NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Parkview Estate, Ikoyi, Lagos State.
“Bullshit! taya za’ai emanuel zaiƙi sanya hannu akan abunda na tura masa, yaushe ya kai matakin daya fara take umarnina?”. Dr Emanuel kenan, ingarman zakin namijin dake zaune kan lumtsatstsun cushion ɗin dake kewaye a matsakaicin parlon ke wannan maganar acikin harshen turanci, muryarsa na fita cikin ƙaraji, ya zare farin glasses ɗin dake sanye a idonsa ya ɗago ya dubi wanda ke tsaye a gabansa.
“ina buƙatar ganin Samuel a office ɗina in the next 3hours”. Yanzunma dai acikin harshen turanci yay maganar, Onoka ya rissinar da kai cike da girmamawa ogan nasa, sannan ya karɓi files ɗin hannunsa ya fita.

2hours Pass.
Emzor Pharmaceutical Industries Limited.

#Comment & Share.
SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

Last Page nayi repeating sunan Emanuel har 2×, ayi min afuwa.

9)
Parkview Estate, Ikoyi, Lagos State.
“Bullshit! taya za’ai Yemi zaiƙi sanya hannu akan abunda na tura masa, yaushe ya kai matakin daya fara take umarnina?”. Dr Emanuel kenan, ingarman zakin namijin dake zaune kan lumtsatstsun cushion ɗin dake kewaye a matsakaicin parlon ke wannan maganar acikin harshen turanci, muryarsa na fita cikin ƙaraji, ya zare farin glasses ɗin dake sanye a idonsa ya ɗago ya dubi wanda ke tsaye a gabansa.
“ina buƙatar ganin Samuel a office ɗina in the next 3hours”. Yanzunma dai acikin harshen turanci yay maganar, Onoka ya rissinar da kai cike da girmamawa ogan nasa, sannan ya karɓi files ɗin da Dr Emanuel ya miƙo masa ya fita.

2hours Pass.
Emzor Pharmaceutical Industries Limited.
Emzor Kamfanin ne na ƙera magunguna wanda aka kafa tun a shekarar 1984 a ƙasar Najeriya.
Kamfanin da aka kafa da manufar yin samfurori masu inganci na magunguna.
Kamfanin yana daga cikin jerun mayan kamfanunuwa guda goma da suka shahara a nigeria. Tun bayan da Obafemi Afafa mamallakin kamfanin ya rasu, Babban ɗansa me suna Tosin Afafa yaci gadon kamfanin kasancewarsa ɗa ɗaya tilo a wurin mahaifin nasa. To shima ayanzu ya maida Babban ɗansa me suna Dr Emanuel Tosin Afafa the CEO of the company, wanda ya kasance mai ƙwazo da himma wajen ganin kamfani na samun ci gaba ƙwarai da gaske. Duk da a baya bai taɓa zaton zai iya ɗaukar ragamar nauyin kamfanin ba, dan acewarsa baya jin zai iya ɗaukar all those responsibilites na shareholdings, business trip and rest, to amma da yake mahaifin nasa General Tosin tsayayye ne wanda baya magana biyu haka dole ya haƙura, yake kuma gudanar da ayyuka yanda ya kamata, kuma a sabbin tsarinsa da yake son aiwatarwa a yanzu yana sone Mahaifinsa ya yarje masa ya shigo da sauran ƙannensa cikin wannan harkar, to amma mahaifin nasa yaƙi ba shi dama, ya sanar masa suma da akwai sauran kamfanin da yake son buɗewa wanda kuma yake tunanin watsa ƙannen nasa aciki wato Joseph da Obi.
Duk da shi ɗin arnene da babu hasken musulunci tare da shi, amma kuma yana da kwarjini, cikar zati haɗe da wani irin farin jini da ko acikin musulmai ba kowa ubangiji ke mallakawa irinsu ba, shi yasa da yawan musulmai da suka san kyawun halayyarsa suke masa adu’ar Allah yasa ya musulunta. Tafiya yake da irin taku mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali na irin mutanen da jin daɗi har yay musu yawa, bai san talauci ba domin bai taso acikinsa ba, haka kuma bai san wahala ba dan bai saba da ita ba, sai dai kuma shi ɗin mutum ne mai tsananin tausayin talaka da son taimaka masa, walau ɗan’uwansa kafiri ko kuma musulmi.
Tunda ya sanyo ƙafa cikin kamfanin ya sauya yanayin fuskarsa inda ya tamketa, dan sam baya bawa ma’aikatan fuskar da zasu aikata abunda suka ga dama acikin ma’aikatar saɓanin yanda yake so su kasance. A duk wani taku da yake Oluwa na biye da shi a baya, hannunsa ɗaya riƙe da ash suite ɗin Oga ɗayan kuma riƙe da brief case nasa, har sanda suka ƙaraso bakin office ɗinsa ne kuma ya miƙawa sakatariyarsa Joy kayan ta ƙarasa shiga dasu. Joy ta shigo ta rataye rigar suite ɗin ajikin hanger, sannan ta kai brief case ɗin ta aje kan table tare da daɗa gyara wurin, ta tsaya tana kallon Dr Emanuel wanda ke tsaye a bakin window, ya zuba duka hannayensa cikin aljihun wando, yana ƙare kallo ga yanayin garin damunar da hadari ya haɗo a yanzu idanu na nuna ruwa na gab da sauka, ko da Joy tayi masa magana sai daya ɗauki tsawon daƙiƙa kamin ya juyo yana zare baƙin glass ɗin dake kewaye saman siririyar farar fuskarsa, Joy tayi saurin janye idanunta daga kallon nasa, ta rissinar da kai tana wasa da yatsun hannunta zuciyarta kuma na bugawa, har ya ƙaraso yaja kujera ya zauna bata sani ba sakamakon lulawa datayi acan duniyar tunani da take yinsa a kullum na son ace yau ta mallaki Oganta.
A hankali ya motsa laɓɓansa kamar wanda bai son yin magana, “ki cewa MD ina son ganinsa yanzu”. Ta ɗago ido cikin rissinar da kai tace masa, “Bayani dangane da Vitro Health suna so ne mu haɗa contract dasu akan magungunan da za’a fita da su ƙarshen watan nan”.
“ki aje takardun zanyi tunani akai first kamin nayi singining, ki kuma ƙara min bincike akan kamfanin sosai kamin na bar office”. Ta amsa masa da to sannan ta ƙara da cewa, “Jiya bayan fitarka babu jimawa kayi baƙi daga EDIG, yanzu haka ma suna reception suna jiranka”. “dama ina da appointment da su ne a jiya da yau ɗin?”. Daga yanda yayi mata tambayar tasan tayi ba dai-dai ba, dan haka saida ta haɗiye wani yawu a maƙoshi kana ta amsa masa,”a’a baka da, hasalima cikin watan nan kaf baka sanya appointment da kowa ba”. Ya bar shafa computer ɗin da yake ya kwantar da kansa jikin kujerar dake juyi da shi, hannayensa a dunƙule ya lumshe ido sannan yace da ita,”amma me yasa kika barsu suna jira?”. Jikinta ya hau tsuma ta fara inda-indar magana,”Naji sunce ne maganar da zakuyi tana da muhimmanci, shi yasa har na amince musu akan su dawo a yau ɗin”. Tai maganar tana aikin sosa ƙasan kuncinta.
Ya girgiza kai a lokacin da yake kallonta ta gefen ido, a ransa yana ƙirga irin matsalolin da Joy ke haifar masa tun zuwanta kamfanin watanni biyar kenan, dama wannan ne last mistake da yake so ta ƙarayi sannan yaywa tufkar hanci. Jin shirun nasa yayi yawa yasa ta ƙara cewa da shi, “Sir zan iya yi musu iso?”. “Am not available, so ki san yanda zaki dasu”. Sanin cewar ko da ta kuma yin magana ba zai saurareta ba ta juya ta fice da gwiwa a sace.
Bayan wucewar daƙiƙu biyar da fitarta MD Simon Ya turo ƙofa ya shigo, har sanda MD ya ƙaraso ya zauna a kujerar da suke fuskantar junansu Dr Emanuel bai ɗago ya dube shi ba, sai dai a yanda yaga yana karanta takardun dake aje kan table ɗinsa da kuma yanda ya dunƙule hannu ɗaya yasan cewar akwai damuwa, sai dai baiyi hanzarin katse shi ba har zuwa lokacin da Emanuel ya ɗago ya dube shi tare da tura masa takardun zuwa gabansa. Md ya ɗauki takardun yana karantawa, ya kalli Emanuel a sanda ya gama karantawar sannan yace, “amma Joy bata yi maka wani bayani dangane da shigar report ɗin ba?”. “na kore ta”. Md ya maimaita maganar tasa,”ka kore ta?”. “yes”. Md ya jinjina kai da faɗin,”amma dai a wannan karan bani zan sake nemo maka wata sakatariyar ba ko?, dan na gaji da nemo maka kana korarsu ɗaya bayan ɗaya haka kawai babu wani dalili”. “Ba zan iya zama da marar gaskiya acikin aikina ba, kai kuma duk marasa gaskiya kake kawo min, so this time around na hutar da kai da kaina zan nemo”. Md yay murmushi kawai, dan yasan a ƙarshe dai dole shi ɗin zaisa ya nemo masa.
“kasan babban abunda ya ɓata min rai?”.
Md ya kaɗa masa kai yana me ƙara duban takardun hannunsa cike da takaici.
“me yasa tun farko Yemi da yasan mutanen nan bana ƙwarai bane yaƙi sanar damu sai bayan da mu kai accepting contract ɗin nasu sannan zai dawo da takardun yace min ba zaisa hannu ba”.
“Dr ka ƙara duba sosai da nazari akan wannan lamarin, in har ba akwai wani mugun ƙullin a zuciyar Yemi ba, Babu yanda za’a ce morethan two weeks yana sane yaƙi signing kuma bai sanar ba sai a yanzu da ake son gama shigar da komai sannan zaice contractor ɗin yayi rejecting, no way dole akwai wani abu a ƙasa”.
Emanuel ya ɗaga kafaɗa, “abun ya min ciwo amma kuma ba zai dameni ba”.
“me yasa zaka faɗi haka? Wannan fa faɗuwa ce ke neman shafar kamfaninmu”. Emanuel ya dube shi sosai sannan yace,”ai tun farko nace bana son kamfaninmu ya haɗa contract with any other companies, amma kai da Dad kuka ce ai NDBH ba abin yadawa bane, dan haka ni na cire hannuna, faɗuwarku ba daga ni bane daga gareku ne, kuje ku shawarta yanda zakuyi”.
Md ya dunƙule hannu ya doki table, “Ya za’ai ana talking of billions kace wai zaka zame hannunka aciki, kasan kuwa irin asarar da kamfanin zai samu, da kusan quarter ɗin kuɗinmu fa mukai amfani”.
Yanda Emanuel ya ɗaga kafaɗa irin ko ajikinsa hakan ya ƙular da Md, ya kuma bishi da ido har zuwa inda ya zauna kan cushion ɗin cikin office ɗin, ya ɗau coffee yana kaiwa bakinsa. “har wani lokacin shan coffee ma kake da shi?”. Emanuel ya kalle shi ta cikin reflection glass na cup ɗin, ya motsa laɓɓansa kan ya kurɓi coffee ɗin sannan ya aje cup yace da shi, “me kake so nayi kuma?”. Md ya girgiza kai ya miƙe ya koma kan kujerar Emanuel ya zauna, ya zari farar takarda yay short rubutu ajiki, Sannan ya miƙe yay tattaki zuwa inda Emanuel yake ya ajiye masa takardar a gabansa, ba tare da Emanuel ya dubi rubutun dake cikin takardar ba ya miƙa hannu ya karɓi biro daga hannun Md sannan yay signing a inda Md yaya masa nuni. Cikin lokacin da basu haura daƙiƙa biyar ba Md ya buga takardar ya ninke yasa a envelop sannan ya fice daga office din ba tare da yaywa Emanuel sallama ba, yana kuma jin sanda Emanuel ɗin ke cewa da shi zai ɗauko ɗan arewa a matsayin sakare na shi, yay banza da shi bai ce masa uffan ba domin ba abune mai yiwuwa ba dan Dad ma ba zai barshi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button