SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Kuyi haƙuri dani aradu na kamu da lalurar ƙiwar typing, ku san yanda kukai kuka samo min magani tun kan lalacewar tayi yawa????.
Comment&Share.
SIRRIN ƁOYE
By Oum Ramadhan✍????
23)
ba ƙaramin daɗi Emanuel yaji ba a sanda driver yace da shi Mom bata dawo ba, dama yayi tunanin ko zata rigasu sauka tunda tace masa ƙila ta biyo flight a yau, to inma dai yau ɗin zata dawo fatansa su rigata zuwa gidan basu je su sameta ba, dan Allah ya sani baya ƙaunar faɗanta.
driver nayin parking acikin gidan wurin da aka tanada domin aje motoci, daga Emanuel har Mairo kowanne ya fito cikin fushi ya ɗauki hanyar cikin gida. ba wai dan tasan hanya ba, sai dai ta tsaya ne sai da yayi gaba sannan tabi bayansa tana aukin ƙunƙuni.
suna shigowa falo Buky(house maid) dake aikin goge tv tayi saurin zubewa tana kai masa gaisuwa, kafin daga bisani ta dubi Mairo tace mata,”welcome Maa”. Mairo ta murguɗa mata baki, sannan ta nemi ɗaya daga cikin lumtsatstsun cushions ta zauna tana lumshe ido, me aikin ta ƙaraso ta duƙa gabanta ta cire mata takalmin ƙafarta me shegen tsini, har lokacin kuma bata bar ɓata rai da faman haɗe gira ba tana girgiza ƙafa.
Emanuel kam tunda ƴar aikin ta karɓi suite ɗin jikinsa daya cire, yay upstairs ɗakinsa, ba tare daya bi ta kan Mairo ba, domin yanda yake jin haushinta duka zai iya biyo baya akanta.
sai data gama kumbure-kumburenta sannan ta miƙe daga kan kujerar, ta tsaya tana duban parlon da tunanin ma ina ne taƙamaiman hanyar ɗakinta, tayi tsaki tana cire top ɗin dake jikinta ta yasar kan kujera, sannan ta ɗauki hanyar dining area, ta ɗaga zara-zaran labulayen dake rufe da wajen, anan taga ƙofar kitchen dan haka kai tsaye ta shiga ciki, ta isa ga oven ɗin data gani a kunne ta kashe sannan ta buɗe ta ɗauko kazar dake ciki tasa a plate, ta sake isa friedge ta buɗe ta ɗauko youghrt me sanyi.
ta wani entrance ɗin daban da wadda ta shigo ta fita, wadda ta ɓullar da ita ga wani part na daban me ɗauke da ɗai-ɗaikun shuke-shuken fulawowi masu kyau. ƙofofin ɗakuna guda huɗu jera da wurin, biyu daga ɓarin hagu biyu daga dama, duka doors ɗin colours guda ne, dan haka tasa kanta tsaye ga ƙofa ta biyu dake a ɓarin dama ta buɗe ta shiga.
bedroom ne me girma da medium italian bed acikinsa, wadrobe na fuskantar gadon sai mirrow dake daga jikinsa, da kuma wani medium glass table dake gaban gadon, rabin bangon bedroom ɗin manne yake da stickers na hoton Ronaldo, ɗakin ya haɗu sosai dan sai zuba ƙamshi yake, ki mai nasa blue and white ne, ta ɗaga labulen da take tunanin window ne sai taga wata ƙofa ce ta daban, nan ta murɗa handle ta buɗe, toilet ne wanda ya haɗu iyakar haɗuwa, daga kallo ɗaya zaka gane komai na cikinsa daga waje akayi order ɗinsa kamar yanda duk wani kaya na gidan yake nunawa, saita janyo ƙofar ta rufe.
da guntun tsaki ta fito daga bedroom ɗin ta buɗe ƙofan kusa da shi, nan kuma parlo ne me ɗan girma shima, yasha wasu azababbun kujeru da kayan ƙawa na decorting parlo, sai medium plasma dake manne daga ɓarin gabas, da hotunan ronaldo a mammane a jikin bangon parlon kamar dai na bedroom ɗin, alamu dai sun gama nuna mamallakin ɗakin cikakken ɗan ƙwallo ne kuma masoyin Ronaldo, ta maida ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso cikin parlon daya gwauraye da sanyin Ac haɗe da wani daddaɗan ƙamshi.
zama tayi kan kujera tare da kunna tv ta nemo channel ɗin da ake wani american film, tana kallo tana cin kaza tana kurɓar youghrt irin na wadda hankalinta ke kwance duniya tayi mata daɗi.
tana gamawa ta jawo tissue ta goge hannu sannan ta jinginar da kanta ga kujerar taci gaba da kallon dake mata daɗi, har sanda idanunta suka fara rufewa tukunna ta miƙe ta koma bedroom ɗin data fito ta kwanta, a yanda take zazzaƙewa ka rantse dama can ƴar gidan ce.
gidan tsit kake jinsa kowa na ɗakinsa, sai tvn parlo dake kunne with low volume, ƙarfe biyar na yamma Granny ta fito daga ɗakinta, ta ƙwalawa Buky kira sai gata ta bayyana a gabanta, tana dubanta tace,”where is Gift?”. a ɗazu da suka shigo Emanuel sai daya faɗa mata sunan Mairo(Gift) kafin ya wuce ɗakinsa, dan haka bata tafi tunani ba akan ɓaƙon sunan daya zo gidansu, kanta a ƙasa tace da Granny,”tun ɗazu ta bar nan, may be she is in her room”. Granny ta kaɗa kai, sai dai a tunaninta wanne ɗaki ta wuce dan Emanuel yace da suka shigo bai nuna mata inda zata zauna ba, shi dai kawai ya barta a parlo, ita kuma abunda ya hanata fitowa ta sami Mairo a lokacin kanta na mata ciwo, kuma ko da tace Emanuel ɗin yasa Buky ta kira mata ita tazo ɗakinta sai yace ta kwanta tayi baccinta kawai, indai Gift ce tazo ƙara mata zafin ciwon zata yi, ba dan taso ba ta kwanta ɗin bata ga Mairo ba a time ɗin, amma tunda Emanuel ya shigo ya bata labarin komai taji zuciyarta ta shiga zullumin son ganin Yarinyar.
a ƙasa babu wani ɗaki bayan nata dana su Joseph da Obi, Emanuel da Mom da Dad duka a sama suke, saboda haka tasan da wuya idan ba part ɗin su Joseph tayi ba, tunda hanyar da upStairs yake indai ba kai ɗan gidan bane ba sani zaka yi ba, haka nata ɗakin ma kamar ba’a parlo yake ba, sai ka san gidan sannan zaka iya sanin ta inda ƙofar part nata yake.
kitchen ta shiga ta sada kanta ga ɓangaren su Joseph, bedroom ɗin Obi ta fara buɗewa dake daga ɓangaren dama taga bata ciki, dan haka saita nufa na Joseph tana buɗewa kuwa ta ganta tana bacci hankali kwance, taja blanket ta rufe jikinta, Granny ta godewa Jesus a ranta da bai dawo da Joseph a wannan lokacin ba ya sameta akan gadonsa, dan shi mutum ne irin mahaifiyarsa da basa son baƙi sam, idan da ya shigo ya ganta sai ya mammaujeta kafin ya kai ƙorafin a sauya masa komai na ɗakin, tunda har wata stranger da basu san daga inda take ba zata taɓa kayansa.
fuskarta na bayyanar da siririn murmushi ta ƙaraso ciki, dama acikin bayanan da Emanuel yayi mata akanta ɗazu, ya shaida mata tana da bacci kamar kasa ko me laulayin ciki, wuyarta taji ta ita kaɗai ko kuma taji mutum a kusa da ita zata ɓingile a jikinsa. ta isa gadon ta zauna daga gefe tana kallonta, tasa hannu ta shafi gefen fuskarta, yarinyar tana da kyau sosai, a yanda fuskar baccinta ya nuna zaka san me ƙiriniya ce ba irin ƙiriniyar yara ba, tun a ɗazu da Emanuel ya bata labarinta taji ta shiga ranta tun bata ganta ba, tana sonta da tausayin halin da take ciki da dukan zuciyarta, haka kuma tayi farin ciki da zuwan yarinyar duk da bawai zama ne na dindin ya kawota gidan ba, ko ba komai gidan zaifi mata daɗi yanzu ta sami ƙawar ɗebe kewa, kullum ita kaɗai take zama a gidan tunda Gloria itama ba zaman gida take ba, ƙarfe 7am take fita office sai 6pm idan tana ƙasar kenan.
Granny ta shiga tashinta da kiran sunanta da suka raɗa mata Gift, dake me nauyin bacci ce har saida tasa hannu tana ɗan taɓa ƙafarta sannan ta shiga buɗe idonta a hankali tana murzasu har suka buɗe duka ta saukesu kan Granny tana miƙa.
Granny ta sakar mata murmushin daya bayyanar da haƙoran tsufanta sannan tace mata,”get up and take shower, we are going out”. ta gyaɗa mata kai kawai tana ziro ƙafafunta ƙasa, tare suka fito, zata shiga bedroom Granny ta dakatar da ita da faɗin,”a’a ba nan zaki shirya ba”. ta faɗa holding her hand to make her way to her own room after she called Buky tayi informing nata tai fixing Joseph’s bedroom.
bata jima a wanka data shiga ba ta fito ta shirya cikin tsangallalun kayan da suka koma kayanta a yanzu, ita da Granny suka fito a tare riƙe da hannun juna, a parlo Granny ta danna landline ta kira wayar driver akan ya tada mota zai fita dasu anguwa.
Acorns & Gold Boutiques, Abuja.
Granny ce keta aikin jidar kayan sawa acikin store ɗin kamar me shirin haɗa akwatin lefe, kaya masu kyau da tsada take ɗiba, tun daga kan gowns, mini skirts, t-shirts, bomshots, bras, high hill and flat shoes, wrist watch, earings, bangles da sauransu, haka ta dinga ɗiba tana zubawa a basket ɗin da Mairo ke biye da ita, sai data ɗibi kayan da take ganin zasu isa Mairo sakawa zuwa ɗan zaman da zatayi dasu sannan suka isa wurin biyan kuɗi tai payment da Atm card.
ma’aikacin store ɗin da kansa ya ɗauki kayan ya kai har mota saboda yasan wace Granny, a kaf Abuja yankin Asokoro anyi ittifakin babu wani family da suka san darajar ɗan Adam suke martaba shi da girmama shi irin gidan General Tosin Afafa, ahali ne da suke kyautatawa kafiri ɗan’uwansu harda musulmi, Allah ya wadatasu da arziƙi me yalwa, kuma basu kasance cikin irin masu arziƙin da suke ƙam ƙam da dukiyarsu ba, dukiyarsu suna bada ita ga kowa ne, wannan dalili na kyautatawarsu ya saka suke samun adu’a iri-iri daga musulmi akan Allah yasa su karɓi hasken musulunci.
daga nan kuma suka wuce Perfect Trust Cosmetics, anan ma kayan kwalliya ne kit guda ta kwasa sannan suka fito suka wuce Agabason Perfumery, anan ma turaruka ne ta kwasa masu tsada da ƙamshin gaske, kafin daga bisani kuma su wuce wurin saloon, aka wanke mata kai, aka wanke ƙafa akai gyaran farce tare da fixing nails, a taƙaice dai ta ko’ina saida Granny tasa aka gyara Mairo ta ƙara fitowa sak a ƴar addinin christian. sai da suka biya suka sha ice cream daga bisani kuma suka wuce gida, basu suka koma ba sai ƙarfe takwas da rabi na dare.
lokacin da suka dawo kowa na zaune a parlo ana hira banda Mom da bata nan, ba hirar komai mahaifin nasu ke musu ba saita rayuwa, su bar ganin shi me arziƙi ne, ya tara musu kuɗin da ko bayan ransa ba zasu yi talauci ba, namiji yay tunƙaho da dukiyar kansa bata ubansa ba shine ya cika namiji, kuma dukiyar kanka ita kake bugun ƙirji da ita, mutum baya kaiwa high level sai ya zama ɗan gwagwarmayar rayuwa sannan, shima ba haka ya sami wannan dukiyar da yake ganin ta masa yawa ba, sai da yay aiki da jininsa da ƙarfinsa, tun yana ɗan 13years yake fita waje yay cuɗanya da mutane iri-iri, shi bai sami wannan gatan da uba zai ɗebi maƙudan kuɗi ya bawa ɗansa ba wai saboda kar ya rasa na kashewa, a’a, tunda ya kai 15years idan ya tambayi kuɗi a gida Babansa cewa yake da shi ka nemi na kanka, su tambayi Granny zata basu labari. ya tsaida kallonsa akan Joseph yace masa,”saboda haka ka sake buɗe idanuwanka, ka farka daga baccin da kake, har yanzu acikinku kaine baka da hankali…kaƙi ka tsaida hankali kayi karatu kana biyewa abokan banza suna ɗoraka a motar da zata kaika tashar dana sani…ball kawai ka saka a gaba Joseph, ball kawai, nasha faɗa maka duk sunan da zakayi sai da ilimi duniya take yayinka, na maka faɗan na maka nasihar kaƙi kaji, kaƙi karatun na kaika company nanma kaƙi zama, ya kake so nayi maka Joseph, ranar da ƴan sanda suka biyoka kasan yanda naji?, saida na rasa jina da ganina na ƴan sakanni, zuciyata har yau bata bar ciwon wannan abin kunyar daka ja mana ba, amma shikenan kaci gaba idan kana ganin hakan shine dai-dai, akwai ranar da zaka wayi gari kaga babu ni a duniyar, na mutu an rufe babin rayuwata, na bar maka duniyar”. ya shiga ciccin magani, faɗan Dad kullum akansa yake ƙarewa, kamar kullum shi yake yin ba dai-dai ba, ya kamata Dad ya ƙyale shi akan batun karatu tunda yace masa baya so, ya ƙyale shi da maganar zuwa aiki tunda yace ba zai ba, ai suna da kuɗin da yafi ƙarfin ya fita yay aiki ako ina ne, shi ba za’a masa dole ba, yana da ƴanci.
a gajiye liƙis suka shigo Mairo na riƙe da handbag ɗin Granny sai lanƙwashe jiki take a lallai ita ta gaji da yawa, a kusa da Joseph ta zauna tana miƙe ƙafafu tare da fadin,”Uncle am very tired”. ta faɗa tana kallon Emanuel da suke facing juna, hararta kawai yayi, a sanda taji Granny na welcoming Dad sannan ne ma ta lura da shi, itama ta buɗi baki da cewar, “welcome back Dad”. ta ƙasan siririn medical ɗin dake idonsa ya kalleta ya amsa mata.
“sai yaushe Gloria zata dawo ne, this time aroud ta jima da yawa”.
Dad ya kalla Granny data yi masa tambayar yace,”they had just arrive back, sai suka sami saƙon zasu yi presenting seminar na oriflame a london, amma tace ba zasu wuce 3-4days ba zasu dawo”. “Yayi kyau”. ta faɗa tana miƙewa tare da cewa Gift ta tashi ta wuce ɗaki ta ajiye kayan.
Mairo ta sami tarba me kyau daga wurin Dad, wanda ya ƙudurta ɗaukanta tamkar yarinyar daya tsuguna ya haifa, ya ɗau alƙawarin zai kula da ita har zuwa ranar da zata sami lafiya tunaninta ya dawo su maidata wurin iyayenta.
a ɗazu daya dawo niyyarsa asaka hotonta a media da kuma sanarwa a gidan radio, ko Allah zaisa wani nata yaji, to Emanuel ya hana shi ya kafa masa hujja me ƙarfi akan rashin aiwatar da hakan, inda yace masa wani kidnapper ɗinma zai iya gani yazo ya karɓeta ba tare da ansa wane shi ɗin ba tunda ita ba’a cikin tunaninta take ba, Dad ɗin kuma ya gamsu, Obi ma ya goyi bayan Yayansa.
ƙarfe tara da rabi na dare suka hallara a dining area dan yin Dinner kamar yanda suka saba, tun daga breakfast, lunch and dinner duka tare suke yi. tun zamansu Joseph ke aika mata da harara, balle da yaga kowa na haba-haba da ita, kamar ɓarauniya zuwan yau kaɗai ta sace zuciyarsu, a hankali ya saki ƙwafar da ita kaɗai ta ji da take kusa da shi, suka haɗa ido ta turo masa baki gaba, cikin zafin nama ya daki dining table ɗin ya fuskantota yana nunata da yatsa da cewa,”Dad yarinyar nan ta raina ni, kalla fa yanda take murguɗa min baki”. Dad ya ɗaga masa murya,”mene hakan kake yi Stupid Brother kawai, is she not your sister…kuma baka kallon bata da lafiya”. yabi kowa da kallo da yanda suka yo kansa, abun ya ɓata masa rai ya ƙara jin tsanar yarinyar a ransa, shine auta a gidan, zai iya rantsewa da wayonsa dai Dad bai taɓa ɗaga masa murya ba sai a yau, yana masifar sonsa kasancewarsa ɗan auta, amma saboda zuwan wannan banzar yarinyar Yau Dad ne ke yin kamar zai duke shi, dama yasan za’a rina ai, tunda Brother ya basu labarinta yasan saita ƙwace masa fada a wurin Dad, saboda yana so ya ganshi da ƴa mace kuma Allah bai bashi ba, yana yawan faɗan yanda yake so ya ganshi da ƴa mace.
ba dan yana gudun kar Dad ya hana shi motar da yake so a siya masa ba, da babu abinda zai hana shi ɗaga waya ya kira Mom ya sanar mata da zuwan wata ƙazamar stranger gidansu, to matsalar ɗaya Dad ya gargaɗe shi yaja masa kunne akan cewar ya sake ya faɗawa Uwarsa sai yaga yanda zaisa ayi da shi a barrack, shi kuma Dad ba ya hane shi bane saboda gudun fitinar Gloria ba, sai dan ya barta ta kammala agenders ɗin dake gabanta, idan ba haka ba yanzu tana jin labari zata baro duk wasu activities nata ta dawo gida, har aka kammala cin abincin acikin ɓacin rai yake, yana jin kamar ya shaƙeta.
a ɗazu da yamma da Emanuel ya fito ya tarar su Granny basa nan, ya saka ƴan aiki suka gyara extra room ɗin da yake a sama na kusa da ɗakin Dad, both the bedroom and parlo, ya zama shine ɗakin Mairo. saboda haka yanzu da za’a tafi kwanciya su uku suka haura sama, da ita da Dad da kuma Emanuel, duk yanda Granny tayi da ita akan tazo su kwana tare taƙi tace,”a’a ni bana kwana da tsoffi, snoring suke a bacci”. basu Obi kaɗai ba, har Dad saida ya dara.
suna hawa stairs ɗin Dad ne ke agaba sai ita ke bin bayansa Emanuel kuma na biye da ita, tacewa da Dad,”ɗazu Uncle yay min faɗa akan nayi mistake wurin hawa flight, har yace zai zane ni”. Dad ya kira sunan Emanuel ya amsa, yace da shi,”baka san ita ɗin Auta bace, kuma ba’a yiwa Auta faɗa, karka sake idan ba haka ba raina zaiyi babu daɗi…ko kaima baka kalla saboda first born bane Mom ɗinka ko hararanka bata yi”. shi dai Emanuel murmushi kawai yake, Dad ɗin kuma yace da Mairo,”kiyi haƙuri ba zai ƙara ba daga yau…kuma duk wanda ya kuma yi miki faɗa kice Dad ya hana ke auta ce yana sonki da yawa”. “tom shikenan Dad ena nima ina sonka”. ta faɗa tana mintsilar hannun Emanuel tana dariya ƙasa-ƙasa, ya kai mata ranƙwashi dai-dai lokacin da suka hayo saman gaba ɗaya kowa ya nufa ɗakinsa dan kwanciya.
****a washe gari ƙarfe shida da rabi Emanuel ya leƙa ɗakin Mairo yace ta shirya da wuri zai kaita school, dan a jiya Dad ya sanar masa a yau ya kaita makaranta duk da agaba zata manta da karatun, to amma shi baya son zaman yaro a gida hakana indai ba ka kammala degree ko masters ba, ko kafin ka sami addimission cillaka wata makarantar yake.
ita dai tunda ya tasheta ɗin ya juya ya fita ta koma baccinta, bata farka ba kuma sai quater to 8, tai sauri tayi wanka ta shirya sannan ta fito, ɗakin Dad ta shiga ta tarar shima yana shiryawa, ta gaida shi sannan ta fito ta sauka zuwa ƙasa.
sakkowarta dining area ta nufa, Eze(me girka musu abinci) har ya kallama girki ya jera a dining ɗin, a yunwace take, dan haka taja kujera ta zauna, ta rasa irin cikinta ita kam ci kamar gara, tana da saurin jin yunwa kuma a asibiti an gwadata babu ulcer. bata tsaya tunanin jiran fitowan kowa ba ta buɗe flask ta fara zuba irishi ɗin da aka soya da ƙwai, sannan ta buɗe tea flask ta zuba tayi haɗin kauri na madara da bounvita. ta ɗauka fork zata kai bakinta Joseph ya isa a wajen, ya ɗaga hannu ya wanketa da mari yana nunata da yatsa yace,”wace ke da zaki zo ki zauna a dining tun Dad bai sauko ba, to bari kiji na faɗa miki karki sake ki ɗauki kanki matsayi ɗaya da ƴan gidan nan, wuyarta Mom ta dawo zaki gane kuranki, banza ƴar tsin….”. bai ƙarasa faɗin ƴar tsintuwar ba Emanuel ya sharara masa maruka kyawawa guda biyu ta kowanne ɓari, a gigice ya ɗago yana duban Yayan nasa da ɓacin rai ke kwance a saman fuskarsa, malolon baƙin ciki ya tokare shi a maƙogoro, ko tantama ba zai ba Yayansa ya hauka ce, kai kowa ma ya haukace akan wannan Yarinyar.
“Brother mari na fa kayi bayan ita ya kamata ka hukunta”.
“baka kalla ita din bata da cikakkiyar lafiya bane, kuma jiya me Dad ya faɗa maka?, to ka shiga hankalinka Joseph”. duka su biyun huci suke kuma kowa a wuya yake da ɗan’uwansa, a fusace Joseph ya bar wajen yana ƙananun maganganu, sai dai a masifar daya tafi yana yi bai rufe baki ba Granny ta buga masa remote a baki, zafi biyu ya haɗar masa, saboda haka yayi fushi ya fice daga gidan gaba ɗaya.
taso ta fahimci wani abu a maganganun da Joseph ya faɗa mata, a iyaka haɗe fuskar daya dinga nuna mata a daren jiya, da kuma hantara duk tayi zaton ko dan ita ɗin tana sakuwarsa ne, to amma a yanzu kuma a mari da kalaman da yayi mata ta gane ba faɗan sako da sakuwa bane, rashin so ne zallarsa, da abunda take son bada tabbacinsa akai, cikin abu biyu kwai ɗaya, ko ya zama ba Mamansu ɗaya da shi ba kamar yanda taji yace Mom zata dawo zata gane kuranta, ko kuma ya zama ba Mamansu ɗaya ba kuma Dad na nuna mata so fiye da shi. sai kuma ɗaya ɓari na zuciyarta yace mata duk cikin hasashenki babu ɗaya, ki tuna a asibiti Uncle yace miki za’a dawo gida kuci gaba da rigimar da ku ka saba kamar kaji ke da Joseph., me yasa ne take jin wasu abubuwan kamar bata taɓa sanin dasu ba?, ko da yake ai Aunt Deborah ta faɗa mata saboda bugewar data yi hakan zaisa ba komai zata ke tunawa ba na baya.
Emanuel ya dafa kafaɗarta ya zaunar da ita kan kujera, yasa handkey yana goge mata hawaye yace,”ki ƙyale Joseph mahaukaci ne yana da cutar Bipola disorder, harma ya kai matakin ƙarshe na Mania, kinga kuwa shi abin aiwa uzuri ne”. “what concern me da ciwonsa”. ta faɗa a sanda ta rufe ido tana girgiza kai. ta kuma yi ƙwafa da faɗin,”Mom zata dawo saita yi mana tsakani da shi idan ba haka kuma nake jangwalo ciwon nasa in kulle shi ɗaki babu wanda ya sani, ba zan buɗe shi ba har sai ya jiwa kansa rauni”.
“shirmen banza kawai ke da shi duk baku da hankalin…ki nutsu tun kan Babanku ya sauko yasa miki belt ajiki, ai dama ƙafa yake ɗaga miki ganin baki da lafiya”. Granny tace da ita a sanda take jan kujera ta zauna.
cikin fushi ta miƙe zata bar wurin ta kuma cewa da ita,”tabbas kina so kiyi kwanan cell, karki hankalta ki gani, gashi nan sakkowa ai”.
“ni dai dariya ce tawa dan ko haƙuri ba zan bayar ba akan cuɗa yara”. Obi ya faɗa a sanda shima yake jan ɗaya daga cikin kujerun ya zauna. lokacin da Dad ya iso ya tambaya ina Joseph, suka haɗu suka rufa masa asiri da cewar Principal nasu ne ya kira shi, dalilin daya sa yay fitar wuri kenan.
har da Obi aka tafi kaita makaranta, Lead British International School Abuja aka kaita, kuma kasancewar speech ɗinta da kyau SS1 suka karɓeta, sai dai sun faɗa mata idan bata dage ba to zata yi repeating tunda yanzu suna ƙarshen second term ne.
bata fara attending class ba saida aka kaita asibitin ido aka mata medical glass, kullum driver ke kaita ya ɗaukota, kuma da yake tana da magana nan da nan sai tayi ƙawaye duk da ba kowacce ƙawa take kulawa ba musamman wadda take ganin ba level ɗinsu ɗaya ba, saita zaɓa ta dirje, taga wadda kuɗin ubanta yay kusa dai-dai dana su, tukunna zata kulata.
to haka rayuwa taci gaba da tafiyar mata acikin tunanin data rasa, sosai ta samu sauyin rayuwa na jin daɗi, hutu da kwanciyar hankali, a wata guda curr da tayi a gidan ba zaka taɓa yarda da cewa ita ɗin bace, ta ko’ina ta sauya, irin kalar ingantaccen abinci da take ci da kuma hutu yay bala’in amsar tsarin garkuwar jikinta, hasken fatarta har ɗaukan ido yake saboda sheƙi, kyawunta na tun usuli shi yake fitowa a yanzu, kalar ƙauye ta bar jikinta, ta sami wata wayewa da gogewa kamar ba ƴar ƙauye ba, ta waye da cuɗanya da ƴaƴan manya dama ita kanta rayuwar, ta kuma goge da ilimin boko dana addininsu, ayanzu haka ita makaranta ke ɗauka ta wakilcesu a duk wani debate, turanci a bakinta kamar baturiya, idan tana speech har tsuma jikin mutum keyi, kwanaki da aka haska vedio ɗinta a BBC tana fighting against irin taimakon da gwanati ya kamata take bawa ɗalibai da kuma samarwa matasa aikin yi, Dad sai yaji gaba ɗaya duniyarsa ta rikice da daɗi, inama ace, inama ace ƴarsa ce daya haifa acikinsa, kuma shima sai ya tafi irin fatan da Emanuel keyi akan kar tayi regaining tunaninta, amma har ayau da shi da ɗansa cike suke da fargabar dawowar tunaninta, dan basa so ko kusa tayi musu nisa, a halin yanzu dai idan akace maka Mairo Adamu Bichi ce zaka rantse da Allah ba ita bace, dan babu ta inda alama tayi nuni da hakan.
ƴaƴan manyan masu kuɗi suntiri suke akanta, duk da sun san ita ɗin yarinya ce, ba yanzu zaai mata aure ba, amma kuma kowa na so ta saurare shi ne ta bashi damar shiga zuciyarta, to amma ita tace bata da lokacin wannan shirmen ayanzu, karatu ne nata, karatu na boko burinta.
harta ɗan gidan mataimakin shugaban ƙasa Ayamandi Kola sai da ubansa yazo nema masa aurenta, ta buga tsalla da ƙafafunta a ƙasa tace da Dad, da zarar an kuma yi mata wannan batu, daga lokacin zata ɗauke ƙafarta daga gidan ta tafi wata ƙasar ta barsu har saita gama karatu zasu ji labarinta, Dad yace to shikenan anyi an gama, ba za’a ƙara ba.
bata samun matsala da kowa a gidan, ta zama cikakkiyar ƴar gida, Joseph ne kawai matsalarta da yake nuna mata tsangwama, dan Allah ne da kullum sai sunyi faɗa, duk ranar da yayi mata dukan da taga ba zata iya jurewa to fa dakuwa suke ita da shi sai kace ƴan restling, randa kuma yay mata lami ƙalau saita ɗana masa tarko ta wani ɓangaren, yabi ya maida kansa kamar wani sa’anta saboda kawai baya sonta, Granny kuwa ido take zuba musu, babu wanda take tsawatarwa tunda baji suke ba, shi zuciya da tsokana, ita kuma rashin haƙuri.
kuma kullum a waya faɗawa Mom yake ta dawo gida akwai matsala, idan ta tambaye shi yace sai dai ta dawo ɗin matsalar ta girmi magana a waya. ita kuma tun seminar ɗin da suka yi na oriflame a london na kwana huɗu, ranar ta shirya zata dawo sai tsintar saƙo tayi ta gmail daga office nasu na Fidelity Bank akan an turata course a itally na tsawon wata 6, takaici iya takaici tayi, struggle ta saba da shi, amma a wannan karan kam ta gaji, saboda tayi kewar mijinta sosai, dan haka dole sai Dad ɗinne ya bita can tunda shi ba shi da wata matsala ta office ko wani abu makamancin haka.
*3:00pm.*
ƙarfe uku da rabi na dare bugawar agogo, Mairo ta farka a lokacin dan shan ruwa, ta duba kan table taga babu roban faro da bata rabo da ajiye shi saboda shan ruwan dare. ɗan tsaki tayi ta duba tulin littafan dake gabanta, karatu take tayi bacci, baccin daya ɗauketa bata sani ba.
ta sakko daga gadon ta fito, ta sauko parlon ƙasa dan babu ruwa a friedge ɗin parlonta, ta gama shan ruwan zata koma sama sai taji kamar maganar mutum, ta tsorata amma bata fasa dawowa da baya ba ta shiga laluben ganin waye.
ta ɓangaren ɗakin ajiyar littafai take jiyo sautin murya na fita a hankali, ta nufa wajen cikin sanɗa, da mamakinta Dad ta gani tsaye riƙe da waya a kunnensa, yana magana ƙasa-ƙasa, maganar data yi kama data sirri, ba wannan ne karo na farko data sha ganinsa a irin wannan lokacin ba yana waya, karo na kusan huɗu kenan, a yau dai ta gama fahimtar akwai wani abu da Dad ke ɓoyewa a gidan wanda baya so a sani, taji muryarsa ta ɗaga cikin faɗa yake cewa, “kai gaba ɗaya ba zaka gane ba…na gama yanke shawarar zan haƙa rami na binnesu, dan haka a gobe ba sai jibi ba, hakan ne kaɗai zaisa na sami nutsuwa hankalina ya kwanta”. sai kuma ya ƙara yin ƙasa da murya yana ci gaba da faɗar abunda bata ji, har sanda ya gama wayar ya buɗe ɗakin littafan ya shiga sannan ya fito, da gudu ta bar wajen ta koma ɗaki.
ta haye gado tana maida numfashi, zan haƙa rami na binnesu. maganar ta ƙara haskawa acikin kanta a karo na barkatai, ba wannan ba ma, me Dad ke ɓoyewa?, me yasa take yawan ganinsa a irin wannan lokacin?, tukunna dai, me yake da bindiga a tsakiyar wannan daren?, lokacin daya shiga store ɗin littafan me ya fito yana gogewa a hannunsa?, SIRRIN ƁOYE, tabbas akwai wani sirri da Dad ke ɓoyewa, ba kuma yaso kowa ya sani, menene shi?, taiwa kanta tambayar a sanda maganarsa ta kuma haskawa cikin kanta zan haƙa rami na binnesu kawai, hakan zaisa na sami natsuwa hankalina ya kwanta..
jikinta har lokacin bai bar rawa ba, ta miƙa hannu ga landline ɗin dake kan bedside drower, dole ta sanar da Brother Ema, ya kamata ya san da wannan, ai dama dukansu sun fara suspecting nasa akan wannan keɓewar da yake cikin dare, Obi ma yace sau biyu yana ganinsa, kuma da bindiga a hannu.
sai dai kuma me, har tayi dialling numban nasa sai tunaninta ya sauya, ta sauko daga kan gadon, ta nufa tulin littafan dake cikin wata drower ta ɗauko wani littafi data aro a library jiya, Malaminsu yace musu littafi ne guda dake ɗauke da bayanin yanda zaka karanci yanayin dake a saman fuskar mutum farat ɗaya.