SIRRIN ƁOYE COMPLETE

11:00pm.
Agogo ya buga ƙarfe sha ɗaya na dare, A hankali na shiga buɗe idanuna waɗanda najj sun matuƙar yi min nauyi saboda kukan dana sha, ko’ina na jikina ciwo yake saboda tsananin galabaitar da nayi, bin ko’ina nake da kallo da son tantance a inda nake dan ban fidda tsammanin na mutu ba.
Ina kallon gefen haguna Adawiyya ce ta kwantar da kanta kusa dani, hannunta cikin nawa ta riƙe, sai Inna Amarya dake shimfiɗe a ƙasa da gani bata ji daɗin kwanciyar ba. Na maido idona ga hannun damana inda Ya Kabiru ke tsaye a kaina ya jingina da bango, da alama tsumayin farkawata yake dan ina ɗaga kai muka haɗa ido da shi, ya sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya tare da lumshe ido sannan ya buɗe. “Sannu”. Ya faɗa a sanda yake taimaka min wajen tashi zaune. “ina yake miki ciwo yanzu?”. Ya tambayeni yana duban ynda nake aikin cije fuska. Nayi masa nuni da cikina, “Yaya cikina ne wani abu ke yawo yana karta min farcensa”. Yay gajeran murmushi tare da cewar, “yunwa ce”. Na girgiza masa kai cikin ƙarfin hali nace, “Yaya wallahi ba yunwa bace, yawo yake yi ta ko’ina fa…zafi sosai”. Yay ɗan jim yana dubana da nazari kana yace, “ko lokacin al’adarki ne yayi?”. Na kuma girgiza masa kai, “a’a Yaya ai a farkon wata nake yi”. “to ƙila an sami sauyin yanayi ne, sannu bari kici abinci sai kisha magani zaki ji sauƙi kinji Mairon Yayanta”. Na buɗa idona daya cika da ruwan hawaye saboda irin azabar da nake ji na kalle shi, ina fashewa da kuka nace, “Yaya ciwo sosai, zafi yake min, ina jin kamar ana tsatstsagani da reza ne”. Ya matso kusa ya kwantar da kaina saman ƙirjinsa yace, “yi haƙuri zai daina kinji”.
Comment&Share.
SIRRIN ƁOYE
By Oum Ramadhan✍????
15)
A wannan daren haka Ya Kabiru ya fita ya nemo min abincin da zanci, tuwan dawa ne da miyar kuɓewa busassa, Inna Amarya ta bani abincin da kanta wanda na samu naci shi da ƙyar shima kuma kaɗan, bayan na gama ci Baba ya ɓallo magunguna na sha da ruwan tofin adu’ar da yayi, Adawiyya na gefe tana ta aikin jera min sannu cike da ɗumbin tausayina, har tsawon wani lokaci da magani ya tsarga min cikina bai bar yi min ciwo ba, ciwon da nake jin inama zare raina akai na huta, tun ina kuka sautinsa na fita har na koma sai hawaye dake sauka ta gefen idona, Baba kansa ya sare da lamarin nawa ya barwa Allah yayi ikonsa akai…cikin hukuncin ubangiji kuma wajen ƙarfe ɗayan dare sai ciwo ya tafi, na neme shi na rasa, kafin asuba nayi garau dan bacci harda munshari, na kuma tashi ras dani, ƙarfe takwas kuma aka bamu sallama muka koma gida.
Inna Zulai na shara muka shiga gida, ganina yasa ta tsaya kallona da maɗaukakin mamaki, kamin ta wurgar da tsintsiyar ta rungumeni jikinta, sannu da barka take ta jera min ba adadi, lamarin nata har ya bani mamaki, ta sakeni ta kama hannuna mukai ɗakin Gwaggo, ƙwalawa Gwaggona kira take tana ta fito taga ikon Allah. Gwaggona data fito ta ganni tsaye da ƙafafuna kamar ba wadda aka fidda ranta daren jiya ba, tsananin farin ciki yasa duk ta ruɗe ta kiɗime, ta yada kwallar dake hannunta ta rungumeni, godiya take ga Allah tana kuma yi min sannu, ta sakeni ta ɗago tana dubana, tana ƙoƙarin maida ƙwallar idonta tace, “Mairo kinga yanda kika rame…babu dai inda ke miki ciwo yanzu ko?”. Ta ƙarashe muryarta da damuwa. Nayi murmushi nace, ,”Gwaggona ki kwantar da hankalinki ni kam na warke, babu inda ke min ciwo yanzu haka”. Ita da Inna Zulai suka haɗa baki wurin faɗin, “Alah ya ƙara lafiya”. Dai-dai lokacin kuma dasu Baba suka shigo, Inna Zulai ta wuce tana musu sannu da zuwa tare da amsar kayan hannunsu, ni kuwa binsu nake da ido da al’ajabin sauyin da aka samu a tsakaninsu.
a ɗakin Gwaggo dai da aka yada zango babu hirar da ake saita ciwo na daya kiɗima kowa, duk faɗi suke basu taɓa zaton zanyi rai ba, Sadiya ta kawo min duka tana cewa inda nasan ba mutuwa zanyi ba ai saina faɗa mata tayi bacci harda munshari, ina dariya nace,”yanzu dai bance kinyi ƙarya ba amma kina so kice min baki bacci ba jiya?”. “hmm ba zaki fahimta ba”. Shine abunda ta iya cewa kawai, Inna Zulai ma tace,”to ai koni nan wallahi baccina sama-sama nayi shi…ga Kabiru ne kaɗai me waya a gidan balle mu kira muji halin da ake ciki, to tare kuka tafi da shi, da asubar fari kuwa da naji su Salisu sun buɗe ƙofe gida bakiji gabana yanda ya faɗi ba”. Na ƙyalƙyale da dariya har ina kifawa jikin Gwaggona nace, “wooo ni Mairon Baba ashe dai a gidan nan ana so na har haka”. Inna Zulai ta ƙwalo min mafici tana miƙewa ta fita dan kawo min Kunu.
Shigowar Kakarmu Yagana sai gida ya ɓarke da sabon bidiri, ita bata san an sallamomu ba, ashe tun a daren jiya da akace mata an kwantar dani a asibiti sai ta ɓarke da gudawa jin ance an tafi dani a sume, ta zauna kan dakalin ƙofar ɗakin Baba tana kuka harda su zuƙar majina, Kuka wiwi kamar wadda aka aikawa saƙon mutuwar shaƙiƙinta, faɗi take, “yanzu ko a wanne hali yarinyar nan take ciki oho, ya Allah ka bata lafiya…shi kuma Adamu da rashin azanci ai sai ya dawo ya sanar damu halin da ake ciki ko kuma ya turo Kabirun, amma duk sai su zauna acan suyi shiru suyi bilin biƙwi, ko da ike zani ce ta tadda muje, danma dai Allah yasa ba Amadu bane, in wannan yaronne sai ta mutu ma a binneta bamu sani ba…to yanzun ma waya sani ma kota cika ni Rakiya…yarinya me hankali da tunani kaf jikokina albarka…Allah na tuba kar nayi saɓo ita cutar ga yara nan rututu a gidan ta rasa wa zata ɗauka sai abokiyar hira ta”. Yagana ta miƙe tana gyara zaman gyalenta da yaƙi zama tana cewa, “ke Suwaiba ɗauko sutararki mubi sahunsu ni ba zan iya wannan zaman jiran tsammanin ba, in jini acan hankalina zaifi kwanciya…ke ma dai banda soluwar Uwa ce ace an kwantar da ƴarki a asibiti amma kina zaune anan hankali kwance wai kin barwa kishiya riƙonta, to idan da mugun nufi aranta fa tayi mata wani abu ta ƙarasata fa…ko da yake ba Zulai bace balle nace, amma itama Aishan ba na shaideta ba tunda ban san zuciyarta ba…tunda yanzu mutane sun zama Allah a fili fir’auna a zuci, kiga suna ta haba-haba da kai suna nuna maka duk duniya ko uwar data santoloka duniya albarka a irin son da suke maka, nan kuwa duk buge ne a zuciya ji suke kamar su kasheka…to matsalar idan kasha tabara kasha yasin sai ka ɗora musu ciwon takaicin duniya su rasa kataɓus”. Tayi shiru tana gyara ɗaurin zane kan taci gaba da cewa, “kizo muje ƙawata Harira ta kawo min ajiyar kuɗi saina ara muyi kuɗin mota da su, nasan har da rashin kuɗin motar ma ya hanaki wanke ƙafa kibi sahunsu tun duku-dukun asubahi…ni gaba ɗaya wannan zama naku na rasa irinsa wallahi, ban taɓa ganin kishiyoyi marasa hankali da tunani irinku ba, ace wai idan ɗayanku na cikin mawuyacin hali baza’a sami mai taimaka masa ba…a’a kowacce ta kama nata ta ɗaure a gindi, to wannan dai ba hali na gari bane sam ku sauya tun kamin ƙasa ta cika muku baki”. Ta ɗago tana duban Inna Zulai wadda tayi kicin-kicin da fuska tun a ɗazu, “yanzu ke Zulai inda ace matar arziƙi ce ai mai iya yiwa gidan nan kuɗin mota ce duka a tafi asibiti tunda ke da sana’arki me kauri a hannu…ta inda nake godewa Allah kenan da Amadu bai yo mugun halinki ba…yanzu ke da me wayo ce ma ai rawar jiki zaki kama ko dan ki samu fada a wajen mai gida…to matsalar ke ba kya jin faɗa balle shawara, da an soma magana sai kice zaki zumɓurowa mutum baki, shi yasa sam bana son zuwa gidan nan, ga shi dai gidan ɗana ba nawani ba…to amma gwara aje gidana a sameni yanda zanyi da dalili idan an min abinda bai gamsarni ba…to Allah dai ya kyauta”. Magana take tayi ta hana kowa cewa uffan, ta nufi zaure tana mitar Gwaggo da nuƙu-nuƙu a wajen shiri, zuwa asibiti ba wajen biki ba ta rasa shirin me ta tsaya yi. “to ni da nace ki ɗauko sutura ba duka kayanki nace ki ɗauko ba fa, ina nufin ki ɗauko abunda zaki sutarta jikinki”. Gwaggo tace, “to ai Yagana kece tunda kika shigo kin hana kowa magana”. Yagana ta saki baki galala tana kallonta, “au so kike kice da asiri na shigo kenan tunda har zaki ce na rufewa kowa baki…to ni wallah ko da ƙawayena da suke bin bokaye ni dai Allah bai taɓa nufata da zuwa ba har na gama tashen ƴan matancina…..”. Gwaggo tayi saurin katseta da cewa, “yi haƙuri Yagana ba haka nake nufi ba, ina nufin kina ta faɗa ne…”. Ai Gwaggo bata ida zancenta ba Yagana ta tari numfashinta, “ai da ike ga jarababba ta afko muku gida…to ni kinga ma nayi tafiyata kisha zamanki, ko da kika ga na damu da naje banda Mairo ce babu abunda zaisa na ɗaga hankalina haka, dan da ace su Sadiya ne sai dai na bisu da aiken gaisuwar jinya”. Har ta isa zaure kuma saita dawo, “ni kuwa ina mara lafiyar gidan nan har yanzu dai bakin bai buɗe ba ko?, wannan Mata tana ganin jarabawar rayuwa, Shekara da shekaru cuta babu sauƙi, Allah dai ya kawo sauƙi…Saleh ungo ka bata wannan alawar nima Mujibu ne ya bani ita jiya da daddare, to ban samu shanta ba ma har yanzu, kai mata wannan ɗayar ni saina sha wannan, haka kawai Allah ya haɗa jinina da ita”. Saleh ya karɓi alawar ya miƙawa Kulu, Adawiyya kuma tace da ita, “to Hajiya Yagana idan kin gama faɗan naki an hutar dake zuwa asibitin, ki dawo ga Mairon a gida sun dawo tun ɗazu, masifarki ta rufe miki ido kika kasa ganinta”. Sadiya tace,”ai da kin barta taje ƙafarta ta gaya mata”. Yagana data kai zaure ta dawo tana zabga salati,”ke Adawiyya amma ku dai halinku sai ku, yanzu tun ɗazu kun san da hakan baku faɗa min ba kuka barni inata zuba”. Na tafi na rungumeta itama ta rungumeni, sai ta shiga matsar ƙwalla tana ƙara faɗin ciwona ya ɗaga mata hankali ainun, dan Allah na dinga kiyayewa da shegen kwaɗayina na ciye-ciye, ba komai ake kaiwa ciki ba dan wani abun guba ne.
Muka koma ɗakin Gwaggo muka zauna aka ci gaba da hira, Ya Kabiru na bada labarin yanda aka karɓemu a asibitin da yanda suka sare da siyan magani, sai da wasu Arna da suke bada tallafi suka zo kana aka sami magunguna. Yagana tace,”to Allah yasa suna da rabon musulunci kamin a sheƙa”. Gwaggo tace mata, “jiya ma ai da za’a tafi babu kuɗin mota Zulai ce ta ɗauko ƴan canjinta ta bayar, da suma aka samu na siyan ruwan da aka ƙara mata”. Ta ajiye kofin kunu data kai bakinta, “to Allah shi albarka yasa kuma dan Allah akayi”. Babu dai wanda yace mata ƙala, saini da muke hirarmu, tana cewa na shanye kunun tas na samu naji ƙwarin jikina. Baba ya dawo ya miƙo min leda, na karɓa nayi masa godiya da adu’a, nama ne balangu aciki, Yagana ta warce ledar tana cewa ba zanci ba, jiya ma aishi naci yasa ni leƙawa lahira amma saboda ban san ciwon kaina ba zan kuma ci, Yaya Kabiru yace mata ai na jiya tsire ne, tace ita dai koma mene ba zanci ba, to ita inta kafe kan magana babu mai iya ja, haka ina ji ina gani dole na maida yawun bakina, ta bawa Saleh tace ya kaiwa tumakinta suci, ta kuma gargaɗe shi akan shima kar yaci.
Suna magana da Baba akan zancen asibiti yana faɗa mata aiko binciken da likitoci su kai sunce ba daga abunda taci bane, amma shi yana tunanin ba zai wuce shawara ba. Yagana ta kifa kai da hannu tana jero salati, “oh ni Rakiya, idan ance ba daga abunda taci bane to kar dai ace mayu ne suke ƙoƙarin kamata”. Baba yace,”ah haba Yagana ciwo ne dai kawai”. “hmm Adamu ka bari kawai, amma ni dai zanyi iya dafa qur’ani mayu ne suke son kamata ko kuma baki”. Ta dubeni tace,”ina dai ce har yanzu halinki dana sani ya nan na rashin barin kota kwana? Dan ko shekaranjiya yaron nan Auwalu ya labarta min irin ɗibar albarkar da kika yi masa kwanakin baya…to billahillazi Mairo ki shiga hankalinki, idan kin san wani baki sa wani ba, in wani ya barki wani ba zai barki ba…to ni dai na roƙi ki rufa mana asiri haka, kar a kuma irin ta ɗan gidan Ladiyo da kika ƙwalawa dutse da kuna yara tasa aka shanye miki ƙafa”. Na tura baki gaba nace,”to ni Yagana yaushe rabona ma da faɗa da wani, ko fita yanzu bayi nake ba…shi kuma Auwalun munafiki daya kai miki gulma ai shi ya fara zaginmu yace mana ƴaƴan me faskare”. Ta gwame baki tace, “to da ƴaƴan shugaban ƙasa kike so yace muku…ko kuwa ƙarya yayi ku ba ƴaƴan me faskaren bane, ni inda yay magana dani ma ai sai in faɗa masa abunda bai sani ba Kakanku ma me faskare ne, kinga idan ya tashi yace ƴaƴan me faskare jikokin me fakare, zancen banza kawai…ke ba ɗiyar kowa ba sai jin kan tsiya…”. Na katseta da cewa,”Yagana babu fa zancen jin kai anan wurin, babu ɗan halak ɗin da za’a zagi ubansa yace zaija baki yay shiru, balle kuma ni Mairo, wallahi kaf faɗin duniya ma ba acikin garin bichi ba babu shegen da zai aibata sana’ar ubana nayi shiru saina rama…kefa da kanki kike ce mana kada ɗan banzan da yay mana muka ƙyale dan za’a raina mu, balle shi shegen munafikin na san ba gaskiya ya faɗa miki ba, dan da kema alokacin ko baki tsine masa ba sai kin masa iyaka da gidanki…kinga kuwa irin cin kashin da yay mana daga Adawiyya ta bige wani tsamurmurin yaro bata sani ba, Wai shi ɗan birnin da naira ta zaunawa ajiki, shikenan su duka suka hauta da masifa saboda sunga bata da baki…ni kuwa na bisu har inda suke nayi musu wankin babban bargo”. Gwaggo ta hamɓareni daga kusa da ita ta hauni da faɗa, “dama irin abunda kike shukawa a wajen kenan, faɗanma ki rasa dawa zaki yi sai da Auwalu yaro me hankali…to daga yau ɗin nan na gargaɗeki, karna kuma ji tunda ba sa’anki bane shi…kuma ita Adawiyyar data na kallon gabanta ta ina zata bige wani har a zageta…shashashai biyu kawai, to wallahi ku iya talaucin gidanku, dan duk ranar da kuka kai wani bango naga kadarar da za’a siyar a ƙwato ku”. Gwaggo bata rufa baki ba Baba ma ya ɗora da nasa, suka hau mu caa ni da Atika faɗa suke mana ta inda suke shiga bata nan suke fita ba, haƙurin ma da muke bayarwa basa ji. Baba faɗi yake,”idan kuma kun sauya wasu iyayen ne sai naji, dan ni dai nasan ba tarbiyar gidana bace wannan”.
Yagana ta taƙaita faɗan nasu da cewa, “kai Adamu naji kana batun tafiyar makarantar yaran nan anjima…to Magana ta gaskiya banda Mairo za’a tafi, ita a barta saita gama warwarewa…”. Nayi karaf nace,”warwarewa kuma ta yaushe, ni naji sauƙi”. Taja carbi tayi hailala uku sannan tace, “kaga ai irinta, indai da Mairo a wuri bata barina na magantu, to kace mata tayi shiru da kai nake magana”. Ta dubi Ya Kabiru tace, “yanzu kaine zaka shirya ka rakani gidan Malam Kabiru, naje na zayyane masa komai game da ciwonta…ai mata rubutu ya bada turarukan sammu…an fara da irin haka ba zai yiwu ta shiga dokar daji babu tsari ba, dole a miƙe tsaye…tunda iyayen ba me lura da ƴaƴa bane, kwanaki ita Suwaiban da nayi mata magana cewa tayi Allah na tare da su…alhalin tana ganin wannan yarinyar halittarta dole a miƙe tsaye akanta saboda baki da kuma ƴan hasidin iza hasadin…Allah ya jiƙan Alhaji da yana raye tun kuna jarirai zaku dinga shan rubutun tsari…dan haka ni dai a matsayina na Rakiyar in har na isa ina kuma da iko akan Mairo to babu inda Mairo zata je ayau, a barta sai wani jiƙon”.
Baba zaiyi magana ta ɗaga masa hannu, dole yayi shiru.