NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Please vote again and again and again.
Comment,Share.
SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

25)
Kirkos, Legacy Luxury apartment Addis Ababa, Ethiopia.
06:30Am.
Here in silence i wait, there’s nothing else i can do, it feels like my heart gonna break, and all i can think of is you, and how many aching arms long to hold you, and show you how much i care, but i’m counting the hours without you, and i dont know how much i can bear, becouse i miss you morethan words can says, and i need you hear in my life always, yeah i miss you.

sautin waƙar i miss you ta Beverley Craven ce ke tashi a hankali acikin madaidaicin living room ɗin, waƙar dake tafiya haɗe da bugun zuciyarsa, kuma a dai-dai lokacin da kalaman waƙar suka ɗan tsaya, a dai-dai lokacin ne Abdurrahim ya kashe laptop ɗin da waƙar ke tashi daga ciki, hannunsa ɗauke da ƙaramin towel na wanka yana goge ruwan dake sumar kansa, yaja tsaki a lokaci ɗaya.
yaci gaba da tsayuwa a kusa da center table, ya ƙarasa sharce sauran ruwan da ya rage a sumar tasa, sannan ya tsaida kallonsa akan Kabiru, wanda ke miƙe akan sofa bed yayi matashi da duka hannayensa biyu ta bayan kansa, idanunsa a rufe, zararan gashin idon nan sun miƙe, in banda shi Abdurrahim ɗin da yasan halin abokinsa, kowa ne ya ganshi a wannan yanayin ba zaice ba bacci yake ba.
yaja tsaki tare da ɗan ɗaga sautin muryarsa yana faɗin.
“waƙa ɗaya! kullum baka da aikin sauraro saina waƙa ɗaya. to ka miƙe haka kayi wanka lokaci na tafiya, you know very well Malamin nan bashi da mutumci”.
ya sani, ya sani wannan tsakin na ƙorafi daya zama ɗabi’ar abokin nasa a halin yanzu dole sai yayi shi, dan haka ya murmusa yana ƙara faɗin, “ni dai nace ka tashi, ka tashi kawai Malam. watanni nawa suka rage?, watanni shida ne kacal suka rage ka koma hutu ka ganta, ka sata a gaba kana kallonta da sauraron muryarta ba waƙar da kake cika min kai da ita a kullum ba”.
shirunsa ya haɗe da buɗe idon Kabir ɗin ya saukesu tar a kansa, idon daya rufesu tun a sanda sautin waƙar ya soma tashi, haka yake a duk sanda ya kunna waƙar, waƙar tana tafiya ne da bugun zuciyarsa, yayin da hoton Maryam(Mairo) ke haskawa a idanun nasa.
kallon Ma’aruf ɗin yake, kallo na ka taɓu, kana buƙatar ganin likita. “watanni shida kace, watanni shida nan gaba da za’a haɗa su bada shekara guda, su zan ƙara kaiwa ban sakata a idona ba?, da wanne haƙurin?, daga ina juriyar tawa take?…baka da hankali, baka da hankali sam Abdurrahim, kaje kaga likita ya duba maka ƙwaƙwalwarka”. Abdurrahim ɗin ya zauna akan sofa yana kallonsa yace,”ko makaho ya shafa tsakanin ni da kai zai faɗi wanda yafi cancanta da ganin likitan ƙwaƙwalwa Kabir, kai ka dace da ganin likita bani Abdurrahim Yusuf ba, saboda ni ban zauce ba kamar kai”.
a lokacin da Kabir ya miƙe yana sauke ƙafarsa a ƙasa, yake cewa da shi,”baho kawai, na tabbata da ace kana da wadda ta shiga zuciyarka tayi bake-bake ba zaka dinƙa yi min wannan shirmammun maganganun naka ba. har yanzu baka san SO ba, ji kake ana faɗansa, ana kuma aiwatar da shi a aikace, amma baka san daɗinsa da zafinsa a zuciya ba, baka sansa a gangar jiki ba, baka sansa a ruhi ba. dan haka idan ka ƙara furta min zancen zan ƙara wata shida anan gaba ban koma ƙasata naga Maryam ba saina daki bakinka ya fashe yayi jini, karka fasa kaci gaba, kaga yanda zanyi da kai acikin gidan nan da muke rayuwa mu biyu”.
ya san hakan zata kasance, masifa, wannan faɗan nasa sai yayi shi, ba a haka Kabir yazo ƙasarsu ba, a me haƙuri yazo, amma yanzu ya tashi daga Kabir ɗin daya sani tun wasu satika na fara rayuwarsu a makaranta tare, ya rikiɗe ya koma wani Kabir ɗin na daban, zautacce wanda ya haukace akan soyayya, soyayyar da yake ganin kamar ta kusa yi masa illa.
gajeran murmushi me sauti ya tsaya a iyaka leɓen Abdurrahim ɗin a sanda Kabir yay shiru da maganarsa, sautin murmushin daya sa Kabir ɗin dakatawa daga tafiyar da yake zai wuce bedroom, ya juyo ya kalle shi, kuma wannan karanma a zafafe ya shiga magana kamar zai rufe Abdurrahim ɗin da duka.
“banda kuɗin jirgin komawa shi kake wa dariya right?”. Abdurrahim ya ɗago da kansa daga barin danna wayar da yake ya kalle shi, tabbas Kabir ya haukace da gaske ba wai a faɗa ba, banda ya haukace a yaushe yaji yayi dariya, murmushi fa kawai yayi.
“to daɗin abin dana zo ƙasar taku ba zaman banza nake yi ba, ina karatuna ina kuma sana’ata, kai ka sani, kuma shaida ne, ka kuma san ayanzu zan iya biyawa kaina kuɗin jirgi kaima kuma na biya maka. ofcourse ni ɗan ƙauyen Bichi ne, amma idan ka tashi rubutu a sabon update list naka na bin ƙwaƙwaf ka rubuta KABIR ADAM BICHI a sahun farko na masu kuɗin garin bichi, labarin da daban, na yanzu ne ke tafiya, kuma ita ake magana, ka san da wan nan, ka kuma bawa wani labari”. yana gama maganar ya juya a fusace ya wuce bedroom, Abdurrahim kuma yabi bayansa da ido yana dariya, yana bashi dariya idan yana wannan masifar, duk da cewar yana bashi tsoro a wasu lokutan saboda yanda idanuwansa ke sauya launi daga asalinsu, to amma shi wallahi a yanzu Kabir ɗin ya zame masa comedian.
gemunsa nan dai me ɗan tsayi shi yake tajewa kamar yanda ya saba koda yaushe a ƙarshen shirinsa. ɗinkin habesha kemise ne ajikinsa, farar riga da akayi aikin jiki da baƙin zare, da kuma ratsin golden, red and blue, sai baƙin wandon plane yadi me kauri, ɗinkin ƴan ethopia ne, shigar da tun ranar daya fara yinta yawanci idan suka ganshi sai suce dama shi asalin ɗan ƙasar ne, bada kayan kaɗai ba, hatta ga zubin halittarsa ma.
ya ajiye ƙaramin cumb ɗin asanda ya gama tazar, abu na ƙarshe daya ɗauko ya saka ayau baƙin glass nasa me O shape, hannaye zube cikin aljihun wandon ya tsaya yana kallon kansa a madubi. Yayi kyau, irin kyan dake haska ƙyalli a idon me kallo, ya fito a cikakken ɗan gayun birni ba ɗan ƙauye mazaunin can ba. ya ƙara haske akan asalin wanda yake da shi, sumar kansa me zubin ta buzaye ta ƙara cika da baƙi, siririn hancinsa ya ƙara tsayi, sai wannan doguwa kuma siririyar fuskar tasa data rame, ramin idon ya faɗa ciki, duk a saboda kewa, kewa kuma ta Maryam, Mairo ta ƙauyen bichi.
ya saki wani murmushi me tattare da tarin ma’anoni, bayyanuwar siririyar wushiryarsa a sanda yay murmushin sai wani kyawun na daban a tare da halittar tasa ya ƙara fita. tana son kyau, tana tsananin son kyawun da Ya Kabirunta yake shi, ya san da wannan, to wane kalar jin daɗi da farin ciki da murna zatayi a sanda fararan idanuwan nan nata masu kyau suka yi tozali da shi a KABIR ba a KABIRU ba?, ta kalle shi a irin yanda take ta hasaso shi a wata rayuwar ta daban, ba irin wadda suke ciki ba, rayuwa ta hutu da jin daɗi, rayuwar cikin birni bata ƙauye ba, rayuwar wayewa da gogewa, rayuwar da kuɗi suka zauna masa ajiki.
“Ya Kabiru wai idan mutumin daya haɗa nagarta da cikar kamala ya samu hutu da jin daɗi da kuma kwanciyar hankali, mutum dai irin wanda ba zai rasa wata ƴar mitsitsiyar matsala ba, me gogewa a fannin ilimin addini dana boko, to wai kyau yake yi irin me ɗaukar hankali, haka naji ana faɗa, to wai hakanne?.” kalaman Mairo a wani lokaci suka haska a kwanyar tunaninsa, a lokacin ya bata amsa ne da, “ki cire wai ɗin, maganar haka take.” ta ƙanƙame shi a sannan cikin murna tana cewa,“Allah ya kai min kai wan nan matakin, matakin da kowa ne ya ganka zaiji ka burge shi…idan Yagana tayi tsawon rai ta tofe min kai da tofin Allah tsine saboda ƴan hasidin iza hasada”. murmushi kawai yay mata a sannan bai ce komai ba, amma ayanzu zaice wani abun, dole ma ya faɗi wani abu.
kamar kuma tana kusa da shi ne, kamar kuma da ita ɗin yake magana, kamar kuma tana sauraronsa ne, acikin muryar nan tasa me taushi da zurfi ya faɗa a fili ba a zuci ba,”Kabir ɗinki ya samu, ya samu wannan abun da kike masa fata, na cikin mafarkinki da kuma hasashenki, domin ya kusa kaiwa matakin, ƙiris ya rage, dan komai ya kammala, linta ɗaya ce tai saura acimma matakin, itama kuma lintar ba me tsayi ba, kwalin degree da shiga office ne kacal, ofishin nan da kika ce kujerar cikinsa zata ke juyawa dani, irin sanyin ɗakin Bella dake fitowa daga inda ba’a sani ba yake sauka ajikina, jin daɗi da annashuwa da annuri suke bayyana a tare dani…daga nan mafarkinki ya tabbata, ya tabbata Maryam”.
yay shiru yana me tsuke baki, inda wannan pink lips ɗin nasa sukai wani kyau a tsukewar. zancen daya gama a fili kuma ya koma na zuci da wata maganar ta daban. a sa’ilin da nawa mafarkin kuma zai tabbata, lokacin da kika gama makaranta, lokacin zan bayyanar da manufata akanki gasu Baba, su aminta da sun bani ke. a ɗaura mana aure na ɗaukeki na kaiki gidana, mu tabbata abu ɗaya, rayuwarmu ta sauya, ta sauya zuwa ta ma’aurata, na daɗa killaceki a zuciyata kamar yanda na killaceki acikinta na tsawon shekaru goma, na fito da wannan ɓoyayyar ƙaunar dana ke ɓoyeta na nuna miki ita zahiran, alokacin zan koma miki tamkar yaro, zan zame miki tamkar ƙaramin yaro a sanda nake faɗa miki kalmar SO, irin son da muka cimma a yanzu ba irin na waccen lokacin ba…dan zan shayar dake wata da madarar so da ƙaunata, ki kasance a kwance a ƙirjina a duk sanda muke tare, ki kasance goye a bayana a duk sanda na dawo wurin aiki…Alƙawari, Alƙawari ne nai miki da duk irin tsarin gidan da kike so acikinsa zaki zauna.
sai dai me zai faru?, zuciyarsa ce yaji tayi wani irin duka da bai taɓa jin tayi ba, a sanda yake tunanin ai ya rabu da duk wani challanges na rayuwa, ashe fa a lokacinne zai fuskanci babban ƙalubale mai girma, lokacin da al’umma zasu shaida auren KABIR ADAM BICHI da MARYAM ADAM BICHI, ƙwayayen da kowa yake da masaniyar cewa ciki kawai suka raba a wajen fitowa, Uwa daban-daban ta ƙyanƙyashesu, amma abun da aka zuba a samar da ƙwan halittar tasu na uba ɗaya ne, Uba ɗaya Malam Adamu Me Faskare, to wanne mahaukacinne zai karɓi waliccin wannan auren? kuma waɗanne mahaukatan ne zasu tsaya shaidar auren da za’a gina akan haramci?, bayan sarki Allah, sai shi, sannan Baba da Gwaggo da kuma ita Kulun datai sanadiyyar zuwan Maryam ɗin duniya, babu wani mahaluƙi daya san Mairo ba ƴar gidan bace, ba ƴar Baba bace, ba kuma ƴar Gwaggo bace, ba kuma ta gadon komai a gidan…to taya shida mahaifiyarta zasu tsira daga hakan su cimma burinsu bayan basa son kowa ya san da SIRRIN ƁOYE?.
zancen zucin ya katse, walwalar fuskar kuma ta sauya, wata walƙiya ta gifta acikin idon nasa, sannan tsawa ta sauka a tsakiyar kansa duk a lokaci ɗaya, lokaci ɗaya da shigowar Abdurrahim cikin ɗakin, saboda haka ya* lumshe idonsa yayi kamar bai sanda da shigowar tasa ba, duk kuwa da sun haɗa ido ta cikin mirrow.
“Pizza nasa akayi order ba zan iya shiga kitchen ba, kazo muyi breakfast cikina ya fara ƙugi”.
ya jisa, kuma Abdurrahim ɗinma ya san ya jisa amma yay kunnen uwar shegu da shi, to amma ya zaiyi da halin abokinsa kuma amininsa a halin yanzu?, haka zaita binsa ta yanda ya sauya ɗin.
yasa fork ya yanki Pizza ɗin ya kai baki ya tauna, har saida ya haɗiye sannan ya ƙara cewa da shi.
“fushi?, baka sakko ba kenan?, to kayi haƙuri, Allah ya huci zuciyar Kabir ɗin Maryam”.
Kabir ɗin ya ƙarazo wurin da ƙaramin table yake me zagaye da ƙananun kujeru guda biyu, ya zauna suna fuskantar juna yana kaiwa Abdurrahim ɗin naushin wasa a kafaɗa. shima yasa wuƙa ya yanki pizzar daidai wadda zata shiga bakinsa. “na gaji da irin wannan cimar ta isheni, abincinmu na gargajiya nake so, dan haka ka shirya gobe zaka fara cin abincin tamu ƙasar, zan mana tuwan dawa da miyar kuka me rai da lafiya, wanda idan kaci kaji garɗinsa sai ka damƙa min Atm card ɗinka kace kullum nake mana irinsa”. Kabir ya faɗa yana kai pizzar bakinsa.
“Tuwon dawa! tun a sunan ma ba daɗi ina ga anzo ci, Abbu ya faɗa min sanda yaje nigeria abincinsu babu daɗi sam, da niyyar sati guda yaje amma kwana ɗaya tal yaji ba zai iya ba…ko Mima ma da take ɗan zuwa da kayan abincinta na nan take tafiya, dan haka ni ba zanci wani abincinkun ba gwara kake mana ordering kawai idanma ƙiwar girkin kake”.
ya faɗa yana kai kofin juice bakinsa.
Kabir yace da shi, “aikuwa sai dai ka koma siyen abinci duk ranar girkina, dan wallahi a yanda nasa Gwaggo tai min aiken garin masara dana dawa da kuma daddawa, to Abdurrahim ka shiga uku da ganin abincin nigeria a idonka, sai dai idan banji yunwar ba…ni ba asararre bane da zanta saka kuɗina akan hanyar siyan abincin da ba ƙoshi nake dashi ba, dama ace irin girkin Leemars Mandi ne a ƙasar taku, to da sai nayita saya nasan duk inda naci plate ɗaya ya wadatar, kuɗina yanzu bana ciye-ciye bane, na ginin gida ne, gidan Maryam”.
ya ƙarasa maganar fuskarsa na faɗaɗa da murmushi.
“A dai rage buri, dan rayuwa bata tafiya daidai da muradin zuciya, kaita adu’a kawai”.
Kabir yay masa wani kallo ta cikin reflection glass cup ɗin da yakai bakinsa yace, “Abdurrahim ka rage baƙin ciki, na faɗa maka kuma shawara nake baka”.
dariya ta biyo baya a duka fuskokinsu, a sanda kuma suka sauya babin firar.
“Fahad yace an fasa yin lectures ɗin…so kaga sai muje ga tafiyarka, na tambayi wani neighbour ɗinmu ya shaida min ranar friday akan iya barin wasu tsirran mutane su shiga Emirate, Sarki yana bada lokacinsa wa baƙin mutane a wannan ranar, so mu tafi tun yanzu ƙila ka taki sa’arka a yau”.
Kabir ya lashi leɓensa na ƙasa sannan yace,”kasan me?”. “a’a saika faɗa”. ya jingina zamansa ga kujerar yana sauke numfashi, “nazo ƙasar nanne da manufofi guda uku kamar yanda na faɗa maka a baya, karatuna, aikinyi da kuma binciken sirri da aka sani. kuma tun zuwana nake a ƙagauce dana shiga cikin masarautar na samo bayan nan da ake so a sani. to amma kamar yanda ka faɗa cewar zan iya taka sa’a ayau, nima kuma nake jin kamar lokacin sanin komai yayi, sai nake jin faɗuwar gaba da fargaba”.
“idan har babu rami to me ya kawo rami Kabir?, ai indai binciken da zakayi bana cutarwa bane to ka cire wannan daga ranka, go straight forward to your work, shine magana kawai”.
Kabir ya buɗe lumsassun idanunsa ya sauke kan Abdurrahim yace,”thank you my friend for encouraging me on so many things…tashi mu fita”.
suka miƙe suka fita, sai da suka je wurin mota Abdurrahim ya shafa aljihunsa yana laluben key ɗin motar.
“wai jiya dana dawo ban baka key ba?”. ya tambayi Kabir ɗin yana tsayawa da laluben. “bayan saida nayi bacci ma ka dawo”. ya bashi amsa.
“to Allah yasa ban yasar da shi ba, dan wallahi ko ɗazu dana duba ban ganshi ba, thats why i din’t show you those files”. “ka koma dai ka ƙara dubawa yana nan, wani wurin ka jefa shi”.
Abdurrahim ɗin ya juya ya koma ciki, ya ɗauki wasu daƙiƙu kamin dawowarsa yana faɗa masa ashe a toilet ya barsu.
Kabir ke driving ɗin yayinda Abdurrahim ke zaune a kujerar me zaman banza, yana yi masa bayanin kan yanda sukai da Abbu(mahaifinsa) akan office ɗin da yake so ya fara zuwa. Kabir yace masa ai ya amsa kawai, ba zaiga alfanun hakan ba sai nan gaba, shi kuma gyaɗa kai yay godiya ga shawararsa.
a wani katafaren store da aka rubuta HAJARA SHOPPING MALL Kabir yay parking motar daga wurin daya saba parking a duk sanda ya shigo store ɗin, ya kashe motar suka fito suka nufa cikin store ɗin, store ne dake ashaƙe maƙil da kowanne irin abin buƙata, yana kuma daga cikin store ɗin da a watanni biyu da suka wuce ya shiga sahun manyan shopping malls da akeji dasu a ƙasar.
shigarsu ciki sun jima sosai, sai dai babu wani abu da suka siyo, dan ko da suka shiga ba wajen ɗaukan kayayyaki suka nufa ba, direct office ɗin Manager dake acikin store ɗin suka shiga, kuma Managern bada kowa yay magana ba sai Kabir, Kabir ɗin da yay masa tambayoyi game da ci da yanda ciniki ke tafiya a kwana uku da bai leƙo ba, Manager ya shaida masa nasarar nan dai da ake samu a kullum har yanzu itace, babu faɗuwa sai Continuancy dake ta ƙara haɓɓaka, dan ajiya ma ya fitar da lissafin kuɗi naira miliyan shida da suke saka ran haɗasu a wata biyu, sai gashi an haɗasu a kwana biyar kacal, ya ɗauko wani file a sanda yake sanar da Kabir ɗin haka ya miƙa masa gabansa.
“Alhamdulillah, Masha’Allah”. Kabir ya faɗa a sanda ya gama duban takardar dake ɗauke da lissafin adadin kuɗaɗen da suka shigo da kuma wanda aka ware za’a ƙara fitarwa wajen yin wata ordar, duk acikin wannan watan kawai, fuskarsa sai fitar da murmushi take.
Hajara Furnitures shine kantin da Kabir ya buɗe a tun watan farko na zuwansa ƙasar, da kyautar kuɗaɗen daya samu daga wurin Bella da kuma kyautar gidan da suka bashi, a tahowarsu ne ya sayar da gidan naira miliyan shida dan ba gidan banza bane duk da cewar flat house ne, to amma zubin ginin kaɗai zaka kalla ka sami tabbacin bada ƙaramar dukiya akayi ginin ba. shi a wurinsa zai riƙe kuɗinne dan buƙatun yau da kullum har ya kammala karatunsa, to sai bayan saukar tasu ne kuma ya sami saƙon check na wasu adadin ethopian birr daga wurin Bella, adadin kuɗin da idan ba ɓarnar banza zaiyi dasu ba zasu isheshi gama rayuwarsa a ƙasar, yaji daɗin kuɗin sosai ya kuma ƙara jinjinawa mutumci da karamci irin na Bella, macen da bata manta alkhairin mutun a gareta ko mai ƙanƙantarsa.
dan haka ne yaga da abu ɗaya ya dace da shi, wanda zai kankarowa kansa mutumci da ƙima shine ya gina kansa, ginin da bashi kaɗai zai amfana ba, har na kusa da shi ma. Abdurrahim shine abokinsa da suka fara haɗuwa a lectures, kuma halinsu yazo ɗaya, shi ya wuce masa gaba wajen taya shi neman hayar shago, sannan ya ƙara wuce masa gaba ya kaishi inda aka bashi haske aka kuma wayar da shi da shigo da kaya daga ƙasashen waya. Furnitures ya fara zubawa a shagon, kamin wata uku ta rufa kuma tuni ya maida kuɗaɗen daya zuba, bai fara komai ba sai daya kira waya ya nemi albarka da adu’ar mahaifinsa daya rage masa, ya sanar da Gwaggo ma, ya kuma sanar da Malaminsa, shima kuma adu’ar yake babu dare babu rana, da sadaƙa, ya kuma yin ƙiyamullaili a kowanne dare, saboda haka yake ta ganin bunƙasa ta yacca baiyi tsammani ba.
bayan barinsu store ɗin kuma kai tsaye Emirate of Harar(masarautar ethiopia) suka nufa, da zuwansa kuma ya taki sa’ar da yake fatan samu, dan shine mutum na biyar a mutanen da akaiwa izinin shiga su sami ganawa da Sarki Abd Ash-Shakur. sai daya ɗauki tsawon awa guda acikin fadar sarkin dake ta amsar bayanai daga wasu makusanta shi kamin ya sami damar ganawa da sarkin ya sanar masa shi ɗin masoyinsa ne na haƙiƙa yazo ne na musamman dan miƙa masa gaisuwa, Abd Ash-Shakur yaji daɗi sosai dan har hoto sai daya sa akayi musu tare, bai baro cikin fadar ba sai da akayi sallar juma’a tukunna.
da fitowarsa kuma ya sami wani dogari daya kwashe duk wani labari daya kutsa acikin masarautar shekaru goma sha biyar da suka shuɗe har zuwa yau, yaji daɗin samun duk wasu bayanai daga bakinsa, irinsu ne ake jin daɗin samu a hakar bincike, dan sai sun feɗe maka biri da wutsiyarsa a duk abinda suka ji suka gani saboda tsabar iya gulma da sa ido.
ba a haka kawai ya sanar masa da komai ba, aikin kuɗi yay masu yawa, shi yasa ko da ya kammala sai daya ƙara tambayarsa idan yana buƙatar ƙarin wani abu na koma menene yasa shi ya nemo masa zaiji bayani. murmushi kawai Kabir yayi, ya gama samun abunda ya shigo da shi cikin masarautar, dan haka ya ɗauki hanyar fita a hanzarce, sam ba neman taimako yaje ba, ko kai ƙorafi ba kamar yanda ake kallon duk wanda ya shigo a wannan lokacin.
acikin fadar ma sai daya dinga ɓoye fuskarsa da p-cap gudun kar su haɗu da Suhail ko Jawad idan su na ƙasar, fitowar tasa daga ciki kuma yayi daidai da ƙarasowar Abdurrahim daya kira ya sanar masa ya gama yazo su tafi.
Abdurrahim yaso, kuma yana son ya san akan me yayi binciken da kuma dalilin yinsa, to amma a yanda ya gama lura Kabir baya so ya san komai duk da yardar da amincin dake a tsakaninsu, saboda haka bai takura kansa akan sai ya tambaye shi yaji ba, may be it is a matter that belongs to him alone, and he does’nt want anyone to know.
kuma tunda Kabir ɗin ya shigo mota bai yi magana ba, haka idanunsa a rufe suke har suka iso gida. duk da cewar Abdurrahim ɗin nata zuba zance amma sai ya lura Kabir ɗin yana sauraronsa ne Absentmindendly, dan haka yay shiru yana bin waƙar dake tashi ta recorder ɗin motar cikin yarensu na Amharic.
sanda suka isa gidanma Kabir ce yay ya barshi a mota zai shigo daga baya, yaso ya matsa masa yaji akan meke faruwa dan yaga ƙyallin damuwar a ƙwayar idonsa, to tambayar ba a wannan lokacin ta dace ba, ya ɗan huce tukunna, kuma may be ya iya sanar masa ko da bai tambaya ba.
Abdurrahim na fita a motar ya zaro waya daga aljihunsa ya lalubi nunbar Kulu, ya sanar mata kaso 50 na aikinta ya kammala, saƙa da warwara yake akan yin kiran, ya kira ko ya bari?, zuciyarsa ta rasa wanne side zata ɗauka, kiran nada muhimmanci ta wani ɓangaren, ta wani ɓangaren kuma bashi da amfani, fushi yake da ita, fushin kuma da yay zuciyar ba zai ƙara kiranta ba sai dai idan ita ta kira shi.
“Ranka ya daɗe su din Ƴan biyu ne, su kaɗai Allah ya bawa mahafinsu, mahaifiyarsu ma ita kaɗaice, nan ba shine ainihin gidansu ba, amma kuma sunyi rayuwa acikinsa, dan tun sanda aka yayesu suka dawo wurin Kakarsu data haifi mahaifiyarsu, shi sarkin wannan masarautar shine wanda ya haifi mahaifiyarsu. shi kuma sarki Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani shine mahaifinsu, shine sarkin ƙasar Qatar tun bayan da yay aure har zuwa yanzu, Aaliyah da Akila shine ainihin sunansu, kamar yanda ka nuna min wannan hoton fuskar a yanzu, haka hoton Poster ɗin sune zai fara yi maka maraba a yayin daka isa masarautar Qatar, Aaliyah(Babbar Hassana) ita aka nema aka rasa har yanzu babu labarinta, Akila(ƙaramar Hussaina) kuma tana nan, itace minister of education a yanzu na wannan ƙasar tamu ta ethiopia da kake karatu acikinta, macece me halin kirki da nagarta, sai dai ƙalubale ɗaya na zagi da ƙananun maganganu da take fuskanta a wurin mutane shine na rashin aurenta tsawon shekarun da take dasu”.
bayanin wan nan dogarin ta haska acikin kansa da idonsa, ba yanzu ba, ba yanzu ba ya kamata ya sanar mata da komai ba sai yaje Qatar ya dawo.
“Distance ɗin dake tsakanimu nan Ethiopia zuwa Qatar kilomita 2,121 ne, wanda yake dai-dai da 1,318 miles, 3hours, 18minutes kenan. zaka iya zuwa ayau ka dawo”.
bayanin ya kuma haska masa. ya cije yatsa yana tunani, kamin wani bayanin ya kuma haska masa, “Ƴa ta huɗu acikin wannan masarautar ta Harar itace take aure a nigeria, inda take auren wani sarki acan daya aureta a sanda ya kawo ziyara wannan masarauta, sunanta Hauwa ƴaƴanta nace mata Ammi, tana rayuwa ne kuma tare da ƙanwar mahaifiyarta data riƙeta a wajenta tun tan ƙarama da kowa ke kiranta da Bella, itama matar sarki ce a baya kamin mijinta sarki Mujahid ya rasu.”
a yanzu zuciyarsa ta yanke shawara ne akan ya fara zuwa Qatar ya dawo sannan ya sanar da Kulu komai, dan haka yay dialling number Abdurrahim, yana ɗagawa yace da shi,”Please come take me to airport ko kuma nace kazo muje tare idan ba damuwa”.
“ina zaka je?”. “Qatar”.
“Qatar kuma?”. muryar Abdurrahim ɗin ta amsa da sautin mamaki.
“ehh Qatar”. “to amma tafiya babu shiri?”. “Abudrrahim kuɗi ne suke aikin komai, ka fito kawai, a yau zamu dawo”. “tom shikenan gani nan fitowa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button