inda bugun zuciyarsa ya tsayar da shi.
tsawonsa da ya bayyana a yanda yake tsaye a gabanta, sai wani irin ruɗani da kasala suka yi barazanar jefar da ita ta zube, tai saurin saka hannu ta damƙo gaban rigarsa maɓalli ɗaya na gaban rigar ya cire, a yayin da shi kuma yay saurin zagaya hannunsa zuwa weast ɗinta ya dakatar da ita daga faɗuwar. wata aba ajiyar zuciya da gaba ɗayansu basu shirya mata ba ta sauka ajikinsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button