NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE


A ɓangaren Dad kuwa zaune yake bakin gado, yana shafa kamfutar dake gabansa, wayarsa dake gefe tayi ƙara, ya miƙa hannu ya ɗauka ba tare daya duba me sunan me kiran ba, sai daya kara a kunne daga can ɓangaren aka kira sunansa da, “Major naga kiranka ina bakin aiki shi yasa ban ɗaga ba”. Jin muryar amininsa ne yasa shi dakatawa da shafa kamfutar da yake sannan yace, “yayi kyau, nayi tsammanin ma ko kana gida kana hutawa ne”. Daga can ɓangaren Major Josiah yace da shi, “ina babu hutu ai, yanzu haka fitowarmu babu jimawa daga meeting da President”. Dad ya sauke numfashi yace, “Kuna sane kuwa da garkuwar da akayi ta mutanen dake kan hanyarsu ta zuwa zamfara state?”. Josiah yace,”ƙwarai mun sani”. “to amma kuma babu wani mataki da zaku ɗauka akan hakan kenan?”. Daga ɓangaren Josiah shima nunfashin ya sauke sannan yace,”bamu da ikon ɗaukan wani mataki, saboda ko a yanzu da aka zauna meeting na miƙa wannan issue ɗin, amma shugaban ƙasa yace bai yarda da mukai farmaki wurin ba…hasalima duk wata magana da muke kawowa akan bada tsaro ga ƙasa sai ya daƙile hakan”. “to amma zaman naku akan menene kuka yi?”. “akan basu tsaro ne iyaka yasu bada sauran al’umma ba”. Cike da takaici Dad ya girgiza kai sannan yace,”Allah ya kyauta…yanzu abunda nake so da kai Emanuel zai dawo yau, shine ina so a haɗa shi da gwarazan securities da zasu raka shi amso mutanen da akayi garkuwa dasu”. Josiah yace,”babu matsala, we will talk letter yanzu zan shiga office ne”. Daga haka sukayi sallama. Dad yaci gaba da scrolling ɗin hotunan waɗanda akayi garkuwa dasu ta cikin kamfutar, mata sunfi maza yawa, sai dai abunda ko da yaushe yake ɗaure masa kai shine me yasa ba’a garkuwa da christians sai musulmai?.
Da dukkan hannunsa biyu ya shafi sumar kansa tare da kwanciya saman gadon fuskarsa na fuskantar POP…ya lumshe ido yayin da hoton wata rayuwa can baya ta shiga haskawa acikin idonsa.

Bichi.
“goben ƙarfe nawa zaka wuce?”. Baba ke maganar da Amadu wanda ke zaune a gefen mahaifin nasa. “jirgin ƙarfe bakwai zai tashi, saboda haka fitar asuba zanyi inda tsawancin kwana”. Baba ya jinjina Kai sannan ya kuma ce masa,”zaka yi kamar watanni nawa kamin ka leƙomu?”. “wallah ban sani ba Baba, a yanda nake so dai ace duk wata biyu zanke zuwa, to amma sai abunda ma’aikatar tace”. Baba ya numfasa kana yace,”shikenan Allah ubangiji yayi jagora, Allah ya tsare hanya…sai dai idan ka sauka bamu san taya zamu sani ba tunda ba waya a gidan”. Ya ɗago da kai ya dubi mahaifinsa cike da tausayawa, yana jin kamar ma yace ya fasa tafiyar, dan tun a ɗazu da suka taru suna masa nasiha sai duk jikinsa yayi sanyi, sai dai babu yanda zaiyi yasan hanyar arziƙi ce ke kiransa. “Baba karka damu dana sauka zan kira wayar Auwalu ɗan gidan Malam Ladan sai ya kawo muku, na faɗa masa zan dinga kiransa yana kawo muku har zuwa lokacin da Allah zaisa ai min albashi kuma na siya muku wayar, ga Lukman sai ya nuna muku yanda ake sarrafata duk da shima ba wayewa yayi akanta ba”.
Na buɗa baki nace,”tabɗi Ya Amadu Allah kam karka wani sa wannan mara mutuncin yaron ya dinƙa zuwar mana gida, gaskiya ƙwamma ba muyi wayar da kai ba indai haka ne, ranar nan fa ya gama zaginmu a waje wai ƴaƴan me faskaran ice”. Mu’azzam ya dokan tsawa da cewar, “dilla can rufewa mutane baki, manya na magana kina sako baki”. Na turo baki gaba nace,”Baba fa ya zaga”. Yana jifana da mugun kallo yace,”nace ki mana shiru ko, indai baki rama ba ai nasa uban ya zaga”. Inna Amarya tace, “rabu da ita dan yace Ƴaƴan Me faskare da ba ƴaƴan nasa bane”. Nace, “to ai Inna ba iyaka nan ya tsaya ba, ni dai sai dai idan bai shigo gidan nan ba Allah saina rotsa wayar tasa dan na tsane shi”. Ban ida rufe baki ba Inna ta gwaɓe min laɓɓana, zafi yasani sosa wajen ina yarfe hannu.
Gwaggona wadda ke zaune daga can ƙofar ɗakinta tace da Ya Amadu, “ni dai na faɗa maka, idan kaje ka ƙara riƙe addininka karka yi wasa da shi tunda kaga dai kai ɗaya ne musulmi acikinsu karsu dulmiyar da kai, kuma kayi taka tsan-tsan dasu domin basu da amana macuta ne, ni wallahi da ace na isa da kai Amadu wannan tafiyar ba zaka yi ta ba, hanyar arziƙi ai da yawa take, baka san ta inda Allah zai kuma ɓullo maka da wata ba…shawarata ka kula da mutuncin kanka”. Ya Amadu ya dubeta yana amsawa da, “insha’Allahu Gwaggo zanyi kamar yanda kika ce”. Inna Zulai tace,”tafiya ce dai tunda ni dana haife shi na amince to sai yayi ta, babu batun wani da kin isa, ko kin isa ɗin idan nace a’a wannan isar taki ba zatayi tasiri ba…saboda haka ni dai ki rabar min da ɗa da wannan maganganun naki na jafa’i da kike jifansa da su, Ba komai ne ke damunki ba sai baƙinciki da arziƙin daya same shi saboda ke Allah bai baki ɗa namijin da zai hidimta miki ba”. Cikin ɗaga murya Baba ya dakatar da maganarta, “Ke Zulai bana son shirmen banza, wannan wanne irin magana ce, Ke ko kunya ma ba kya ji a gaban ƴaƴanki kike wannan sokiburutsun, to ki rufe min baki tun kamin na saɓa miki, shashancin banza kawai, ke kin girma amma baki bar cin ƙasa ba”.
To haka dai Baba yay ta bawa Ya Amadu shawarwari da kuma nasihohi akan zaman da zaiyi idan yaje can, ya jima yana jaddada masa akan yayi ruƙo da gaskiya akan aikinsa, domin ita kaɗai ce zata bashi nasara a aikinsa ta kuma ɗaukaka shi harta ba shi kariya, shi kuma yana amsawa da insha’Allahu, muma ƙannensa duk muka bishi da adu’a, ni dai harda guntun hawayena alokacin da Ya Amadu ya miƙe zai wuce ɗakinsu, yake cewa mu yafe shi kuma muyi masa adu’a dan ba lallai mu gana ba gobe tunda daga masallaci zai wuce, sai naji kamar yana mana sallamar ban kwana ne ba zamu ƙara ganawa da shi ba.
Sai ƙarfe kusan goma sannan kowa ya wuce ɗaki dan kwanciya, har na kwanta naji shiru shiru Adawiyya bata shigo ba, na sauko daga kan gado zan fita, Inna dake sauya kaya tace ina zani, nace mata,”naga Adawiyya bata shigo bane”. tace min, “ki ƙyaƙeta kawai ba lallai uwarta yau ta barta kwana nan ba”. Nace,”a’a bari dai naje na gani, dan naji tace min kanta na ciwo ɗazu”.
Da sallama na ɗaga labulen ɗakinsu, Inna Zulai na zaune tana jina amma bata amsa min ba, na shiga daga ciki ina cewa, “Inna ina Adawiyya?”. Ta ɗago ta kalleni da masifarta tace,”uwar me zaki yi mata da wannan daren, yarinya sai shegen kinibibi irin na uwarta”. Lallai ayau na tabbatar da cewar wani na cin darajar wani, banda haka tun a furucinta kan Gwaggona a ɗazu naso na yaɓa mata magana ba ruwana da girmanta, to sai taci darajar mahaifina da kuma ɗanta daya maida uwata tamkar ita tayi naƙudarsa. “Inna naji tace ne kanta nna ciwo shine nazo dubata”. Cikin ɗaga murya ta kuma cewa dani, “to da kika zo nan lafiyar zaki bata ne uwar iyayi, to lafiyarta ƙalau kwana ne dai na haramta mata shi a ɗakinku, tun itama baku asirce min ita ba kamar Amadu, saboda haka zoki fice min a ɗaki kamin ranki ya ɓaci, idan ma barbaɗe aka turoki yi aniyarku ta biku”. Ni dai ganin haukarta na daɗa yin yawa na bar gabanta na wuce wajen shimfiɗarsu Sadiya, tabbas akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanina da Adawiyya, duk da cewar sun rufe kawunansu da zanen rufa hakan baisa na kasa ganeta ba, na yaye zanen daga saman kanta, haka kawai na saki murmushi saboda kallon fuskarta da nayi, nasa hannu na taɓa goshinta naji sanyi ƙalau, sai naji daɗi a raina kenan ta rabu da ciwon kan.
A hankali na shiga tashinta ina kiran sunanta, sai da aka daɗe sannan ta amsa min, na kamo tafin hannunta nasa a nawa na riƙe, na kai bakina saitin kunnenta nace,”tashi mu tafi ɗakinmu”. Daga irin yanda take motsa idonta nasan cewar ba bacci take ba tana jina. Nasa hannu ina girgizata da salon wasa, cikin hargowa tace dani,”dilla Malama ni ki ƙyaleni”. Sai na ɗanyi dariya na daɗa girgizata ina cewa, “to ki tashi mu tafi saina ƙyaleki, ai kan naki ya daina ciwo, kin san dai ba zan iya bacci ba kya kusa dani ba”. Taja tsaki ta juya kwanciyarta tana cewa, “Ni dama ba wani ciwon kai da nake…kuma idan baki kwana tare dani ba ki mutu, kinga ma wallahi idan baki rabu dani ba zan tashi na shaƙeki har sai kin bar numfashi, ko lallai ne saina kwana a ɗakin uwar kareren naki”. Sosai naji ba daɗin kalamanta, na saki baki ina duban gefen fuskarta da mamaki, ban san me nayi mata ba yau, dan tun bayan dawowarmu daga masarautar bichi ta sauya min, ko magana nayi mata bata amsa min sai dai tayi ta jan tsaki, dana lura da wannan ne ma na tambayeta menene tace min kanta ke ciwo, ashe ba hakan bane, to ko dai nayi mata wani laifin ban sani ba?, tun tasowarmu wani abu bai taɓa shiga tsakaninmu ba akan rigima, dan faɗanmu ma na wasa ne, ko abinci ɗazu ma da aka zuba mana raba mana tayi kowa yaci nasa, bayan bamu taɓa cin abinci daban ni da ita ba, ko da an zuba mana idan ɗaya baya nan to sai ɗaya ya jira ɗaya, dalilin da yasa ma Baba wani lokacin ka kiramu da tagwaye. Na kuma kamo hannunta nace, “Adawiyya wani abun nayi miki?”. Sai ta fizge taja tsaki tana daɗa rufe kanta da zane, na miƙe na fita jiki a saɓule, Inna Zulai ma da nake mata saida safe ci kanki bata ce min ba.
Shigata ɗakin Inna tace, “kije Gwaggonki na kiranki, idan kin dawo karki manta ki rufe mana ƙofa bacci zai iya ɗaukeni kamin ki dawo”. Na amsa da to sannan na nufa ɗakin Gwaggona, ina shiga na tarar da ita ta gama wanke allo, na zauna gefanta kamar mara lafiya, zuciyata cike fal da tunanin laifin da nayiwa Adawiyya wanda ban san shi ba. Bayan Gwaggo ta gama bawa Basma rubutu sannan nima ta miƙo min sai aikin kauda fuskarta take daga gareni, na miƙa hannu na amsa nayi bismillah sannan na kafa baki na sha kaɗan, ina ajiyewa ta jefeni da wawan kallo, “ɗauki ki ƙarasa shanye shi”. Ba shiri na ɗauka na rumtse ido kace maɗaci aka bani, ina kuma shanyewa kawai saina fashe da kuka ina kifa kai da gwiwa. “me aka yi miki kuma?, idan har akan rubutun nanne to kuwa tabbas yau zan fara sa miki waya ajiki”. Nai saurin girgiza mata kai ina cewa,”a’a Gwaggo ba rubutu bane, Adawiyya ce take jin haushina ko magana bata son yi min”. Gwaggo taja guntun tsaki ta miƙe tana nufar gadon ta da cewa, “a halinki na rashin kyautawa kika yi mata wani abun”. Nace,”Allah Gwaggo ni ba abunda nayi mata”. Ta ɗan murmusa sannan tace, “to ni yanzu me kike so nayi miki, faɗanku ne dai wanda ya shiga tsakani kunya kuke ba shi…kuma wata ƙila saboda faɗan da Malam yaywa Uwarta ne take tayata kishi”. “a’a Gwaggo tunfa dawowarmu a ɗazu ne”. Bayan ta kwanta tace, “to kin gani kuwa dole kin mata wani abun, ai shariya ba halinta bane, ke kuma halinki sai ke…ki kwana anan ba sai kin koma ɗakin Innarki ba”. Na miƙe kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki na hau kan gadon, saida na maƙalƙale Gwaggona sannan na samu bacci ya ɗaukeni sakamakon faɗuwar gaba da naji ya tsananta garen.
Can cikin dare na farka dan gabatar da sallar dare wadda a yanzu ta zame min jiki, idan ban riga Gwaggona tashi ba to ita zata rigani, dama ita kusan kullum cikin raya dare take, na murza idona dan wartsakar da baccin dake cikinsa sannan na zuro ƙafata na ɗan ƙaro hasken fitila. A tunanina Gwaggona ce ke sallah saida na ƙaro hasken fitila na ganta kwance tana bacci. Na ƙaro hasken fitilar sosai sannan na kai dubana ga Kulu wadda ta ɗaga hannaye sama tana roƙon ubangijinta, na zuba mata ido sosai kamin nayi la’akari da kukan da takeyi, kana iya jiyo kalamanta da take cikin yarenta, da sautin muryar kuka dake neman cin ƙarfinta, tun muryar nata na fita a hankali har ta bayyana sose inda nake jiyo maganganun nata raɗau ba tare da sanin me take cewa ba tunda bada yaren da nake ji bane, hawaye gaba ɗaya ya wanke mata fuska, Fatarta ta koma ja. A hankali kuma sautin kukanta dana muryarta ya ragu, ta kifa fuska a tafukan hannunta tana mai ci gaba da kuka a hankali. Tsananin tausayinta ya kamani, nasa hannu na goge hawayen da nima suka sauko min, Lallai a duniya babu marasa tausayi irin iyayen Kulu, babu abunda zuciyata ta ƙissima min akan wannan kukan nata face rashin iyayenta, waɗanda suka manta da ita da rayuwarta tun tsawon shekarun da naji Ya Amadu ya labartag min.
Na sauka daga saman gadon cike da tausayi da jin ƙanta na isa gabanta, nasa hannu na ɗago da fuskarta, na sanya ƙwayar idona cikin nata idon da haskensa ya cika min idanu, lokaci ɗaya ruwan hawayen daya kuma saukowa daga idonta nima ya sauka a nawa, nasa hannu na goge mata, ban ankara ba naji ta rungumoni jikinta ta matseni tsam a ƙirjinta har ina iya jiyo bugun zuciyarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button