SIRRIN ƁOYE COMPLETE

To Fah!!! Masu karatu the Saga begins????…wa kuma ya san me zai faru next, Mairo zata dawo kuwa?, haka kawai aka ɗauketa ko kuma sanyawa akai a saceta?, ko Kulu zata bayyanar da kanta a matsayin da take da shi ga Mairo?, kai to waima tsakanin Gwaggo da Kulu wace Uwar ta haƙiƙa ne?.
ni dai please vote and comment ba dan halina ba kunji ƴan albarka????
Share.
SIRRIN ƁOYE
By Oum Ramadhan✍????
19)
Hankalin Gwaggo da Kulu a tashe yake matuƙa gaya, dukansu sun kasa samun stabilify, sam sun kasa yarda Mairo ta ɓata ɓat, har gwara Kulu ma ta iya jurewa, amma Gwaggo kuwa tunda rana ta faɗi ya gama tabbata babu Mairo babu daliinta, shikenan ta yanke jiki ta faɗi, shikenan duk wani budget nata akan Mairo ya rushe, nan da nan aka ɗauketa zuwa asibiti, kuma a lokacin ne Kulu ta fito dan ta sulale ta gudu amma halin da Gwaggon ke ciki yasa dole ta janye ƙudurinta domin idan tayi hakan tayi butulci, daga ita sai Inna Zulai aka bari a gida, bata da aikin komai sai share hawaye lokaci zuwa lokaci.
Gwaggo ce kwance kan gadon asibiti, a kallo ɗaya zaka gane fitar hayyacin da tai, amma dai for now ta fara regaining conciousness, likita ya shigo ya auna BP ɗinta sannan ya kalli Malam yace,”to Alhamdulillah jininta ya sauka, zuwa Magrib zamu iya sallamarku sai dai a kula dan Allah wajen kiyaye damuwarta, and then da shan magani in time saboda gaskiya lafiyarta na cikin haɗari”. Malam ya ɗaga masa kai da cewar,”tom za’a kula…sannu da ƙoƙari”.
zuwa Yamma aka sallamesu suka koma gida, tun bayan dawowarsu kuma gida ya ɗinke da jama’a sai shige da fice suke ana jaje kamar gidan mutuwa, da waɗanda suka zo jaje tun ranar farko da masu dawowa yanzu dan duba jikin Gwaggo sai gidan ya zama babu matsaka tsinke. Yagana duk wanda yay mata jaje bata iya cewa da shi komai sai kallo da ido, bini-bini kuma saita sa gefen mayafi ta matse ƙwalla. Matar Liman tazo ana gaggaisawa ta tambaya ko waɗanda su kai garkuwar da ita sun kira waya?, Amarya tace da ita,”ai Hajiya babu lallai Kidnappers ne tunda har yanzu babu wani saƙo ta waya, munfi tunanin ko ƴan yankan kaine suka saceta, yanzu kwanciyar hankalinmu ma bai wuce ace ko gawarta ne a gani ba zamu fi samun nutsuwar ruhi”. Hajiya Saratu ta girgiza kai cikin jimanta al’amarin,”to ubangiji dai shi ya san a halin da yarinyar nan ke ciki. Allah yasa ta faɗa hannu na gari…in Allah ya yarda za’aita adua dan yanzu haka ma tun jiya Malam yasa almajirai suka sauke mata alƙur’ani”. Yagana ta face majina cikin muryar kuka tace,”ai duk wanda ya ɗauke yarinyar ba zai gama da duniya lafiya ba, kuma sai Allah ya isar mana tsakaninmu da shi…fatanmu Allah ya tsareta ya kareta a duk hannun da faɗa”.
wata cikin ƴan jajen tace,”kwanaki muma fa haka akayi a layinmu, daga fitowar yaro da daddare ke tun ana zuba ido ana saka ran zai dawo shiru har yanzu kusan wata biyu kenan, iyayenma sun cire rai da shi tunda babu irin neman da ba’ai ba, cigiya har gidan talabijin”. Marka me koko tace,”ai waɗan nan azzalumai Allah dai yay mana maganinsu shine adu’a kawai”.
Sunusi ya shigo rungume da buhun shinkafa, Lukman na biye da shi ɗauke da kwalin taliya biyu dana makaroni ɗaya, sai ga Mu’azzam shima ya shigo da galan ɗin manja. kafin Amadu ya mara musu baya bakinsa ɗauke da sallama, sai dai kana ganinsa kaga wanda ke ɗauke da matsananciyar damuwa, a tsaitsaye ya gaida jama’ar dake tsakar gidan sannan ya wuce ɗakin Gwaggo. kishingiɗe jikin pillow ya taddata, ya ƙarasa gabanta ya zauna, har tsawon wasu daƙiƙu baice komai ba sannan ya buɗe baki kamar mai shirin yin kuka yace,”sannu Gwaggo, Allah ya baki lafiya”. ta amsa da,”amin Amadu, ashe kana tafe”. “ehh da yake ma tafiyar mota ce shi yasa na makara”. Sai Gwaggo ta fashe da kuka,”Mairo dai ta ɓata, ban san a wani hali take ciki ba yanzu”. yay saurin kawar da fuskarsa dan baya son ganin hawayenta, ya lumshe idanunsa da sukai jazur ya buɗe kana yace,”su da ba fita suke ba dan ubanta gidan uwarwa taje a ranar?”. yay tambayar a zafafe. Gwaggo na goge hawaye tace da shi,”to ai ita kasan bata rabo da gidan Yagana, laifinma dai nawa ne kuma duk da haka Allah ya riga ya shirya faruwar hakan, kuma ita Yagana tace lafiya lau sukai sallama da ita ta wuto gida, to ƙarshe sai da safe da ana laluben hanya aka tsinci ledar dubulan ɗin data bata a hanya, ananne ma aka tabbatar ɗauketa akayi”. yana huci yace,”ni dama gidan Yagana ba son zuwanta nake ba tunda ba wani iya kula da ita zatai ba…itama shashasha data ga daren yayi ai saita haƙura ta kwana acan”. Gwaggo tace,”ko ɗaya ba laifin Yagana bane kasan Mairo ma da shegen taurin kai, kaifi ɗaya ce”. “duk da haka akwai laifin Yaganar”. Yagana ta faɗo ɗakin tana matse ƙwalla ta hau sababin,”yo ni dama tunda akace min zaka zo garin nan na sallama babu wanda zaka ɗorawa alhakin ɓatanta saini, to ni dai sai dai nace Allah ya saka min tunda yana ji yana kuma gani, ai kowa shaida ne ina ƙaunar Mairo, taya za’ai nasa a saceta, me ta tare min, kuma ni wallahi ma bani da wannan matacciyar zuciyar da zansa hannu acutar da rai”. tunda ta fara maganar Amadu ke kallonta, har kuma ta gama baice mata ƙala ba, sai data gama sharar hawaye sannan ta dube shi da cewar,”yanzu kuwa ɗan nan ba zaka nemi yafiyata ba?”. ko kallonta baiba ya miƙe yana zira hannu a aljihun wando, ya zaro ƴan ɗari biyar guda shida ya miƙawa Gwaggo, ta amsa tana saka masa albarka. “yanzu ina zaka je? da kayi zamanka anan ka huta kaida kasha hanya”. “Gwaggo zanje asa cigiyarta ne a gidajen radio, idan nace zan zauna babu lokaci kwana ɗaya ne aka bani a wurin aiki”. “tom shikenan saika dawo…Allah ya bada sa’a yasa a dace”. yasa kai zai fita Yagana tace,”ni dai dama bance ka ban silanka ba balle ka dinga hararata har kana neman bigeni, ɓatan Mairo shi ya dameni ba karɓan kuɗinka ba”. He is not in the mood ɗin da zai tsaya bata amsa amma duk da haka dai ta bashi dariya, sai ya gimtse kawai ya wuce ɗakin mahaifiyarsa.
ganinsa yasa Inna Zulai ta rasa inda zata tsoma ranta dan daɗi saboda yanda ɗanta ya sauya cikin watannin da basu haura biyar ba. ji take kamar ta maida shi cikinta, sauyin weather yasa yayi wani looking fresh, shaddar dake jikinsa kanta ba ƙarama bace ga wata makekiyar waya da yake riƙe da ita a hannu, cikar haibarsa ta ƙara fitowa, kana ganinsa kaga wanda kuɗi suka soma zaunar masa. ta kamo hannunsa ta zaunar da shi bakin gado tana yi masa sannu da zuwa, shima kuma anasa ɓangaren yana ta farin ciki da ganin mahaifiyarsa. ta ɗebo ruwan sanyi a randa ta kawo masa ya sha, suka zauna suna hira duk da cewar shi ɗin dai ƙarfin hali yake amma hankalinsa baya nan kwata-kwata. yana dubanta yace,”Inna ya na ganki ke kina cikin ɗaki ga jama’a kuma a waje”. fuskarta na nuna damuwa tace,”to kasan halin Kakarka ai, naga tana neman ɓatan raine shine nayo ɗaka kamin zuciyoyinmu ni da ita su huce”. ya miƙe tsaye yana faɗin,”Allah ya kyauta”. sannan ya zaro dubu biyar ya bata, ya kuma shaida mata zaije kano asa cigiyar Mairo a radio, ta bishi da adu’a da fatan nasara. yana jin Yagana sanda zai fita tana faɗin,”miskili kawai”.
yau kwanan su Mairo biyar a hannun kidnappers, kullum kuma sau ɗaya ne ake kawo musu abinci shima biredi ne da zuma zasu tsoma suci, daga nan sai washe gari su da ƙara ganin wani abincin, sai uban ruwa da ake ɗirka musu, bayin Allah duk har sun saba da hakan.
Mairo dai gaba ɗaya tafi kowa lalacewa saboda yanda taga anata ɗaɗewa ana barinta, wasu an biya kuɗin fansarsu wasu kuma an gaji da ajiye sune sai a siyar dasu, ko kuma dan rashin imani sai a kashe su.
Matar data saba da ita ƴan’uwanta sunzo sun fansheta, shi yasa bata jin daɗin wurin gaba ɗaya, ita yanzu jira take kawai su kasheta ta huta, domin ta jima da sallamewa da rayuwa tun a sanda taji adadin kuɗin da zaa amsheta, dama ita tasan bata da me biyan wannan kuɗin, dan kaf danginsu babu me shi, yanzu tashin hankalin da aka sasu aciki ma sa iya cinye kuɗin a magani.
la’asar ɗin yau suna zaune aka banko ƙofar ɗakinsu, suka zabura suka zubawa ƙofar ido, inda sabo yaci ace sun saba dasu to amma sanin cewar basa shigowa su fita basu kashe rai ba yasa basa samin nutsuwa da zuwansu, har sunfi so suji su nesa dasu, kuma yau dan mugunta ma ko abinci har yanzu ba’a basu ba.
su uku ne shuka shiga suna saita da bindiga, a tsorace kowa ya dinga ja da baya musamman Mairo dake daga bakin ƙofa. Ogansu ya nuna wani Dattijo ya manyanta sosai yace,”taso”. sannan ya kalli Mairo yace,”ke kuma ki shirya”. sannan suka fice tare da wancan mutumin. manyan mutanen da duk suka san nufin maganarsa akan Mairo sai suka fara ƙwallar tausaya mata. ta kalli wata sabuwar mata da aka kawo jiya data fara sabawa da ita tace,”Yaya ina zasu kaini?”. ta rungumeta tace,”nima ban sani ba”. hankalinsu ya karkata kan wani mutum daya kalli gabas ya ɗaga hannu yana adu’a, “ubangiji Allah ka dubi wannan yarinya ka ceceta daga hannun azzaluman nan, Allah karka basu ikon keta mata haddi”. ya duƙar da kai tare da fashewa da kuka. kamin su ƙara motsi aka kuma banko ƙofa, wanda ya shigo ya kalli Mairo acikin kaushin murya yace,”taso muje”. jikinta ya hau rawa saboda tsoro, ta ƙundundune jiki tana kuka tana bashi haƙuri, uwar tsawar daya sakar mata yasa ta gimtse baki, ya ƙaraso ciki ya figo hannunta sukai ƙofa, mutumin nan dake ta bin Mairo da kallo yana jin inama ace yana da damar da zai ƙwaceta yace,”dan Allah ku tausaya mata yarinya ce ita…ku ƙara haƙuri iyayenta zasu zo su fansheta amma karku lalata rayuwarta”. wani mugun kallo ya juyo yaywa mutumin yana kai taba bakinsa ya zuƙa, ya saki ƙwafa ya juya zasu ƙarasa fita mutumin ya ƙara cewa,”Ƴata kiyi ta ambaton Allah cikin hukuncinsa da ikonsa zaki kuɓuta insha’Allah”. yana rufe baki mutumin ya saita ƙirjinsa ya bashi harbin bindiga take ya mutu, shi kuma yaja Mairo dake turjewa ya fita.
cikin wani ɗaki da suka kafa na leda ya nufa da ita, yana zuwa ya tankaɗata ciki tare da cewar,”Oga gata nan a huta lafiya”. tsohon ya taso ya nufo gareta fuska babu annuri, yay tsaye kanta yace da ita,”tuɓe”. ya faɗa murya a ɗage. take sabbin hawaye suka shiga kwaranyowa Mairo, tsoro ya ƙara ninkuwa a zuciyarta, tana girgoza masa kai tana faɗin,”a’a”. yasa ƙafa ya take mata ƙafa cikin kakkausar murya ya kuma ce mata,”kamin naje na dawo ki tabbatar da kin tuɓe idan ba haka ba kuma zan kasheki”. ta rumtse ido ta buɗe kafin nan ta sami ƙwarin giwar ce masa,”abunda kake neman yi ne bashi da kyau cin zarafin ƴa mace ne ubangiji ya haramta…”.bata ida zancen ba yasa bakin bindiga ya gwaɓe bakin nata nan take ya fashe. “wannan ɗan ƙaramin wa’azin naki babu amfanin da zaiyi anan dan haka ki rufe min baki, kiyi abunda kawai nace”.
“sai dai ka kasheni amma ba zanyi abunda kake so ba”. ya jinjina kai sannan ya daki tsakiyar kanta da gindin bindigar, ta saki wata ƙara,”ba zaki gane abunda nake nufi ba saina dawo na sameki a yanda na barki”. yace da ita tukunna ya miƙe yasa kai ya fita ya barta da ruzgar sabon kuka, tare da neman tallafin ubangiji.
“bana tunanin akwai wani abun cutarwa da zai riskeki ki kasa guje masa saboda ke ɗin ƴar baiwa ce. ba wannan macijin da kika gani kaɗai ba, har mutum sai kinso zai ya cutar dake, dan haka duk sanda wani abu mara kyau ya riskoki ki ambaci Allah sannan kuma kiyi kamar yanda na faɗa miki”.
wannan Kalaman na Kulu suka haska acikin kaina a wannan lokaci, dan haka ban tsaya wani aune-aune da tunani ba na dunƙule hannayena tare da rumtse ido, tsam. tsohon ya dawo daga shi sai sauran kajeran wandon daya rage masa yana ƙoƙarin cire shi. sa’annan Mairo ta buɗe idanunta ta watsasu cikin nasa, sauyin launin daya gani a ƙwayar idon nata yasa shi razana yaja da baya, sai kuma ya dake ya ƙara tamkewa yana dawowa zuwa ciki, lokacin Mairo ta buɗe tafin hannunta daya jima a damƙe aikuwa nan take wani abun mamaki da alajabi ya bayyana wanda ita kanta saida ta tsorata. kunamu ne manya kamar suna sauka ne daga jikinta sai dai ba daga jikin nata suke fitowa ba, nan da nan kuma suka cika ɗakin kamar nanne rumbunsu, gaba ɗaya sai suka yi kan mutumin kamin ya farga daga guduwar da yake sonyi tuni sun haye masa jiki, ya fara ihu tare da kiran sunan ƴan’uwan nasa akan suzo su taimake shi, wanda ke gadinsa a baƙin ƙofa shi ɗaya ya iya jin ihunsa, dan haka ya shigo ciki a guje, sai dai abunda idonsa yay tozali da shi yasa ya dakata yana jefawa Ogan tambayar meke faruwa. cikin tsananin azabar da yake ciki yay masa nuni da Mairo wadda ke rakuɓe daga jikin bango tsoro duk ya gama cikata, “ku fita da ita ba mutum bace…wayyo Allah ku nemo maganin kunama karsu ƙarasa kasheni”. Yaron yace,”to Oga”. ya juya da sauri ya fice ya zagaya ta baya, ya zuge rigar rumfar ta ɗaya ɓarin ya janyo Mairo waje da lallaɓawa yana faɗin ta ɓace musu da gani, sannan ya zuge rigar rumfar duka wai ko da hasken rana zaisa Kunamun su koma inda sika fito ko kuma su mutu, amma ga mamakinsa sai ya ƙara ganin suna sake shigewa jikin mutumin shi kuma yana ihun harbin da suke masa. sauran abokan harƙallar suka yo kansa anata ƙoƙarin ganin an janye shi daga cikin kunamun amma babu hali, Mairo tasa kuka dan a ganinta idan ya mutu ita ta kasheshi bayan kuma ita bata san taya akai kunamar tazo ba, tana tsaye anan tana dubi-dubi taji an janyo hannunta, mutanen da akayi kidnapping duk suka sami fitowa saboda babu attention ɗin wani security akansu, duk hankulansu yayi kan Ogansu da ganin ta yanda za’ai su kuɓutar da shi. “zo mu tsira da ranmu”. Matar dake riƙe da hannun Mairo ta faɗa tana janta ita kuma turjewa. “Ki tsaya acire masa wancan kunamar ni ban san ya akai tazo ba”. Matar bata saurareta ba ta ƙara figarta ganin sauran na neman tsere musu. duk yanda Mairo taso ta ƙwace kanta daga hannun matar amma ta kasa, ƙarshema mutum biyu suka haɗar mata suka jata. haka suka nausa jeji suna ta gudu, babu hanklin kowa daya kawo kansu sai daga baya nan suka fara sakin harbin bindiga, sunyi nasarar samun wasu, wasu kuma Allah ya taimaka sun tsira. sai da suka yi gudun kusan awa sannan suka rarrabe kowa yay ta kansa.
ni kaɗai na fito titi ina tangal tangal ina haki, idanuna ko gani basa yi bare na san inda nake jefa ƙafata. nayi nisan tafiya ina yiwa kaina jagora, ƙafafuna kuwa sai zubda jini suke saboda irin abubuwan dana taka kasancewar babu takalmi a ƙafata, ga raɗadin zafin da ƙafar keyi min, ga ban san a inda zan iya tsayawa ba bare na zauna ta huta, haka dai na shiga lalube da hannu harna kai ga wata bishiya na taɓota, na sauke ajiyar zuciya nauyayya na jingina da jikin bishiyar sannan naja jiki na sulale na zauna ƙasa. babu abunda nake buƙata a wannan lokacin irin ruwa, maƙogarona ya bushe yawun bakina ya ƙafe. cikin azama na miƙe naci gaba da tafiya a wahalce dan ban manta da maganar mutanen da muka gudo tare ba suna jadadda min akan karna tsaya ko hutawa sai na tabbatar dana kawo inda mutane suke, basu san da cewar ji kawai nake ba amma ganin Mairo ya ɗauke tuni, kuma ganin ana cikin nafsi-nafsi yasa ban faɗa musu a halin da nake ciki ba, illa godiya da nai musu na kamo hanya har Allah ya fito dani nan da ban san ina bane, sai dai na kanji kamar sautin gimlawar ɗai-ɗaikun motoci.
a sanda naji na ɗora ƙafata bisa kwalta, daga gefe naji an hankaɗani nayi sama na faɗo ƙasa tim. Kafin na samu damar yin wani tunani akan inda nake, ko neman taimakon a ɗagoni sai naji duk jikina yay collapse, idanuna sun lumshe, hankalina kuma na neman gushewa gaba ɗaya.
duk yanda mai motar ya kai muƙara wajen taka burkin motar tasa dan ganin ya kaucewa Mairo sai daya ƙwace masa, yasa duka hannu biyu ya doki stearing tare da kifa goshinsa akai. yay shiru kamar ba zai ɗago kamin yaja dogon numfashi ya furta,”help me Jesus”. muryar tasa ta fita acikin wani irin amo, sannan ya ɗago ya dubi yarinyar daya buge sheme ƙasa jini na malala, da hanzari ya buɗe motar ya fita ya ƙarasa gareta da sassarfa ya ɗago kanta, bakinsa motsi kawai yake amma ya kasa cewa komai sai bin jikinta yake da kallo da kuma jinin dake zuba daga kanta. ya ruɗe, ya rikice, ya dabarbarce ya rasa abunda ya dace yayi, sai yaji kawai ruwan hawaye sun cika masa ido, ya janyota zuwa saman cinyarsa yana tattaɓa fuskarta, “Girl, Girl open your eyes”. a sama-sama take jin maganarsa, sai dai sam bata fahimtar me yake cewa, ta buɗe lumsassun idanuwanta ta zuba ƙwayar idonta akansa tamkar tana ganinsa, sai kuma ta mayar ta rufe, numfashinta na up and down, da murya can ƙasa tace,”ruwa”. baiji me tace ba dan haka ya kai kunnensa saitin bakinta yana cewa,”say it clearly i can’t hear you well”. ba dan taji me yace ba sai dai ta ƙara maimaitawa dan a yanzu babu abunda take buƙata sama da ruwan, Daga haka bata sake sanin komai ba jikinta ya saki gaba ɗaya. nan take Emanuel ya kuma ruɗewa, kun san inyamuri da tsoro, gani yake daya miƙe da ita mutane zasu yi masa caa aka duk da yasan hanyar ba hanya ce ta jamaa ba, babban tashin hankalinsa ma kar yarinyar ta mutu.
ya ɗaukota jini duk ya wanke mata fuska, ya buɗe bayan mota ya zirata aciki, hannunta ya faɗi akan ƙirjinsa ta damƙo sarƙar cross ɗin dake wuyansa ta tsinko. ya dubi sarƙar ya dubi hannunta ya rumtse ido, dama shi tun tasowarsa daga abuja yaji ajikinsa wani bad abu zai faru da shi, tunda yaga star ɗin jikin sarƙarsa tayi duhu, ya buɗe hannunta zai cire sarƙar sai yaji ta riƙeta da kyau dan haka ya barta ya rufe murfin ya zaga ya shiga yaja motar with high speed, tuƙin yake amma hankalinsa gaba ɗaya na kanta, ya miƙa hannunsa guda ta baya ya riƙo nata, yaci gaba da dariving da hannu ɗaya, fatansa karta mutu, gashi there is no any hospital nearby bare ya miƙata, haka dai har ya shigo garin ikoyi.