SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Afuwan Masoyana, shirun da kuka ji bada gangan bane, da dalili me ƙarfi ne, ina rubuta exams sai a yau na sami interval, hakan yasa nace bari na nishaɗantar daku da wannan…insha’Allahu acikin hutun interval ɗin dana samu zaku ci gaba da jina har sau uku, kamin na kammala kuma kana muci gaba da gashi…amma kamin nan ina barar adu’arku daga baku nanku masu albarka akan samun nasa akan wannan jarabawar tawa.
Binti idris traditional herbal medicine and more
Sanyi mugun ciwo ne sanyi shine babbar cutar da take taka rawa wajen raba ma’aurata ta hana su suku da jin dadi yar uwata kada ki tsaya kunya ki tashi ki nemi magani domin babu cutar da ubangiji ya saukar be saukar mata da maganin ta dan haka ni Bint idris ibn Abdulwahab
Nake Kira gare ku yan uwana mata da maza kuyi maza ku garzayo ku nema wa kanku lafiya ga masu neman karin bayani sai su tuntube ni ta wanan number Kira ko WhatsApp 07066959285
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
INA MASU FAMA DA DATTIN MARA KO AMOSANIN MARA WLH GA QAQQARFAN MAGANIN WANKIN MARAR MACE KO NAMIJI
DA KASHE DUK WANI SANYIN DAKE MARAR MACE KO NAMIJI
1* QURAJEN GABA
2* ‘DA’DEWAR GABA
3* SA’BAR GABA
4* QAYQAYIN GABA
5* WARIN GABA
6* RASHIN SHA’AWA
7* RASHIN NI’IMA
8* YAWAN’BARIN CIKI
9* JIN ZAFI LOKACHIN SADUWA
10* RASHIN JIN DADI YAYIN SADUWA
11* Tsinkewar maniyyi rashin haihuwa
12*ciwan jiki kai kayin jiki
13yawan ciwan kai
Da dai sauran su
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Maza ku garzayu kuzo ku nemi naku maganin a farashi mai sauki munyi ragi kasu talatin cikin Dari na kayan mu kada ku sake wanan garabasar ta wuce ku yan uwa ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Comment&Share.
SIRRIN ƁOYE
By Oum Ramadhan✍????
11)
Area 4, House NO2, Asokoro District, Abuja.
Gida ne na gani na faɗa wanda aka narka dukiya a wajen gininsa, tun daga waje kana iya ganin Ƙaton balcony dake fuskantar gate ɗin gidan, dogon namiji ne me cikar zati yana tsaye ne daga cikinsa da irin tsayuwa ta jaruman sojoji ya sarƙe hannayensa ta baya, jikinsa sanye da t-shirt irin ta kakin soja haɗe da baƙin wando jeans, sumar kansa ba wata mai yawa bace sai dai irin askin dake sumar aski ne bana musulmi ba, idanunsa kewaye da siririn medical glass. Farin dattijo ne kyakykyawa me kimanin shekaru 56-57, a irin tsayuwar da yay zaka ce ko an dasa shi ne a wurin, hancinsa ne kawai ke fitar da numfashi sai ƙwayar idonsa dake kan get ɗin da yake fuskanta, a kallo ɗaya zaka yi masa ka gane yayi nisa acikin zurfin tunani. Har tsawon wucewar wasu mintuna bai motsa ba, sai a sanda me gadi ya tashi ya zuge gate ɗin da ake dannawa hon da ƙarfi, sai bayan da farar motar ta nauso ciki sannan ya haɗe murfin idanunsa ya buɗe kana yabi motar da ido har zuwa wurin da aka tanada na ajiye motaci tayi fakin. Mahaifiyarsa Madam Merry tare da Matarsa Madam Gloria suka fito daga bayan motar kowannensu hannunsa riƙe da jaka da alama daga wajen wani taron suke, bayan wucewarsu ne ɗansa Joseph wanda shi yay tuƙin ya fito daga mazaunin driver shi kuma hannunsa riƙe da jarida, yayi tattaki me ɗan nisa sannan ya tsaya yana nazari, sai ya juya ya koma motar ya jefa jaridar aciki, duk abunda yake idon mahaifinsa na kansa wanda ya fahimci dalilin da yasa ya maida jaridar mota, hakan ne yasa shi ɗan murmusa kuncinsa kamin ya daɗa lumshe ido ya buɗe.
Madam Gloria ta ɗauki tsawon daƙiƙa 2 tsaye a bayansa amma sam bai san da zuwanta wurin ba, hakan yasa ta ƙara yin tattaki zuwa gabansa ta tsaya, anan ta fuskanci da gasken bai san da zuwanta ba, domin kuwa kansa a ƙasa yake idanuwansa a rufe. Tayi wani ɗan guntun tsaki na ɓacin rai sannan ta ƙara matsowa kusa da shi sosai ta ɗora hannu ɗaya saman ƙirjinsa, ta ranƙwafo da fuskarta saitin tasa, acikin harshen turanci tace da shi, “Me ya sami Jarumina?, ni ce ko kuma wani ne daga waje?”. A yanzu ne yasan da zuwanta wurin hakan yasa shi buɗe ido yana dubanta, gaba ɗaya ya ɗago kai lokaci ɗaya kuma cikin zafin nama yay wurgi da jaridar dake hannunsa ta baya nan ta sauka a saman fuskar Joseph dake shigowa, Joseph yasa hannu ya dafe jaridar a fuskarsa kamin ta kai ga faɗuwa ƙasa, tsoron abunda ka iya haifuwa yasa Madam Gloria saurin ja da baya, ta maida kallonta ga Joseph dake tsaye suka haɗa ido yay mata alama da meke faruwa, ta ɗaga masa kafaɗa na cewar bata sani ba itama. Ta marairaice fuska tayi ƙasa da murya cikin nuna damuwa ta sake cewa, “Oh Jesus Crise, Daddyn Emanuel me yayi zafi haka?, ko wani abu ka gani a jaridar daya ɓata maka rai?”. Zuciyarsa na tafarfasa ya dubeta cikin ƙarajin murya yace da ita,”wai shin har sai zuwa yaushe ne ƙasarmu zata gyaru ne?, sai yaushe shuwagabanni zasu gane al’umma amana ne a hannunsu?, har sai yaushe zasu yi hani da aikata ta’addanci?, har tsawon wane lokaci za’a ɗauka kamin gwamnati ta fara martaba jami’an tsaro?, me yasa shuwagabanninmu basa tsoron Allah?”. Muryarsa ta fita acikin turancin daya banbanta dana Matarsa, yaja doguwar ajiyar zuciya sannan ya juya yay tattaki zuwa inda kujera take ya zauna, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana girgiza su. Madam Gloria ta ƙarasa inda yake itama ta zauna a kujerar dake kusa da shi, sannan tace da Joseph ya bata jaridar, ya miƙa mata jaridar, ya fita babu jimawa ya dawo hannunsa riƙe da glass cup da kuma kwalin exotic na pineapple, yaja ƙaramin glass table zuwa gaban mahaifinsa ya tsiyaya lemu aciki sannan ya ajiye, Dad yay masa kallo ɗaya sannan ya miƙa hannu ya ɗauki lemun yasha, ya kuma matse kofin kamar zai fasa shi. Madam Gloria data gama karanta jaridar ta taɓe baki tana duban mijin nata tace,”sai kuma me?, wanne abu ne aciki daya shafeka da har zai saka damuwa irin haka?”. Sai kuma taja tsaki ta ƙara cewa,”kayan haushinka yana da yawa, before duk ka ɗaga hankalina, nayi tunanin wata matsala babba ce, kawai sai kake ɗora damuwa akan mutanen da ba addininku ɗaya ba, if ace there are all chritians shine sai ka ɗaga hankali irin haka”. Ya kalleta yace,”baki gane rubutun dake ciki bane?”. “na gane mana, ba magana bane akan kidnapping da akayi, to kai mene naka aciki?, akwai ɗanka ne ko kuma ɗan’uwanka?, ko kuma ance maka dani akayi garkuwa ko kuma Mama?”. “take a look!”. Ya faɗi hakan yayin da yake ɗaga mata hannu da dakatarwa Kansa a ƙasa, sannan ya ɗago ya dubeta da jinjinawa rashin tausayi irin nata yace, “Addininmu bai ce muso namu ba, muƙi wanda ba namu ba…to bari kiji, da har yanzu ina kan matsayina na Major General na rantse miki da saina sadaukar da raina wajen ƙwato mutanen nan…ki kwatantawa kanki idan wani naki akai garkuwa da shi ya zakiyi? Ko da ace kuwa kina da kuɗaɗen amso shi, haka abun yake ga ahalin waɗan nan bayin Allah, suna nan hankalinsu ba’a kwance ba…saboda haka ni na ɗaukarwa kaina alƙawarin fidda dukiyar da Allah ya bani wajen ganin na ƙwato su”. Yana kai nan ya kwashi wayoyinsa ya fice ya barsu a wurin, mahaifiyarsa dake hayowa saman benen ta bishi da ido har sanda ya shige ɗakinsa ya banko ƙofa garamm, ta girgiza kai sannan itama ta wuce balcony inda ta sami Madam Gloria tayi jugum, Joseph kuma na gefenta yana maganar cewar, “Mom ki dinga shiru da bakinki akan nuna tribalism a gaban Dad tunda baya so, hakan shine kwanciyar hankalinki dana kowa ma acikin gidan nan…eventhough nima ba wai son muslims nake ba, amma a ɓangaren kidnapping ina tausayin kowa musamman ace mata ne akayi garkuwan dasu”. Cikin fusata ta kai hannu ta bugi bakinsa, hakan yasa shi tsuke baki yay shiru yana aikin sosa wurin. Madam Merry wadda ke tsaye daga bakin ƙofa tana kallon Joseph tace, “tashi anan wurin”. Ya taso ya tsaya a gabanta ita kuma ta kama hannunsa, sannan ta fara magana da Madam Gloria, “wannan ya zama karo na ƙarshe da zaki ƙara saka hannunki ga jikokina, na jima ina faɗa miki hakan da kike babban kuskure ne, ina tsananin son jikokina bana son abunda zai wanzar musu da ɓacin rai ko kuma abunda zai taɓa lafiyarsu”. Madam Gloria ta ɗago kai tana duban sirikar tata tace, “Ma! Yanzu baki duba yanayin damuwar da nake ciki ba sai ɗan dukan da naima jikanki…ke kenan duk sanda ɗanki ya ƙunsa min kema sai kin ƙunsa min, shikenan ai”. Ta ƙarashe maganar tana tasowa ta wuce ta gabansu har tana bangaje Joseph. Ya kalli Kakarsa da damuwa yace,”Granny…”. Bai faɗi abunda zaice ba tasa yatsa a leɓensa, “Shhhh dont stress your self kaji…indai akan banbancin addini ne Mominka ba zata taɓa sauyawa ba, saboda haka kaima kake daina zuwar mata da zancen daya danganci hakan”. Ya ɗaga mata kai, suka maida hankali kan Kukun gida dake sanar musu cewar Lunch is ready. Nan suka sauka ƙasa inda suka wuce dining section, har tsawon wucewar rabin awa Dad da Mom basu fito ba, dan haka saisu uku suka yi lunch ɗin, suna kammalawa kuma Joseph da Obi suka fita ɗauko Yayansu Emanuel a airpot wanda jirginsu zai sauka da ƙarfe huɗu.