NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Comment&Share.
SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

14)
Muna buɗa ledar wani daddaɗan ƙamshi ya bugi hancinmu, na fito da kwalin dake ciki wanda aka nannaɗe shi da abun ado, Adawiyya ta karɓa daga hannuna ta shiga kiciniyar buɗe shi amma saboda irin naɗin da aka masa ta gagara kuncewa. “kinga ki bari Ya Kabiru ya dawo ya buɗe mana”. Bata saurareni ba taci gaba da ƙoƙarin yanke abun da reza, na tashi na fita daga ɗakin ina ce mata, “ni dai idan kin buɗe kin gama gani kya kawo min ɗaki”. Gaba ɗaya ma na manta da babin wata Kulu, sai dana shigo ɗakin naga ta tsareni da ido. Na turo baki na wuce na zauna ina cewa,”ai kin fara magana dan haka idan ba zaki min magana da baki ba to ki bar kafeni da wannan manyan idanun naki masu firgitarwa”. Naci gaba da abunda nake yi, ihun Adawiyya daya karaɗe gidan shi yasa ni tashi na fita da gudu, cirko-cirko na samesu bakin ƙofar ɗakinsu Mu’azzamu sai Inna Zulai dake cikin ɗakin tana watsa ruwa a wutar data kama a ɗakin, na zaro ido waje wanda tashin hankali ya cika cikinsu na dubi Adawiyya dake aikin yarfe hannu nace da ita, “garin ya haka?”. Bata bani amsa ba sai Habiba ce tace,”inaga fa fitila ce ta suɓuce daga hannunta ta fashe, ƙila kuma da kaya kusa da wurin ta kama bata sani ba”. “Allah ya kiyaye gaba”. Na faɗa ina riƙe yatsan Adawiyya data ƙone ina mata tofi, ta rungumeni tare da fashewa da kuka tana bani haƙuri, haƙurin da ban san na menene ba har sai data ce min ledar kayan da Bella ta bani ce ta ƙone. Har raina naji babu daɗi sai dai to ya zanyi tsautsayi ne, saboda haka ma ban tsaya jin ba’asin Kyautar mene aciki ba sai dai da Gwaggo ta dawo na faɗa mata, tace to ai babu komai ba rabo bane ita kuma Bella an gode mata.
Hankalin kowa a gidanmu bai gama kwanciya ba sai da Auwalu yazo yace sunyi waya da Ya Amadu yace sun sauka lafiya, idan ya sauka a masaukinsa zai kira, Nan Baba yayma Auwalu godiya da ƙoƙarinsa. Bayan anyi sallar magriba Ya Kabiru yace nazo na raka shi unguwa, Inna Amarya tana tayi masa tsiyar wai ko taɗi zan rakashi, shi dai murmushi kawai yay baice komai ba, ya kama hannuna muka fita, wani shagon kayan kwalliya muka je ya siya min ɗan kunne da turare, akan hanyarmu ta dawo sai dana sa ya siya min tsire tukunna muka ɗauki hanyar gida. “idan kin aje kayan kizo”. Yace dani sanda muka shigo zaure. Ina shiga na bawa Gwaggo kayan nace ta ajiye min kuma kar aci min tsire, tace na dawo na ɗauki kayana ita bata amsar kayan kashedi, ina ƴar dariya na wuce ina cewa ni dai na bada kuma na faɗa.
Da sallamata na shiga ɗakinsu Ya Kabiru, yana zaune kan yaloluwar katifarsa da littafi a hannunsa, haka yake shi sam baya gajiya da duba takarda. Na ƙarasa kusa da shi na zauna na sarƙafe hannayenmu sannan na ɗora kaina bisa kafaɗarsa. “Yaya wai baka gajiya da duba takarda ne?”. Ya rufe littafin yana ce min,”lokaci ne Mairo kema soon zaki zama irina tunda ba kya wasa da karatu”. Ya faɗi hakan yana shafa kumatuna. “Yaya ɗazu Suhail yazo baka nan”. “ehh munyi waya da shi yake faɗa min”. “yana da kirki sosai…yauwa ka kalla ma Bella ta bada kyauta a kawo min”. Ya muskuta yana gyara zama yace, “ahh ke dai Allah ya haɗa jininku da Bella, to shine kuma ba za’a nuna min kyautar ba”. “ta ƙone”. Ya kalleni ta gefen ido sannan yace,”kaman ya ta ƙone?”. “Tsautsayi, Adawiyya ta ɗauko fitila ta suɓuce ta faɗi kuma a kusa da ledar, kamin ta ɗebo ruwa ledar ta kama gaba ɗaya”. Shirun da yay yasa na ɗago na dube shi, kamin nayi magana ya tari numfashina da cewar, “wannan ai shashancin banza ne”. Ganin zaiyi faɗ na hau bashi haƙuri.
Ya sarƙafe yatsun hannunmu wuri guda yana ce min,”Mairo nah”. “na’am Ya Kabiru nah”. “do you know what i want from you?”. Tuni na ɗauke tambayar da yayi min cikin turanci, kasancewar tunda akace zamu tafi makaranta yana zaunar damu ya koya mana kalmomin turanci, kuma ina ganewa sosai dan a makarantarmu ba wani turanci ake mana ba malamai sunfi yin hausa wai ai makarantar gwamnati ce. Na gyaɗa masa kai, “No Yaya saika faɗa”. Ya gyara zamansa inda ya fuskantoni, yasa hannu ya ɗago haɓata, ya umarceni dana sanya ƙwayar idona cikin nasa. “ki kula min da kanki a makaranta dan Allah, banda shirmen banza da ƙawaye, Karatu ya kaiki dan haka shi kawai zaki yi, ki dage ki zama mai ƙoƙari abar kwatance a wurin Malamai…sannan ban lamunce miki ba daidai da ranar ɗaya Suhail yaje makarantar ya buƙaci ganinki kije, bar ganin sune silarku a makarantar, wallahi naji labari sai ranki ya ɓaci fiye da tsammaninki, karki ga bana ƙasar kiyi tunanin ba zan sani ba…zuciyata zata ke sanar min halin da kike ciki da dukkan abunda kike aikatawa…kuma ki tabbata in har kika wuce ta ɗaya a aji to la shakka zamuyi hannun riga dake”. Na gyaɗa masa kai nace,”insha’Allahu Ya Kabiru ba zanyi kiyaye”. Na faɗa ina ƙoƙarin maida ƙwallar data taru a idona. Ya ɗauko wani zobe a aljihunsa fari mai kyau ya saka min, sannan y umarce ni dana tashi naje na kwanta da wuri kar azo tafiya gobe bacci bai isheni ba. Ina shiga na tarar kowa na zaune yana cin abinci, yau an makara acin abincin dare kasancewar Inna Amarya ke da girki kuma yau sunje unguwa basu dawo ba sai gabanin magariba. Na wuce na zauna kusa da Adawiyya ina cewa,”lallai ma ke ɗinnan, to kinci rabonki”. Fuskar nan tata a haɗe ta galla min harara ta ɗauke kwanon abincin ta juya min baya, idan nayi amfani da hankalina har yanzu dai bata bar fushi dani ba, saboda haka na miƙe naje nace da Inna Amarya ina nawa abincin, tace na tambayi Adawiyya ai haɗe mana tayi, kamar ba zan tambayeta ba kuma sai nace da Basma ta tmbayo min ita aina ta aje min nawa. “ta duba ɗakin girki yana murfin tukunya”. Abinda tace da Basma kenan a ƙufule. Na shiga na ɗauko, abincin ma naji duk ya fita akaina dan haka na tashi daga kansa na fita na bawa almajirai, dan har ga Allah ni bana jin daɗin cin abincin ba tare da ita ba.
A ɗaki na sami Gwaggo zaune tana sauraran radio, na tambayeta “Gwaggo ina ajiyata?”. Tace, “na bawa Innarki”. Na wuce ɗakin Inna tana lazimi ta min nuni da inda ta ajiye naje na ɗauka, Basma tazo ta ƙaraci nacin zamanta na hanata ko ɗanɗane nace wallah bata ci. Sai dai tun a yankan farko dana saka a bakina cikina ya ƙulle, ina gama ci kuma sai amai kamar zan amayar da kayan cikina, numfashina ya fara neman sarƙewa, tari yaci ƙarfina babu ƙaƙƙautawa cikin ƙanƙanen lokaci na fita hayyacina. Inna Amarya ta sallame daga lazimin tayo kaina cikin salati da kiɗima, ta shiga ƙwalawa Gwaggo kira itama tazo, ganin abun dai ba me ƙarewa bane Ya Kabiru ya bawa lukman yace yaje chemist ya karɓo maganin amai, babu jimawa sai gashi ya dawo, ba zan iya haɗiya ba saboda halin ha’ula’in da nake ciki, sai Inna Amarya ce ta jiƙa da ruwa kaɗan Gwaggo ta buɗe bakina aka tsiyaye min ya wuce da ƙyar, duk da jiƙe-jiƙen magungunan da Gwaggo keyi tana bani ina sha, da tarkacen magungunan asibiti da Ya Mu’azzamu ya ɗebo, amma abu babu sauƙi sai a wurin Allah dan abu sai gaba yake daɗa yi. Baba duk ya rikice ya rasa abunyi, sai can da ya saita hankalinsa ne yay tunanin yi min tofi, haka Baba ya dinga tofin adu’a ana bani ina kwankwaɗewa.
Ya Kabiru na sassarfa ya fita ya kira Ado me chemist anan kusa damu, yana zuwa ya duba ni yaga mawuyacin halin da nake ciki, nan ya shawarci Baba akan a tafi asibiti kawai, Baba ya amsa masa to ya kuma yi masa godiya dan yayi min allurar tsaida amai yace kuma a bar kuɗin. Kowa yay jigum ana jiran ganin ikon Allah akan allurar da aka min, amma ina amai yace bai san wannan ba, ciwon ciki ma haka, dan kuka nake kawai ina kiran mutuwa zanyi, ina kiran a yafe min, furucina yasa jikin kowa yay sanyi, tashin hankali ya ƙara bayyana a fuskonin kowa.
Gwaggo kuwa kuka kawai take tana riƙe dani ajikinta, ni dai na tabbata a yanzu babu abinda ya rage acikina illa kayan ciki, amma abinci da ruwa kam babu su, dan a yanzu haka idan nayi kakarin aman sai dai na tofar da jini, hankalin kowa ya daɗa tashi, ƴan’uwana duk kuka suke. Ya Kabiru yace da Baba, “Baba mu wuce asibitin tunda kaga babu sauƙi”. Baba wanda damuwa ta bayyana ɓaro-ɓaro a fuskarsa, yay shiru bai ce komai ba, Inna Zulai dake shafa min ruwa ajiki saboda zafin zazzaɓi ta ɗago ta dube shi tace, “Malam kayi shiru, halin da take ciki fa yafi kamata da asibitin”. Baba kamar zaiyi kuka yace,”ku kun san halin da ake ciki, asibiti wajen kashe kuɗi ne masu yawa, a yanzu kuwa idan muje wa zai bamu?, aina zamu samo?, ni da ban ajiye ba ban bawa wani ajiya ba, yanzu haka babu ko kuɗin mota ajikina…dan haka mu zubawa sarautar Allah ido insha’Allahu sauƙi zai sauka gareta”. Sunusi yace da Baba, “to ai Baba ba asibitin kuɗi za’aje ba, na gwamnati zamu”. Baba yay murmushi mai ciwo sannan yace, “Sunusu ina nusar daku ne ku gane ko munga likita kyauta akwai kuɗin magani, ko kuma shima maganin kyauta zasu bamu?”. Shiru ya ratsa biyo bayan tambayar Baba, can Ya Kabiru ya laluba aljihunsa yace, “Baba muje ga ɗari biyar ajikina zata ishemu zuwa asibiti, magani kuma ko ba’a siya duka ba sai a nemi mai muhimmanci ciki a siya”. Baba yana dubansa yace, “kana dana siyan magani kenan?”. “Allah zai kawo Baba”. Gwaggo na gefe tana goge hawaye tace da shi,”Kabiru jeka da sauri samo mota, kaga numfashinta neman ɗaukewa yake gaba ɗaya”. Ya fita jiki na sassarfa, yana fitowa ƙofar ɗaki kuma yay karo da Kulu a tsaye tana kuka. Ya tsaya yana dubanta da kuɗin dake hannunta, kuɗaɗen da bana ƙasar nan bane, yaja numfashi ya sauke, kamar zaice da ita wani abun sai kuma ya wuce kawai, ta bi bayansa da ido a sanda hawaye ke daɗa sauka saman fuskarta, sannan ta koma ɗaki taci gaba da ruzgar kukanta tare da nemawa Mairo sauƙi a wurin mahallicinta.
Babu jimawa Kabiru ya dawo da mai adaidaita, yana shigowa ya kinkimi Mairo wadda ta jimawa da sumewa, an watsa ruwa an watsa amma babu alamar zata farfaɗo. Dan a sami sauƙin kuɗin mota Malam yace Inna Amarya da Adawiyya ne kawai zasu je asibitin, Gwaggo dai taso dai ita aka tafi, sai dai babu yanda zatayi dole tayi alkunya, bata kuma da haufi akan kulawar da Inna Amarya zata bawa Mairo kamar yanda zata bata. Inna Zulai ta tattaro wasu ƴan canjikanta na saida mafici ta bawa Malam tace a haɗa dasu, Malam ya karɓa ya baiwa Kabiru yace ya haɗa dana wurinsa.
Da zuwansu cikin ikon Allah suka sami ganin likita har aka basu gado, ɓangaren Gwaggo hankalinta yay ƙololuwar tashi da jin zancen, tace zata nemi kuɗi ta taho a yanzu Baba yace a’a ta zauna ai jikin da sauƙi tunda harta farfaɗo daga suman an kuma yi mata allurai bacci ya ɗauketa. A ɓangaren Malam kuwa faɗa ya sha shi a wajen likitoci, na ɓata lokacin da akai wajen kawota, har suke ce msa da sun ƙara wasu lokuta sai dai su kawo gawarta, sun kuma shaida masa a duk iya binciken da suka yi basu gano wani ciwo a cikin nata ba ko kuma a abincin data ci, sai dai sunyi ƙoƙarinsu wajen ganin sun bata taimakon da zai tsaida aman da shi ciwon da take ji idan ta farka.
An rubuta allurai da magunguna masu tsadar gaske wanda akai umarni da a gaggauta wajen siyo su, Baba yay shiru domin ba shi data cewa, dama tun farko abunda ya ke ji kenan, idan sun gudarwa asibitin kuɗi, nan ma fa ba komai zasu yi musu kyauta ba. Yana tsaye ya zubawa Mairo ido, wadda fuskarta tayi muguwar rama kamar wacce ta shekara guda a kwance cikin ciwo. Tsausayin kansa dana iyalinsa ya daɗa kama shi, ya maida dubansa ga Kabiru wanda yasa kai zai fita daga ɗakin cikin mutuwar jiki, ya dakatar da shi daga tafiyar da cewa, “Ban amince maka da rancen kuɗin kowa ba Kabiru, idan kuwa kai hakan to bada yawuna ba wallahi, kuma fushina zai tabbata akanka”. Kabiru ba shi da tacewa saboda haka dole ya dawo ciki ya zauna, Inna Amarya tasa hannu ta goge hawayen daya sakko mata, “To Malam ko can gida zaka kira a ɗebi samiru na akaiwa Matar liman ta siya”. Malam ya girgiza kai yace, “babu abunda za’a siyar, mu jira ruwan da aka saka mata ya ƙare, insha’Allahu lafiya ƙalau zata farka”.
Har ruwan da aka saka mata ya ƙare bata farka ba, ma’aikaciyar jinyar tazo ta ƙare jarabarta ta tafi babu wanda ya tankata, dan tun a ɗazu take zuwa tana tambayarsu alluran da akace a siyo suna cewa tukunna dai kamin ruwan ya ƙare, ga shi har ruwan ya ƙare shiru. Wata mata dake kusa da gadonsu itama tana jinyar yaronta ta taso tazo kusa da Inna Amarya tayi musu ya mai jiki, Amarya ta amsa da Alhamdulillahi. Sannan matar ta dubi Malam tace da shi,”ku ƙara haƙuri nan da ƙarfe tar da rabi akwai wanda yake taimakawa marasa lafiya a wajen sayan magani da abubuwan dai da asibiti suka buƙata…suna yin abin nasu cikin tsari ne zasu bi gado gado har sai an biyawa kowa buƙatarsa”. Kabiru ya duba agogo yaga lokacin har tara da rabi saura minti goma, saboda haka suka fasa tafiyar da Malam yace ayi suka ƙara jira.
Tara da Rabi dai-dai kuwa sai ga wasu maza sun shigo su biyar jikinsu da rigunan aikin asibiti, sai mata biyu dake biye dasu, ɗaya dattijuwa ɗaya tsohuwa. Madam Merry da Madam Gloria kenan, daga kan gadon su Mairo aka fara amsar katin, Madam Merry ta karɓi katin daga hannun Kabiru tayi saka hannu sannan tace ya wuce can wajen karɓo magani ya amso, a haka suka dinga zagaye gado zuwa gado har sai dai ta tabbatar ta saka hannu akan katin kowa sannan suka bar ɗakin, masu zaman jinya suka rakata da godiya da kum adu’a.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button