NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Wattpad: Oum_Ramadhan.
08145146915.

Comment&Share.
SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

20)
Lagoon Hospital, 17B Bourdillon Rd, Ikoyi, Lagos.
shigowarsa cikin hospital ɗin yana yin parking ko rufe motar bai tsaya yi ba ya ɗauketa ya nufi emangency da sauri, nurses ɗin dake tsaye a emergency ɗin suna ganinsa suka turo gado suka shiga special room da ita, Emanuel na tsaye a varander yana ta kaiwa da komowa hankali a hargitse, tsawon minti ashirin likita ya fito daga room ɗin sannan ya buƙaci nurse data ce Emanuel ya biyo shi office.
acan office Dr Simon kema Emanuel bayanin sai anyi mata surgery aciki saboda glass ɗin daya caki cikinta ya shige sose, kuma rashin aikin zai iya haifar da matsala babba ga yarinyar at the end ma a rasata. Emanuel ya rumtse ido gam tare da dafe goshi, ba shi da wani choice daya wuce ya amince, tunda shine silar halin da take ciki, kuma ko da ace ƴan uwanta zasu zo suma amincewar zasu suyi saboda ta rayu. ya karɓi takardun da Dr Simon ya miƙo masa, yasa hannu akai sannan ya bar office ɗin ya koma mota, yana kallon yanda wayarsa keta ringing da sunan MD da kuma Sectery amma babu kiran da yayi picking aciki, ƙarshe daya ga kiran na neman damunsa sai ya kashe wayar gaba ɗaya.
“Nurse! bring injection quickly”. Dr Simon ya faɗa yana ci gaba da aikinsa. da sauri Nurse ɗin ta miƙo allurar ya amsa yaywa Mairo, tunda aka kammala tiyatar Dr ya tsaya yana duban fuskar Mairo da ƙirjinta na tsawon daƙiƙu, sannan ya maida dubansa ga Nurse ɗin kusa da shi yana girgiza kai yace,”her health is fading. Bring the oxygen fast”. yana saka mata oxygen ɗin yake ƙara faɗin,”Nurse prepare the CPR”.
wucewar awa da mintuna shiru-shiru basu fito daga ɗakin tiyata ba, ganin shirun yayi yawa tsoron da Emanuel keji ya ƙara ninkuwa, ya fito daga motar jiki a mace ya nufa ward ɗin da suke, zuwansa yayi dai-dai da fitowar Dr Simon daga ICU da waya maƙale a kunnensa yana magana da wani likitan. Emanuel yasha gabansa dan sam Dr Simon bai lura da shi ba, ya dafa kafaɗar Emanuel yana ci gaba da tafiya. Emanuel ya tambaye shi,”Dr what is her condition now?”. ya tambaya anxiously. “Your patient is in dire state, we can not say anything for now. but relax we are trying all we can”. likitan yace da shi yana ci gaba da tafiya. Emanuel ya nemi kujera yay zaman daɓaro, yanzu idan yarinyar nan ta mace ya zaiyi alhalin bai san daga ina take ba. acan ɗakin tiyata kuwa ayanzu manyan likitoci uku ne akanta kowanne acikinsu jiki sanyi ƙalau, almost 3hours kenan da gama yi mata surgery ɗin amma har yanzu bata farfaɗo ba, wanda hakan yasa suka fara cire rai da farkawarta, rigima ta fara kaurewa a tsakanin likiticin su biyu, Dr David na faɗa akan mene ma yasa Dr Simon yay gaggawar yanke hukuncin ai mata Surgery, yanzu gashi nan idan yarinyar ta rasa ranta zai iya jawa asibitinsu matsala, shima Dr Simon masifar yake masa ai rashin sanin makamar aikinsa ne ya shi yake faɗin haka, Dr Friday daya zama madiater shine me aikin basu haƙuri. sai kowannensu ya nufi ƙofa zai fita a zuciye, amma ƙarar na’urar da ke nuna cewar Mairo na da rai shi ya dakatar da fitar tasu, Dr David ya dawo da sassarfa, haka ma Dr Simon da Nurses suka ƙarasa gareta a hanzarce.
Bayan wucewar wani lokaci Doctor Simon ya fito, Emanuel yay tsaye jingine da bango yana fuskantar ICU ɗin, da sauri ya sha gaban Dr ɗin yana ƙara tambayarsa halin da ake ciki, yay masa murmushi tare da cewar ya biyo shi office, haka Emanuel yabi shi sai dai bai bar waigen bayansa ba, har sai da idanunsa suka ga an fito da Mairo anyi wani room ɗin da ita kana ya sami natsuwar bin bayan likitan, but still zuciyarsa bata bar taraddadin abunda likitan zai faɗa masa ba.
Emanuel ne zaune kan kujera yana facing likitan tare da sauraron bayanin da yake masa, tun a furucin farko daya ambaci amnesia yaji hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi.
“mun samu ta farfaɗo and we thank God jikin nata da sauƙi, sai dai kuma ta sami matsala ta Memory Loos ciwon da muke kira da amnesia saboda buguwar da tayi aka, so she will be Inability to remember her past for a long period of time…”.
ya sauke ajiyar zuciya yace da Dr,”for how long will she remember everything?”. “zai iya taking nata 3-5months.”. ya miƙa hannu ya karɓi kati na magungunan da za’a siya sannan ya fita. kai tsaye pharmacy ya nufa ya siyo magunguna da alluran duk da ake buƙata kana ya wuce ɗakin da aka kwantar da ita. tun daga window yay tsaye yana kallonta yanda aka ɗaura mata drip, fuskarta naɗe da bandage haka ma ƙafarta ɗaya, yafi tsawon daƙiƙu uku a bakin tagar yana jin kamar ba zai iya shiga ciki ba saboda yanda tsigar jikinsa ke tashi, sannan ya dawo bakin ƙofar room ɗin ya tsaya, har sanda Nurse ta shigo ta karɓi ledar pharmacy ɗin daga hannunsa, ta ƙarasa taje tayi allura a ruwan drip ɗin, bayan fitarta ya ɗaga ƙafa kamar mara lakka ya ƙarasa bakin gadon, tsananin tausayinta yay mugu mugun kamashi, daga irin yanda take numfashi ya isa ya fahimtar da shi irin mawuyacin halin da take ciki. jin zafin ciwon nata yake ajikinsa, haka duk wani shiga da fitar numfashinta auna shi yake da nasa. ya zauna a gefen gadon ya kai hannu ya taɓa wuyanta yaji temperature nata very high, yayi saurin ɗauke hannu sannan ya miƙe ya fita da sauri ya koma office ɗin Dr Simon yake shaida masa yanayin zafin jikinta daya zarce tunani, tare suka dawo da Dr wanda yana zuwa ya kuma yi mata aune-aune sannan ya ƙara tabbatar masa da babu wata matsala da zarar ruwan ya ƙare zata farka kuma temperature nata ma zai dawo normal. kuma ko da ta farka kar abata komai becouse aikin da aka mata general anesthesia ne zai iya ɗaukanta 24hrs kamin taci wani abun, amma idan an samu Bowel sound ya zama present to za’a iya bata ruwan tea tasha, Emanuel babu abunda ya iya ce masa sai knooding kansa da yayi.
bayan fitar likitan Emanuel ya roƙi Nurse ɗin dake gyara table ɗin da aka ɗora magungun,alfarmar ta zauna ta kula da ita zaije ya dawo. baifi 30minutes ba sai gashi ya dawo hannunsa riƙe da manyan ledoji, ya zaro 5k a aljihu ya bawa Nurse ɗin ta amsa tana ta murna. shaf ya manta da batun wata waya sai ayanzu daya jiyo ringing ɗin wata wayar daga waje sannan yasa hannu ya ɗauko tasa a aljihu ya kunna. yay dialling number MD sai da kiran ya kusa yankewa sannan MD ya ɗaga yana masa masifar ina ya saka wayarsa. yace da shi,”i got an accident…hankalina bai dawo jikina ba sai yanzu”. a zafafe Md yace,”Emanuel are you Mad?, you have an accident kuma ba zaka kira ka faɗi situation ɗin da kake ciki ba…yanzu kana wane hospital?”. “ka bari zuwa safiya zan sanar da kai, amma please karka bari Dad ya san da wannan. idan ya tambayeka akaina ka san ƙaryar da zaka yi masa”. dan haushi ma Md ya kashe wayar ba tare daya amsa shi ba, shi kuma yaƙi faɗa masa ne gudun karya faɗawa Dad ko kuma shi yace yanzu zai taho alhalin kuma yana da iyali.
har drip ɗin ya ƙare bata farka ba, har sha biyu na dare yana tare da ita kamin ya tashi ya tafi hotel ya kwana acan, ya barta da Nurse ɗin ɗazu yace ta kwana da ita. washegari bai shigo asibitin ba sai around 9, hankalinsa gaba ɗaya na kan Mairo da ita ya kwana a ransa, abunda ma ya hana shi sammakon shigowa sai daya biya office. kai tsaye ɗakin da take kwance ya shiga, tare suke shida Md, da mamakinsa sai yaga bata kan gadon kuma babu kowa a ɗakin, yana dube-dube sai yaga Nurse ta fito da ita daga toilet tana dafe da kafaɗar Nurse ɗin tana takawa da ƙyar, ya zuba mata ido sai ya miƙe ya ƙarasa ya ɗaukota ya kawota kan gadon ya jinginar da ita ajikin pillow. Nurse ɗin tayi masa bayanin jikin nata da sauƙi dan Dr ma yace zuwa dare za’a iya warware mata bandage ɗin fuskarta. Mairo tayi shiru tana sauraronsu dan jinta take a wata sabuwar duniyar, ita kanta maganar da suke yi ba ganewa take ba, gashi ba ganinsu takeyi sose ba hasalima saita kusa rumtse ido gaba ɗaya ne take samun ganin abu very tiny. “How are you feeling now?”. Emanuel ya tambayeta yana kamo hannunta ya riƙe cikin masa. ta dai ji maganar da yayi amma bata san me yace ba, tayi shiru sai Nurse ɗince tace da shi,”i noticed like she is not hearing english”.
Md ya girgiza kai da cewa,”i also noticed that”. Emanuel ya dube shi yace,”to mene abunyi kenan?”. “amma ai lossing memory baya shafar language na mutum”. Debora tace,”um baya shafar yaren mutum, ita din bahaushiya ce tunda ɗazu da hausa tayi magana”. Md ya ɗaga kafaɗa,”alright, shima english ɗin da sannu ai zata iya making”.
“me taci data farka?”. Emanuel ya tambaya. Deborah tace da shi,”babu komai yanzu dai za’a iya bata”. ta ɗauki ƙaton tea flask ɗin da suka zo da shi ta zuba tea a mug sai ƙamshi yake, ta miƙawa Mairo cup ɗin tana cewar ta amsa da yake ita tana jin hausa kaɗan-kaɗan kasancewar tayi zaman Kano. Mairo ta miƙa hannu tana laluben ta inda zata amsa Cup ɗin, Duka suka tsaya dubanta da mamaki kafin Debora tace da ita,”me ya sami idon naki ne, gata inda nake miƙo miki abu ke kuma kina miƙa shi ta wani wurin”. muryarta na rawa kamar zata yi kuka tace,”ai bana ganinki ne sosai”. “ba kya gani sosai?”. Mairo ta ɗaga kai, “ehh ina ganin duhu amma bana ganin hannun naki”. Debora ta sauke numfashi sannan ta dubi Emanuel wanda ya tsareta da ido yana jiran cewarta tace masa,”akwai matsala fa a idanunta, she says she cant see very well”. Emanuel ya juyo yana duban Mairo da mamaki, how comes hakan zai kasance, to ko dama ita makauniya ce shi yasa ta sanyo kanta kai tsaye titi har ya kasa kauce mata. Md ya katse masa tunani da cewar,”what are you thinking?”. yace da shi, “ina tunanin mene yay cousing na ciwon idon nata, dama can da ciwon ko kuma a accident ɗin nan ne?”. Md yace,”gashi kuma babu wani abu da zata iya tunawa bare ta bada amsa”. Emanuel yayi shiru, Md ya ƙara cewa da shi,”ya kamata fa Police su shigo cikin lamarin nan, tunda ba za kai ta zama da yarinya ba, ai kayi iyaka yinka tunda ka kawota asibiti akan lokaci”. ya girgiza masa kai,”bana so Police su shiga zance i have already told you that…ko asibiti ma da sukai maganar rufe bakinsu nayi da kuɗi”. “to kana nufin zaka ke ta zama da itane?”. ya bashi tabbacin hakan ta hanyar jijjiga masa kai. “to office fa?”. “ai kana nan, ko ba zaka iya aiwatar da aikin company ba idan bana nan?”. Md baice da shi komai dan ya rasa ta cewa gaba ɗaya.
Debora ce ta bawa Mairo tea ɗin tasha, sannan ta bata magunguna dayi mata allura. Emanuel ya tashi daga kan kujerar da yake ya koma gefen gadon ya zauna, yana riƙe da hannunta ya tambayeta,”what is your name?”. da mamakinsa sai yaji tace,”my name…”. sai kuma tayi shiru. “ehen said it your name is what?”. “i dont know my name”. a yanda tayi maganar saita bashi tausayi.
suna ta hira shi da Md ita kuma duk tana jinsu bada sanin abunda suke faɗa ba ko kuma ganinsu ba, ita dai har tsawon awannin da suka shuɗe Emanuel bai saki hannunta ba. sai around ƙarfe biyu na rana sannan suka fita shi da Md zuwa restaurant suka ci abinci suka dawo, time ɗin kuma tayi bacci, ya tambayi Deborah ya sauƙin jikinta tace masa, “ai bayan tafiyarku tana ta kuka wai idonta na ciwo”. “ko asibitin ido za’a kaita?”. ya jefa tambayar ga Md. sai Deborah tace masa akwai likitan ido da yake zuwa da daddare.
misalin bakwa na dare Md ya umarci abokin nasa daya tashi su tafi, Emanuel yace da shi ya tafi shi zai kwana nan ne. Md ya dube shi da tsantsar mamakinsa yace,”zuwa wane lokaci zaka bar yarinyar nanne ka koma harkar gabanka?”. “ni kuma for how many times kake so nata maka repeating cewar zanke zama da ita anan zuwa lokacin da za ai discharging nata”. “amma kana tunanin zasu sallameta nan kusa ne?, muna fa da meeting cikin satin nan kuma kasan ya kamata kake shigowa office saboda hakan”. “zanyi posponding meeting ɗin”. “zuwa yaushe?”. “time ɗin da zamu bar asibiti”. “then sai kayi ya da ita kuma?”. “zata zauna tare damu har lokacin da tunaninta zai dawo a nemi iyayenta”. Md ya tsaya yana yi masa wani irin kallo, ya lura gaba ɗaya nema yake ya maida al’amarin yarinyar kansa, shi kuwa Emanuel gani yake kome ya faru da yarinyar shine sila dan haka dole ya tsaya ya kula da ita tunda babu kowa nata.
Md ya nufa ƙofa yana ce masa,”so ni dai good nite”. kamar ba zaice masa komai ba sai yace,”karka kawo mana tea da safe na lura kaman bata sonsa”. “to sai mene take so?”. Emanuel ya ɗago yana tsareta da ido, dariya ta suɓucewa Md yace da shi,”ask her mana”. Emanuel yay masa wani wawan kallo sannan ya ɗauko wayarsa daga aljihu ya kira Deborah, ko minti biyu ba ai ba sai gata tazo, yace ta tambayi Mairo abunda tafi son ci, Mairo ta girgiza kai a sanda Deborah ta tambayeta alamar babu komai.
Emanuel yana latsa wayarsa yace da Md,”abu soft ake da buƙatar taci so please ka taho da curstard and do not be let”. Md ya kyaɓe baki yace,”aini ba ɗan aikinka bane da har kake faɗa min wani karna makara, you will see me a duk sanda na gama hidiman gabana”. “ka barshi ma ba sai kazo ba”. Md yay dariyar ƙularwa sannan yace,”anyway no escort?”. “kasan hanya ai”. Deborah dai murmushi tayi saboda tun ɗazu tana ganin yanda suke buga dirama, kuma duk Md ke jansa da tsokana.
yayi shiru ya kasa ɗauke ido daga kanta, tausayinta yake da dukkan ransa, dan ji shine silar wannan halin da take ciki, kansa yake ta ɗorawa laifin duk da cewar itama akwai nata na rashin bin ƙa’idar tsallaka titi, dan haka ba zai yafewa kansa ba har saita sami lapia completely.
around 9 likitan ido yazo dubata, yay gwaje-gwajensa ya tabbatarwa da Emanuel tana da buƙatar aikin ido a babban asibiti da yake musamman na ido ne, amma for now zai bata wasu maganin da zata yi amfani dasu ciwon ya lafa. tare suka fita da Dr ɗin yaje ya siyo maganin daya rubuta, tana baccin ya ɗiga mata maganin sannan yaywa Deborah sallama ya wuce makwancinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button