SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Dan Allah ina barar adu’a daga bakunanku masu albarka akan samun nasara da sa’a akan jarabawata, da kuma wani al’amari dana saka a gaba…na gode muku, Allah ya amsa mana baki ɗaya.
Comment&Share.
SIRRIN ƁOYE
By Oum Ramadhan✍????
28)
“innaillahi wa’inna ilaihi raji’un”. gaba ɗayansu suka faɗa suna duƙawa gabanta, Amadu na ɗago da kanta daya daki wani dutse a wurin gefen goshinta ya fashe, kuma tuni ta suma. gaba ɗaya kuma sai rabin dandazon jama’ar dake wurin zaman makomin suka yo wurin anata salati, Baba daya ƙaraso wurin cikin saurin da za’a iya kirashi da gudu ya shiga raɓawa ta jama’ar da sukayi ma ta rumfa harya samu ya kutso ciki zuwa gaban Mairo dake shimfiɗe a ƙasa. me zaiyi?, gaba ɗaya ya rasa taƙamemen me yake ji acikin zuciyarsa, abu biyu ya haɗe masa a lokaci ɗaya baƙin ciki da farin ciki, sai dai baƙin cikin ya rinjayi farin cikin, dan ya tabbata yay rashin da ba zai taɓa maye gurbinsa ba a rayuwa a dai auren mace kamar Suwaiba tun bayan Hajara.
yay ƙarfin halin tattaro sauran kuzarin da ya rage masa yasa hannu ya ɗagota zuwa jikinsa. “ai ba tsayawa zaku yi ba, Lukuman ma za ka samo ruwa”. yay maganar yana me duban Lukman ɗin, sannan ya dubi Amadu yace da shi,”aina ka samota?”. “Baba maganar bata yanzu bace magana ce me tsayi”. ya bashi amsar zuciyarsa na wani irin harbi.
Malam yay ajiyar zuciya kawai, ya karɓi ruwan dake hannun Lukman wanda ya kawo a yanzu ya yayyafa ma ta a fuska, duk da haka bata farka ba saida ya shafa ma ta ruwan a fuska da wuyanta kamin nan taja wani dogon numfashi. wannan dogon numfashin da ta ja dake nuni da cewar tana raye shi ya wanzar da ƙullutun baƙin ciki a zuciyar Adawiyya, wadda ke duƙe daga gefen Mairo tana aikin kukan munafurci tun a sanda Mairon ta zube, dan ihun da taita zabgawa ne ma yajawo hankalin mutane kansu, ihun da a wurinta yake na farinciki da dukkan fatanta na duniya ace mutuwa ce itama tayi awon gaba da ita, don gani ta ke idan har ita da Mairo zasu ci gaba da rayuwa to zatayi rayuwa tagayyararriya me cike da ƙunci, dan ta tabbata saita rasa duk wata walwalarta, saboda tunda tai ido huɗu da canjin da halittar Mairo ta samu taji duniyarta tayi duhu cike da feshin baƙin ciki tamkar aman dalma. har zuciyarta ke ingizata akan ta caka ma ta kibiyar da idanuwanta suka gani a ƙasa, ta yanda babu mai lura da hakan, kuma alokacin da ta ke ƙoƙarin aikata hakan sai Allah ya kawo Mu’azzam, wanda shine yaje ya sanarwa da Baba cewar Mairo ce ta dawo kuma ta faɗi ta suma.
zuciyar Adawiyya ta wani tarwatse in to atoms, gaba ɗaya ji ta ke duniyarta ta gama rikicewa, tayi wani duhu tayi baƙiƙƙirin, ba haka taso ba, sam ba haka taso ba, taso ace tabi bayan uwarta, dan a yanzu abinda ta ke ji game da Mairo yafi ƙarfin ta kira shi da haushi ko kishi, baƙin ciki ne tsurarsa da kuma zallar ƙiyayya.
amma ko a yanzu ma gani ta ke kamar fatanta zai cika, tunda nunfashi kawai ta ke babu motsi kuma idanuwa a rufe, bin ƙirjin Mairon ta ke da ido ta yanda yake nuna fitar numfashinta da sauri-sauri, acikin tunaninta lissafin yanda zata ga bayan Mairo da gaske take, alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta ba zata taɓa bari Mairo tafi ta ba, ta tabbata yanda tafita komai a yanzu to samari zasu daina tururuwar da suke akanta su koma kan Mairon, Suhail ɗin data gama mallake zuciyarsa! Masarautar data ƙwallafa ran shigarta a matsayin sirika!…tai saurin girgiza kai bata shirya rasa abubuwan da ta ƙwallafa rai akai ba, kaf tsarinta babu lissafin cewa Mairo zata fita da koma menene a duniyar nan, ita zata kasance a sama Mairo kuma a ƙasa a koda yaushe. sai gashi tun ba’aje ko’ina ba lissafin nata na neman tarwatsewa, yabi ta dai-dai da lissafin boko?, ta rumtse ido tare da cizon leɓenta na ƙasa.
“Baba nah”. muryar Mairo da ta fito cikin shashsheƙar kuka ta gifta acikin tunaninta, ta baro daga waccen duniyar gaibun da ta shiga ta dawo duniyar zahiri dake gabanta.
“Alhamdulillah, Sannu Mairo”. Baba yace dani yana mai dubana da idanun tausayawa, na lura so yake ya goge ƙwallar dake neman sakko mishi acikin dabara amma ya kasa saboda tsaresa da idon da nayi, kuma yay ƙasa da kansa kamin ya yunƙura ya miƙe yana me cewa da Adawiyya, “ki kama hannunta ku shiga cikin gida”. kafin na ƙara cewa wani abu ya bar wurin, Adawiyya kuma ta rungumeni da sautin kukan dake ƙara karyar da zuciyata, ni dai na zama kamar gunki, bana ko motsi illa bin bayan Baba da nayi da ido har ya ƙarasa cikin rumfar da ake zama, ta tsakankanin mutanen dake miƙo masa hannu suna musabaha na ƙara shaida ehh da gaske rayuwarta ta sauya daga ranar yau, don yanda bakinsa ke fitar da amsar kalmomin ta’aziyyar ko na nesa da shi can zai fahimci me bakinsa ke furtawa balle kuma ni da nake kusa-kusa da shi, don haka a lokacin kuma na gama yarda da gaske na rasa Gwaggona, mutuwar nan dai dake raba tsakanin ɗa da mahaifa ta rabani da uwata da duk duniyar nan bani da tamkarta.
tunanina da hangena ya tafi akan taya zan shiga gidan na tarar da cewar yanzu fa babu rayuwar Gwaggona aciki?, taya zan zauna acikinsa babu mahaifiyata?, taya zan ci gaba da rayuwa acikinsa babu wannan jarumar macen da idan ta ɗaga hannunta ga ubangiji kamin ta roƙawa kanta ta roƙa min?, taya zan rayu acikinsa babu wannan gwarzuwar macen da ta sadaukar da lokacinta, jininta, jikinta, ƙarfinta, zuciyarta tun daga ranar dana zo duniyar har girmana?, taya zan rayu acikin gidan babu Mahaifiyata abar ƙaunata da bata iya kai abinci bakinta sai ina cikin gidan?, taya zan iya rayuwa acikin gidan babu wannan jajirtacciyar macen da bata samun nutsuwa a duk sanda bana cikin gidan?, taya zan rayu acikin gidanmu babu Gwaggona, babu Gwaggona dake hana idanuwanta bacci daga sanda na fara rashin lafiya har zuwa samun sauƙina?, take naji ƙwaƙwalwata na karanto min kalmar innalillahi wa’inna ilaihi raji’un acikin raina.
maganar Adawiyya da ke fita cikin matsanancin sheshsheƙar kuka ta gifto ta cikin tunanina.
“ki tashi mu shiga Mairo…har yanzu ba’a kai Gwaggo ba amma nasan an gama shiryata, ki tashi muje kuyi sallama da ita, tunda ciwonta ya tsananta ke ta ke ta kira har numfashinta ya tsaya”. kukan daya ci ƙarfinta kuma yasa tai shiru, kamin ta ƙanƙameni sose cikin sautin daya fi wancan shiga jikina tace,”Mairo baki ga komai bane, har yanzu baki shiga ko’ina a tashin hankali balle har ki nutse acikinsa, akan gaɓa kawai kike, tashin hankali naga lokacin da kika ɗora idonki akan gawar Gwaggo da babu ƙafa ɗaya”. nayi wata zaburar dana kasa sarrafa kaina a wajen miƙewa da jin wannan furucin nata, kuma kamar na jefa ma ta tambayar dake raina ne sai naji ta bani amsa,”ciwonta da yay tsanani sai da aka yanke ma ta ƙafa saboda kullum kuka ta ke yi da ƙafar, kuma shikenan daga wannan lokacin, daga wannan lokacin muka rasata Mairo, wayyo Allahnmu”…
me zan bari ta ƙarasa faɗa min?, babu! ai na tashi na ƙarasa cikin gidan shi yafi min, inje idanuwana su gasgata min abinda har yanzu nake tantama akansa, dan ba zan gama yarda da cewar Gwaggona ta mutu ba sai naga gawarta da idona.
tsoro nake ji da gaske, tsoro nake ji na shiga gida naga gawar Gwaggona, tsoro nake ji na shiga gidanmu naga babu wannan fuskar dake tarbata da murmushi a duk sanda na fita waje na dawo. jan ƙafafuna nake da suka min nauyi na kasa ɗagasu, jina nake tamkar wadda ta faɗo daga wata sama me nisa. kuma tunda na shigo gida ko’ina ajikina sai ya shiga rawa, yayinda nake bin ɗimbin mutanen dake cike a tsakar gidanmu, wasu na kuka wasu kuma sun zabga tagumi cikin jimami, kuma idona bai ƙara sauka akan kowa ba sai Basma dake tsakiyar yayyun Gwaggo suna lallashinta da ba ta haƙuri, ita kuma ihu kawai ta ke tana kukan dake tsuma zuciyar duk wani me saurarensa.
“Basma ga Mairo ta dawo”. Adawiyya ce ke faɗa ma ta hakan, don haka bata san ta yanda akai ta fizge daga hannun Anty Saude ba tayo kaina da gudu. “Yaya”. kuma sunan nawa kawai ta iya faɗa tayi shiru muka rungume juna, ita kuka ta ke da sauti, ni kuma kukan nake babu sauti sai tsiyayar ruwan hawaye kawai. “Basma da gaske ne rayuwarmu ta gama rushewa gaba ɗaya? da gaske ne mun zama marayu?”. muryata ta fito cikin rishin kuka da kakkaryewar kowanne harafi. ta gyaɗa min kai tana cewa,”Yaya shikenan bamu da uwa, Gwaggonmu ta mutu ta barmu Yaya. dan Allah kije kice ma ta ta tashi ke nasan zata ji maganarki, tun ɗazu inata cewa ta tashi zaki dawo amma taƙi jina, bata tausayawa maraicin da zamu shiga idan babu ita, wannan kulawar tata Yaya, wannan adu’artata, wannan soyayyartata Yaya duk mun rasa su”.
na janyeta daga jikina na kama hannunta mu kai ɗakin Gwaggonmu, da dukan fatana na duniya zanje naga akasin abunda nake ta ji tun ɗazu, muna zuwa ƙofar ɗakin naji ƙafafuna sun riƙe saboda kukan da nake ji na tashi acikin ɗakin, Hajiya Laraba wadda take kaka a wurin Yayar Babar Gwaggo ita ke faɗin,”haɗuwarmu ta ƙarshe da ita ranar da taje gidan Inuwa take shaida masa Mairo na fama da ciwon ido kuma halin da suke ciki sai du’ai, ƙila ma har aiki sai anyi ma ta”.
saina yaye labulen ɗakin a hankali ina kallonsu, gaba ɗaya cikin ɗakin ƴan’uwan Gwaggona ne sai Inna Amarya dake can gefe tana nata kuka, idanuwana kuma suka sauka akan gawar Gwaggo dake a tsakiya an lulluɓeta da wani sabon zanen atamfarta da Wansu yay musu kyauta da sallah ta ɓoye tace insha’Allahu sai bikina zata ɗinka tunda atamfar me tsada ce. wata tsohuwa ƙawar Yagana ta yaye zanen daga fuskarta tana cewa,”Allah sarki kinga har yanzu annurin fuskarta bai gushe ba”. Yagana ta rushe da kuka, ni kuma idanuwana suka kasa karɓar Gwaggona da suke gani a matsayin gawa, gangar jikina kuma nema take taƙi amsar mutuwar Gwaggo gaskiya ce. jiri ya kwasheni nayi tangal tangal zan faɗi akai saurin riƙoni, Kulu ce wadda sam ban lura da zamanta ba a bakin ƙofar ɗakin, idanuwanta da farar fatar nan tata sunyi jawur wadda zasu tabbatar maka da taci kuka ne ta ƙoshi, kuma tana cikin yinsa. ta kama ni ta shigar dani ɗakin na duƙe a gaban gawar da har yanzu nake ganin kamar mafarki nake, a yanzu kam idanuwana sun ƙafe, hawayena ya bushe, na kai hannu na yaye duka zanen dake rufe ajikin Gwaggona, anan na tabbatar da abinda Adawiyya ke faɗa min, ƙwarai ƙafar Gwaggona ta dama ta zama rabi, domin tun daga gwiwarta zuwa ƙasa babu, jikina kuma sai ya mutu gaba ɗaya, Baba Lami ta matso ta ɓanɓare zanen da nake damƙe da shi a hannu ta mayar ta rufe Gwaggona, Yaya Jummai(ƙanwar Gwaggo) kuma tazo ta janyemu gefe ni da Kulu, wacce ke riƙe da ɗaya hannuna tai masa wata damƙa, sai dai inaa, fizgewa nayi daga hannun nata naja ɗuwawu na koma gaban gawar na kamo hannun Gwaggona na riƙe gam, abu ɗaya kawai na sani shine babu wani mahaluƙi daya isa ya fitar da gawar Gwaggona daga gidan nan, cikin ɗakin nan, babu shi, babu kuma wanda ya isa ya raba hannuna da nata, sai dai idan ita mutuwar ce zata zo ta ɗaukeni nima.
ina jiyo Baba Lami na cewa da Kulu,”kiyi haƙuri ki daina kuka, domin ba shi da wani amfani, mutuwa ce Suwaiba tayi kuma kukan ba zai dawo da ita ba, illa ma ya ƙara dagula zuciya da raunana imaninta…dan haka mu bawa zuciyoyi haƙuri mu bita da adu’a ita tafi buƙata a halin yanzu”.
ta ke zuciyata ta kuma karyewa, sai kuma murya Baba Mujibu ta shiga kunnena a sanda ya ɗaga labule yana faɗin, “Amadu shigo da makarar”. jinsu kawai nake, babu wanda idona ke kansa, so kawai nake naga me ƙarfin halin da zai iya zuwa ya ɗauki Gwaggona ya sakata acikin makarar har yace zai ɗauka. na rantsewa kaina sai dai idan nima numfashin na daina sannan ne za’a iya fita da gawarta daga ɗakin nan, amma ba ina raye ba kuma a kusa da ita.
Baba ya shigo ya tsuguna a gefen kanta, da wata iriyar raunanniyar murya yake faɗin,”Suwaiba na yafe miki, Allah ya yafe miki, halinki na gari ya biki, yasa mutuwa ta zama hutu a gareki, haƙiƙa ke ƴar aljannah ce Suwaiba”. sai kuma yay shiru yasa tafukansa ya rufe fuskarsa saboda kukan daya ci ƙarfinsa. kuma a sannan na kurma wata ƙara da ta cika gidan gaba ɗaya, ba komai ya haddasa hakan ba sai ganin Baba Mujibu da Ya Amadu sun kama Gwaggona sun sakata acikin makara sun ɗauka zasu fita da ita, ban san taya akai suka cire hannuna daga nata ba. inaji ina gani suka fice min da uwata daga ɗakin, suna ikirarin wai zasu kaita wani gidan wanda yake shine gidanta na gaskiya. nai wani kukan kura na warce daga riƙon da Anty Jummai tai min nabi bayansu da gudu na danƙo bayan rigar Baba Mujibu, kuka nake ina roƙonsa da dasashshiyar muryata akan,”dan girman Allah Baba Mujibu karka rabani da Gwaggona, ka tausaya min ku ajiye min ita, na yarda na amince ta mutu amma dan darajar Allah ku bar min gawarta na dinga gani ina rage raɗaɗin zafin rasata”. gunjin kukana dana Basma dana Kulu ne kawai ke tashi acikin gidan, Inna Zulai ce kawai tayi ƙarfin halin iya zuwa ta janyeni sannan suka iya samun damar fita da gawarta. “Mairo ina sonki, a duk duniya bayan iyayena duk wani bawa ko wani abu da nake so to ya biyo bayanki, dan Allah ki rage zafin rai kinji, ki koyi haƙuri, ki zama me haƙuri da tawassali a rayuwarki, kuma a duk wani hali da zaki shiga na tsanani a rayuwarki ki riƙe Allah…saboda haka ki bar kuka dan Babanku ya siyawa Adawiyya da Sadiya kaya babu ke, tunda kika ga yayi haka bashi da kuɗinne, kiyi haƙuri kinji ko, zan ɗauki waccen kwallar tawa na siyar na cika da kuɗin gurina kema na siyo miki kayan da zaki fitar suna da su, kema ba za’a barki a baya ba, muddin ina raye Mairo ba zan taɓa bari ki koka akan wani abu ba, sai dai idan ta Allah ce ta kasance dani, ko kuma nayi iya fafutukar samu na rasa”. wannan maganar ta Gwaggo a can kwanakin baya ita ta haska a cikin kaina, kuma daga wannan kallon da nayiwa ƙofa naga shigowar Ya Aminu yana ajiye buta yana faɗin,”ehh har anyi ma ta sallah ma gasu can sun tafi”. daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai farkawa nayi na ganni a gadon asibiti.