SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Abuja, Nigeria, A wan nan ranar.
If you want to use your investigative skills to truly fight crime, pursuing a police detective career is the best choice for you. It’s a great career fit for people with meticulous attention to detail, a strong ethical compass, and the patience and perseverance to investigate criminal cases that may progress slowly. Qualities of a Good Detective include:- (1)The ability to talk to people. (2)job knowledge. (3)Observation skills. (4)Report writing skills. (5)Attention to detail. (6)Ability to think outside the box. (7)Courtroom testimony skills. (8)Positive attitude and tenacity.
Bayanan na fita ne ta cikin system ɗin dake ajiye a kan stool, yayin da Mairo wacce ke zaune akan kujera a balcony ta tattara hankalinta gaba ɗaya a wajen sauraren jawabin da farar baturiyar keyi tana fahimtrsa daki-daki. taci ado cikin wata armless gown blue, kan nan babu ɗan kwali an baza gashin a gadon baya, ƙafarta ɗaya akan ɗaya tana girgizasu.
bata san ya shigo wajen ba, bata san da zuwansa ba, haka bata san da tsayuwarsa a kusa da ita ba, domin hankalinta ba anan yake ba, ya tafi ga bayannan da take saurare da kuma hasashen yanda zata cimma karatun take.
Detective Gift Tosin Afafa. ya kira sunan nata a sanda yake saka pause a vedion da take saurara. murmushi tayi daya tsaya a iyakar leɓenta, a kaikaice ta waigo tare da ɗaga kai ta kalle shi, lokacin kuma data saki murmushin daya bayyanar da haƙoranta. ta kamo hannunsa tana matsa masa kusa da ita ya zauna tace da shi, “what is going on Sir Obi Tosin Afafa?”. yay murmushi yana ɗora hannu saman kafaɗarta sannan ya bata amsa, “i salute to the daughter who is willing to find out the secret her father was hiding”.
hala Labarin ya daina maku daɗi ne na tsaya da rubutun ko?, tunda babu comment da vote, to koma dai baku ban amsa ba naga hakan a tsakanin post ɗin shekaranjiya da jiya, saboda haka nima na ɗauki hutu sai ranar da kuka ganni, zan huta na kwanaki, kafin nan kuma kun ƙara hutawa sosai.
08145146915
Vote&Share.
SIRRIN ƁOYE
By Oum Ramadhan✍????
26)
ya ɗora zancen da cewa,”amma ba kya ganin akwai rashin dacewa a game da abinda kike shirin aiwatarwa?, Dad mahaifinmu ne, mun sansa da kyawun halinsa, duniya ma ta shaida kyawun zuciyarsa, to akan mene kike tunanin zai iya aikata wani mugun abun?, yafi mu sanin dalilin da yasa yake ɓoye mana koma menene, shin ba kya tunanin ko abinda yake ɓoyewar abune daya dangancin aikinsa ne kasancewarsa na soja?, idan yana ƙoƙarin kare ƙasarsa ne fa?”.
kallonsa take tun daga lokacin daya buɗe baki ya soma magana har sanda yaja baki yay shiru, sannan ta sauke numfashi tace da shi,
“ba wai ina binciken bane dan in gano shi da aikata wani mugun aikin ba…i have 100% sure ba wani mugun abun yake ɓoyewa ba, kai baka tunanin abunda yake ɓoyewar ya shafi rayuwarsa ne kuma hakan zai iya jefa shi cikin haɗari?, to wannan dalilin yasa nake so na koyi yanda zanyi binciken akan abinda yake ɓoyewar, dan muga ta inda zamu taimaka masa mu warware bakin zaren, mu fitar da shi daga tashin hankalin da yake ikirarin acikinsa yake”. tayi shiru sannan ta jinginar da kanta a saman kujerar, taci gaba da cewa,”sai dai kuma akwai wani hanzari ba gudu ba, idan har abunda Dad ke ɓoyewa ya zama shine me cutarwa, ko yana cutar da iyalansa ko kuma yana cutar da al’umma ta wata hanyar, to ba zan ƙyale ba, zan gargaɗe shi akai, idan kuma yaƙi ji zanyi ƙararsa ga hukuma ta hukunta shi”. Obi yay mata wani kallo na baki da hankali, kamar ya sanar mata da matsayinta, sai kuma dai baiyi hakan ba saɓanin wani tunanin daya gimla masa, dan haka yace da ita,”a matsayinki nawa zaki ƙararsa?”.
tayi wani guntun murmushi a sanda take kora lemu mai sanyi a maƙoshinta, “ba lallai saina kai wannan level ɗin da nake son kaiwa na Detective ba sannan ne zan iya yin ƙararsa, as far as i got the evidences magana ta ƙare, you know me well akan bigiren gaskiya nake, kaima kasan da hakan”. Obi zai sake magana ƙarar wayarta ya katse abinda zai ce, a shekaranjiya ne Dad daya dawo daga London yay mata kyautar waya babba mai tsada saboda sakamakon data ƙara fitowa da shi me kyau na wannan term ɗin, Emanuel kuma yay mata kyautar system ɗin da take kallo acikinta yanzu. bata ko kalli screen ɗin wayar ba dan ganin sunan me kiran, saboda tuni ta gane me kiran tun a taken waƙar dake tashi, ringing ɗinsa dabanne dana kowa, Emanuel! Emanuel Brother ɗinta da take so da ƙauna, shi yasa take banbanta komai nasa a wajenta dana kowa.
Obi ya kai dubansa ga screen ɗin ganin taƙi ɗauka, hasalima ɓata rai take. “Brother ne fa ki ɗaga mana”. cikin turo ƙaramin bakin nan nata gaba tace da shi,”ka ƙyale shi munyi faɗa”. “da Brothern?, Gift kin cika rigima ke dai, to akan mene kuka yi faɗan?”. Obi yay tambayar dariyar fuskarsa bata ɗauke ba. tayi narai-narai da idanu tana shirin fashewa da kuka, “wai haka yake cewa bani da lafiyar tunani, na shirya zai wuce dani lagos za’a ƙara min hoto a duba lafiyata”. kuma zaman nasu sai ya ƙare a sa’ilin da Buky ta shigo Balcony ɗin tana sanar musu da kiran Dad.
Da yamma tana zaune a parlo tana bitar karatu, karatun bokon da bata gajiya da shi sam, Dad da kansa har ya fara yi mata faɗan akan ta dinƙa sassautawa, ƙwaƙwalwa na buƙatar hutu.
ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ƙwalawa Buky kira tazo, “maida min da Aljazeera”. Buky ta ɗauki remote ta kamo channel ɗin da ta umarceta.
ita kuma ta karkata hankalinta ga tvn gaba ɗaya, tana son labarai sosai, kallonta a tv baya wuce sauraron news ko kuma wani program da ake gabatarwa me amfani, shi yasa Dad yake cewa idan aka cire Emanuel to duk tafi sauran wayewa a gidan, ranar taji daɗi sosai kam.
Granny ta ƙaraso ta zauna itama a ɗayar kujerar, suka ci gaba da sauraran news ɗin tare.
“azumin yau akwai wahala kam”. Granny ɗin ta faɗa tana hamma da alamar gajiyawa tare da ita da kuma sautin maganar tata.
Azuminsu ta ɗauka na ƙarfe shida na safe zuwa shida na yamma, ta ɗauke shi ne musamman saboda Dad daya ce tayi masa adu’a akan wani al’amari dake neman jagula lissafinsa, tayi masa adu’a Allah ya saita masa kan komai, dalilin daya sa ta fara azumin tun ayau.
“kema Granny kin san kina fama da ulcer me ya kaiki ɗaukan wani azumi, gashi sai yanzu ma 12 tayi”. “azumin Dad ɗinku ne ai”. “umm Jesus ya amsa”. Mairon ta faɗa tana kai ayabar da ta ɓare bakinta. baccin daya fara ɗibanta ne yasa ta miƙe, “Granny bari na kwanta a ɗakinki, bana son hawa sama. idan Thomas yazo a taso ni, Dad yace ya fara koya min mota, so nake mu fara a yau saboda zuwa bikin Abigail ina so ace nima na bada gudun mawa wurin kai friends party”.
“shi Dad ɗin yace a fara koya miki driving? ina ce yace ne sai kinyi candy?…wayar ma fa ya baki itane dan ta dinga ɗebe miki kewa ba wai dan kin isa riƙewa ba…kuma shine saboda samun guri har kike ikirarin wani fara driving yanzu salon ki daina maida hankali akan karatunki”.
ta ɗan doki ƙafa a ƙasa tace,”Ohh Granny cikas, karki ɓata min budget mana. ke dai ba ruwanki ido naki kawai, ai kema kin san wace ni, ina son karatu sosai dan haka babu wani abu da zai ɗauke min hankali akansa”. Granny ɗin na dubanta tace,”to naji zaki koya yanzu, amma kike fita da ita kam ba yanzu ba sai after kinyi candy, Yayyanki ma duk haka aka masu, bare ke da kike mace”. wannan maganar ta Granny yasa ta wuce ɗakinta ta fasa zuwa na Granny cikin fushi.
around 2:00pm Emanuel ya dawo gidan, saboda PTA meeting da za’ai a makarantarsu Gift, dan haka Dad yace ya dawo ya wakilce shi ba zai sami zuwa ba. sanda ya shigo gidan Mairo na ɗakinta dan haka bata san da dawowarsa ba, shima kuma har yay lunch bai nemeta ba a zatonsa ko bacci take kamar yanda Granny ta shaida masa, nan kuwa tana ɗaki tana aikin karatun data saba babu dare babu rana, Obi har tsokanarta yake da Mangopark da kansa.
har zai shiga ɗakinsa a sanda ya hayo saman yaje ya kwanta dan huce gajiya, sai yaji ba zai iya bacci a yanzu ba tare daya ga Gift ba, wata guda kenan rabonsa da sanyata a idonsa a zahiri, kuma wannan idanun nasa irin nata masu kama da bacci suna kewar ganinta, haka zuciyar dake tunaninta a kowacce daƙiƙa tana kewarta, ata vedio call kawai yake ganinta, kuma shi wannan baya gamsar shi, yayi kewarta sose da rigimarta, kuma dawowar nan tasa ma yasan sai sunyi rigimar, dan yana batun komawarsu asibiti ne, tunda likita ya sanar da shi idan har ta kai watanni shida tunaninta bai dawo ba to su koma a ƙara bincike, to gashi harma ana neman shiga wata na bakwai, ba wai dan zuciyarsa naso zai aiwatar da hakan ba, bama shi kaɗai ba har Dad…sai dan basu da yanda zasu yi ne, domin ayanzu Duniya ta ɗora ido akan ƴar da ba’a san shi da ita ba tsawon shekaru 33 da aurensa, babu wanda yasan da ita da kuma tarihinta, sai a yanzu da tauraruwarta ta haska a duniyar, dalilin da yasa Duniyar ta fara qalubantarsa akanta.
parlonta ya shiga sai yaga bata nan, dan haka ya dawo ya murɗa handle ɗin bedroom ɗinta, fitowarta daga wanka kenan tana tsaye gaban mirrow tana goge jiki da ƙaramin towel ɗin dake hannunta, ya kafeta da ido yana kallonta daga sama har ƙasa, kallon daya haddasa tasirin jin wani abu ajikinsa. Shi mamakin cikar girmanta yake a yanzu, dan ba a haka ya sameta ba, lokacin ƴar siririya ce firit, breast ɗinta ma ko cika basu da shi, amma a yanzu ka kalleta saika kuma kallonta, ba’a irin surarta ne lafiyayyan namiji ke ɗora idonsa ya ɗauke ba, ta samu cikar diri da komai, samun ingantaccen abinci, hutu da jin daɗi da kwanciyar hankali yasa komai na halittarta ya sauya.
a zatonta ko Obi ne ya shigo saboda haka ba tare data juyo ba ta jefa tambayar,”what my brother need?”. yay murmushi ya ƙarasowa ciki, yay tattaki zuwa inda take ya rungumeta, babu wanda ya taɓa mata haka so a tsorace ta buɗe baki zata saka ihu yay saurin saka hannu ya rufe bakin.
haɓarsa akan wuyanta yace,”Beb its me”. jin maganarsa yasa ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya, sannan ta ɗauke hannunsa dake kan cikinta, ta gyara ɗaurin towel ɗin daya kunce yake neman faɗuwa, ta fuskanto shi tana kallonsa da shagwaɓewa tace,”ka bani tsoro”. ya bawa kumatunta light kiss sannan yace,”am so sorry”. ya faɗa ɗumin iskar bakinsa na sauka a saman breast ɗinta da suke a cike suka yo sama. hakan ya haddasa jin wata iriyar kasala ajikinta me tattare da wani irin yanayi, yanayin data saba jinsa a lokuta da dama, yanayin da tun bata gane masa ba har ta gane masa a matakin data ke kai a yanzu, na samun gogewar karatunsa daga wurin ƙawaye.
tun ɗaukewar last two period nata ta fara jin wanzuwar abun, taji tana so ta fitar da abunda ke ƙunshe a mararta, ta hanyar ɗanɗanar wannan daɗin data ji su Sarah suna faɗa. ta daki ƙafafu a ƙasa da sakin tsaki alamar ƙorafi, Emanuel ya ƙara matso da ita ya rungumeta a jikinsa tsam, gogayyar da aka samu tsakanin ƙirjinsa da albarkatun nata ƙirjin sai ya haddasa masa ɗarsuwar wani abu ajikinsa, saboda haka ya lumshe ido a yayin da yake ɗora haɓarsa saman gashin kanta yana shafa gadon bayanta.
“menene ya taɓa min Beb?”. ya faɗa da sauyawar sautin muryarsa. tana cikin matsala ne a yanzu amma shi ba zai gane ba, ba zai fahimci wannan ƙamshin turaren nasa yana jefata cikin wani yanayi na daban ba, Yayanta ne shi dan haka bai kamata take jin abunda take ji a game da shi ba, amma ta rasa me yasa? me yasa akansa ne shi ɗaya tal? wani ƙwayan mutum da addininsu ya haramta mu’amalar da take so ta kasance a tsakaninsu?.
hawaye kawai taji na sakko mata, domin ta samu sauƙin raɗaɗin abunda take ji ta kewaye shi ta matse tsam ajikinsa, bashi kaɗai ba da mazantakarsa ta motsa ajikinsa, hatta ita saida taji motsawarta anata jikin.
a hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta sake shi, amma har yanzu bata bar jin wannan baƙon yanayin ba dake zuwar mata lokaci zuwa lokaci, yake kuma neman cakar da ita, ta janye daga jikinsa tana duban idanunsa da suka kafe breast ɗinta da kallo, kallon irin yanda ƙirjinta ke hurowa sama yana sauka, da ƙasƙantun idanunsa ya figo hannunta ta dawo gab da shi, ya sunkuyo da fuskarsa yana laluben laɓɓanta da yake matuƙar buƙatar tsotsa a yanzu.
hakan ba komai bane a wurinsu, dan haka tayi dariya tana buɗe bakinta kamar yanda taga ya buƙaci hakan, kissing nata yake passionatlly har sanda yaji ya gamsu da hakan tukunna ya ƙyaleta, suka kalli juna suna sakin murmushi.
“zancewa Dad kana son mace a kusa da kai, ai dama Granny ta faɗa”. ta faɗa da sigar zolaya. baice da ita komai ba ya juya ya fice a ɗakin, domin idan yaci gaba da tsayuwa tare da ita wannan sirrin zai iya fallasuwa, komai kuma ya iya faruwa, dan tabbas wanzuwar abinda zuciyarsa ke ƙissima masa sai ya faru.
Da yamma suna zaune dukansu anan main parlo suka ji maganar Mom akansu, babu zato ba tsammani dan babu wanda yasan da dawowarta, ba gaban Emanuel kaɗai ba, hatta Obi saida gabansa ya faɗi, yasan Mom, yasan Mom sarai da abunda zata aikata, a yau wani ikon ubangiji ne kawai zaisa Mairo ta ƙara kwana a gidan.
ita kuwa shigowar tata ma sam bata lura da Mairo ba, tana ta amsa sannu da zuwa daga bakin ƴaƴanta da kuma sirikarta, da ƴar me aikin data zo karɓar jakar hannunta.
Mairo kam ko kallon inda take bata yi ba, balle dawowarta ta dameta, haushin Mom ɗin take ji tun a ranar da Granny ta shaida mata ba ita ta haifeta ba, Mom tata ta rasu tun tana jaririya. ta ritsa Granny da tambayar ne sanda ta kasa danne damuwar dake ranta na nuna halin ko in kula da Mom ɗin keyi akanta kamar ba ƴarta ba, sai dai taga kowa na waya da Mom amma banda ita, kuma ko ta yo waya zata tambayi kowa banda ita, sannan ko da aka bata waya numbar Mom ɗin ta fara kira amma sai tace ma ta ai tayi ɓatan number, ita bata haifi wata ƴa mace ba balle ƴa me suna Gift.
wannan maganar yasa ta ɗorawa kanta ayar tambaya in har wannan alamun da suke bayyane da kuma furucin da Mom ɗin tayi mata to tabbas akwai wani ɓoyayyan abu, ta san dai Dad shine mahaifinta, to ita ina tata Uwar?. sakkowar data yi babu shiri daga sama kenan ta sami Granny da tambayar ina tata Mahaifiyar, Granny kanta tayi mamakin tambayar dan alokacin tsayawa tayi kawai tana binta da ido, kuma Mairon bata bata damar yi mata wata tambayar ba ta fashe mata da kuka akan ta sanar mata ina tata Mom ɗin, dan Mom ɗinsu Joseph ta shaida mata ba itace Mamanta ba, dalilin daya sa Granny tayi mata ƙarya kenan da cewar Mamanta ta rasu sanda ta haifeta, kuma Mom ɗinsu Joseph ita Ƴaƴanta kawai take so, kamar bata yarda da zancen Granny ɗin ba dan taga alamun rashin gaskiyar maganar ɓaro-ɓaro a tare da ita, to amma sanda Dad ya dawo ya tabbatar mata da hakan dole ta yarda, ranar kuwa tayi kuka kamar zata shiɗe, kuma data tambayi hoto sai suka bata hoton Cousin Sister ɗin Dad da Granny ta riƙeta ta mutu shekaru uku kenan.
sam batayi niyyar mata sannu da zuwa ba dan a ƙullace take da ita, to amma haɗa idon da suka yi da Emanuel yasa taci wata daraja ta ɗanta, sai data ɗauke kai gefe tukunna tace, “welcome back Mom”. kuma a sannane Madam Gloria ta juyo a sukwane daga ɗaukar hanyar stairs da take ƙoƙarin yi, sabuwar murya ce taji, muryar da bata taɓa ji ba balle kuma zamanta a gidan, saboda haka ta shiga bin kan kujerar da kallo har sanda ta sauke ganinta akan Mairo.
sai ta tsaya da bawa Buky jakarta tace,”what are my eyes seeing?, what is this thing?”. ta faɗa tana nuna Mairon da hannu kamar wadda taga abin amai, kamin kowa yace mata wani abu ta ƙara da cewa,”heyy who are you?, me ya kawoki gidana?, zaman me kike min a parlo?”. duk a cikin saurin murya ta jefa mata tambayoyin, kuma duk a lokaci ɗaya ta maida kallonta gasu Emanuel cikin shouting tace,”kuna ji ina tambaya kunyi shiru da bakinku anan kaman na kwaɗi”.
Joseph yace da ita,”tafiyarki da kwana biyu tazo gidan nan”. da ƙifƙiftawar idanu dan son ƙara tabbatarwa ganinta da kuma abunda ɗanta ke faɗa ta buɗi baki tace. “you mean all these while that am not around tana gidan nan?”. “yes Mom”.
“to me take yi?, ina da ƴan aiki wadatattu nasan bata da wani space da zata karɓa, so zaman me take yi?, ina tambayanne ga dukanku kunyi shiru sai Joseph ke bani amsa”. tayi maganar da dukansu a tsawace.
“wai sabuwar daughter ce a gidan nan”. ya ƙara amsa mata. ita dai Granny tana jinta, tayi shiru ne kawai har sanda zata gama kumfar bakin sannan ta faɗi abunda idan ta faɗe shi ya zauna.
amsar Joseph ɗince tasa ta jefar da jakarta saboda gigita, da sassarafa me kama da gudu ta ƙarasa gaban Mairo ta kamo hannunta ta miƙar tsaye, ta kai hannu idonta tana faɗin,”kin wane kafeni da wannan ƙwalaƙwalan idanunki zaki cinyeni, to kurwana yafi ƙarfinki…this house is for only me and my childrens, so kinga hanya bi ki koma inda kika fito”. ta faɗa tana nuna mata ƙofa.
Mairo ta ƙwace hannunta, itama tana cije fuska tace,”nida gidan ubana ace na fita, to babu inda zani…kawai saboda Mamana bata raye sai ace za’a tsangwameni, daɗin abin my Dad loves me, and he can do anything akaina. so kibi a hankali, ke matarsa ce, ni kuma ƴarsa ce, akwai tazarar matsayi me nisa a tsakninmu. ke zai iya rabuwa dake, ni kuma ƴarsa ce da ba zai taɓa rabuwa dani akanki ba, saboda…”. sauran maganarta ta katse a sanda taji saukar mari a fuskarta, Mom ɗince ta kifeta da shi, kamin ta ɗago gaba ɗaya Emanuel ya ƙara kwasheta da wani marin,”she is my Mom ki iya bakinki akanta, zan iya zuba miki ido akan komai amma banda ita…dama ko Mom bata tambaya ba nasaka araina cewar duk ranar data dawo zaki san matsayinki a gidan nan, uzuri ɗaya zan miki na rashin sanin komai amma da sai kin gane baki da wayo akan abinda kiks aikata”. ya faɗa yana huci akanta.
Mom ta kama hannunta tana janta, dai-dai lokacin da Dad ya sako kai parlourn. Sakin baki da hanci yayi yana kallon yanda Mom ke janta ita kuma tana turjewa.
“Gloria mene hakan?, wai ke me yasa sam baki san baƙo ba, ba kya kallo ita ɗin yarinya ce, kuma mara lafiya”. ta dube shi tana yatsine fuska tace,”baƙuwa! yarinya! mara lafiya!…baƙuwar ce zata zauna a gidana a rufe min saboda munafurci?, ko kuma yarinya ce zata kalleni ta faɗa min cewar nan gidan ubanta ne sai dai ni na fita ba ita ba?, mara lafiyar ce ke tsaye da ƙafafunta haka har tana yunƙurin karawa dani?…to what ever dai zamanta a gidan nan yau ya ƙare, in har kuma ba kana so na tabbatar da zarginka da zuciyata ta fara a yanzu ba”. ta faɗa tana sake figo Mairo dake ta son ƙwacewa amma ƙarfin ba ɗaya bane.
Dad ya dakatar da ita acikin tsawa, “wai ke wace iriyar macece mara tausayi, an faɗa miki bata da lafiya she miss her tought, idan kin kwantar da hankalinki tana zaune damu ne zuwa ranar da zata sami lafiya akaita wurin iyayenta, ki tsaya a fahimtar dake abu amma kin tsaya kina hargagin banza”. a fusace tace da shi,”wane irin alaƙa ne tsakaninka da ita da ka ɗora alhakin kulawa da lafiyarta akanka?…Major ka faɗa min gaskiya tun ban aika da ita lahira ba, aina ka samota da kake cewa da Yarana sister ɗinsu ce, ko hakan na nufin kaci amana ne?”. ƙarashen maganartata ya fito da sautin karaya da kuma tsantsar tashin hankali acikinsa gami da fargabar jin amsarsa, Dad cike da takaici yace da ita,”ke kin san ni ba irin wannan mazan bane, kin san da cewar ni me kare mutunci kaina ne…kuma har kullum ina faɗa miki ba sai kana da alaƙa da mutum kake taimaka masa ba, balle ɗa wanda yake na kowa, ke uwa ce kuma irin uwar dake tsananin ƙaunar ƴaƴanta, ki kimanta aranki inda ace ƴarki ce a irin situation ɗin da take ciki ya zakiji a sanda wani ke wulaƙantata?, to ni na ɗauketa matsayin ƴata tun a ranar data shigo rayuwarmu, saboda haka zata ci gaba da zama acikin gidan nan har zuwa ranar samun sauƙinta…gida nawa ne bana kowa ba, nike da ikonsa”.
Gloria ta saki wani murmushi me ciwo,”kaga Major, just go streight to the point kace min kaci amanata ka munafurceni ka samar da wata ƴar a waje, ai dama you have said, kana haihuwa har yanzu dan haka zaka haifi ƴa mace ko min daren daɗewa”. sai kuma ta ƙara fusata acikin ƙarajin murya tace,”saboda naƙi baka haɗin kai shine ka fita waje kaje ka auri wata?”. Dad ya tsinka mata mari rai a ɓace yace,”you know me well ni ba sakaran namiji bane da zan tsaya jin surutan banzanki akaina ba, ga ɗanki shine sanadin zuwanta gidan nan, sai ki tambaye shi a inda ya samota”. Ya faɗa rai ɓace yana barin wajen bayan ya nanata,”Gift ba zata bar gidan nan a yanzu ba, saɓa maganata zai haifar da babbar matsala tsakaninmu dake”.
Madam Gloria ta juya to dubi Emanuel daya sunne kai a ƙasa yana murza yatsu tace da shi,”dama nan police station ne?”. yay saurin girgiza mata kai alamar a’a. tana ƙara matsowa kusa da shi ta kuma cewa,”nan gidan ophanage ne?”. nan ma yace a’a. “So i din’t get you well, mene alaƙanka da ita daka maida ita ƴar gidan nan?”. “Mom bata da lafiya ne kuma nine silar ciwonta”. “Ohh yaushe ka zama likita banda labari?, you are just telling me ka bigeta kuma kaine sila, and so?, daka bigeta shegiya ce ita da ta rasa iyayen da zasu kula da lafiyarta?, shashasha kana 32years amma baka haɗa hankalinka ba, to mace shaiɗaniya ce, kana kallonta haka saita jefa ka a ruwan zafi ta wuce ta barka aciki, mumu kawai”. ta ƙarasa zancen tana dungure masa kai, sannan ta juya ta koma kan Mairo, ɓacin rai fiye dana ɗazu tace,”yanzu tunda kin gane ba gidan ubanki bane sai ki fita, ki warke acan waje amma ba’a gidana ba…idan kuma kinƙi ji to tabbas zanyi reporting naki to police nace kin maƙalewa ɗana da mijina, su nasan zasuyi mana tsakani”. bata jira wani Abu ba tasa duka hannu biyu ta watsa ta waje, ita kuwa ba komai ya haddasa suman tsayen da tayi ba sai furucin data ji anayi akan ita ba ƴar gidan bace.
masifar Madam Gloria da jarabarta ya hana kowa motsi, faɗa kuwa kamar zata zane Emanuel, Granny ɗinma bangajeta tayi ta wuce tana faɗin,”kowa ma munafiki ne a gidan nan, anci amanata kuma ba zan yafe ba…Joseph biyo ni ɗaki”. sai kuma ta nuna Emanuel da Obi,”kar wanda ya kusantoni acikinku, tunda daku zaa haɗa baki a cuce ni…har kun saka na fara tantamar anya ku jina ne?”.
Mairo dai tunda aka wurgota waje ta zube a entrance na shiga parlon tana kuka, kukanta bana korar da akayi mata bane, kukan bala’in da take ciki a tata duniyar ne. idan har da gaske nan ba gidansu bane to ina ne nasu gidan?, kuma Dad ba mahaifinta bane?, Brother ba Yayanta bane?, to su wane iyayenta?, and me ya sameta da har ta kasa tuna komai bacin rayuwar da tayi a lagos zuwa yanzu.
tarin tambayoyin dake haskawa kenan acikin kanta, sai dai bata san ta inda zata samu amsarsu ba, saboda haka ta kuma cusa kai a tsakanin ƙafafunta ta fashe da sabon kuka mai tsuma zuciya, tunda har Dad ya faɗi haka to tabbas hakanne dan haka dole ta bar kokoton alaƙarsu da ita.
Emanuel ya fito yazo gabanta ya tsuguna, ya dafata da faɗin,”Gift kiyi haƙuri duk ni naja miki”. bata ɗago ba, domin ɗagowarta a halin yanzu zai iya janyowa tayi masa abun da zai haddasa tashin hankali fiye da wanda take ciki ayanzu, domin shine silar wanzuwar komai dake faruwa a duniyarta.
wayarsa ce tayi ƙara, yasa hannu ya ɗaukota daga aljihu. “Hello Sectery ka ƙaraso ne?”. daga can ɓangaren Amadu yace da shi,”eh na ƙaraso, ina bakin layin gidan”. “oak ka tsaya ga Obi nan zuwa ku taho tare”.
ko mintuna goma ba’a ɗiba ba saiga Amadu da Obi sun shigo gidan, yazo ne a bisa wasu muhimman takardu da ake buƙatar Emanuel daya saka hannu akai, ba’a kawo takardun ba kuma sai a jiya bayan tahowarsa daga can, saboda haka ne kawai ya biya masa kuɗin jirgi yace ya kawo masa dan bai saka lissafin dawowarsa cikin wannan satin ba.
“me aka mata take kuka haka?”. Amadu ya tambayi Obi a sanda suka ƙaraso wajen, Emanuel ya ɗago ya dube shi, kamar ba zasu ce da shi komai ba kowa yay masa shiru, to amma rashin samun mafitar da suke nema dole yasa su sanar da shi ɗin, duk da yasan in ya sanar da Md zai sama masa mafita to amma kamin wannan sai ya gama dagula masa lissafi shi kuma bai shirya ɗaukan hakan ba.
saboda haka ya sauke numfashi yana duban Amadu, bai ɓoye masa komai ba ya sanar da shi duk abunda ya faru har zuwa halin da ake ciki yanzu.
“karka damu ranka ya daɗe, ko mai zai warware cikin sauƙi insha’Allahu, amma abunda baka so ɗin dole shi za’ai, hotonta zamu ɗora a media a shigar da cigiyar iyayenta ko kuma wanda ya santa”.
Obi ya jijjiga kai tabbacin ya gamsu da shawararsa, Emanuel kuwa ido kawai ya zubawa Mairo dake duƙe tana ruzgar kukan da har mutyarta ta fara dashewa. Amadu ya duƙa a gabanta, da muryar nan tasa data ƙware a iya fitar da tausasan lafuza yace da ita, “ƙanwata ki daina kuka kinji, ki ɗago ni zan kaiki gidanku, nasan su waye mahaifanki…amma sai kin daina kuka fa tukunna”. tana jin hakan ta ɗago da sauri tana goge hawaye, gefe na zuciyarta na ƙissima irin matakin da zata ɗauka kamin barinta cikin rayuwarsu mutanen gidan nan.
duk da canjawar da tayi hakan bai hana shi ganeta ba, bai san ya zai kwatanta yanda yaji ba a sanda idanuwansa suka yi tozali da ita, abu ɗaya kawai ya sani ya razana, razana kuma bata tsoro ba, irin razanar data haifar da ɗimbin tashin hankali acikin ƙwayar idonsa da zuciyarsa.
Mairo! Mairo dai ƙanwarsu, yau itace tayi rayuwar watanni bakwai acikin ƙedarun arna, kuma ta rayu a tsawon watanni bakwai ɗin bata kallon gabas, ya yasar da maɗaukakin al’ajabin dake lulluɓe da shi yace, “Mairo ce!”. ya faɗa da ƙarfin sauti, ya sauke nauyayyan numfashi ya miƙa hannu ya taɓota dan tabbatar da gezon da yake tunanin idanuwansa nayi. tabbas Mairo ce, Mairo ƙanwarsa, Maironsu da suka fitar da rai da sake ganinta, ashe tana raye kuma a kusa da su.
ya ɗaga hannu sama yay hamdala ga ubangiji, tare da ƙara matsowa kusa da ita zai kamo hannunta tai saurin ja da baya, idonsa cike ƙwallar tausayinta yace,”me yasa kika baro mu?, kin san tashin hankalin da kika saka mu aciki kuwa?, me yasa kika mana haka?, ko kin san tun ranar da kika barmu har zuwa wannan ranar Gwaggo bata ƙara takawa da ƙafafunta ba, watanni bakwai kenan tana zubar da hawayen rashinki, Mairo me yasa?, me yasa?”. ya faɗa kamar zaiyi kukan farin cikin ganin nata.
ita dai kallonsa kawai take, binsa take da ido ba dan ta gane shi ba, ko kuma wai ta san shi, mamakinta ɗaya ne daya nuna yasanta ita kuma bata sansa ba, waye shi? daga ina yake? mece alaƙarsu da yake waɗan nan zantukan da suka saɓa masaniyarta?.
Obi da suke tsaye mamaki ya cikasu yace da Amadu,”kana nufin ƙanwarka da ta ɓace ne kwanaki?”. jijjiga masa kai yayi tabbacin haka, sannan ya umarci Mairo dan ta tashi su tafi amma taƙi tace sam ita ba zata bishi ba, shima zaije ne ya biya buƙatarsa da ita ya tozartata.
daya fusata dai ya kai hannu zai kai mata duka, ƙarar bindiga daga suka jiyo daga cikin gida yasa duka suka zabura, banda Mairo da tai saurin saka hannu ta toshe kunnuwa tare da rumtse ido gam jikinta na kyarma, kuma acikin muryar kuka, muryar dake naɗe da firgici da tashin hankali, muryar da babu ƙwarewar hausa acikinta ta fita da ƙarfi wajen furta,”Gwaggo”. kuma a lokaci ɗaya duhun dake cikin ƙwayar idanunta ya hasko mata sanda suke gudun fitowa daga cikin dajin nan dan su samu su tsira da ransu daga wurin kidnapers, har lokacin da fito bakin titi tana rangaji, daga nan kuma ba zata ƙara tuna komai daya faru ba, abu ɗaya da zata tuna sun baro cikin dajin da mutane da yawa, kuma abu na ƙarshe data san kunnuwanta sunji shine harbin bindigar daya dinga tashi kamin kuɓutarsu daga hannunsu.