NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Ethiopia, 2:00pm.
zaune suke shida Abdurrshim suna cin abincin rana, Kabir abincin kawai yake ci amma hankalinsa ba awajen yake ba, yana can wata duniyar ta tunanin ƙalubalen da zai fuskanta akan tabbatuwar mafarkinsa, Aure! aurensa da Mairo.
ya furzar da iska daga bakinsa yana maida kansa jikin kujera, idanuwansa a lumshe ƙirjinsa na motsawa. “wai dan Allah ba zaka faɗa min abunda ke faruwa bane Kabir?, a ranar yau kaɗai na fuskanci akwai damuwa a tare da kai kuma kake ɓoye min…duk da ban sani ba amma zan iya cewa akwai alaƙar damuwarka da masarautar Qatar da muka baro, dan Allah ka faɗa min ko zan iya baka tawa gudunmawar wajen ganin komai ya warware maka”. idanun Kabir har yanzu a rufe suke bai buɗe ba, yace da shi,”karka damu Abdurrahim, damuwar ƴar kaɗan ce wanda ba zan iya maganceta ba ko wani ya magance min, Allah yana sane da lamarina, shi zai shiga cikin lamarin ya warware min matsalar”. rufe bakinsa yay daidai da shigowar kira a wayarsa, Kulu ce dan haka yay saurin ɗagawa, muryata ta fito a hankali da ce masa, “ya ake ciki ka sami ganin Hussainar?”. nauyayyan numfashin dake ƙunshe a zuciyarsa ya saukar, sannan ya fesar da numfashin daga bakinsa. “komai ya kammalu, fallasuwar ɓoyayyen sirrin kawai ya rage…ina jin wani nauyi a ƙasan zuciyata kamar an ɗora min babban dutse, ki saka min muryar Maryam ko zan iya samun ƙarfin jikina ya dawo daidai”. daga cikin banɗakin da Kulu ta ke ta dafe goshi a ranta ta furta Ya Salam, yanzu ya zata yi, ɗazu ma fa ƙarya tayi masa, ita dai kota sanar masa da gaskiyar ɓatan Mairo ne ta huta da kwane-kwane?, ɗayan ɓarin zuciyarta ya kwaɓeta akan faɗa masa hakan, kuma tana cikin neman mafitar ƙaryar da zata sake yi masa Yagana ta shigo gidan, maganarta kuma ta karaɗe cikin gidan, Kulu ta sauke wata ajiyr zuciya da yin hamdala ga ubangijinta, sannan ta maida wayar ta kara a kunnenta tana ce masa,”Kabir anya kuwa karaɗin Yagana zai barka ka ji muryarta?, ka kalla tunda ta shigo gidan ta ke sababi ta hana kowa magantuwa, ga shi nan ma fita zasu yi da Mairon”. bai san ya akai ya tsinci guntun murmushi a fuskarsa ba, murmushin daya haifar da shan jinin jikin Kulu dan tasan bai yarda da maganar tata ba, amma sai taji yace,”naga ranar da Yagana zata shigo gidan nan bata yi sababi ba, shikenan ki nutsu kamin wani ya shigo banɗakin zan miki bayanin komai”.
gida biyu ta raba hankalinta, kaso ɗaya a tare da Kabiru kaso ɗaya a tare da Gwaggo wacca ke can ɗaki likita ke kanta jikinta yay tsanani.
“kin san me ya faru?”.yay mata tambayar a sanda ya miƙe daga living room ya wuce zuwa bedroom, Abdrrahim ya bi bayansa da ido da son gano wani abun. Kulu tace,”a’a saika faɗa”. yace,”ban taɓa ganin abinda ya tsoratani ba irin kamanninku ke da ƴar’uwarki, na tsorata ainun a lokacin dana shiga office ɗinta na sameta, tsoro fa bana wasa ba, saboda a tsammanina ma kece, Allah da iko yake, bayan kamarku hatta muryarku ma iri ɗaya ce”. tai murmushin daya sauka a iya leɓenta,”da kamanninmu da muryarmu iri ɗaya ne, amma kuma idan ka ganmu tare zaka iya banbance mu”. “tayaya kenan?, to kin san Allah sanda nai tozali da ita nai zaton ko wasa kike da hankalina, ƙila kina so ki haɗa min gadar zare ne, sanda na kiraki banyi magana ba ai dan na tabbatar da bake ɗin bace yasa na kira, gaskiya ga duk wanda yake da saurin firgita idan ya ganku tare to zai iya suma”. tai gajeriyar dariya da cewa,”ka jira ka ganmu a taren tukunna, da kanka zaka zaƙuloni ba tare da rikicewar lissafi ba, akwai abinda ya banbantamu”.
yace,”to ai shikenan…kamar yanda kika sani nayi duk abinda kika ce, na shiga masarautar Al-Harar harma na sami ganawa da Mai Martaba, sannan naje Qatar ma amma shi ban sami shiga cikin masarrautar taku ba saboda tsaron dake cikinta, amma naga Al-Hassan kuma naga Umm da idanuna, sannan na sami labarin Abi daga wurin limamin wani masallaci.
daka duka waɗannan ɓangarorin an sami saɓanin tunaninki akansu, daga ta kowanne ɓangare cike suke da kewarki da kuma cigiyarki da basu daina ba har yanzu, liman Shaik Albani ya shaida min ko a sallar asubahin yau sai da Me Martaba yay hawaye akan rashinki, yana adu’a iyakar adu’a akan idan har kina raye a duniya to ubangiji ya bayyana musu ke a duk inda kike…Umm ma akan yawan kukan rashinki ta kamu da matsalar ciwon ido…duk abunda ya riga ya faru y riga ya faru, burinsu a yanzu na ki dawo garesu ne, fatan iyayenki ki dawo garesu suna raye ba bayan ta Allah ta kasance ba…kin san me?”.
tace,”a’a saika faɗa”. ta faɗa tana goge hawayen dake sakko mata.
“Hussainarki tana da kirki sosai, naje ma ta a matsayin ɗalibi me neman taimako har ta saka min hannu a takardar dana kai ma ta, kuma tun shigata office ɗinta har fitowata tana kirana ne da Ɗan’uwana. tace min tayi min taimakon dan Allah ne, amma tana buƙatar adu’a daga gareni akan Allah ya bayyana ƴar’uwarta da ta ɓata, na kuma yi ma ta alƙawarin hakan, itama kuma ina miki albishir ɗin tana nan cikin ƙoshin lafiya sai dai kallo ɗaya zaka yiwa fuskarta kasan tana ɗauke da wata damuwa a ƙasan ranta, bakinta kuma yana faɗin idan har ta mutu baku gana ba, ba zata yafewa kanta ba”.
tana tsayar da kukanta tace,”tayi aure ne?”. “a’a batayi ba, kuma a dalilin hakan tana ta fuskantar ƙalubale daga wurin mutane…ita kuma ta yiwa kanta alƙawaarin ba zata yi aure ba sai sanda kika dawo”.
sai kuma ya ƙyalƙyale da dariyar dake nuna yana cikin nishaɗi, tace da shi,”ni ina hawaye kai kana dariya, mene abin dariyar acikin wannan yanayin Kabir?”. “kiyi haƙuri, da akace ne ana cigiyar within ƙasashen larabawan nan shine abin ya ban dariya, nace to dama taya za’ai a ganki alhalin kina ƙasar bichi ƙunshe a wannan gidan ƙasar tamu ba um ba umum sai kallo da ido”.
ita kanta bata san lokacin da dariya ta suɓuce ma ta ba, daga haka kuma tai masa godiya sosai sannan suka yi sallama da cewar idan Yagana ta tafi zata ƙara kiransa.
sauke wayarta daga kunne ta jingina da ƙyauren banɗakin, tana son komawa cikin ahalinta, amma kuma tana tsoro saboda Hassanarta, Hassana zata rusa ma ta duk wani shiri da sukayi idan ta koma, allura ce zata tono garma idan ta koma, saboda Hassana Adamant(kaifi ɗaya) ce, idan ta kafe a abu babu wani mahaluƙi da yake sauya ra’ayinta ko da iyayenta ne, ta inda suka sami banbanci a hali kenan, shi yasa idan Mairo ta kafe a abu takan kalleta tayi murmushi aranta tace Babarki kika yo.

CardioCare Specialty Hospital, Abuja, Nigeria, A wannan ranar.
“to kinji dukkan abinda ya faru dake tun daga ranar da kika ɓata”. Amadu ya kai ƙarshen zancen da wannan maganar, tun harbin bindigar nan da suka jiyo ta cikin gida, wanda Mom tai silarsa akan fusata Dad da tayi na korar Mairo, tsananin ɓacin ransa da zuciya ke sa shi aiwatar da komai acikin fushi ya ɗauki bindiga zai harbeta, Granny tai saurin ɗaga hannunsa sama ya harbi saman, amma da babu abunda zai hana shi alburushe Mom.
kuma Joseph ya fito a rikice yana sanarwa dasu Obi Mom tace in har Mairo bata bar gidan ba, to ko Dad bai koreta ba ta rantse da jesus saita kashe kanta. dalilin daya sa suka rikice kenan Obi ya roƙi Amadu akan ya ɗau Mairo su bar gidan da hanzari, dan Mom tana faɗar abinda zata aiwatar ne ba abinda ke tsayawa a iyakar fatar bakinta ba, gwara Dad idan ya fusata ne yake aikata koma menene, amma da zarar Granny ta shiga lamarin shikenan.
Obi da duk ya rikice yace da Amadu,”Friend ka ɗauketa ku tafi ko ba dan komai ba sai dan lafiyarta, kaga yanzu tawo cikin tunaninta, wannan rikicin zai iya haifar ma ta da wata matsalar, ko ta koma gidan jiya ko kuma wani abu makamancin hakan ya faru”.
kuma ita a lokacinma duk a ruɗe ta ke, kuka take kawai tana kiran sunan Gwaggo da Baba da Ya Kabiru, dan tun sanda ta ɗago kai taga ƙaton compound ɗin fayau sai shuken fulawowi ta ko’ina ta daɗa hargitsewa, dan tunaninta har yanzu bata bar wannan ƙaton jejin da suke ciki ba, kuma ko da taga Amadu sunkuye a gabanta saita fashe da sabon kuka ta rungume shi, sai kuma ta fara complain ɗin ciwon da kanta keyi ma ta kamar zai rabe gida biyu. dalilin da yasa suka zarto da ita asibiti kenan, kuma likitan daya dubata ya tabbatar musu da cewar,”ehh ta dawo cikin ainihin tunaninta, amma duk da haka ba wai zata manta duka abubuwan da suka faru da ita a sanda take cikin ciwon bane, a’a wasu abubuwan suna nan zaune akanta, kamar yaren da bakinta ya kama, karatu da kuma giftawar wasu tsirarrun al’amuran da ta sakasu a ranta sosai”. abu ɗaya ya saka Amadu jin daɗi shine karatun da tayi, yana adu’ar Allah yasa karta manta da shi.
kuma tun a lokacin da aka cire ma ta drip, lokacin dake nuna ta gama dawowa gaba ɗaya cikin tunaninta, tambayar da ta farayi masa itace,”Ya Amadu ya akai ka tsinto ni?, hanyar dajin fa da aka kaimu babu kowa sai mu kaɗai da muke rayuwa, har sanda na fito titi ma na rasa wanda zai taimaka min”. ya sauke numfashi yay mata nuni da Emanuel dake tsaye shima hannayensa sarƙe a ƙirjinsa, zuciyarsa cike fal da tarin abubuwa mabanbanta, yace ma ta. “bani na tsintoki ba, wannan shine ya tsinto ki”. ta ɗago ido ta dubi Emanuel, wani irin kallo ta ke masa mai kama da kamar ta san fuskarsa sai dai ba zata iya tunawa ba. “shine uban gidana, shi ya bigeki da mota ya ɗaukeki ya kawoki asibiti…”. daga nan kuma ya shiga zayyane ma ta labarin duk abinda ya faru har zuwa gaɓar da ake kai yanzu, to amma da mamakinsa tun daga lokacin daya soma maganar har sanda ya kai aya idanunta ƙyar suke akan yatsun ƙafarta, hancinta da bakinta na fitar da hucin numfashi na zafi da raɗaɗin dake tashi daga zuciyarta, babu wani motsi da ta ke kamar wadda ta suma.
Amadu ya zago ta gabanta yaja kujera ya zauna, dubanta yake da irin yacce hawaye ke sintiri saman fuskarta, ya kamo hannunta ya riƙe tare da tambayarta,”mene kuma na kukan?, ki godewa Allah daya kawoni a gaɓar da ta dace, da banzo ba me kike tunanin zai ƙara faruwa?”.
ta ɗago da ido ta kalle shi, acikin birkitacciyar hausarta irinta yare tace da shi,”kace har yanzu Gwaggona bata da lafiya?”. ya gyaɗa ma ta kai,”tun a ranar da kika bar gida, sai dai ayau nasan ciwonta yazo ƙarshe, yau zata warke a sanda idanuwanta sukai tozali dake”.
ta saki wani murmushi me ciwo, a ƙasan ranta tana adu’ar samun sauƙi ga Geaggonta, amma hawayen nan masu zafi basu bar sintiri a saman fuskarta ba, hawayen jin ɗaci da zafi akan addinin kiristancin da ta rayu acikinsa tsawon watanni bakwai, tsawon wata bakwai bata sallah! tsawon wata bakwai aka katangeta da bautawa ubangijinta daya halicceta akan tufarkin Annabi Muhammadu(S.A.W), aka cusa ma ta wata aƙidar ƙazamin addini har tai rayuwa acikinsa, wannan shine abinda yafi damunta a halin da take ciki, shi yafi ma ta ciwo, zata so ace keta haddinta Kidnappers ɗin nan sukai akan ƙazamin addinin da ta shiga, zata so ace ta mutu ne akan rayuwa da tayi tare da ƙedararrun arna.
zuciyarta tayi wani irin duka, ta lumshe idanuwanta ta mayar da kanta ga jikin gadon tare da rufe ido, tasa hannu ta dafe saitin da ƙahon zuciyarta, dan jin zuciyarta take kamar zata faso ƙirjin nata ta fito saboda irin masifeffen harbawa da ta ke, wata iriyar masifa ce ke azalzalarta akan azzaluman kafiran da suka raineta.
wucewar wasu daƙiƙu ta buɗe ido a zafafe ta zubesu akan Emanuel dake ma ta kallon sabuwar halitta, ta tsare shi da idanu kamar wacce ke kallon tv, ayanda take kallonsa gaba ɗaya masifa ce ke ƙara cin ranta, ita ba taimakonta yayi ba cutarta yayi, cutarwa mafi muni, da yasan irin abinda zuciyarta ke ayyana mata akansa da baici gaba da tsayuwa anan wurin ba, domin ji take kamar ta kashe shi, da niyyar taimakonta yayi da gaske ba zai biye son azzalumar zuciyarsa da babu ƙaunar Annabi Muhammadu acikinta ba ya shigar da ita cikin addininsu, da cigiyarta zai saka a duniya, duk da ita ba kowa bace, kuma ubanta ba kowan kowa bane, amma hakan ba zaisa a rasa wanda ya santa ba.
shi kuma wannan kallon da ta ke masa sai yayi tunanin ko tana so tayi magana da shine, dan duk maganar da sukayi ita da Amadu bai fuskanci me suke cewa ba tunda da hausa ne suke maganar. dan haka yayo tattaki zuwa gabanta ya tsaya tare da buɗe baki yay ma ta sannu, a zafafe ta diro da ƙafafunta ƙasa ta daki ƙirjinsa da duka hannayenta biyu ta damƙi kwalar rigarsa.
acikin harshen turanci da tasan maganganunta zasu shiga kunnensa da kyau, acikin muryar da ta gaji da kuka take faɗin, “ka cuceni, ƙaton arne ka cuceni, kasa na rayu acikin ƙazanta, kasa na shiga addinin da ba a cikinsa ubangijina ya halicceni ba, kasa na bautawa wanda ba shine Allah ba, mugu azzalumi wallahi ba zan yafe maka ba…na tabbata sanda ka tsintoni baka ga nayi maka da wadda ta tashi cikin ƙedararrun arna irinka ba, amma saboda zuciyarka azzaluma ce, saita ta ke gaskiyar da idanuwanka suke gani ɓaro ɓaro ka cusani cikin ƙazamin addininku…dama Gwaggona tace ku ɗin azzalumai ne macuta masu bin son zuciyarsu su cuci musulmi…ka riga ka gama dani, tsakanina da kai sai dai Allah ya isa, danni ba kuyi min taimakon komai ba, ba kuyi min gatan komai ba, kuma insha’Allahu ba zaka taɓa samun rabon hasken musulunci ba bare Allah ya yafe maka, haka zaka mutu kana mushiriki makomarka ta zama wutar jahannama”. ta ƙarashe zancen tana ɗauke shi da zazzafan marin da ya kai fuskarsa ƙasa, “idan baka bar gabana na daina ganinka ba zan iya ɗaukan komai na rotsa maka, zan iya kaika lahira, zuciyata na faɗa min na kasheka ne, na kasheka Emanuel”.
shi kuwa tsantsar mamaki da al’ajabi ne ya hanashi wani motsi sai binta da ido da yake, sam yanda ta ke kalamanta akansa ba haka suke ba, dai-dai da ƙwayar zarra ba shi da niyyar cutar da wani a rayuwarsa balle kuma ya cutar da wadda shine silar shigarta halin manta duniyarta ta baya, yes! yasan yayi laifi da bai shigar da cigiyarta ba. dukan tunaninsa kuma yay ket ya katse sanda yaga ta rarumo wani ƙarfe tayo kansa da shi yay saurin kauce ma ta. “ka daina kallona a matsayin waccen matsiyacin sunan da kuka raɗa min na Gift, ka kalle ni a Mairo, Mairo ƴar gidan Malam Adamu Me Faske, Mairon da zata aiwatar da kowanne irin haɗari saboda kishin addininta”. tayi maganar a sanda ta kai hannu ta maƙuri wuyansa, tana kuma ƙoƙarin soka masa ƙarfen aciki, lokacin kuma Amadu ya dawo daga fitar da yayi waje dan karɓo wasu magunguna da aka rubuta ma ta.
ya ƙaraso ciki da sauri yasa hannu yay cilli da ita gefe sannan ya wanketa da mari, ya hauta da faɗa yana balbaleta da rashin dacewar abinda ta ke yunƙurin aikatawa.
“mahaukaciyr banza da wofi, muna farinciki da ganinki ashe ke da dabbanci kika dawo, to dan ubanki ki kashe shi ɗin kiga idan ke za’a barki da rai, ki gani idan shi zai wuce wuta”.
ta wani ja doguwar ajiyar zuciya ta yarfar da hannun Amadu dake riƙe da ita, a zafafe ta shiga magana,”ya za’ai ya dakeni kuma kace ba zanyi kuka ba…tsawon fa watanni bakwai kenan ya rabani da bautawa mahaliccina, ya dulmiyar da tsaftacceiyar duniyata zuwa tasu ƙazama, to na rantse Ya Amadu idan baka matsa ka bani wuri ba zan haɗa hukuncin harda kai”.
ya santa, ya san wace Mairo sarai, irin Gwaggonta ce masu zafin rai, masu aiwatar da abunda suka faɗa, masu tsayawa akan ra’ayinsu, shi kansa ya sani sanyin Mairo ya soma ne daga lokacin da Baba yay ma ta wata nasiha me ratsa jiki, kuma kowa yay mamakin wannan sauyawar zafin ran nata, zafin kan da da idan tanayi zaka rantse kana hasko irin turirin dake fita ta saman kanta, kuma zaka ji zafinsa ajikinka idan ta fitar da iskar baki.
dan haka ya dubi Emanuel yace da shi,”Sir kayi haƙuri ka tafi kawai, mun gode sosai da taimakon da kayi ma ta”. Emanuel ya juya ya fice, bai fita dan jin tsoron abinda zata aikata ba, ya fita ne saboda yanda yake jin kansa a irin yanayin da ta ke jin kanta, shima kansa tafasa yake, numfashinsa kuma na fitar da turirin zafi, zai aiwatar da abinda yafi nata muni, idan ta sha anono to shima wannan zafin ran yasha shi a nono na tsawon shekara uku ciff, kuma zafin ran da zai rantse yaci uwar nata, to sa’a ɗaya kawai taci, shima da shine wasu suka yi sanadin shigarsa addinin musulunci zaiyi fiye da hakan dan shima me kishin addininsa ne, kuma taci daraja, darajar Amadu.
sai da Amadu ya tabbatar zuwa yanzu Emanuel ya bar asibitin sannan ya dubi Mairo dake duƙe a ƙasa tana rusa uban kuka, ya doka ma ta uwar tsawa akan ta miƙe su tafi, amma ko gezau ba tayi ba, wannan tsoron nasa da shakkarsa ta manta dasu, ji ta ke sama ta ke shi ayau.
ganin zata masa taurin kai kuma tana neman tara musu jama’a ya fizgi hannunta ya miƙar ɗa ita tsaye, yajata suka fita tana aikin turjiya da ihun kuka ita akan ya barta, ya ƙyaleta ta fara zuwa taci uban waɗancan kafiran, amma inaa bai saketa ba har suka shiga mota zuwa tasha, anan ma taso zille masa dan kwasa tayi da gudu zata koma shima yabi bayan nata a guje yasa jamaa suka riƙo masa ita, ya kuma ɓalli reshen bishiya yace,”wallahi ko ki nutsu ko kuma nayi miki dukan mutuwa a wurin nan”. ba dan furucinsa yasa ta haƙura ba, ta haƙura ne saboda Gwaggonta kawai, zuciyarta yanzu Gwaggonta ta ke da muradin gani, amma ko ba yanzu ba sai kafiran da suka riƙeta sun gane bala’i suka ɗaukarwa kansu.
kuma tunda suka shigo motar babu wanda yay magana acikinsu har suka iso cikin kano, ai anan ma saita kuma birkicewa Amadu, da suka zo wucewa ta wajen wani store ta kalli kanta a cikin glass ɗin store ɗin.
“Ya Amadu bana son kaina na tsani kaina, gaba ɗaya ƙyamatar kaina nake, dan Allah kafin mu tafi ka kaini wurin da za’a sabule min wannan dattin dana kwaso a gidansu, ko da kuwa da wuta, ni ba zan koma gida da dattin fatar arna ba, Gwaggona ma ba zata so ganina a haka ba”.
kuma shima sai a yanzu ya kula da Sarƙar cross ɗin dake wuyanta, dan haka ya fizgota gabansa ya cire sarƙar ya jefar, ita kuma ya matse bakinta yay ma ta nuni da kan titi yace,”kinga wannan ƙaton titin, to ni me iya jefaki kansa ne mota tabi ta kanki dan ubanki, cikin ƴaƴa goma sha biyar da an rasaki ba komai bane”.
tasan zai iya aikatawar tunda ya faɗa, saboda haka ta nutsu ta saita kanta.
kuma a sanda suka shigo garin bichi, layin gidansu, ƙofar gidansu, gidan Malam Adamu me faskare, idanuwansu suka yi tozali da abunda ya ɗaure kawunan kowannensu, dandazon mutanen da tunaninsu ya kasa sarrafa kansa. lokaci ɗaya kuma suka saki hannun juna, jikinsu ya saki, ƙafafunsu suka gaza ci gaba da ɗaukansu, a sanda suka hango Baba ya fito daga cikin gida yana goge hawaye, kuka yake, tabbas idanunsa kuka suke, suka ɗago kai a tare suka dubi junansu. Mairo tasa hannu ta dafe kanta da taji yana neman rabewa, ta rufe idanuwanta ta buɗe, sannan cikin kakkaryewar harafi tace,”Ya Amadu waɗancan mutanen fa?, kuma me Baba yakewa Kuka?”. kan ya buɗa baki yace wani abu zuwan Adawiyya wajen ya sanar dasu abunda yake faruwa.
sun fito daga layin gidan Yagana ta hango Amadu, sai dai bata taɓa tsammanin Mairo bace a tare da shi har sai da ta zo dab dasu, nan ma kuma sai datai da gaske sannan ta iya shaida Mairon da kamar sake halittarta akai, ta ke taji wani abu y tokare ma ta a ƙahon zuci, kuma da ƙyar da iya haɗiye wani ƙullutun abu daya tsaya a maƙogoronta, sannan ta ƙaraso gabansu, ta fasa ihun da ta ke jin kamar tayi hauka saboda baƙin cikin ganin sauyawar da Mairo tayi da kuma dawowarta, amma sai tayi pretending ihun akan tashin hankalin da gidansu ke ciki, ta faɗa jikin Mairo ta rungumeta tana fashewa da wani makirin kuka, “Mairo! Mairo ina kika tafi baki dawo ba sai a sanda Gwaggo ta mutu, Mairo Gwaggo ta rasu tana ta kiran sunanki, Mairo Gwaggo ta mutu ta tafi ta barmu”.
take wata tsawa me tsaida sauti ta buga acikin kan Mairo, zuciyarta ta motsa, ta ture Adawiyya daga jikinta ta ɗauketa da mari. “idan kika kuma cewa Gwaggona ta mutu saina illataki, zan manta da cewar ubanmu ɗaya nayi miki abinda ni kaina banyi zatonsa ba”. sai dai kuma me?, kafin ta kai ga ɗaga ƙafa ta taka dan ƙarasawa gida maganar Lukman dake tabbatarwa da Amadu mutuwar Gwaggo tai sanadiyar zubewarta a wajen.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button