NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Naso yi muku da yawa, to ina typing ɗin nayi baƙi, kuyi haƙuri da wannan.

Comment&Share.
SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

16)
To babu yanda dai Baba ya iya, dan dole ne bin umarnin Yagana tunda ana son kwanciyar hankali, Baba kuma yana neman albarka.
Ta yunƙura ta miƙe Sannan tace da Ya Kabiru,”tashi muje ka rakani kamin lokacin tafiyar taku yayi”. Yace da ita,”A’a fa Yagana ki kama hanya ki tafiyarki ke ɗaya kawai, ni da zan kai yara makaranta, yaushe muka je muka dawo har na shirya”. “to amma dai naga ai da sauran lokaci tafiyar taku, yanzu ne fa zamu dawo ba zama zamuyi ba…ina so ne a haɗa har kai da Amadu na amso muku na farin jinin ƴan mata”. Ta faɗi hakan tana ƙunshe dariyarta. Nace da ita,”abun ai ba rashin farin jini bane jan aji ne matsayinsu na ƴan boko”. Ya Kabiru ya kalleni yace,”barta ni tuni ina da matata a hannu, dan haka ta riƙe taimakonta Amadun ma baya so”. Ta doki cinya tai bakin ƙofa tana faɗin,”kwayi da wata”. Ta fice tana cewa su Gwaggo saita dawo, suka rakata da adawo lafiya. Tana nufar zaure tana jaddadawa Gwaggo a jiƙa min tagarzaje na sha, shima ance yana maganin mayu, kamin dai Allah yasa taje ta dawo ɗin. Ya Kabiru na binta a baya yace, “ke dai a dawo lapia…zancen tagarzaje kam ba zata sha ba haka kawai ya kuma hargitsa mata ciki…mu magani indai ba Nafdac bama sha”. Ta tsaya salolo tana dubansa tace, “shi kuma Naufdak ɗin mene?”. Yace,”baki san shi ba”. a ƙufule tace,”saboda ban sani ba ɗin ai na tambayeka, Allah sa kuma ba zagina kayi da harshen nasara ba…daɗin Amadu kenan shi magana bata dame shi ba balle har ya faɗa maka ba daɗi”. Ya Kabiru ya girgiza kai,”to ni yanzu Yagana me nace acikin maganata mara daɗi”. “yo gashi kuwa ina cewa a bawa yarinya maganin da zai taimaketa kana ce min ban isa ba…to ka tambaya Uwar zoman data karɓi haihuwarka ko Uwarka Allah ya jiƙan rai sai data sha tagarzaje kamin ta sulluɓoka, ah to kuma bata mutu ba a lokacin sai data haifi biyu bayanka”. Bai ƙara cewa da ita komai ba ya wuceta zuwa ɗakinsu. Muna jiyota a zaure ita da Auwalu wanda ya kawo waya Ya Amadu ya kira, yana bata su gaisa tana ce masa a’a ita ba sai sun gaisa ba sauri take akwai inda zata je me muhimmanci, a dai ce tana gaishe shi, kuma dan Allah karya manta ya turo mata sallahun manja data bashi. abun takaicin manjan ma kwalba biyu ne, wai ƙawarta ta faɗa mata ɗanta da yake zuwa lagos yace acan akwai ragin ɗari a kowacce kwalba akan yanda ake siyarwa anan, haushi ya cika Lukman yace da ita”idan baki cika ɗari biyu kin siya anan ba kya kuma biyan kuɗin manjan gaba ɗaya a kuɗin mota”. bata dai ce da shi komai ba tai gaba tana zikiri.
sai da kowa ya gama gaisawa da Ya Amadu sannan na karɓa, yay min sannu da jiki sannan yace na kaiwa Gwaggo wayar, tana ɗaki tana aikin maida kayana ƙasan gado na miƙa mata wayar, kamar ba zata amsa ba sai kuma ta karɓa tana amsa sallamarsa aciki, da tana tsakar gida ne a zaune, amma tunda taji maganar Auwalu yana cewa Amadu ne ya kira ta tashi tayo ɗaki, sai kuma tayi rashin sa’ar gashi na biyota da ita, na kuma saka a handsfree.
“to ya wajen naku?”. ta tambaya shi kamar wadda akaiwa dole, ko da yake dolen akai mata. shima da ya gane yanayin muryar tata acikin sanyin murya yace “lafiya lau, yauma na fara zuwa aiki, kuma Alhamdulillah wurin yana da kyau…ga ogan ba shi da wata matsala, yanzu haka ma ya bani dubu hamsin yace na siyi kayan abinci da abubuwan da zan buƙata, albashina kuma duk wata za’ake bani dubu ɗari…insha’Allahu gobe zan buɗe account zan turo dubu ashirin da biyar sai a siyi kayan buƙatar gida”. “to Allah ya shi albarka…ya yanayin ibadarka a wurin tunda ance babu musulmai?”. Gwaggo ai babu wani banbancin addini a wurin, sallolina duk nayi su a office ɗina”. “to yayi kyau a dai ƙara kulawa”. ya amsa da, “insha’Allahu”. sannan ya ɗaro da, “cikin kuɗin Gwaggo sai a bawa Mu’azzam dubu biyar ya sai waya a hutar da Auwalu haka…Kabiru ma ashe ya gyaro tasa ban sani ba sai yanzu yake faɗan”. “umm ya gyaro jiya, shima ai tafiyar tasa ta matso kusa sunce jibi zai wuce…sun gama yi masa komai na tafiya jiya ma ya amso tikitin jirgin”. Ya Amadu yace,”haka yake faɗa min…ai nace da Baba ya daure yaje masarautar da kansa yayi musu godiya”. Gwaggo tace,”nima na faɗa masa sai yace ai niyya suka yi bashi ya roƙa ba, baya son yaje a fara cewa yana zuwa maula…to ɗazu dai Yagana ta masa magana yace zaije bayan tafiyar Yaran nan”. shiru kamar babu me kuma cewa komai sai Gwaggo ta numfasa tace da shi,”ni dai dan Allah ka dinƙa kulawa da arna nan Amadu…Allah yi muku abarka sai anjima”.
Inna Zulai ta aikemu gidan ƙawarta da za’ai bikin ƴarta, ta sai mifitai dozin biyar da za’ai rabon kamu. ta gargaɗemu sosai akan karmu zauna Kabiru ya shiga wanka kuma shi shirinsa ba mai wuya bane. muna kan hanyar dawowa muka ga Malam Liman, har ƙasa muka duƙa muka kwashi gaisuwa da neman tabaraki, “Mairo dai ƙara girma ake gashi nan har kin gama taddo Yayar taki”. mukai murmushi bamu ce komai ba, sai ya ƙara cewa,”Malam Adamu kam ai ya kamata yanzu kuma ya karkata hankalinsa kanku…ku ƙarasa gida Allah yay muku albarka”. can munyi nisa Adawiyya ta kwaɗa uban tsaki tace,”Allah Mairo kina baƙantan rai”. ta faɗa cike da zafi. ban dubeta ba naci gaba da jan karana ina tafiya nace da ita,”yi haƙuri to…amma dai ma me nayi miki?”. ayanzu dana ɗaga kai na kalleta sai naga ta zabgeni da wata harara, ta nuna ni sama da ƙasa da hannu kana ta kuma cewa,”dan Allah dube ki…Wai ke sai yaushe zaki sauya ne, duk sanda za’a fita ba ruwanki da wani gyara jiki ke kawai ki fita a harbutse, haba dan Allah kinfa girma yanzu, ki fara cin ganiyar ƴan matancinki kuma”. taja tsakin takaici, “shi yasa ai har yanzu gaki nan kin gagara yin saurayi, ba me kawo miki sile da sunan kyauta…suma mazan ƙauyen fa sunfi son mace ƴar gayu, ke baki kalla yanda samari suke rawar jiki akan Sadiya da Habiba bane…amma ke kullum jiki ba man arziƙi balle ƴar hoda ko jambaki, a’a ke kawai ki fita zaro zaro kamar tsohuwar bazawara indai zaki je ki biya buƙatr kanki shikenan, kina tafe sangalolo babu rangwaɗa babu ɗan karya ƙugu, alhalin ke jiki ba jiki ba kamar sillan kara, gaba a shafe baya a shafe”. na kalleta na harareta nace,”wallahi ƙarya kike kice ta ko’ina a shafe nake, ai baki leƙa gaban kin gani ba”. ta kawo min duka da karan dake hannunta, har yanzu kuma bata saki fuska ba. “ni Allah maganar gaskiya nake miki ba wasa ba, biki san irin kishin da nake ba idan naga ana zuwa zance wurina ke banda ke, karki buɗa zuciyata kiga irin damuwar dake ciki tun ace naga samari na kawo min kayayyaki ke kuwa sai wanda aka sai miki a gida… ko me baƙin jini ai sai haka, ki fita babu me kulaki sannan a gida ma babu me zuwa wurinki…kina biye maganar Yagana tana hure miki kunne da cewar ke matar manya ce…to matan manya ai sai wanɗa suka fito daga babban gida, ke kuwa ba ƴar kowa ba…to Allah ki gyara haka, indai ba so kike mu kuma yin faɗa ba, kina dai jin abunda Baba yace ko ba muyi candy ba mijin aure yazo aurarmu zaiyi”. na dakatar da zancenta da cewa,”kinga maida wuƙar ki daina ɓacin rai, kishin samari akaina kiyi fatali da shi…dan in faɗa miki maganar gaskiya burin rayuwar Mairo bata gina ta akan samari ko aure nan kusa ba, tunda Mairo ta mallaki hankalin kanta, ta gina burin rayuwarta akan karatu, karatun boko, karatun da zai bata mutunci da martaba a duk inda ta shiga…amma saurayi kam baya gaban Mairo”. ta tuntsire da dariyar ƙeta har da sunkuyawa, “sai dai na jiki amma ba in yarda ba, dan wallahi babu macen da zata ce saurayi baya gabanta…a ƙaddara ma hakanne, yanzu alal misali Suhail yace yana sonki zaki amince mishi ko kuwa shima zaki fatali da shi ne?”. na waigo na dubeta, “wane kuma Suhail?”. nai tambayar bilhaƙƙi bada rainin wayo ba. tace, “Suhail dai da kika sani ɗan ethopia abokin Ya Kabiru”. nayi tsaki, “to ai bashi ba, ko sarkin ethopia ɗinne da kansa wallahi baya gaban Mairo balle wata tsiya Suhail”. nayi gaba abuna na barta da maganganunta.
a taƙaice dai da gudu na shiga gida saboda cikina daya murɗa, ina sallama kuwa na faɗa banɗaki, ruwan tsarki ma ce nayi da Zubaida ta biyoni da shi. gama tsarkina kenan na miƙe, kallon gabana da zanyi naga maciji sharfaɗeɗe baƙi wuluk ya ɗaga kai yana ƙoƙarin kawo min sara, a gigice cikin ɗimauta na kurma ihu ina kiran sunan Gwaggo, “na shiga uku Maciji a banɗaki”. na sandare saboda hasken idonsa daya dallare ni da shi, ƙafafuna sun kasa gaba sun kasa baya, na zama kamar wadda aka dasa a wurin, dan ko motsi na kasa, ba wai saboda tsaro ba, sai dan nima ban san dalili ba. kuka nake ina neman agajin jama’a, ga mazan gidan duka sun fice, Matan babu abunda zasu iya yi min, duk sunyi cirko-cirko a bakin ƙofa suna kallona suna ihu da neman taimakon maƙota, kan kace mene wannan gidanmu ya cika, kuma da yake juma’a ce maza duk sun wuce masallaci. idan Gwaggo tai yunƙurin shigowa sai ya maida bakin saran nasa gareta, hakan yasa na haneta shigowa. siffanta munin kamanninsa ya zarce tunani, ganin yana ƙara kusanto ni na rumtsa ido gam so nake naja da baya amma ina abu yaci tura kamar aikin tsafi. hawaye ne ke gangaro min, rayuwa kam tuni na sallama da ita. na riga na gama fidda tsammani da sake yin nunfashi a doron ƙasa, sai ji nayi an riƙo hannuna, na buɗe idanuna dake a rufe ina kallon Kulu data yi shahadar shigowa, ita kanta saita bani tsoro, dan ko a maza babu me ganin wannan macijin yace zai kawo ɗauki indai ba wai dama da shirinsa ba, to ko Uwar data haifeni ma ta kasa wannan sadaukarwar, amma ita saboda ganganci da rashin hankali tana ganin mutuwa tana tunkararta. na haɗiye wani wahaltaccen yawu a maƙoshina a sanda na maida kallona ga Macijin da a yanzu ya maida harinsa kan mu biyun.
Kulu ta damƙe hannuna sosai, su Inna kiranta suke da kwakwazo akan ta fito amma kamar bata jinsu. murya ta na rawa nace,”ki fita dan Allah kar kema ya cuta dake”. ganin dai bata da niyyar fita nai ƙoƙarin hankaɗata gefe amma ko kusa na kasa motsa jijiyar jikina. sai muka tsaya muna kallon kallo da ita, kamin tasa hannu ta juyar da fuskata ga majicin da bana ƙaunar ganinsa saboda girmansa da baƙinsa. “wallahi Kulu idan biki fita ba yau zan tona miki asiri acikin gidan nan”. na faɗa ina kuka. tayi ƙasa da murya tace,”alƙawari kika ɗauka, kuma alƙawari kaya ne, wanda kuma duk ya saɓa wutar Allah zata ci shi”. ta kasheni da dukkan jijiyoyina, dan tabbas nayi mata alƙawarin ba zan faɗawa kowa tana magana ba har zuwa ranar yankewar numfashinta, duk da cewar bata san dama can nasan tana maganar ba.
ta ƙara yin ƙasa da murya sosai tace,”ke ɗin ƴar baiwa ce, kina da baiwar da ba kowa Allah ke bawa ba cikin bayinsa, dan haka zaki iya da wannan macijin duk ƙarfin cutarwar kuwa da yake da ita, karki karaya, ki buɗe ido ki razanar da shi daga baiwar da Allah ya halicce ki da ita”. na rumtse idanu gam ina girgiza kai da cewar ba zan iya ba.
“zai sareni Mairo”. sautin Muryar Kulu cikin kuka ya sauka a kunnena, nai hanzarin buɗe ido na dubeta da yanda ta kare jikinta da hannunta tana ƙudundunewa ajikina. ban san lokacin da wani ƙarfi yazo min ba, nasa hannu na kaiwa kansa duka, shima sai yay saurin kautar da kansa. mamaki, al’ajabi da kuma tsoro suka kamani a sanda nayi jarumtar ƙura masa ido, sai naga nan take ya karayar da kai ƙasa sai kuma jikinsa ya motse, da gudu kuma ya fara jan jiki saina neme shi na rasa.
daga haka kuma ban ƙara sanin me ya faru ba, sai farkawa nayi na ganni shimfiɗe kan tabarma, Baba a gefen damana yana min tofi, Gwaggo na min firfita, sai sauran ƴan gidan da suke kewaye dani. Inna Amarya ta kamani na yunƙura na miƙe zaune ina maida numfashi. Baba yace dani, “Sannu”. na amsa da,”yauwa Baba”. Yagana ta taso daga inda take ta juye rubutu a kofi ta miƙo min tace na shanye, zanyi gardama ta rufeni da faɗa, ba shiri na amsa na kafa baki zan sha amma sai na kasa, Ya Kabiru ya amsa kofin daga hannuna ya buɗe bakina ya toshe min hanci ya tsiyaya min a haka har na shanye. “Ina ne kuma yake miki ciwo?”. Yagana ta tambaya. “ba ko’ina, aini lafiyata ƙalau”. na faɗi hakan ne gudun kar na ɗaga hankalinsu, na kuma yi silar rugujewar tafiyar su Adawiyya, amma a zahirin gaskiya idona da nake kallonsu da shi ba sose nake ganinsu ba, ganina ya sauya dishi-dishi nake gani, ga zafi da jijiyar idon nawa keyi. Inna Zulai tace,”kin tabbatar dai babu abunda ke miki ciwo ko?”. nace,”ehh Inna ni lafiyata lau”. Yagana tayi ƙaramin tsaki tana cewa, “mun sani dama, indai kece ai ba kya cuta”. sai kuma Gwaggo ta hauni da faɗa akan ai bana adu’a nake shiga banɗaki, nace mata wallahi ina yi yaune kawai na manta banyi ba kuma shima dan na taho a matse ne, Baba yace to karna kuma mantawa, ita adu’a ba’a sakaci da ita.
su Adawiyya suka ci gaba da shirin tafiya makaranta, zumuɗi yasa ko abinci ma ta kasaci, tunda Ya Kabiru ya tafi nemo mota ta kasa zaune ta kasa tsaye dan daɗi, faɗi take yanzu tunda ba tare zamu tafi ba zata wuceni a aji kenan. nace mata ai nima ba jimawa zanyi ba, da wannan tsohuwar ta gama rigimar tata shikenan zan taho. jikina duk yayi sanyi lokacin da suka fito zasu tafi, na ƙanƙame Adawiyya ina kuka itama tana kuka, ina cewa ba zan iya zaman gidan babu ita ba dan Allah a barta mu tafi tare, itama kukan take tana faɗin ba zata iya zaman makarantar babu ni ba, sai da Baba ya tsawatar mana sannan ta muka saki juna.
ba zan iya kallon tafiyarsu ba dan haka na juyo gida na bar su Gwaggo a waje, na shigo ina bin jikin bango, Kulu ta taso tana tambayata menene, na kaɗa mata kai nace,”ba komai”. dan itama nasan muddin na faɗa mata cewar bana gani sosai to zata iya faɗawa Gwaggo, tunda itama na lura ta damu da al’amurana kamar ciki ɗaya muke, har na shige ɗakin Inna Amarya ina jin kallon da take bina da shi ajikina, na malale akan gadon ƙarfen Innata ina fuskantar rufin kwano, idona a rufe yake inaji da raɗaɗin ciwon da yake min.
nayi shiru kamar mai bacci, amma ba bacci nake ba, na lula ne acan wata duniya ta tunanin wasu murɗaɗɗun al’amura dake addabar ƙwaƙwalwata tun kwanakin baya, to amma basu suka fi damuna ba ayanzu. ayau rana ta farko bacin tausayin Kulu da nake ji sai naji ina sonta, nasan idan a haife ne ta haifeni, dan haka naji ina mata so irin na uwa, ba dan komai sai dan sadaukarwar da tayi akaina yau, banda taimakon Allah da kuma taimakonta da tuni na zama tarihi, dan tabbas macijin nan sai ya sareni…lallai ya kamata na saka mata da wani abun a rayuwarta, take zuciyata ta ƙudurci aniyar nemawa Kulu hakkinta na wofuntar da rayuwarta da iyayenta suka yi…dan haka dole na miƙe tsaye, na ƙara ɗaura ɗamarar yin karatun boko mai zurfi dan ganin na cimma matakin da Gwaggona ke so na kai, bayan Babana da zan taimakawa itama Kulu na taimaka mata.
tafiyarsu Adawiyya da kwana uku shima Ya Kabiru ya tafi, ranar tafiyarsa kuwa na sha kuka kamar raina zai fita, har nafi jin tafiyarsa akan ta Ya Amadu, dan shi da zai tafi da ƙyar aka ɓareni ajikinsa, shi kansa sai Yagana ce ta tuge hannunsa daga rungumeni da yayi ajikinsa, kuma harda kukansa, hawayen da naji su har ƙasan zuciyata, suka kuma tugunzuma tunanina, a sanda ya duƙa ƙasa gabana ya zube gwiwoyinsa yana hawaye yana roƙona akan na kula masa da kaina, kar nayi abunda yake ba dai-dai ba, sai naji duk duniya babu wani abu da yake min daɗi, ji nake tamkar nayi bankwana da farinciki. a sannan nima na tsuguna gabansa na faɗa jikinsa na ƙanƙame shi, kuka nake me tsuma zuciya, ina kwaɓar zuciyata daga wautar da take yi. tunda na mallaki hankalin kaina na sani, bayan so na jini da zuciyata take yiwa Ya Kabiru harda wani ƙazamin so da ba zai zama me amfani a garen ba.
“Ya Kabiru dan Allah ka tafi dani”. na faɗi hakan a sanda na ɗago kaina daga ƙirjinsa na zuba masa idanuwana masu kama da jin bacci, ya ƙara damƙe hannuna yana faɗin,”banda iko, da ace ina da iko Mairo babu abunda zai min ni shamaki da tafiya dake, to Baba ba zai bari ba…amma ki sani tafiyar nan zan yita ne saboda ke, haka abunda zanje nema acan zan nema ne saboda ke, saboda ke kaɗai Mairo, ke ɗaya tal da kika zama jini da tsokar Kabiru…burina a rayuwa na jiyar dake daɗin cikinta, na shayar dake farin ciki na rayuwa, na zama katanga a tsakaninki da baƙin cikin da duk zai kusanto ki…ki cika alƙawarin da kika ɗaukar min kinji ƙanwata”. yay furucin ƙarshe yana mai ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali.
ayanzu gidanmu da babu Adawiyyata babu Ya Kabiru jinsa nake babu daɗi sam, gidan ya zamar min tamkar kango, Sadiya ba wata hira muke zama muyi da ita ba saboda shegen son girmanta, Basma kuma Yayan Gwaggo daya zo daga kano ya tafi da ita gidansa, wata ƙila ma ta koma can da zama a yanda naji Gwaggo na faɗa, Zubaida kuwa ba zama take ba saboda makarantar Allo.
duk da cewar ina da karaɗi acikin gidanmu to amma yanzu babu jigona, duk sai nayi sanyi, dan tun tafiyar Ya Kabiru kullum ina ƙunshe a ɗaki ina kuka, naci kukana na ƙoshi ba tare da sanin kowa ba, kukan da gangar jikina kaɗai tasan ma’anarsa, sai zuciya dake jin zafi da raɗaɗin rashin Ya Kabiru a kusa da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button