NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Comment&Share and also Vote kunji ƴan aljannah.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

(38)
“me yasa ba kya so ya mutu?”.
“saboda ina sonsa, dan Allah Mami karya mutu”. na faɗa ba tare da sanin ma’anar da furucin nawa zai haifar ba, ina ƙara ƙanƙameta kamar zan karya ƙasusuwan jikinta, sai naji tayi wani murmushi da sautinsa kawai na iya ji, sannan tace da ni,”akwai wasu kalmomin dake bada tarin ma’anoni da yawa…Maryam a shekarunki goma sha bakwai nasan kin san ma’anar So, haka kuma kin san rabeben So…ina so ki faɗa min wanne irin so kikewa Kabir bayan na ƴan’uwan taka?…ba daga fatar bakinki nake son jin amsar ba, ki ba ni ita daga ƙasan zuciyarki”.
sai naji na tsaya cak daga motsi na wucewar wasu sakanni, yawun bakina kuma ya ƙafe, abinda Mami ta faɗa daga ƙarshe shi ƙwaƙwalwata ke ƙara biya min, “bayan so na ƴan’uwan taka, wane irin so kikewa Kabir?.”, tabbas tambayar na ɗauke da ma’anar da nake ganin kamar taiwa kaina girma. to ma wacce amsa zan bawa Mami a yanzu bayan wacce nake da ita ta riga ta faɗeta acikin tambayar da zata min, bayan so na ƴan’uwantaka dama akwai wani so ne da nakewa Ya Kabir wanda ban san da shi ba?, so ɗaya na san ina masa soyayyar Yaya da Ƙanwarsa, irin so na amatu ɗin da zan iya shiga wani hali in har mutuwa ta rabani da shi. “ehen…”. maganar Mami acikin shirun da nai tasa kayan cikina hautsinawa, sai dai a lokacin da zan buɗi baki nai magana a lokacin na godewa Allah da kuma Ya Amadu da maganarsa ta katse zancen na mu. “Mami likita na magana”. “oak Ahmad jeka mana”. “no yace ke yake son gani”. Mami ta jayeni daga jikinta sannan ta miƙe ta fita, ni kuma na zauna kan kujerar da ta tashi na tsurawa Ya Kabiru ido wanda motsinsa kawai nake so na gani ko na sami ƴar natsuwa a tare da ruhina. “goge fuskarki”. Ya Amadu yace da ni a sanda ya ƙaraso wurin yana tsaye daga gefen gadon, hannunsa kuma daya miƙo min handkerchif ɗinsa ne, na miƙa hannu na amsa sai naji shi da damshin ruwa, na ɗago idona na dube shi naga ya kafeni da ido da irin kallon da ban taɓa ganin ya min shi ba a ƙwayar idonsa. kallon daya haifar da jin wani abu ajikina, ba shiri na haɗiye guntun yawun dake maƙogorona na haƙura da jin ba’asin dalilin daya sa zan goge fuskana, kuma ban fahimci dalilin hakan ba sai dana ɗora Handky ɗin ina goge fuskar, ashe a bushe ta ke, bushewar ruwan hawayen da nake zubarwa tun tasowarmu daga Qatar har saukarmu ƙasar nan. “amsar guda ɗaya ce, ƙanwa! daga wannan matsayin so na ƙanwa, daga wannan matsayin karki yarda ki baiwa wani abu me tasiri damar shiga cikin kanki ya sauya tunaninki”. tabbas banda kallonsa nake a sanda yake maganar, zan rantse da Allah ba Ya Amadu ne yay maganar ba, saboda yanda bakinsa yake a gimtse, haka kuma laɓɓansa basu motsa ba, kuma yanda yay maganar kamar bada ni yake ba, dan idonsa sam ba’a kaina yake ba, yana kallon wani wuri na dabanne, sai dai saɓanin tunanin cewar hankalinsa ma ba’a kaina yake ba yasha banban a sanda na kusa zamewa daga kan kujera zan faɗi yay saurin saka ƙafarsa ya riƙe kujerar da kuma hannunsa guda wajen riƙoni. na rufe idona sai dai kamin na buɗe har ya bar kusa da gadon, sai kawai nabi bayansa da kallo a sanda yake daf da fita daga room ɗin, da tarin wasu abubuwa fal da ban san ma’anarsu ba a cikin kaina. bayan fitarsa na kasa hana hannuna daga riƙo na Ya Kabiru da yake ta sonyi tun ɗazu, ɗumin tafin hannuna da nasa suka haɗe, na lumshe ido tare da jinginar da kaina ga gefen ƙarfen gadon, tunani nake, tunanin da ban san na mene ba, har zuwa sanda idona ya kai kan jakar Mami na ɗauko na zuge zip ɗin na zaro tab ɗinta. da security ajiki, kuma duk abinda yazo kaina idan nasa sai taƙi buɗewa, haka na tsurawa hoton Ummi dake kan screen ɗin wayar tata ido ina kallo, tunanin saka sunana a password ɗin yazo kaina duk da banda tabbacin zata iya sakawar, dan gani nake Mami tafi son Alhassan akaina, ni kawai dai na amsa sunan ƴane a wurinta, amma banda wani matsayi a zuciyarta, amma kuma ko dana saka har sunan Alhassan ɗin bai buɗe ba, hakan kuma yasa ni mamaki, sai dai mamakin daya haska cikin ƙwayar idona da cikin kaina a yanzu yafi na lokacin dana saka sunan Alhassan yaƙi buɗewa, _Maryam. ina rubuta sunana wayar ta buɗe, kuma da buɗewarta hoton jarirai biyu ya bayyana akan wallpeper, hoton dana tabbatar da mune time ɗin da muna jarirai, dan haka ban san lokacin da na kai hannu ina shafa hoton ba tare da haɗewar saukar murmushi a fuskata. ƙaunar Mamina, Soyayyar Mamina, Bigen mahaifiyata, wannan Mahaifiyar, Uwa, Uwata da ta ɗauki cikina tsawon wata tara tana rainonsa, ta kuma haifeni bayan mawuyaciyar naƙudar da Allah kaɗai yasan adadin azabar dake cikinta, wadda ita kaɗai ce zata ƙaunace ni, ƙauna ta haƙiƙa a duk yanda nake, da duk yanda na kasance.

5:00am.
ƙarfe biyar ɗin asuba agogo ya buga a washegarin abinda ya faru, kuma kaɗawar agogon ta haɗe da buɗe idon Kabir a wannan lokacin, ya shiga wurga idanuwansa da sukai masa nauyi akan kowanne bango na ɗakin, inda ganin nasa ya tabbatar masa da cewar a asibiti yake, kuma kwance akan gadon asibiti, sai ya maida murfin idon ya rufe na sakan ɗaya sannan ya kuma buɗewa ya saukesu a saman ɗakin.
Yagana dake zaune bisa darduma a wannan lokacin tana lazimi, wadda ta kafa ta tsare da jiran farkawarsa, dan ko bacci bata iya yi ba, kwana tai tana roƙarwa Kabiru sauƙi a wurin Allah, haka kuma zuciyarta bata bar taraddadin farkawar tasa ba, dan ita gani ma ta ke kamar ko likitocin ƙarya sukai musu an ɓoye musu ne amma Kabiru ya mutu, shi yasa ko a daren jiyan da akai-akai taje gida Amadu zai kwana da shi taƙi yarda ta tafi, domin tana ganin kamar sai da safe ne za’ace ma ta harma an kaishi ƙabarinsa.
tun buɗewar idanuwansa na farko idonta ya kai kansa, kuma sai taga abin kamar a mafarki saboda haka ne batai magana ba sai a yanzu da ta kalla ya buɗesu tangararau ya zubesu a sama, a lokacin ta ƙarashe laziminta da faɗin,”Alhamdulillah”. sannan ta yunƙura ta miƙe tana kiran sunan nasa,”Kabiru ka farka.” ya juyar da ƙwayar idonsa zuwa kanta sannan ya ɗaga ma ta kai. sai tai murmushi tana saka hannu ta shafa sumar kansa.
“Yagana tsautsayi ne amma ban bige shi da gangan ba, nayi iyakar yina wajen ganin na kauce masa amma sai ya dinƙa ƙara shiga gabana…ina fatan bai mutu ba Yagana, bana so zunubin kisa ya hau kaina, ban san wane shi ba, amma jikina ya bani dama ya shiryawa faruwar hatsarin namu”. Muryarsa ta fito a hankali yana kallonta, kuma muryar ta fito da ƙoƙarin dawo da ita cikin hayyacinta daga tunanin wacca tai silar faruwar hatsarin nasa.
jin shirun amsarsa daga bakinta lokaci guda jikinsa yay sanyi, daga yanzu kuma wannan lokacin ya ɗaura niyyar azumin kaffara. “babur ɗin shima ya mutu ko kuma ya tsira?, na Anas ne na ara ya kuma jadadda min kar wani abu ya taɓa lafiyar machine ɗinsa”. Yagana ta sauke numfashi kamin tace,”daga wanda ya bigeka har machine ɗin suna lafiya babu wanda ya mutu acikinsu, Anas ɗinma ya karɓi babur ɗin nasa daya zo dubaka, shi kuma wanda ya bugeka yana can a hannun hukuma.”
nan ta ke ya sauke wata ajiyar zuciya ta farinciki, ba murnar tsiran babur ɗin ba, murnar tsiran rai ne, dan idan babur ne yana da kuɗin biyan sabo bama gyara ba.
“Maryam fa?”. wannan karan muryar tasa ta fito ne da wani irin amo da ita Kanta Yagana ta kasa tantanceta, kuma sautin muryar daya fito a hankali ta cikin shirun ɗakin shi ya farkar dani daga baccin da nake, kuma acikin tunanina na ƙoƙarin tantance inda na jiyo kiran sunan, aciki ne na tsinci maganar Yagana na cewa.
“ta dawo, sunzo tare da mahaifiyarta ta ainihi”. da mamakin Yagana sai ta kalla yay murmushi haɗe da cewar. “na san komai Yagana, babu abinda Akila ta ɓoye min dangane da ita, tun a lokacin da tasa ni yi ma ta bincike ta gama buɗe min cikinta…ina Maryam ɗin?”. ya ƙara tambaya a karo na biyu, kuma kafin Yagana tace wani abu na taso daga inda nake, ina takowa kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki, irin takun tafiyar marasa gaskiya, irin takun tafiyar wadda ke tsoron amsar ɗanyan hukunci, kuma a lokacin dana ƙaraso bakin gadon, zan iya kiran kallo ɗayan da yay min da kallon tsautsayi, dan bada niyya yay ba, yay kallon ne bisa rashin sanin cewar ƙwayar idonsa zata sauka akaina ne.
“Ya Kabiru sannu”. na faɗa muryarta na fitowa a hankali, da kuma rawar jikin da ban san ta mece ba, kuma sai naji sam babu daɗi da rashin amsa mini ɗin da yay, shin bai san a halin da nake ciki ba ne akan ciwon nasa? da har zai nuna halin ko in kula akaina, banfa iya bacci ba sai da Yagana tasa nurse ta min allurar bacci ta dole, amma har sanda aka min allurar ina zaune a gefensa, gefen wannan hannun nasa da nawa ke riƙe da shi da ban san lokacin da aka rabani da shi ba.
“naga kamar ruwan ya ƙare, ki cire masa tunda likita ya nuna miki yanda za kiyi ɗazu”. Yagana ta faɗa a sanda ta juya tana faɗin,”Allah baka lafiya ya kuma bi maka hakkinka Kabiru, ba kai kaɗai ba dukanmu sai Allah yay mana sakayya tsakaninmu da waccan algunhumar matar Amarya, ƴar banza me kama da ƴaƴan birinya, tsinanna makirar mace, zamanta dai acikinmu kam ya ƙare, ƙwarai ta shammacemu kuma ta ɓata wayonta. wallah da muka je naso ofishin ƴan sanda nan naso an bani kulki na mummuƙawa ƴar banza a kafaɗa… kai bari nayi sallah naji masallaci na tayarwa”.
na zagaya ta gefen inda aka saka masa ruwan, sai dai sam na kasa zare masa allurar da jininsa ya fara biyowa ta ciki kasantuwar ruwan drip ɗin ya ƙare, ba wai dan ba zan iya cirewar ba ne, a’a sai dan kawai ina jin ba zan iya cire masa ba, kaman zanji masa rauni ne, kuma bana so yaji zafin cirewar.
ganin jinin na ƙara fita da yawa na kai hannuna dake rawa kan butterfly ɗin, kuma kamin na kai ga ɗaga bandage ɗin sai naji ya riƙe hannuna ya ɗauke daga kai, ya juyo ya zare da kansa. sannan ya yunƙura zai miƙe daga kan gadon ya sauka ƙasa, sai nai saurin dawowa ta gaban nasa ina dakatar da shi cikin saurin muryar da ban taɓa yi ba wajen faɗin,”Ya Kabiru ƙafarka akwai ciwo, Dr yace karka taka”. gaba ɗaya a wani kiɗime nayi maganar ina riƙe ƙafafun nasa na maida kan gadon.
ban kalle shi ba, amma a jikina nake jin irin kallon da yake bina da shi, kuma a wannan durƙusawar da nai sai naji ƙafafuna kamar an riƙe su, sam na kasa ɗagowa, sai kaina dake kallon ƙasan tiles ɗin, idona na zubar da hawayen da ban san dalilin zubarsu ba, abu guda da na sa ni shine ba zan taɓa yafewa kaina ba idan har na zama silar wanzar da ɓacin rai akan wannan fuskar ta Ya Kabiru.
wucewar kusan rabin sa’a kafin maganar Yagana ta haifar da kuzarin da ya gushe min lokaci baya kaɗan.
“ke ba kya sallah ne?”. sai dana saka hannu na goge hawayen fuskata kan nace ma ta. “zanyi Yagana.” tukunna miƙe na shiga banɗaki dan yin alwala.
ƙarfe goma saura su Ummi suka zo, kamin shigowarsu drivern Mami ne ya fara shigowa da manyan basket guda biyu kowanne shaƙe da manyan coolers na abinci, sannan Alhassan ya mara masa baya shima hannunsa riƙe da madaidaicin kwandon kaba da tarin fruites aciki. daga baya kuma saiga Mami da Ummi sun shigo, na miƙe da saurina naje na rungume Mamina ina ma ta sannu da zuwa, sai Ummi ta tsaya tana kallona a sanda ta harɗe hannayent tana jinjina kai, sai naji nauyinta ya kamani dan haka na sa ki Mami na tafi gareta ina murmushin dake bayyanar da haƙorana gaba ɗaya na rungumeta itama.
“a’a Maryam ki dai nuna min wariyar launin fatar kawai, na yarda zan ɗauka a hakan, ai daɗin abinma ina da Alhassan bake ɗaya bace”. sai na ƙunshe fuskata ajikinta ina cewa,”to ai Ummi kece kika shigo daga baya, amma dake ne kika fara shigowa ke zan fara rungumewa kamin ita”. tana murmushin itama tace,”ba wani nan ni ban tsaru ba”. da haka muka kama hannun juna zuwa kujerar da zata zauna, na duƙa na gaisheta ita da Mami, Alhassan ɗin kuma dake hararata na murguɗa masa baki…Baba ma yace ai yaga alamar yanzu idona baya ganin kowa sai Mami kawai, dan yaga alama shima tun jiya na manta da shi, duk sai naji kunya ta kamani, dan cikinsu babu wanda ya faɗi ba dai-dai ba, yanzu hankalina gaba ɗaya na kan Mamina ne.
Alhassan ya yunƙuro zai ƙwalo min jarkar hannunsa akan murguɗa masa bakin da nai karaf idon Mami akansa tace,”ka buga ma ta sau ɗaya, ni kuma naita buga maka har sai kanka ya zama ƙwalele”. gaba ɗaya akasa dariya har da Ya Kabiru dake amsar magani daga hannun Yagana. dariyar tasa kuma tasa ni jin daɗi, daɗin da har saida na motsa laɓɓana, sai dai kuma jikina yay sanyi sanda muka haɗa ido da shi naga ya ɗaure fuska.
karo na huɗu kenan tun daga farkawarsa, idan na gama fahimta a yanzu Ya Kabiru sam bai son ganina, fushi yake da ni, to laifin me na masa?, tambayar da bani da amsarta, kuma nai ƙoƙarin na sameta tun sanda ya zamana daga ni sai shi a ɗakin amma yaƙi bani dama, lokacin nan da Yagana ta fita nace masa. “Ya Kabiru inata maka sannu baka amsa ba”. bai responding nawa ba har sai dana tambaye shi sau uku tukunna yace da ni,”sannu indai daga bakinki ne bana sonta, ba sannunki kaɗai ba, ganinki ma ba so nake ba”. furucin nasa kuma daya sani a damuwa ya ɗaga hankalina a lokaci ɗaya.
“ki tashi kuje gida ki wanka, zuwa anjima sai ku dawo bayan kun huta”. maganar Ummi ta dawo dani daga duniyar tunani, nace da ita,”Ummi ni ba sai naje ba, Yaganan dai ta tafi”. “haka za ki zauna kina tsami da warin asibiti?”. sai Mami tace,”barta zuwa anjima ma tafi tare, zanje ganin gwamna nan da 12″. Ummi tai knodding kanta kawai tana ci gaba da karanta takardar da suka amso daga wurin likita akan ciwon Ya Kabiru. kuma barin kallona da zanyi daga kanta muka haɗa ido da Mami wacce ke magana a wayar dake kare a kunnenta, tai min nuni da cinyarta na tafi na zauna akai kaman yanda ta buƙata, zaman nawa ya zama lokaci ɗaya da gama wayartata, sannan tasa hannu ta juyo da fuskata tana goge min wani abu da ban san mene shi ba, a yayinda a gefe guda gangar jikina da ruhina ke daɗa tsargawa da so da ƙaunar mahaifiyata.
“dilla tashi, sai kin karya ma ta ƙafa”. Alhassan yay maganar cikin ɗagowa kaman zai fizgoni, na turo bakina gaba kamin nace wani abu Mami ta rigani da cewar,”sai kasa ta tashi dole tunda ƙafar taka ce”. ban san lokacin da dariyar ta suɓuce min ba ina kallonsa tare da haɗa masa da gwalo.
Mami kuma tace,”gyara zamanki da kyau Autata, cinya taki ce bats kowa ba”.
Yagana dake yafa mayafi zasu tafi ta taɓe baki da cewar,”goɗe goɗe dake akan cinya ko kunya”. nace,”Yagana bafa a taki na zauna ba”. “yo kice ma za ki zauna akan tawa ki gani”. sai kuma ta juya kan Mami da cewa,”wannan ƴa taki dai ba halin ƙwarai gareta ba, dan haka karki nuna ma ta son da zaisa ta sangarce, wahala za ki sha wurin taƙwarata, ko da yake anan dai albasa tayi halin ruwa”. na kalli Yagana na ɓalla ma ta harara saboda jin haushin maganarta ta ƙarshe, sai ta murmusa kunci da cewa,”Allah na kaɗai nake tsoro, dan haka Maryama dai-dai nake da hararki wallahi, ni Rakiya ba, da ni kike zancen, ai akwai ranar ƙin dillanci”. harar tata dai na kuma yi bance ma ta komai, suna gabanin fita a ɗakin tace da Ya Kabiru,”kai kuma Malami ka daure ka zama namiji ka tashi haka, ni ba zai yiwu na dinga zaman jinyar asibiti ba, jiya haka naita faman tsartar da yawu kamar wata me ƙaramin ciki. saboda haka ka warware dan tafiyar nan tawa daka ga nayi ba zan dawo ba, iyakaci nake maka aiken sannu…idan kuma na biya Amarya tazo tai jinyarka ne to?.” ta ƙarasa zancen nata tana ƙunshe dariyar dake neman fitowa, shi kuma yace,”indai kin shirya yin takaba ki aikota ai ba wani matsala bace Hajiya Yagana”. sai ta dawo daga baya tana cewa,”au kai na manta ban faɗa maka ba, wannan ja’irar yarinyar ta min alƙawarin kujerar makkah fa, ka ma ta godiya idan ka gama ciwon bakin akanta.”
da haka ta juya ta fita, har ta fita kuma ta dawo tambayar yace ko dai shi direban ba irinsu Mami bane shima baya jin hausa, dan indai shima irinsu ne to gwara a haɗata da dutse ta tafi ta san ta tafi da wanda bai san me ta ke ba da hujjah.
Ya Amadu dake tsaye ya girgiza kai da cewa,”muje dan Allah karki cika mutane da magana”. “ah toh Amadu idan ba za ka iya da maganar tawa ba ka toshe kunnenka mana ina dalili anan, haka kawai Allah ya tsagan baki kace ba zanyi magana ba…ni dai wannan hali naka na ba ni takaici, banda cuta ce da ba’a ƙaunarta ai sai nace dama kaine a maimakon Kabirun, haba sai kake takura min kamar wani Babana”.
shi dai tafiyarsa yay ya barta a wurin, bayan yace da Alhassan ya taso su tafi tare, kuma Alhassan ɗin na zuwa wucewa ta gabanta ta riƙo rigarsa da cewar,”kai zagalo tsaya, Allah ya sa ni wannan tsayin naka tsoro yake bani, bari nai gaba sai ka biyoni a baya”. daga ƙarshe dai gaba ɗaya harni akai tafiyar.
kuma abinda bamu sa ni ba da ni da Yagana da Ya Kabiru dake kwance, shine, Mami ta saya mana sabon gida anan Saye ɓangaren masu kuɗin anguwar, ashe tun bayan saukarmu a ƙasar tasa aka nema ma ta gidan, kuma abinda ta bari su Baba suka kwasa a tsohon gidanmu ƙalilan ne duka ƴan abinda ba’a rasa bane da suka zama na amfanin dole.
gidan flat ne me kyau da part daban daban, dan ɓangaren su Inna Zulai daban, na Baba daban, ni da Yagana a ɓangare ɗaya, sai mazan gidan ma aka haɗasu ɓangare ɗaya kowa da ɗakinsa, Ya Kabiru da Ya Amadu kawai part nasu daban daban, tsohon gidan kuma tasa an bige shi ana gyarawa tace Baba sai ya zuba ƴan haya aciki.
duk wannan bayanin sai a yanzu da muka taho Ya Amadu ke bamu shi, adu’a da sa albarka kuwa da Yagana keyi ma ba zai faɗu ba, dan tun kamin mu ƙarasa gida tace da Alhassan,”kai Zagalo kira min gyatumarka na ma ta godiya”. shi da bai san me tace ba sai ni na amsa wayar na kira ma ta ita.
kuma nima sai da muka ƙara gidan na shiga godewa Mamina a sanda naga haɗaɗɗan ɗakina da yanda aka ƙawata shi, komai anyi shi da favorite colour ena white and blue, ɗakina na kallon na Basma sai na Yagana dake daga can ɓangrenmu, tamfatsetsen parlonmu kuwa ba’a magana.
dan haka ina fitowa daga wanka na baje akan lafiyayyan gadona dan huta gajiya, sanyin Ac sai ratsani yake. kuma maimakom baccin da nake saka ran zanyi sai na kasa, wani tunanin na daban ya shiga cikin kwanyata, tunanin dake neman hargitsa min lissafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button